← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 160

Sashe 102

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A maimakon yafahimceta saima d'auketa mari da yayi yana fad'in bata isa ba tagurb'ata masu jini da yaron da ba'asan asalinsa ba, tunda har aka fara jita jitar cewa shid'in bad'an halak bane to tabbas akwai qamshin gaskiya aciki, don haka dole ta yakicesa azuciyarta don bazaya tab'a barin ta auresa ba koda shikad'aine namijin daya rage aduniya dole tahaqura tarabu dashi, kasancewar yariga daya b'ata batool tun farko saboda soyayyar daya nuna mata fiye data sauran 'ya'yan da yake dasu yasa takasa saurararsa ballema har tafahimci abunda yake cewa tabar wajen aguje tana kuka, ta tabbata irin soyayyar da yake yimata ita zatasa ya sauko idan tayi hakan don baya qaunar b'acin ranta balle kukan ta gashi takafe kai da fata batacin komai sai kuka duk don yasauko daga dokin naqin daya hau. Amma sai taga abun yasha banban awannan karon don ko kad'an baibi takanta ba balle tayi tunanin zaibarta tayi abunda takeso kamar yanda yasaba mata akoda yaushe, mahaifiyarta kuwa hajia salmah da suke kira da hajia mama tayi lallashi har tagaji amma batool taqi saukowa kullum sai kuka, qaramar yarinyace da anriga ansabo mata rayuwarta cikin gata da sangartawa don tun tanada shekara biyar aduniya duk abunda tace tanaso ayi agidan shi akeyi, idan kuma tayi fushi taqi cin abinci shikad'aine ke zuwa ya lallasheta yabata abaki sannan taci kuma har tagirma haka take shiyasa duk girman mutum bata shakkar tsayawa agabansa tafad'i abunda keranta don yariga daya saba mata da hakan, inda kawai rayuwarta take da sauqi shine batayin fad'a ko wata rigima sai da dalili, bata son reni shiyasa batayar da tasa qarya acikin sha'aninta ba, takan girmama babbane idan ya got kansa amma daga lokacin daya bari yayi abunda zai jawo zubewar girmansa agareta to komai tsufansa zata iya tsayawa tayi masa tas akan gaskiyarta, wannan halayyar tata natab'awa hajia mama rai amma idan tayi magana sai mahaifin nata da take kira da Abba yace a qyaleta ai yarinyace, ita kuwa hajia mama babu abunda take tsoratarwa rayuwar 'yar tata kamar gidan wani zata ace tanada kafuwa da rashin d'agawa kowa qafa indai tana bisa gaskiyarta ita kuwa rayuwa ba haka take ba musamman ta gidan aure da kanaji kana gani da gaskiyarka za'a take maka ita kuma dole ka haqura, sai gashi yau tun ba'aje ko ina ba zata fara shan wahalarta a hannun wanda shine ya d'orata akan tarbiyar,

Da kuka hajia mama taje ta iskesa tafad'a masa halin da batool d'in ke ciki amma duk da yaji badad'i haka yaruntse idanuwa yace ta tafi tabashi waje, matuqar bazata haqura dayaron nan ba to saidai tamutu, hakan yasa takoma wajensu uncle h tasanar dasu halin da ake ciki,

Uncle hassan da kansa yaje qofar d'akin nata ya bubbuga had'e da kiran sunanta, lokacin tana kwance sai faman juye juye takeyi saboda yunwar data isheta, daqyar ta tashi taje tabud'e gambun tare da b'are baki tafad'a jikin uncle hassan tana kuka, da yake yanada sanyin hali ba kamar uncle Hussain ba ya d'agota yana sallallami yace da hajia mama.

Kingani ko hajia abunda muke fad'a masa akan yarinyar nan yakasa fahimta!, don ALLAH dubi yanda baqar sangarta da kafiya irinta yarinyar nan daya d'orata akai kenema ta illatata babu gaira balle dalili, meye amfanin wannan rayuwa haka?

