Sashe 12
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"A'a don Allah kujirani ba jinawa zanyi ba yanzu zan dawo." tana gama fad'ar haka bata jira mezasu ceba tanufi wajensa, tana isa inda yake tsaye wajen iccen dalbejiya tace, "malan gani"
"Yawwa Rashida dama akan maganar da mukayi dake jiyane."
"Meyafaru malan" tafad'a had'e da duqar da kanta qasa, murmushi yayi sannan yace
"Babu abunda yafaru, Amma kin tab'a sanarwa da mahaifinki abunda kika fad'a mani?." Saida tagyara zaman jikkar dake saman kafad'arta sannan tace
"Nafad'a amma sai yayimun fad'a sosai tare da gargad'ina akan cewa kada insake inqara yimasa wannan maganar, inajin mahaifiyarsa nayi masa magana amma sai yace tafita batuna ai banida hankali karatu yakamata ace nayi yanzu, ni kuma daga lokacin ban sake yin maganar ba."
Girgiza kai yayi sannan yace ta tafi, koda takoma ta samu har lokacin suna nan a tsaye bakin gate suna jiranta, tambayoyi suka fara jefo mata amma ko kad'an batabi takansu ba tawuce abunta tana dariyarsu,
Anayin sallar la'asar yaje gidansu had'e da yiwa mahaifinta sallama ya fito, dattijo ne sosai amma saboda yanada yalwar wadatar da za'a iyaci sau uku agidansa kowace rana bazaka iya fahimtar hakan ba, kujeru yasa aka kawo masu guda biyu qofar gida, bayan sun zauna suka sake gaisawa sannan malan Idris yayi masa bayanin koshi waye tare da cewa
"Dama nazone akan batun Rashida 'yarka"
"Tofah injin malan bawani shashancin ta aikata ba?." Mahaifin nata yafad'a tare da muskutawa ya gyara zamansa, "ko kad'an baba, kawai yanayin yanda take karatune yasa nace bari na bincika ko akwai wata matsala da kukasan tana fama da ita don asan wane irin taimako yakamata a matsayinmu na malamai mubata awannan gab'ar, saboda idan kalura awud'annan shekarun nata kamata yayi ace yanzu tana makarantar gaba da primary wato secondary amma ace gatanan har yanzu a primary kuma bata fahimtar komai kaga wannan matsalace da yakamata ace anbinciki dalilin da yasa takeyin haka." jinjina kai mahaifin nata yayi tare da fitar da wani iska abakinsa sannan yace, "Hmmm! Malan karabu da wannan yarinyar, babu wata matsalar dake damunta in banda daqiqanci da kuma shashanci, ko kad'an bata son karatu tuntana 'yar qanqanuwarta, haka mukayita fama da ita har takai wud'annan shekarun, hatta aji shiddan da kagata saida nabiya kud'i masuyawa sannan nasamu akaturata saboda tasamu takardar shedar qare primary don insamu inkaita tagaba da ita wato secondary, alokacin tana qarama na d'auka quruciya ce sai yanzune data girma na fahimci cewa abun nata iskancine da rashin maida hankali wajen karatu, ko kad'an ba tason karatun shiyasa takeyin hakan."
"Amma baba ai wannan babbar matsalace da yakamata ace kazaunar da ita katambayeta saboda ataimakawa rayuwarta, duk yaron da kake gani anhaifesa da baseera, kawai rashin samun daidaituwar layin d'aya kamata su haune kansa kaganesu haka, inada yaqini akan da za'a fara magance mata matsalar da kesa ta kasa maida hankali ga karatu to da tabbas za'asha mamakin ganin baiwar da ALLAH yayi mata,"
"Taya zan iya magance mata matsalarta malan bayan bazata yuyu ba?, Shekarunta duka sha biyar aduniya yanzu tashigo shekara ta sha shida, taya zan iya aurar da ita awannan lokacin? Yarinyar da batasan komai ba aduniya ga kuma rashin ilimi da yake d'awainiya da ita, wakake tunanin zai iya karb'ar amanarta idan na damk'a masa?"
