← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 160

Sashe 26

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Habibty kidena wannan kukan bana so, akwai basosa masu girma da kike bina wajen rarrashin zuciyarki daga abubuwan da nine silar data b'aci har ta tinzira kyawawan idanuwannan naki fitar da wud'annan tsadaddin wayen, kiyimun afuwa kada kisa zuciyata tayi mani tsattsauran hukunci akan haka, kinfi kowa sanin tarin qaunar da nakeyi maki azuciyata saboda haka gada kibari shaid'an da sharrin zuciyar wasu yasa maki kokwanto ko wani shakku akaina, muneera yarinyar baffa Ali ce, tana matuqar sona amma ban tab'a jin qaunarta azuciyata ba shiyasa tazo tana maki wannan haukar, kiyi haquri daga yau nayi maki alqawarin bazata sakeba kinji?."

Saida ta share hawayen da suka jiqa mata fuska tana sake jan majina sannan tace

"Amma meyasa ka aureni bayan kasan tana sonka.?"

"Saboda ke kad'ai nakeso habibty, ke kad'aice keda mallakin dukkanin wani sansani dake cikin zuciyata, gangar jikina, zuciyata da Kuma rouhina duka mallakinkine babu wani qanqanen fili daidai da k'warar zarrah da zan iya baiwa wata aduniya, Wannan dalilin shiyasa ban aureta ba."

"Amma ai 'yar uwarka ce, inaga kamar ita tafi dacewa ka aura." Murmushi yayi tare da kamo hannuwanta biyu ya riqe yana murzawa a hankali yace.

"Idan ita 'yar uwatace ke Kuma rayuwa tace habibty, shin da d'an uwa da rayuwa wayafi dacewa ace mutum yariqa da kyau da kuma muhimmancin da zai zamo masa abokin zama"

"Rayuwa mana"

Ta furta ahankali tana murmushi, murmushin shima yayi had'e dasa yatsa ya lakutar mata hanci yana fad'in

"Gud gel" Da sauri tasa tafin hannayenta tarufe fuskarta, "yawwa bari naje nadawo yanzunnan kinji habibty, kada kisake kuka daga wannan lokacin saboda yau ranar farinciki ce agaremu."

Kad'a masa kai tayi sannan yafice daga d'akin bayan ya d'auki makullan shiyar tasa dake gefen bedside d'inta, yana fita yajawo qofar yasa makulli had'e da juyawa zai bar gidan, yanaji Inna ruqayya matar baba Ali na zage zage harda fad'in.

"Lallai nura ya lalace yanzu ya dakeki akan bare, kina 'yar uwarsa zai walaqantaki akan matarsa lalle dole Yaya hawwa tasan abunyi, ke ya dokeki?"

Tasake nana tawa tana d'agowa muneera kanta, murmushi yayi tare da kad'a kai sannan yawuce abunsa, ita kuma tab'are baki tare da nunawa inna ruqayya tsakiyar kanta,

"Yishiru taso muje wajen yaya hawwa, wlh yau sai ranar nan tazamo masu ranar bak'inciki, yishiru nace maki" taja hannunta suka nufi sashen Yaya hawwa lokacin tana zaune bisa abun sallarta Bata dad'e da gamawa ba, kukan muneera da taji yasa yasa tayi tsaki tare da ajiye tasbahar hannunta gefe kai kace tasan ALLAH tana tofe addu'a had'e da shafewa a fuska.

"Ke.ke. lafiya aka zomun qofar d'aki ana mani reren kuka sai kace munafukar amarya!." Tafad'a tana lunke sallayar had'e da komawa saman gadonta zata kwanta,

"A'a Yaya ai kwanci bai ganeki ba saboda waccan itace munafukar amaryar da naji kina fad'i, fisabillahi ace daga kawo yarinya yau har tajawa yarinyarnan duka awajen d'an uwanta don tana muna fuka...zonan nuna mata inda ya dokeki muneera don bazan yarda ba."

"To sakaryar uwa mai malalaciyar 'ya yanzu akan d'an rank'washin da yayi mata akai zaki zomun kawo qara don rashin mutunci ko nace takakka."