Qara lafewa jikinsa tayi tana kuka saiga uncle Hussain shima yashigo, tsawa ya katsa mata had'e da cewa tanemi waje ta zauna, wani kukan tasake sawa da qarfi da yasa abban nata fitowa, yana ganin 'yan uwan nasa tare da ita yajuya zai koma uncle Hussain yace.

Ina kuma zakaje? Ai sai kaqaraso ka ida aikin naka tunda mun fiddo maka da ita, da sauri hajia mama taje ta d'auko abinci ta ajiye a tsakar falon uncle hassan yaja hannunta yaje da ita ya zaunar da ita gaban abincin.

Ganin yanda ta canza cikin kwana biyu ba yanda take son ganin taba yasa Abba d'an sassabtowa daga fushin da yayi ya matso kusa da ita, tana ganin haka tamiqe zatabar wajen yayi saurinsa hannu ya riqeta,

Batool yanzu saboda naqi amincewa ki jefa kanki cikin quncin rayuwa da yaron da baida asali kike nema ki illata kanki, yafad'a yana qare mata kallo yanda tad'an fad'a cikin kwanaki, juyawa tayi tana kallon uncle Hussain had'e da cewa, kaji ko uncle?, Fuskarta kamar zatayi kuka,tsabar takaici da bazai iya tsayawa yana kallon wannan kayan haushi ba yasa uncle hussain yayi tafiyarsa, haka hajia mama da uncle hassan suma bayansa sukabi suka ficewarsu suka barshi daga shi sai ita suyi yanda suke so...

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___74💎

Murmushi yayi tare da juyawa yana kallon batool data kasa tashi sannan yace, gimbiya kidaure kitashi, lalle ayau nafara hango gwagwarmayar da zakisha wajen tattala mani soyayyarki, kidaure komai za'ayi maki akaina kijure matuqar zuciyarki tayarda da cewa nid'in zan cika maki alqawarin dawowa agareki da kuma zamowa Abu sumayyarki da kike mafarki akaina, ni kuwa ina tabbatar maki da cewa zanja daga kuma nayi d'amarar yaqi da duk wani da zai shiga tsakanina dake,

Bubbuga saiti zuciyarsa yayi sannan yaci gaba da cewa, wannan zuciyar ta Abu sumayya takice ke kad'ai gimbiyata, zagi da aibantawa basu isa suhanata qaunarki ba, kisa aranki ina sonki, Ina sonki, Ina sonki kuma ina qaunarki fiye da tsammani, cike da wani irin farinciki tamiqe tsaye tana murmushi tare da dawowa gabansa tana kalonsa tace, da gaske kakeyi kana sona?, kana qaunata? Kamar yanda kafad'a?.

Sosai kuwa gimbiya, fiyema da kalaman da bakina suka fad'a, kisa aranki nid'in nakine kuma kema tawace komai tsanani komai wuya, ba gudu baja da baya kinji ko?.

Nayarda, na amince kai d'in zaka zame mani tamkar wata fitila da zata haskake duk wani duhu dake tare dani kuma zaka zamo ruwa da zasuyi maganin duk wata datti da zata demeni aduniya, maida kallonsa yayi ga hajia nafeesa data koma tamkar wani mutum mutimi tsaye agabansu bud'e da baki tana kallon batool data daddage tana zarowa masoyinta kalaman da zasu dad'asa ya yadda da tsantsar soyayar da takeyi masa d'ari bisa d'ari sannan yacewa batool, kinyi alqawari?

Nayi alqawari Abu sumay..., Bata qarasa ba sakamakon buge mata bakin da hajia nafeesa tayi had'e da jan hannunta tabar wajen da ita, shidai baice da ita uffan ba saima kallon batool d'insa da take faman ja yakeyi itama tajuyo tana kallonsa had'e da sakar masa wani sassanyar murmushi mai cike da tarin ma'anoni kala kala shima yana mayar mata har sukabar wajen,

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke had'e da cewa, coming home Abba, hakan d'ai zai bani damar mayar da duk wani martani ga waccan baiwar ALLAH,

Ai baka isa ba, domin duk wanda yasai rariya yasan zatayi zuba kuma ita halak ana barinta ko don kunya, kuma dama ai duk wanda yaqiji bayaqi gani ba, ummace kefad'ar haka da itama tun d'azu tafito da taji halshen hajia nafeesa tana koro kalamai marasa dad'in ji data tabbatar da cewa da jikan natane takeyi.