"ALLAH shine masani baba, tunda wannan itace matsalarta zaifi kyau ace anyi mata auren da ace anbarta ga tutar babu, ba ilimin kuma babu auren daga qarshema inba ALLAH yakare ba abunda ba'aso yabiyo baya, ni Ina ganin da zakayi hak'uri kayi mata auren da yafi, shekarunta basuda illar da zasu hanata aure saboda ada iyayenmu da shekaru goma sha biyu ake aurar dasu kuma su zauna lafiya har su haifemu ba tare da sunyi wani karatu ba."
Rai b'ace mahaifinnata ya mik'e had'e da cewa, "ni bazanyi hakan ba, domin wancan zamanin daban wannan ma daban saboda haka idan wannan yakawoka tashi katafi don wlh ko bataso dole sai tayi karatu, wayasani ko kune kuke b'ata mana yara kuna juya masu ra'ayi saboda son kanku."
"Subhanallahi, gyara kayanka baba ai bazai zamo sauke muraba ba, a matsayina na malami don na bibiyi matsalar dake jawowa d'alibina rashin fahimtar karatu bazai zama illa ba, kuma wannan ai shawarace nabaka saboda kasamawa 'yarka maslahar rayuwa da kuma kai kanka, idan kana ra'ayi saika d'auka idan Kuma baka ra'ayi kanada damar da zaka ajiyeta, meye abun b'acin rai da har zaikai ga wud'annan kalamai haka!."
"Naji kuma nagode kama hanya katafi."
Mik'ewa malan Idris yayi ransa duk babu dad'i had'e da gyara tsayuwarsa sannan yace
"Zan tafi kayi hak'uri don ALLAH bisa shiga rayuwarka data ahalinka da nayi amma karka manta annabi yace _kullukum ra'in wa kullukum mas'ulun an ra'iyatihi_ damu malamai da kuma ku iyaye dukkaninmu makiyayane kuma dukkaninmu abun tambayane akan abubuwan da aka bamu kiwo, kayiwa ALLAH godiya daya baka 'yar da zata iya fad'a maka gaskiyar abunda ke ranta sab'anin wasu 'ya'yan da saidai iyaye suganesu da abun kunyar da son ransu ne ya jawo hakan." Yana gama fad'a yabar wajen cike da mamakin iyayen dake tafka kuskure irin haka da zai kaisu ga dana sani....
*_ALLAH KAJIK'AN IYAYEN MU_*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶♀️🚶🏻♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻♂️🚶♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️
Page___10💎
Misalin qarfe goma na safe baba yanufi makarantar su Rashida yasa aka aka kirawo masa malan Idris, cikin girmamawa yayi masa sallama tare dasa wata d'aliba ta d'auko masu kujeru guda biyu ta aje masu a k'ark'ashin inuwar wata bishiya dake a tsakiyar compound d'in makarantar, hannu ya basa suka gaisa had'e da cewa "bisimilah baba" yana nuna masa kujerun, tare suka jero har suka iso wajen, saida ya zauna sannan shima yazauna yana nazarin abunda yakawoshi bayan jiya sun rabu baran baran dashi, shiru yabiyo bayan gaisawar tasu kafin can baba ya nisa yace "Ina fatar kaganeni malan?, nine bashar mai takalma wato mahaifin Rashida wanda jiya kaje wurinsa" murmushi malan Idris yayi kafin yace "naganeka baba, ya gida? Ya iyalin?, Injin dai ko lafiya naganka yanzu?"
