← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 160

Sashe 105

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga lokacin tamanta da duk wani Abu dake faruwa tacigaba da gudanar da harkokinta yanda tasaba amma akullum safiyar ALLAH son da takeyiwa Abu sumayya sake lunkuwa yakeyi a zuciyarta, wanda hakan ba qaramin farinciki ya saka hajia mama ba dama shi abban da kansa, Amma ta qarqashin qasa yasa wani amininsa dake can borno ya binciko masa komai akan Abu sumayya da mahaifiyarsa, inda ya tabbatar masa da cewa tabbas ba'asan mahaifin yaron ba kawai anwayi garine anga mahaifiyar tasa da iyayenta acikin garin ne, mijin 'yar uwar tasa hajia nafeesa shike kula dasu shida babban d'ansa, yasamu qeshe qashin labarin cewa su d'in 'yan asalin nan kano ne amma bazai iya cewa sud'in konsuwaye ba, yanzu haka dai mijin hajia nafeesa shike auren kakar yaron saboda ALLAH yayiwa mijin nata rasuwa, ya tabbatar masa da cewa iya gaskiyar abunda yasamu kenan acikin binciken da yasa yayi masa, kusan mutum biyu Abba yasake sa suka sake yimasa bincike amma dai duk amsar d'ayace Babu banbanci, hakan ya matuqar b'ata masa rai, wai yau 'yarsa da yakeso fiye da sauran 'ya'yan da take dasu tarasa wanda zata soyayya dashi sai shege wanda ba'asan asalinsa ba, kuma har tanace akan cewa wai shi kad'aine zai iya bata farinciki aduniya, wata irin tsanar little marar misaltuwa yasake ji aransa, tabbas koda zai rasa 'yarsa ne bazaya tab'a bari da girmansa da mutuncinsa ba tazubar masa da kima acikin garin, zai bita yanda take so har zuwa lokacin da take tsammanin cewa zai d'auketa da hannunsa ya damqawa wanda bayada asali, inyaso alokacin zai nuna mata cewa shi d'in ubane da soyayyar da yake yiwa d'a bata Isa tahanasa yanke hukuncin daya dace akansa ba.

••• ••• •••
A b'angaren little kuwa tuni yafara karatunsa cikin maida hankali da kuma qwazo da son ganin ya cikama mahaifiyarsa burinta, kamar dai yanda akoda yaushe batool ke kwana da tashi da soyayyarsa azuciyarta haka shima ta b'angarensa Babu wani banbanci, yana yimata so da bazai iya misaltashi ba, musamman yanzu da basa tare da juna kuma sukayiwa kansu alqawarin nesanta da juna har zuwa lokacin da suke tunanin mafarkinsu zai cika,

