Sashe 61
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Alhamdulillah, inaga in Sha ALLAH anyi nasara, dama ba shigarsa sukayi ba, sun shafesa ne kuma muna sa ran yanzu zasu qyalesa idanma basuyi hakan ba to inada tabbaci akan ayar ALLAH zata qona mana su tare da sauran maganukkan da za'a kula dayi masa amfani dasu."
Cike da jin dad'i Dr. Nura yamiqa masa hannu yana murmushi yayi masa godiya sannan malmin yace yabishi ya karb'o maganin da za'a fara yiwa yaron amfani dasu.
*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶♀️🚶🏻♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻♂️🚶♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️
Page___45💎
Zaune inspector najida take saman kujerarta ta office ta jingina kanta a jikin bayan kujerar idanuwanta arufe tana jujjuyata a hankali, gaba d'ya ba abunda keyimata yawo a kwakwalwarta irin abubuwan da Yaya hawwa ta aikata, tambayar kanta tashigayi, wace irin rayuwace muke ciki yanzu?, Wane irin son kaine mutane suke cikinsa?, Meyasa mutane ke aikata zunubi adoron qasa tamkar wud'anda basada zuciya da d'igon tausayi atare dasu?, Haqiqa bakomai yajawo wud'annan abubuwan ba face zallar rashin imani da kuma tsoron ALLAH, tabama kanta amsa tana mai jin tausayin rayuwar Rashida tunawa da tayi da irin yanayin da tabar gida, nan take taji tsanar Yaya hawwa tarufeta har tanajin tamkar taje tarabata da lumfashinsa naqarshe saboda wannan abun data aikatawa qaramar yarinya 'yar cikinta.
Tajima zaune ahaka kafin can tajawo waya takirawo baffa, kusan kira biyar tayi masa amma bai d'aga ba saboda wayar na gida yabari tana chaji shi kuma yana kasuwa yaje kai sauran 'yan dabbobinsa da yakeson saidawa yaqarawa Nuraddeen kud'in akan zancen tafiyarsa don yau sati biyu ya rage tafiyar tasa, tuni yayo screening da sauran abubuwan daya kamata da taimakon baffa Usman daketa qarfafa masa akan tafiyar saboda yanda qarara yanuna baya da buqatar tafiyar tunda baisan halin a ina Rashidarsa take kuma awane hali take ciki,
Ganin takirasa har ba adadi bai d'aga ba yasa ta ajiye wayar agefe tare da d'aukar file d'in wani case dake gabanta tana daddubawa,
Shi kuwa Baffa bai samu yabaro kasuwar ba sai gab da magrib, tafe yake riqe da ledar kud'in daya saida shanayensa guda biyu da tumaki uku da suka rage masa aduniya, bayansu yanzu baida komai sai rayuwa da kuma gona k'waya d'aya da iyayensu suka barmasa ta gado, kasancewar yanzu yanajin babu wani abu da yai masa saura arayuwa na farinciki yasa yazab'i ya saida abunda ya rage masa saboda ya tallafawa d'ansa tilo aduniya wanda ayanzu shikad'ai ne farincikin daya rage masa aduniya sai kuma d'an uwansa baffa Usman da akoda yaushe yake jib'intar al'amurransa. sauri sauri yake tafiya yana sake rumqe ledar kud'in kamar wanda yasato har ya iso gida ya tarar da Nuraddeen zaune saman 'yar barandar d'akin da suke kwana ya rabka uban tagumi, babu abunda yake tunani kamar halinda mahaifiyarsa da matarsa ke ciki, gashi ita mahaifiyarsa tayi masa shamaki tsakaninta dashi alokacin da yake matuqar buqatarta akusa dashi duk kuwa da mugun halinta, ita kuma matarsa nisan tashin da akayi da ita yasa gaba d'aya natsuwarsa da komai nasa sun qaura daga garesa, a kullum bayada wani aiki daya wuce masa tunaninta dake neman ya zautar dashi, abun har yakai idan bacci yakeyi mafarkinta yake riqe da jariri sunata kallonsa suna kuka, idan