"Eh lafiya klw alhamdulillah, dama nazone inbaka hak'uri bisa abunda yafaru jiya, sai daga baya dana zauna nayi nazari nafahimci nayi kuskure akan abunda nayi maka, saboda shi gyara kayanka bazai zama sauke muraba ba, zuciyata ta gamsu kuma ta amince da shawararka don haka nazo inbaka hak'uri, don ALLAH kayi hak'uri bisa kausasan kalaman da nayi agareka, kasan duka mai rai ajizine" kansa na aqasa yana murza 'yan yatsun hannunsa ya d'ago yana kallon baba sannan yace
"Karka damu baba, wlh babu komai ai haka rayuwar tagada, wasu mutane nada saurin fahimta da kuma yarda wasu kuma akasin haka, koma dai meye ni babu komai araina nayafe maka, saboda haka kamanta da komai babu wata damuwa, mukan yiwa ALLAH laifi ya yafe mana balle mudaya halitta." Jinjina kai baba yayi yana qara yaba hali irin nasa tare da tunanin ta inda zai b'ara b'ullo masa da d'ayan zancen daya kawoshi, cikin dakewa yayi gyaran murya had'e da cewa "madalla malan naji dad'i sosai kuma nagode, Allah yayi albarka yasa agama lafiya, hak'ik'a samun mutum irinka awannan duniyar da za'ayiwa laifi kuma adawo arok'esa yafuwa kai tsaye yayafe nada wahala, nagode sosai"
"Babu komai ba ai yawuce"
"To bari natashi natafi nasan bazaka rasa ajin da zaka shiga koyarwa ba yanzu"
"Ai yau aji d'ayane agareni baba kuma tun safe nagama dasu saboda first period ne, Bari dai akirawo maka Rashida ko?"
"A'a kyaleta kasan yau juma'a bawani dogon lokaci bane gashi lokacin zuwa masallaci na gabatowa" mik'a masa hannu yayi suka sake gaisawa sannan yajuya zai tafi, har yayi taku biyu sai kuma ya tsaya had'e da juyowa yace
"Emm nace bakaji ba?." Juyowa malan Idris da har yafara tafiya shima yayi had'e da cewa
"Na'am baba, magana kakeyi?."
"Eh, dama nace baka fad'amun sunan kaba da kuma inda kake don da alama bautar qasa takawoka nan!." Saida yayi murmushi sannan yace,
"Sunana Nura idris aliyu, Amma anfi sanina da Idris aliyu saboda da haka abokanan karatuna suke kirana a makaranta shiyasa sunan yabini, ni d'an garin nanne a qauyen bebeji."
"Ikon ALLAH, inada aboki acan kuwa, sunansa malan idi ko kasanshi, muna had'uwane idan munje cin kasuwanne dashi."
Dariya yayi had'e da cewa, "in dai malan idi mai awaki kake nufi toshi d'in ai mahaifina ne."
"Allahu akabar malan dawo mu zauna." Baba yafad'a yana maijin cewa in sha ALLAHU haqarsa zata cimma ruwa, dama shi kuma malan idris kamar yanda yafad'a bayada wani ajin yanzu don haka ya sake dawowa suka zauna, "Aikuwa aminina ne sosai, sharabona dashi tun watanni biyar da suka wuce yacemun zaiyi tafiya to har yanzu kuma bamu sake had'uwa ba, ko har yanzu bai dawo bane?"
"A'a baba yadawo amma a hanyarsa tadawowa yasamu had'ari yanzu haka yananan gida zaune ana jinya yau sauqi gobe ciwo, wannan watansa na hud'u kenan baya zuwa ko ina"
"Subhanallahi, gaske mukajisa shiru kuma gashi ALLAH baisa mukabi bayansa ba muji ko lafiya? Sai satinnan daya wuce muka fara shawarar zuwa nemansa don munzata tafiyar tasa mai dad'ewa ce shiyasa muka jisa shiru, ubangiji ALLAH yabashi lafiya yasa kaffarane, insha ALLAH ranar lahadi munanan tafe mudubashi, bawan ALLAH! malan idi ai mutumen kirkine."
"Amin baba ALLAH ya yarda." Wannan zancen da baba yaji shine yahana yayiwa malan Idris zancen Rashida alokacin amma sosai yasake samun natsuwar mik'a aurenta a hannunsa kodon nagartar mahaifinsa da kuma tasa, sun d'an jima suna hira anan yake sanar dashi yau d'innan in ALLAH yaso zaije can qauyen yadubo mahaifin nasa kuma insha ALLAH zai fad'a masa cewa yana gaisheshi sannan baba yawuce bayan yakarb'i address d'insa.
Bayan yawuce malan Idris yayi dariya tare da cewa "ALLAH mai iko!haka rayuwa take shiyasa akeson kazauna da kowa lafiya, da ace jiya bayyita tausar zuciyarsa ba akan abunda baba yayi masa daba qaramar kunya yau yajiba kasancewarsa abokin mahaifinsa." Sake murmushi yayi sannan yakoma cikin office d'insa