Sashe 46
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan kwana biyu kullum Yaya hawwa cikin zuba idanuwa take taga abunda zai samu Rashida amma shiru har lokacin babu abunda ya sameta saima lafiya da take taqara samu, haka ma ta b'angaren boka bargaji duk iya sihirce sihircen da zaiyi yayi amma yakasa samun nasara ko daidai da qwarar zarra da zai iya cutar da, yatura baqaqen aljanu da mugaye kala kala don su juyar mata da qwaqwalwa saboda tsananin fusatashin da tayi nason ja dashi tahanyar nuna gazawarsa ga aikin amma duk wanda yatura a qone yake dawo masa ko kuma naqashe saboda qarfin addu'o'in da takeyi da yawan sauraren karatun alqur'ani, ko kad'an Rashida bata wasa da azkar kuma bata yadda tazauna babu arwala ba ko kuma cikin janaba balle yasamu damar aiwatar da aikinsa wanda hakanne yaqara mata matuqar tsaro da kariya daga sherin shed'anun, musamman ya tura mata aljanun da zasu dinga tsereta koda zatayi kuskuren mantawa dayin addu'a lokacin kwanciyarta ko kuma lokacin da zata Tara da mijinta, a tunaninsa yafi komai sauqi Amma sam agurin Rashida bata wasa da hakan, haka ma tsakar dare yakan turo wasu da zasu dinga zuwa suna tsoratata shima da sunje saisu tarar da ita tana nafilfili wanda takanyi hakanne aduk lokutan da tajita cikin tsoro ko miyagun mafalkai, ko kad'an nauyi da girman cikinta basusa tayi sakaci da ibadar taba domin ita tad'auka a matsayin jigon dake tafiyar da rayuwarta cikin aminci, babban farincikin ta d'aya aduniya shine yanda hankalin Yaya hawwa bai karkata wajen cutar mata da abunda ke cikinta ba wanda ako yaushe idan ta tuna da hakan takan yiwa ALLAH godiya,
Yauma kamar kullum tana zaune saman kujera taba qofar falonta baya tana karatun al-qur'ani saboda tuni ta kammala girkinta da kuma 'yan gyare gyaren gidan da takeyi sai ga Nuraddeen ya shigo cike da farinciki yana kiran, "habibty, habibty, habibtyyy..where are you my habibtynah?."
Kasancewar takama farkon aya yasa takasa katsewa ta amsa masa har sai da takai k'arshen ayar, juyowa tayi daidai lokacin daya shigo yayi saurin zuwa yarungumota ta baya had'e da sumbatar gefen wuyanta yana fad'in,
"Masha ALLAH da samun nagartacciyar mace ma'abociya riqo da addini kamarki, ALLAH yayi maki albarka momyn chuluv d'ina."
Hannunsa dake saman kafad'arta tasa hannunta tariqo had'e da sumbatarsa tace.
"Welcome habiby abban chubby d'insa, ALLAH yasa alkhairine wannan kira da naji kana yimun tun daga bakin qofa?."
Dawowa gabanta yayi ya amshi qur'anin dake hannunta ya saka mata alama a inda take sannan yarufe tare da ajiyesa gefe, hannunsa ya d'ora akan cikinta yana murmushi, daidai lokacin abunda keciki ya motsa, da sauri yacire hannunsa yana zaro idanuwa awaje, dariya ta bushe masa da ita had'e da cewa.
"Lafiya abban chubby d'insa?"
"Kai!.motsifa naji yakeyi habibty.!"
"Eh mana, baka tab'a ji bane?, Ai shine cikakkiyar lafiyarsa idan yana wannan motsin inji likita, ai wannan bashine karo nafarko daya fara motsiba, kaine kawai baka tab'a cin sa'a ganin saba alokacin da yakeyi."
"Najifa tsoro!" Nuraddeen yafad'a cike da mamaki yana kallon idanuwanta, kallo d'aya zakayi masa kasan tsokana ce tasa yafad'i haka, dariya tayi had'e da cewa.
"Tab lallema habibtyn! nan, to meye abun tsoro anan? Kenan ni da yake ajikina sai in mutu idan naji motsinsa?"
"Ahh..rufamun asiri bance haka ba, to idan kika mutu ni kibarni Ina?, Yihaquri dama zolayanki nakeyi." Yafad'a yana dariya,
Dukan wasa takai masa a gefen kafad'a had'e da d'an harararsa cikin shagwab'a tace.