A campus d'in makarantar gwaggo wato Rashida mahaifiyarsa taso ya zauna amma sai Dr yace a'a agidan baba balarabe zai zauna don har yagama magana dashi, ko kad'an rashida bataso hakan ba Amma babu yanda ta iya dole tahaqura, sosai baba balarabe yaji dad'in zamansa wajensa koba komai yana tunanin zai iya gyara kuskuren daya aikata na tsawon shekaru duk da ba'ason ransa ba, yaso tuntuni yaje ya sanarwa da baffa cewa anga Rashida da kuma qaruwar d'a da Allah yabata tsakaninta da d'ansa amma sab'anin daya nemi b'arkewa tsakaninsa da 'yar uwarsa tilo data rage masa aduniya shiya haifar masa da kama bakinsa akoda yaushe, yayi kuka ba adadi kuma marrar misaltuwa lokacin da qaddara tasa yasanar da 'yar uwar tasa yaya Maryam cewa yana son xuwa yaroqi baffa gafarar abunda yafaru daga nan kuma ya sanar dashi cewa Rashida da abunda tahaifa naraye basu mutu ba saboda yanda yaga ransa yab'aci lokacin da suka zo gaisuwar aminin nasa amma sai tanuna masa bata amince da hakan ba saboda ita aganinta babu wani kuskure da suka aikata aciki da har zai d'auki zafi akan abun yanuna ransa ya b'aci don duk iyaye nagari zasuyi fiye da abunda sukayi akan 'yarsu, sannan tunda d'ansu baya gari meye amfanin sanar dasu?, Zasu iya yunqurin cewa takoma d'akinta zasu kula da ita tunda bai saketa ba idan kuma suka nuna qin amincewarsu suce abasu jikansu wanda duk duniya idan zata nad'e wlh bazata bari araba Rashida da d'anta ba don haka inhar zasu sanar dasu komai to sai d'ansu yadawo qasar tukuna kuma shima d'in bawai don takoma dasu ta zauna bane, a'a sai don araba igiyar dake tsakaninsu ne, ita kad'ai tarage masu da zasu kalla amatsayin d'an uwansu suji sanyi don haka babu yanda za'ayi subarta a inda za'a iya sake salwantar mata da rayuwa tunda ba surukar tata kad'ai bace bata sonta ance harda wasu 'yan uwan mijin nata, idan kuwa yaje yasanar dasu wani abun akan Rashida da d'anta bata yafe masa ba a matsayinta na 'yar uwarsa kuma wlh babushi babu ita saidai ya sake wata 'yar uwar, da yayi yunqurin nuna mata muhimmancin fad'a masu musamman ko don d'an uwansa da sanadiyar hakan yarasa rayuwarsa sai tafashe masa da kuka wai yana son surasa marainiyar ALLAH kamar yanda suka rasa mahaifinta, duk iya qoqarinsa naganin tafahimta amma takasa sai nanata take duk ya aikata hakan to babu shi babu ita, wannan dalilin yasa babu yanda ya iya ya haqura saboda tsoron kada zumuncinsu ya lalace itama ya rasata, amma kullum cikin addu'a yake ALLAH yadawo da Nuraddeen yahad'u da iyalinsa ko wannan nauyin zai rage masa azuciya, a kullum cikin bibiyar al'amurran ahalinsu baffa yake asirrance koda zai samu labarin dawowarsa amma shiru, hatta auren da baffa yayi duka yaje, haka lokacin da yasamu labarin abunda yafaru da Yaya hawwa shima d'in yaje amma duk bai samu ganinsuba sai dai ya aika yaro yace aje ace balarabe daga yarimawa yace yana gaida marar lfy, saidai bayada masaniya akan saqon na isa ko kuwa, damuwarsa taqaru alokacin da yaji labarin cewa wud'anda sukaje karatu da Nuraddeen sun dawo amma shi yace bazai dawo ba sai daya yasa yasake komawa yaroqi Yaya Maryam akan don ALLAH tabari bawan ALLAH nan yahad'u da jininsa ko yasamu sassaucin halin da yake ciki saboda shi mutumne mai matuqar muhimmancin da bai cancanci ace ya amshi irin wannan sakamakon daga wajen suba amma for taqi amincewa saima cewa da tayi karya sake nufota da wannan maganar tunda har d'an nasa yace bazai dawo ba kenan yanuna cewa ya manta da yanada wani ahalin anan qasar don haka suma dole su manta dashi kamar yanda ya manta dasu, alokacin yakira umma yasanar da ita hukuncin da Yaya Maryam ta yanke kozata roqeta ta sassauto ko don cikawa marigayi burinsa, amma da yake itama alokacin cike take da b'acin rai akan abun sai tabashi amsa da cewa ai 'yar tace tanada iko akanta kamar yanda shima yake da iko akanta don haka ita babu abunda zatace akai, hakan yatabbatar masa da cewa itama umma tad'au zafi akan lamarin yanzu baida yanda zaiyi dasu, sun sha had'uwa da baffa akasuwa amma banda sallamar musulunci da gaisuwar mutunci babu abunda keshiga tsakaninsu, yana so ya sakijiki da baffan Amma saboda yanda baffan ya d'auka da zafi musamman akan rasuwar aminin nasa da sukaqi sanar dashi yaqi samun fuska daga wajensa, hakan kesa aduk lokacin daya tuna yazauna yayita kukan rashin d'an uwansa don ya tabbata idan yana raye hakan bazata faruba duk da kuwa gaba d'ayansu qanne suke agareta amma saboda suna su biyu shi zaisa su iya galaba akanta, yanzu kuwa zamowarshi shi kad'ai yasa masa raunin da bazai tab'a iya jayayya da ita ba, Yauma kamar kullum ya zaune a zauren gidansa idanuwansa na zubar da qwalla saiga little ya dawo daga makaranta sargahe da jikkar littafansa da laptop d'insa daya azo daga saman wuyansa zuwa gefen hannusa na dama ta sauka a qarqashin kafad'arsa, yana ganinsa yayi saurin kauda kansa gefe yana sharar qwalla, murmushi little yayi kafin yaqarasa wajen yana fad'in "kai d'an tsoho mai ran qarfe" da yake hakan yake kiransa dashi saboda yanda ya manyantar da yayi, "meyake damunka d'an tsohona har kake qwalla, fad'amun idan matan can nawane naje nabasu saki uku uku su barmu muhuta."

