← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 160

Sashe 94

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Alhamdulillah malan, naji dad'in yanayin dana ganeka aciki, inafatar wannan qanwar dakace zaka samo mani tayimaka kyakkyawar tarba da kulawa kafin na iskoka, tsakanina dakai babu komai sai alkhairi idan ma kuma katab'a yimani wani abun nayafe maka duniya da lahira inafatar kaima baka tafi dani da komai acikin ranka ba kuma ina roqon ALLAH daya tsarowa rayuwarmu haka akan wannan bawa naka daka jiqansa da rahama, kagafarta masa ka amintar da rouhinsa." Rashida ta amsa da amin.

Tana gama fad'ar haka tagoge hawayen idanuwanta sannan tamiqe suka fito, ayanayin da tafito kad'ai idan ka kalleta zaka tabbatar da cewa tagamsu da yanda taga mijin nata kuma tana yimasa kyakkyawan zato..

_karku manta mutuwa wajibice ga duk wanda keraye, azahiri ma idan munyi tunani soyayyarmu ko kuma qiyayarmu ga wata rayuwa bazata hana idan lokacinsa yayi ba ALLAH yakarb'i abunsa balle littafi, dayawan lokuta ALLAH yafi karb'e mana mutanen kirki aduniya fiye da na banza, da son samune nafiso baffa Ali yamutu fiye da baba amma ayanayin labarin mutuwar baba kad'aice zata haifar da rabuwar da Nuraddeen yayi da mahaifinsa har ya girma kamar yanda kuka gani a farkon littafi, Amma matuqar yana raye dattakonsa bazai bari hakan tafaru ba, don haka kuyi haquri da yanda labarin yake plzzz, ALLAH YAJIQAN BABA DA RAHAMA_👏

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

_Masha ALLAH, a gaskiya zafafan comment d'inku akan yanayin da Nuraddeen keciki sun tafasa k'wak'walwata, da banyi niyar cewa komai ba but yazama dole nace wani abun wataqil hakan zaisa kud'an fahimceni, A iya sanina qarfin imanin mutum qarfin jarabawar da ALLAH zai yimasa😅alkawarin ALLAH ne cewa duk wanda yace yayi imani to dole za'a jarabcesa tako ina arayuwarsa don atabbatar da ingancin imaninsa, don haka kuyi haquri da halin da Nuraddeen ya tsinci kansa aciki, ba burina ku karanta littafin ku nishad'antu dashi kawai neba, a'a ina son kutsinci darussan dake cikine tare da fahimtarsu, karku manta alqalamin marubuci bayana ta'allaqa kawai bane akan nishad'antarwa da burgewa, dole yazamo ansamu ilmantarwa, fad'akarwa da kuma luraswa aciki, hakan shi zai bashi damar isar da saqon da ake son isarwa ya yanda yakamata, da fatar nima kun fahimceni yanda yakamata_🥰

Page___70💎

Haka rayuwar Nuraddeen taci gaba da kasancewa acan batare da mahaifinsa sun san komaiba, sukuma jami'an dake kulawa da lamurran karatunsu babu abunda basu sani ba, duk iya matakan daya kamata su d'aukar masa suna iya qoqarinsu amma hakan tafaskara, ganin yana karatunsa yanda yakamata d'abiarsa ce kawai yagagara gyarawa daga yanda take yanzu zuwa yanda take ada yasa suka qyalesa, a qa'ida tsarin karatun nasu shekara shida zasuyo acan sannan su kammala, amma bayan shekara uku zasu dawo gida hutun wata d'aya sannan sukoma su ida qarasa sauran shekaru uku.

Lokacin da suka shekara uku acan aka tashi dawowa hutu Nuraddeen kafewa yayi kai da fata shi babu inda zaije, Babu irin yanda ba'ayi dashi ba yace shi gaba d'aya baya buqatar hutun balle har yakoma qasarsa, kasancewar yanada matuqar qoqarin da tun daga d'aliban makarantar har zuwa malanta Babu wanda bai sanshi ba, don haka sai 'yan uwansa mazauna kano da sukazo tare sukaje suka sanar da wani malamin halin da ake ciki, koda yaje shima yayi masa magana irin amsar daya basu ya bashi, nan take malamin yaje ya sanar da shugabar makarantar da yake macece (Miss Florence Jackson) tasa aka kirawo matashi tayi masa magana, tayi iya juyin duniya akan yabi 'yan uwansa amma yaqi amincewa daga qarshe ma sai yafara riqe kai irin alamun maganar na neman saka mashi damuwa, don haka sai tace subarshi zatayi magana da jagororinsu na nan qasar zai zauna awajenta saboda su awajensu kowa nada 'yancin kansa yayi duk abunda yakeso, hakan kuwa akayi gaba d'aya d'alibban da sukaje tare dashi suka dawo gida cike da farinciki zasuga ahalinsu da iyalansu bayan tsawon shekaru uku da suka sharikke awaccan qasar.

Baffa nasamun labarin dawowarsu cike da farinciki ya sanar da baffa Usman, Kwana da yini sukayi suna jiran isowarsa gida amma shiru wannan dalilin yasa baffa ya isko baffa Usman har gida cike da damuwa ya sanar dashi cewa tunda sukaga bai iso gida ba to tabbas ba lafiya yakamata suje su tuntub'i manyannasu suji meke faruwa?,

Ba qaramin tashin hankali baffa yashiga ba lokacin da akayi masa bayanin abunda yafaru na cewa Nuraddeen yaqi amincewa yadawo wai har sai sun kammala karatun gaba d'aya nan da wasu shekaru uku masu zuwa, kusan fad'uwa zaune yayi daga tsayen da yake saida Baffa Usman yayi saurin riqosa, ba abunda kefita bakinsa inba.