'Dan sosa qeyar kansa ya shigayi yana kallonta taqasan idanuwa ita saima yabata dariya, don gaba d'aya kamanninsa basu nuna yadamu da kalaman da hajia nafeesa tayi masa ba, mere baki tayi had'e da juyawa zatabar wajen tana fad'in, to ai shikenan duk tsuntsun da yajawo ruwa shi zasuci, yayi saurin cimmata had'e da d'ora kansa asaman kafad'arta yariqe hannunta yana cewa, kiyi haquri 'yar tsohuwa, ya zanyi da cutar data riga tashigeni kuma narasa magani,

Ai sai kayi indai Aishatu ce tana gefe iya karta dakai addu'a,

Yawwa kakata takaina, indai addu'arki natare dani nasan Babu abunda zai shiga gabana tunda tariqe gwaggona cikin amincewar ALLAH.

Sarkin salo, to ai saika cikani kuma ka d'agamun kafad'a kada angona ya shigo ya hangoka.

Eyyeee! lallai ummarnan karkisa kishina ya motsa yau aja daga tsakanina da shi, har kinada wani ango daya wuceni?.

Soqo tayi masa ga kai har zata sake kai mas na biyu yayi saurin d'auke kansa daga kafad'arta tare da sakin hannunta yabar wajen aguje yanufi sashen ammie yana dariya, tace ja'irin banza kawai sannan tawuce part d'inta.

Cike da sheshshekar shaqiyanci yashiga falon na ammie yafad'a kan kujera yana dafe qirjinsa, ammie dake zaune tana karatun qur'ani ta d'ago kai tana kallonsa bayan takai aya had'e da cewa.

Maigida lafiya?,

Ummace ke neman saka qwaqwalwata ababireshon saboda wani soqo data kaimun, shinefa zata qara nagudo wajenki don nasan ke tattalina kikeyi. Saida tayi murmushi had'e da rufe alqur'anin sannan tace, to halama kai mekayi mata ne?

Banyi mata komai ba, wai kawai don nace batada angon daya fini kuma sai naja daga da tsohon mijinnan nata shinefa take nema tasaka qwaqwalwata awaqi'a..

Ai kafin yarufe baki itama ammie ta d'aga hannu zata sakar masa wani soqon tana fad'in, to bari natayata nima tunda qashinka yagi daya girma shiyasa kake neman jan daga da gudan alhajin namu, da sauri yaruga yana cewa, kai ashe gudun gara nayo..saiga dady yashigo had'e da cewa, ai kuwa ka fad'awa zago, fad'amun meka aikatawa matan nawa suke nema yau sukarya munkai, ga hajia nafeesa can nabaro tun daga bakin gate najita tana fad'a da yarinyar nan da tazo wajenta, sai gashi dana shiga kuma takawomun qararka, yaqare maganar tare da azo hannunsa saman kafad'arsa suka dawo cikin falon,

Cike dajin kunya yazube qasa bayan ya zauna shikuma dady nakan kujera ya sunkuuar da kai tare da gaishesa ya amsa yana kallonsa yana dariyar abunda hajia nafeesa tace masa azuciya, wai takamashi zai b'ata mata 'yar uwa, to gaba d'aya nawa yaron yake kuma cikin gidan inane da wurin da hakan zata iya faruwa batare da angansa ba, ahankali yafurta ALLAH yakyauta yana sauke wata irin ajiyar zuciya, sannu da zuwa tayi masa tare da kallon little Nuraddeen tace, to katashi kugwada mana, sum sum yamiqe yafita dady yace dawo ka zauna.
Chapter 102 · 0% Book details