Dariya baba balarabe yayi saboda yanayin yanda little yayi maganar cikin kwaikwayon yanda 'yan daaga ke magana ya kaimasa d'an naushi a gefen kafad'a yana fad'in.

"Kaganka ko! ALLAH yarabaka da wahala."

Little na dariya yashafa wajen yana cewa.

"Awwwshhh...Ashe kakan nan nawa da sauran qarfinsa, kai! ai sai ka b'allamun kafad'a irin haka kabarni jinya a hannun wud'an can tsofaffin matan naka jinya."

Baba balarabe nata dariya, ba ko shakka zuwan little a gidan alkhairi ne agaresa domin yana rage masa rad'ad'in dake damunsa azuciya, kuma yana d'ebe masa kewar d'an uwansa sosai, little bai bar wajen ba har saida yaga damuwar daya iske qarara a fuskarsa ta b'ace sannan yamiqe had'e da cewa.

"Yawwa d'an tsohona bari naje na watso ruwa sai na d'auko abincina anan inzo inci kana bani labarin jarumin yayan nan naka mai mata d'aya tilo kamar rai."

Jawo carbinsa yayi ya d'aga zai dka masa da sauri yabar wajen yanufi cikin gida yana dariya,

"Ja'irin banza daya gado taqadirancin gyatumarsa."

Yafad'a tare da komawa ya kishingid'a ga pillow d'in dake gefensa ajiye ya cigaba da tunanin rayuwar duniya da kuma qalubalen dake cikinsa.

Ba'a wani jima ba little yadawo d'auke da plate d'in shinkafa da miyar tasha baqin kifi da kuma salad, gefen sa yaje ya zauna tare da fara motsa abincin ya d'ebo a cokali had'e da kai masa abaki yana fadin.

"Ungo naga tunda nashigo kake kallon plate d'in duk yawunka sunbi sun tsinke."

Ba musu baba balarabe yabud'e baki yasa masa abincin yana dariya.

"ALLAH bazan qara maka ba, ashe da gaske zakaci."

"Anfad'a maka nasan gatsene! Yimaza kaci kagama muyi magana dakai, so nake idan ALLAH yakai ranmu gobe karakani kasuwa kaji ko?,

Saida ya had'iye lomar abincin daya saka abaki sannan yace.

"Aikuwa da naji dad'i kamar kasan ina son zagayawa cikin garinnan Amma narasa Wanda zai rakani, su uncle hassan basa zama gida balle naroqesu, gaskiya d'an tsohona naji dad'i sosai dama gobe bamuda lectures sai zuwa qarfe d'aya. sai naje na bud'ikke qeyar idanuwana."

"A'a fa lele (little) nifa ba yawo nace zaka rakani ba, kasuwa nace karakani don haka kama kahutar da kanka zancen d'ebe qeyar idanuwa."

"Kai d'an tsoho, sunan nan nawafa little ne ba lele ba."

"To meye banbanci, ai shima d'in lele ake nufi dashi, saboda haka ni da lele zan kiraka tunda iyayenka suka saka maka sunan da ban iya ba."

Duk sukasa dariya, little nafad'in to ai shikenan, haka sukaci gaba da firarsu cikin tsantsar soyyayya ai in kagani kace shine kakan nasa na ainahi.

Tunda sassafe baba balarabe bayan yagama karyawa yasa uncle Hussain kamar yanda little ke kiransu ya kirawo masa shi, dama tuni yayi shirin wucewa kasuwa shikad'ai yake jira.....
Chapter 105 · 0% Book details