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, qadarallahu wama sha'a fa'ala."

Tabbas jikinsa yanzu nabashi akwai abunda kefaruwa akan d'ansa wanda aka b'oye masa, Aikuwa daya matsa lallai sai ansanar dashi dalilin da yasa hakan zata faru sai suka sanar dashi gaskiyar halin da Nuraddeen keciki don bazasu iya cigaba da b'oye masa ba a matsayinsa na uba awurinsa kuma suka sanar dashi cewa yana cikin qoshin lafiya sannan kuma yana maida hankalinsa ga karatunsa sosai don haka yakwantar da hankalinsa.

Awannan ranar gaba d'aya guiwowin baffa saida suka sare had'e dayin sanyi kuma ya yadda cewa tabbas rayuwar mumini kullum cikin jarabta ta akeyi, idan yafita wannan jarabawar sai kuma wata takunno kai, yashiga kwararo addu'a ALLAH yabashi qwarin guiwar da zai rinjayi zuciyarsa har zuwa lokacin da ALLAH zai canye dukkanin jarabawowinsa.

Bayan sun dawo suna tsaye a qofar gida suna tattaunawa akan yanda zasu b'ullowa matsalar, baffa Usman nata rantsuwa cewa tabbas koma meye akwai abunda badaidai ba don yayi imanin bazai tab'a aikata abubuwan da akace ba, idanko har gaskiya ne to tabbas bayin kansa bane, Ashe duk abunda suka fad'a Inna ruqayya da zata fitowa tajisu don haka sai takoma cikin zaure ta lab'e tana saurarensu.

Tsabar farinciki da jin dad'in abunda kunnuwanta suka jiyo mata nassa taji wani irin sanyi azuciyarta kuma ta gamsu cewa tabbas haqarsu ta cimma ruwa kuma abunda suka dad'e suna dakon jira amatsayin fansar da suke son d'auka ya tabbata, fasa fitar tayi takoma cikin gida fuskarnan tata tamkar ambiya mata makka tashige d'aki tana tiqar rawa had'e da cewa da SANNU SANNU zakuga aikina da ciwa, kad'an kuka gani ai indai ina raye saina qumsa maku baqincikin da kuka qumsa mani nida 'yata akan yaronku, tashi baffa Ali da bai jima da kwantawa ba yayi yana kallonta cike da mamaki, dama dawowarsa kenan daga d'aukar hatsinsu da suka girbe ta tambayesa kud'i ya hanata shine tafita tana kumburar fuska wai zataje ta aro wani wuri, sai gashi bata jima da fitar ba yaga kuma tadawo fuskarta d'auke da farinciki tana dabsar rawa, tun kafin ya tambayeta ta shiga zayyane masa abunda taji 'yan uwan nasa nafad'a akan halin da Nuraddeen keci acan qasar.

Nan shima fa yatayata har yana fad'in wai anzo wajen!, sai su baffa sunyi dana sani da nadamar turasa qasar waje yaqaro katu, don bazaya tab'a dawo masu amatsayin wanda yayo karatu ba, sai dai yadawo masu a matsayin d'an iska lalatacce da baza'a iya tab'a banbance tsakaninsa da arna ba tunda suka zab'i turasa can akan aurar masa da 'yarsa, bayan duk walaqancin da akayi masu da wanda Yaya hawwa tayita masu alhalin ansamu damar da za'a iya aura masa ita, yazama dole yaje yabiya malan bakada imani don yanzu kam yatabbata yayi masu aikin daya dace, fatanshi kawai ALLAH yaqara duhu don girman d'ib.

Ashe duk wannan abun daya samu Nuraddeen aikinsu ne, su suka kaishi wajen malamin tsibbu sukace ayi masa asarin da zai lalace kuma idan yabar qasar ya manta da kowa nasa, asamashi tsanar qasarsa gaba d'aya yadena sha'awarta balle ma yatuna da iyayensa ko matarsa, duk wata hanyar da zatasa yaci gaba a dwad'e masa ita hatta karatun da akace zaije yi ya kasa yinsa, aganinsu yin hakan shine kad'ai zaisa su d'aukar fansar abunda baffa yasa akayi masu, fansar da batada wani tushe balle asali.

Ba'ayi wata da faruwar hakan ba su baffa sukaje sokoto asibiti wajen karb'owa Yaya hawwa sallama don ba laifi tafara samun sauqi, duk iya qoqarin su naganin ambasu sallama aranar hakan ta cutara daga qarshema sai ankace suje sai bayan sati biyu su dawo, ko kad'an basuso hakan ba amma babu yanda suka iya dole suka koma gida, sati biyu nacika suka sake komawa, awannan karonma saida sukayi da gaske sannan aka basu sallamar, itama d'in da sunan transfer ne akayi masu izuwa asibitin PSYCHIATRIC dake can kano sannan aka d'aukosu da motar asibitin.

Inna Bilkisu ita tagyarawa Yaya hawwa d'akinta kafin su iso, acan asibitin aka kaisu sukayiwa wani babban likita bayani akan suna son komawa da ita gida sugwada yimata maganin hausa idan ALLAH baisa aka dace ba sai sudawo, cikin sa'a da yake bahaushene kuma musulmi ya amince masu tare dasa hannu akan file d'in nata sannan aka aai aka ajiyesa inda yakamata, kuma ya fad'a masu aduk lokacin da buqatar kawota asibiti takama ba matsala sukawota in Sha ALLAH za'a dubata, data dai takowace irin hanyace ALLAH yabata lafiya, sunyi matuqar jin dad'i bisa karamcin daya yimasu kafin suyi masa godiya suwuce da ita gida.
Chapter 94 · 0% Book details