"Kai ko!"
"Afuwan bazan qara ba, yanzu dai albishirinki?"
"Goro fari qalqalqal."
Yanzu muka gama waya da baba yace zancen komawarki gida wanka abarshi tunda anan kike awo har sai ALLAH ya saukeki lafiya sai amaidaki dake da babyn, kinga dai nima zan d'an qara morewa Ina dinga ganinki keda chuluv d'ina kafin lokacin.?"
'Bata rai tayi kamar zatayi kuka don har tafara shireshiren komawarta sati mai zuwa amma sai gashi yazo ya wargaza mata tsari, cike da jin haushi tafara kaimasa duka 'yan k'wallah nafito mata shi kuma yana dariya,
"Wato zuwa kayi kafad'awa su baba kada abarni na koma?, Kuma shine za kazo ka aza mani dariya ko? Why habiby meyasa zaka yimun haka?."
Tafad'a tare da fashewa da kuka, ganin da gaske takeyi saboda hawayen da suke zubowa daga idanuwanta yasa yatsaya da dariyar da yakeyi yana qoqarin riqe mata hannuwa.
"Srry habibty ba haka bane, wlh bana son kiyi nesa dani ne?, Kuma idan kin lura duka duka kwanaki nawa suka rage ki haihu?, sati biyu kacal fane, ai kinga da ace kin koma can Kuma haihuwar tazo ankwasoki anyo nan k'ara kiyi hak'uri ki haihu nan abunki, kinga ranar da kika haihu idan an sallamome nayi maki alqawarin da kaina zan d'aukeki in kaiki gida kinji ko?." Yaqarasa maganar cikin sigar rarrashi, fad'awa tayi ajikinsa tana kuka ya rungumeta yana shafa kanta zuwa bayanta cike da mamakin yanda abu kad'an ke sata kuka yanzu, sun jima ahaka yana cigaba da rarrashinta tahanyar dad'ad'an kalamai masu sanyi da kwantar da zuciya kafin ya d'agota yana kallon idanuwanta, sadda nata tayi qasa yasa hannu ya tallabo fuskar yana goge mata hawayen. "Kina so in fad'a maki wani albishir da zai faranta maki rai.?"
'Dago idanuwanta tayi takallesa tare da cuno baki gaba tace, "ni bana so idan kasan zai sake b'atan rai."
"No..no..wannan nasan zakiji dad'insa Kuma zai saki farin ciki sosai." Yafad'a yana sumbatar 'yan qanan lab'b'anta, "ALLAH da gaske?"
"Sosai kuwa."
"Ok. Ina saurarenka." Tafad'a tana qarasa goge hawayen dake nema su bushe a fuskarta. Murmushi yayi yariqo hannuwanta had'e da cewa
"Habibty!, nasamu gurbin cigaba da karatuna, sunana yafito ajerin sunayen wud'anda gwamnati ta d'auki nauyin zuwansu qasar malesia don suqaro karatu, baban farinciki anan ma shine dana dawo naje Ina sanarwa da baffa yake fad'amun cewa yasama mana gida haya da zamu zauna idan kindawo daga wankan biqi kafin nawuce, kinga sai musha soyayyarmu hankali kwance babu takurar gidan yawa."
Cike da farinciki tarungumesa tana fad'in. "Alhamdulillahillazi bini'imatihi ta timmusswalihat, congrat habiby gaskiya nayi farinciki sosai, ALLAH sarki baffa ai da yabarmu anan d'in, kullum baya gajiya dayi mana hidima da son faranta mana, ALLAH yabiyashi yasaka masa da mafi qololuwar alkhairinsa."
"Amin ya rabbhi habibty." Yafad'a yana dariya cike da jin dad'in addu'ar da tayiwa mahaifinsa,
"Amma habiby yaushe ne zaku wuce?" Tafad'a tana d'agowa daga jikinsa, shiru yayi kamar mai wani tunani kafin yace
"Ehmm..inaga kamar nan da wata uku sukace, amma ungo takardar kiduba kigani." Yafiddo takardar daga aljihunsa yana miqa mata.
"A'a kabarta, Amma gaskiya abun ya matse sosai, kamata yayi ace ko nan da wata biyar ne, kaga lokacin chubby child d'inka yad'an saba da kai..." tafad'a tana d'an b'ata rai.