kuma a farke yake haka zai dinga ganin tana yimasa gizo riqe da jaririn suna kuka, lokaci guda har abun yakai ga koda yaushe cikin jin qarar sautin kukan jaririn nayi masa yawo a kunnuwa a kowane lokaci sai ya zamana kullum bayada aiki sai kuka da tunaninta, gaba d'aya abubuwan da suka faru bayan watanni biyu da satikka da suka wuce sun sake dawo masa sababbi fal azuciya tamkar yanzu suka faru, yanayin daya shiga awannan lokacin sai ya zamana ya lunka wanda ya shiga a baya sosai, musamman daka kalli Nuraddeen zaka fahimci yanda alokaci d'aya yazama wani irin zautaccen mutum, bayada wata magana data wuce matarsa da jaririnsa, gashi lokacin tafiyarsa sai gabatowa yakeyi dad'a yi, hakan yasa su baffa dagewa wajen yimasa addu'o'i tare da nema masa taimako agun malamai har ALLAH yasa yafara dawowa hayyacinsa, wannan dalilin yasa suka sake jajircewa akan zancen tafiyarsa qasar waje wajen qaro karatun cike dasa ran cewa idan yayi nesa da qasar gaba d'aya hakan zai taimaka masa wajen rage tunani kuma yasama masa natsuwa,
Sallama baffa yayi har kusan sau uku amma Nuraddeen baima sanma yayi ba balle yasan da shigowarsa har saida ya qaraso kusa dashi ya dafa kafad'arsa, firgigit Nuraddeen ya farko daga duniyar tunanin da yakeyi had'e da kallon mahaifin nasa da nan taje fuskarsa tanuna rashin jin dad'in yanayin daya iskosa aciki, murmushin da iya lab'b'ansa ya tsaya yayi had'e da cewa. "Baffa sannu da dawowa, tun d'azu nake dibon dawowarka naji shiru, nama zata kuna can tare da baffa Usman."
Saida Baffa ya zauna daga qasa gefensa fuskarsa cike da damuwa sannan yace. "A'a Nuraddeen, kasuwa naje na saikar da 'yan sauran dabbobin da suka rage, dawowata kenan yanzu inata sallama amma naji shiru baka amsan ba, maganar gaskiya naji matuqar damuwa awannan yanayin dana iskoka, gaba d'aya banji dad'i ba."
Yafad'a tare da fashewa da kuka, da sauri Nuraddeen yadawo gabansa ya durqusa, "Don ALLAH baffa kayi haquri kayafeni, kada kabari zubar wannan hawayen naka yasake jefani cikin wani mawuyacin yanayin, ka gafartan baffa zanyi qoqarin fitar da komai araina amma baffa kayimun uzuri dole sai ahankali hakan zai kasance."
Jawosa baffa yayai ajikinsa ya rungume sosai hawaye nasake kwararo masa afuska, wata irin qauna da soyayyar d'an nasa yakeji na ratsa dukkanin sassan jikinsa da kuma rouhinsa. Ahankali yabud'e baki yace,
"Kayi haquri Nuraddeen, yanayin da kake ciki iyayenta sunfika shigarsa, Amma baka yanda bayin ALLAH nan suka haqura ba, suka yarda da jarabawar da ALLAH yayi masu saboda qarfin imani, ka qoqarta kaima kazama mai koyi dasu kuma ka rarrashi zuciyarka in sha ALLAH ubangiji bazai barku ahaka ba zai faranta zukatanku da suka kasance cikin qunci da baqin ciki komai daren dad'ewa, shin zaka iya tuno mani da abunda annabi yaqub (A.s.w) yafad'a lokacin daya sake rasa d'ansa bilyamin bayan ya dad'e da rasa d'ansa annabi yusuf (a.s.w) a cikin suratul yusuf ayata tamanin da uku (83)?."
A hankali Nuraddeen ya d'aga masa kai, cirosa yayi ajikinsa yana saurarensa, cikin qira'arsa mai dad'i yayi ta'awizi da basmala sannn yafara karanta ayar kamar haka.
_Qala bal sawwalat lakum anfusukum amrah, faswabrun Jamil, asallahu anya'atiyani bihim jami'ah, innahu huwal alimul hakim_
Ma'ana annabi yaqub yafad'a alokacin da 'yan uwan annabi yusuf suka zo masa da zancen bilyamin yayi sata a misra anriqesa (a.s.w) yace.