Yaya hawwa tafad'a tana kallon Rashida da tawani duqo Kai tana nuna mata da yatsa tanaci gaba da reren kuka "ke dallah rufemun qaton bakinnan naki kamar rijiya kona ci ubanki, ca nake uban waye yakaiki shiyarsa har ya rankwasar maki kai." turo baki tayi tana susar kai had'e da cewa.

"To ba amaryar naje gani ba, shine nake jamata fad'amata ni 'yar uwarsa ce Kuma ni nake sonsa..."

Bata k'arasa ba Yaya hawwa ta kwatseta tana fad'in "maza fitarmun d'aki shashasha mai gwalmammin qafafuwa ke kuma da bakisan abunda kikeyi ba kika kwasota kuka iskeni ko yanayin da nake ciki bakya tunani ke tama 'yarki kikeyi, to idan kinfita kijamun qyaurena zanyi lokacinsu su kuma."

"Amma Yaya hawwa ya zakiyi mani haka?"

"Kije kafin dukkanin damuwata taqare akanki rakkiya."

Afusace tafita tare da rafko qofar d'akin tana suruttai jar ta iso shiyarta, tun tana tsammanin wani zai tankata har tagaji tahaqura saboda rashin samun wanda ya kulata.

••• ••• •••
Acan b'angarensu umma da baba kuwa tun cikin mota yaya Yaya maryam ta gargad'i kowa akan kada atada zancen abunda yafaru saboda kada atayarwa mahaifiyarta da hankali, haka da akazo qofar gida saida tasake gargad'insu, kasancewar itace babba yasa kowa kama bakinsa aka shiga ana fatan Allah yasanya alkhairi, aunty marwiyya kuwa da zata tafi Saida tacewa umma "to aunty bawai kinnrabu da 'yarki ba Kuma shikenan, a'a tashi tsaye zakiyi wajen yimata addu'a da nema mata kariya wajen ALLAH daga sharrin miyagu da mahassada." Gaban umma ne yafad'i tace.

"Marwiyya injin dai ko lafiya kika fad'i haka.?"

"Lafiya klw aunty kinsan dai halin gidan yawa dole baza'a rasa gutsiri tsoma aciki ba, amma babu komai." Wata ajiyar zuciya umma ta sauke duk da dai bata natsu da amsar da tabata ba had'e da cewa.

"Shikenan marwiyya, Allah yatsare da tsarewarsa amma addua'a dama ai baza'a dena ba, ngd sosai Allah yabar zumunci, ki gaida mun da alhaji."

"Amin aunty zaiji in sha ALLAH, ALLAH yahutar da gajiya."

"Amin seda safe a gaida yara." Tunda tafita umma taji ta kasa samun natsuwa har baba yadawo, cikin gajiya had'e da nuna kasalar dake tattare dashi yafad'a gefen gado yana fad'in.

"Wayyo ni bawan ALLAH." Murmushi tayi jiki a sanyaye had'e da mik'ewa takoma ta gefensa ta zauna tana d'an mammatsa masa k'wandunansa,

"Sannu da hidima malan."

"Sannu mamn Rashida ya gajiyar taku hidimar.?"

"Alhamdulillah, saidai Ina matuqar kewar yarinyata sosai."

"Naga hakan atattare dake amma ya zamuyi tunda ita mace dama 'yar gidan wani ce, ni kaina ina kewarta sosai, ki kwantar da hankalinki addu'armu kawai itace ubangiji ALLAH yabasu zaman lafiya."

"Amin ya gaffar."

Tafad'a tana goge 'yan qwallan da suka zomata.

••• ••• •••
Nuraddeen nafita yanufi wajen masu saida naman kaji dana rago ya siyo namansa na kaza sannan yasa akayo masa d'aurin naman rago guda biyu, da gorar fresh yaghouth guda biyu, uku wajen baffa yanufa ya kaimasa qulli d'aya sannan yanufi sashen Yaya hawwa bakinsa d'auke da addu'a, tura gambun yayi ahankli daga can kwance tace

"Waye?"

"Innar mu nine yafad'a yana qarasowa cikin d'akin, gefe ya zauna tare da gaisheta ta amsa daga kwancen da take batare da ta taso ba, shiru yayi na mintoto kafin yace

"Innar mu ga wannan?" Ya ajiye ledar abakin gadon,

"ALLAH amfana." tafad'a tana qyaren d'ayar ledar dake hannunsa,

"Saida safe innarmu." Yafad'a tare da miqewa ya nufi qofar fita, har ya aza qafarsa tace,

"Miye wannan a d'ayar ledar?"