"Karki damu zan iya cewa a d'agamun lokaci saboda matata da chuluv na buqatata akusa dasu koda nan da zuwa wata goma ne idan kina buqata."
"A'a rufamun asiri, ai dama ce ta lokaci d'aya idan tasamu to yayi amfani da ita.. ALLAH yakaimu lokacin kuma yasa munada rayuwa."
"Amin habibtynah. Shiyasa nake qara sonki saboda wannan kaifin fahimtar da kike da ita."
"Bawni wayau da zakayimun, ALLAH zamuyi kewarka sosai idan katafi." Taqare maganar tana shafa tulelen cikinta daya qara girma sosai cikin kwana biyu d'innan.
"ALLAH dai ya saukeki lafiya kuma yabamu rayayye mai albarka."
"Amin habiby."
"Yawwa nace wane suna kike so mu sakawa babynmu idan kin haihu?."
"Emmm..idan macece sunan Inna nake so a saka mata hawwa'u mudinga kiranta (jiddah) idan kuma namijine sunan ka nake so yaci wato (Nuraddeen)."
Tuni baffa yagama samarwa su Nuraddeen hayar wani d'an madaidaicin gida acan farkon gari kusa da asibiti mai d'auke da d'akuna biyu da falo d'aya sai kitchen da toilet, sai tsakar gidan da girmansa bai wuce iya mutum biyar su kwanta ba, yayi hakanne don su samu sakewa su huta da takurar Yaya hawwa shi kuma yasamu yaqaro aure ko yakoya mata hankali, wannan itace shawarar daya yanke tsakaninsa da baffa Usman da tuni yayi magana da Inna Bilkisu za'a bashi auren 'yar yayarta da ALLAH yayiwa rasuwa tagudo tadawo nan garin sanadiyar wahalar da take Sha a hannun 'yan uwan mahaifinta, qaramar yarinyace da Bata wuce shekara goma sha uku zuwa Sha hud'u ba da yake su can qauye basu d'auki abun wani abubu har da shekara goma zuwa goma sha biyu suna aurar da yarinya, cikin sa'a kuwa iyayen Inna Bilkisu suka yarda saboda yanda sukaga baffa Usman yariqe masu 'yarsu hannu biyu shiyasa suka yarda da nagartar yayan nasa suka amince da aura mashi yarinyar koba komai hakan zaisa idan 'yan uwan mahaifinta sukaji tayi aure su dangana da batun komawarta can.
Duk wannan abun da akeyi Yaya hawwa batada labari tana can tana haukar rashin ganin aikin boka da bai kama Rashida ba, gashi wannan bokan ba'a yimasa katsalandan ko tambaya balle takoma taji ba'asi, gaba d'aya abu ya isheta ya sha mata kai tarasa yanda zatayi, Inna ruqayya kuwa tuni itam tabazama wajen bokaye tunda taji abunda Yaya hawwa tafad'a akan bazata had'a zuria dasu ba don arufe mata baki Kuma akarkato masu da zuciyar Nuraddeen ga muneera har sai ya aureta,
Adaidai wannan lokacin da Rashida da Nuraddeen ke cikin halin tsaka mai wuya a hannun bokaye cikin Rashida ya cika wata wata tara dam da haihuwa, duk abunda yakamata Nuraddeen ya tanada na kayan baby da mamansa gwargwado ya tanada, haka kuma duk abubuwan da mahaifiyarsa keyiwa matarsa bai tab'asa ya yarda haqqinta ko d'aya ba akansa, duk wata kyautatawa yana yimata daidai gwargwado kuma kullum dashi har Rashida basu fasa zuwa gaisheta ba amma Rashida bakinta d'auke da addu'o'i take zuwa gaisheta ko yaushe sanin halin da ake ciki, musamman itama ya saimata kaya kala biyu ya kimata da zimmar taci suna dasu idan ALLAH ya sauki Rashida lafiya, yau tunda safe Nuraddeen yatashi da fad'uwar gaba wacce yarasa dalilinta amma yanata addu'ah batare daya bari Rashida ta fahimci halin da yake ciki ba,
Da daddare suna kwance ta mulmulo wajensa had'e da d'ora kanta saman kafad'arsa tana yawo da hannunta saman qirjinsa, a hankali yayi gyaran murya had'e da cewa.
"Habiby lafiya yau naganka sai ahankli, meyake faruwa da kaine?"