_"Ã'a, zukatanku sun qawata wani al'amari agareku. Sai haquri Mai kyawo,akwai tsammanin ALLAH yazo mini dasu gaba d'aya (Yusuf da d'an uwansa.). Lalle ne shine masani, mai hikima."_
Ajiyar zuciya baffa ya sauke had'e da kallon Nuraddeen yace. "to ina son kaima kafad'i hakan tare dayin imani da tattara dukkanin yardarka ga ubangiji, Inada yaqini akan cewa komai tsawon dad'ewa kaima ALLAH zai dawo maka da matarka da kuma d'anka, kamar yanda aka dawowa annabi yaqub da 'ya'yayensa biyu daya rasa alokacin dabai tab'a tsammani ba."
Cike da soyayya Nuraddeen ke kallon mahaifinsa kafin yace.
Baffa _"Fa swabrun Jamil, asallahu anya'atiyani bihim jami'ah, innahu huwal alimul hakim_"
Yaqaresa ayar had'e da rungume baffa yana jin wani sanyi azuciyarsa.
Murmushi baffa yayi shima yana mai godewa ALLAH da duk tsananin jarabawar da suke ciki bai rabasu da imaninsu ba sannan yamiqe yashiga cikin d'akin ya adana kud'in kusan dubu d'ari biyune da hamsin, yana fitowa ana fara kiraye kirayen sallar magrib yace.
"Nuraddeen mutashi muyi harma, kaji ankira sallah."
Miqewa Nuraddeen yayi ya zubowa baffa ruwa abuta shima ya zubama kansa sukayi arwala sannan suka nufi masallaci,
Bayan sun dawo ne suka tarar da baffa Usman bakin qofar gida riqe da ledar kwanonin abincin data zama dole kullum sai yasa ankawo masu daga gidansa ko kuma yazo da kansa yakawo masu, da sauri Nuraddeen yaqarasa wajensa had'e da gaishesa sannan yakarb'i abincin yayi cikin gida, fuskar baffa sake taqaraso wajensa shima yamiqa masa hannu suka gaisa yana fad'in, "agaida malan usmanu baban Nuraddeen sannu da zuwa kazo adaidai don yanzu nake tunanin inkiraka awaya."
"To gani nazo, ALLAH yasa kan wasu nerorine zaka bani in take." yafad'a cike da raha,sun jima suna zolayar junansu abun gwanin sha'awa kafin su qarasa shiga cikin gidan, inda suka hango tabarmar da Nuraddeen ya shimfid'a masu suka nufa suka zauna tare da aza wata sabuwar fira wacce mafi yawancinta duk akan maganar tafiyar Nuraddeen ce, a nan baffa ke sanar dashi maganar kud'in da yazo dasu d'azu wud'anda ya saida dabbobinsa, sosai baffa Usman ya nuna masa rashin jin dad'in hakan da yayi tare da sheda masa cewa akwai wasu shima ahannunsa da yake da niyar bashi yaqara amma saidai basuda yawa dubu talatin ne.
Nan dai sukaci gaba da firarsu har kusan qarfe goma da rabi sannan baffa Usman yawuce,
Bayan wucewarsa ne Nuraddeen yakawo masa abinci yaci shima suka d'an ta'ba fira sannan suka bid'in inda zasu aza awazzansu, a lokacinne baffa ya d'oko wayarsa da niyar sanya masu karatun baqara don haka yakeyi har safe saboda ta d'ebe masu kewa, sai gashi yaga kusan 5missed call kuma duka na inspector najida ne, har ya danna lambar zai kirata sai kuma yayi saurin katsewa saboda agogon wayar daya nuna masa kusan qarfe 11:45 na dare, don haka bazai yuyu yakirata awannan lokacin ba duk da dai yaso yaji dalilin kiran nasa da tayi don yasan akwai wani abu mai muhimmanci da aka samu wanda shine yahaifar da kiran data yimasa, fasa kiran nata yayi har zuwa gobe da safe idan ALLAH yakai mana rai.
_Kuyi haquri dis days sai ahankali abubuwa sunyi yawa kawai Ina squatting ne nad'an yimaku typing._