Shiru yayi yakasa Bata amsar don baisan me zaice mata ba,

"Dawo itama ka ajiye."

"Innar mu.."

"D'auka duka biyun ka b'acemun da gani" tafad'a a fusace, cike da mamakin mahaifiyar tata ita dako bud'a abunda ya kawo mata batayi ba amma tace a ajiye mata duka, duk ya zatayi dasu, dawowa yayi ya ajiye ledar sannan yace.

"Kiyi hak'uri innar mu seda safe" sannan yafice kamar zaiyi kuka, gashi gaba d'aya duka kud'in ya kashe naira d'ari biyu kacal ta rage masa, tsaye yayi bakin rumfar yana tunanin yanda zaiyi ya samu wasu kud'in gashi abokanansa duka sun shige Kuma bazai iya iske baffa yace masa yabashi kud'i ba bayan duk wannan jidima daya yimasa, yanke shawarar zuwa ya siyo naman d'ari biyun yayi ko kuma idan abule Mai naman ya amince ya karb'i bashi har gobe don bazai iya koma mata babu komai a hannu ba, daidai ta wajen d'akin baffa zai wuce yaji yakira sunansa, shiga yayi had'e da cewa.

"Gani baffa lafiya."

"Lafiya klw Nuraddeen, wai wannan tsumuiniyar da kakeyi ta lafiya ce kabaro yarinyar mutane ita kad'ai zaune, daga Ina kake yanzu kuma Ina zakaje?." d'an sosa kansa yayi had'e da cewa,

"Daga wajen innar mu nake baffa yanzu zan dawo bajimawa zaniyi ba." Yaqare maganar yana kallon agogon hannunsa saboda lokacin tashin abule ya kusa, daga cikin idanuwansa da Kuma yanayinsa baffa ya fahimci komai, aransa ya tabbatar da cewa Yaya hawwa tayi tsiyar don zata iya komai don ta quntata masu awannan ranar, "tashi katafi" yafad'a yana mai addu'ar ALLAH yaganar da ita, har zai fita sai Kuma baffa yace,

"Yawwa Nuraddeen zo d'auke ledar nan naman nan yayimun qarfi bazan iya ciba."

"Amma baffa mai taushi nace yasa maka bansan ya akayi yasa mai qarfi ba."

"To nidai naci d'aya hakanan ALLAH yayi albarka d'auka katafi dashi." d'auka yayi don yasan halinsa baya son gardama yaji yace.

"Had'a da madarar nan tayimun sanyi sosai naga har qanqara gareta, gobe kasiyomun fura da nono nafi gane masu."

Shiru Nuraddeen yayi don yagama fahimtar mahaifinsa ya gano komai shiyasa yayi haka,

"Baffa ka ajiye ko zuwa gobe sai asake dafa maka, ita madarar Kuma dama kamar nono take tahuce sai kasha."

"A'a d'auka tafi dasu nace maka" dole ba yanda zaiyi ya d'auka had'e da yimasa saida safe ya fice, baffa na kallonsa ya koma cikin gida batare da ya fitar daya tashi yiba, murmushi yayi yace, "ALLAH ya kyauta sannan ya komawarsa ya kwanta, sashensa yabud'e ya shiga tare da karanta addu'a ya rufe.

Koda ya shiga ya tarar har tayi bacci ya ajiye ledar hannunsa had'e da nufar inda take kwance da alama sallolin magrib da isha'i tagama bacci ya d'auketa, hannuwansa yasa ya tallabota tare da cire mata hijabinta ya dinga hura mata iskan bakinsa a fuska, ahankali tafara bud'e idanuwanta suka sauka saman fuskarsa ai kamar wacce aka mintsila tayi saurin zamewa daga hannunsa tana tattaro hijabinta tana rufe jikinta, murmushi yayi daga duqen da yake tare da cewa "tashi muje ki wanko bakinki a toilet." Yaqare maganar had'e da mik'ewa ya riqo hannunta suka nufi toilet d'in tana biye dashi tana kallonsa, bata tab'a kula da kyan da ALLAH yayi masa ba sai yau...

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___19💎
Chapter 26 · 0% Book details