← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 160

Sashe 73

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwashe kayan suka farayi suka wawwanke komai had'e da gyara wajen sannan suka bi bayansa, dama kayan Rashida nacikin mota ba'a fiddo komai ba inba 'yar jikkar baby bag d'in little dake sagale a hannunta ba, shiyasa shikad'ai ta gyara ta sauyawa kaya ita kuma tamaida wud'anda ta cire ajikinta.

Kasancewar akwai 'yar jayawa sosai tsakaninsu yasa koda suka isa anguwar tasu Rashida qarfe tara da rabi nadare har yayi, duk d'okin da Rashida keyi nason zuwa taga iyayen nata suna nufo anguwar taji gabanta yafara fad'uwa, a hankali tafara kirawo sunayen ALLAH tana mai neman tsarinsa daga dukkanin sharrin dake iya cutar da ita ko d'anta.

A daidai bakin qofar gidan ya tsaya da yake akwai wutar nepa da d'aid'aikun mutane dake kai da kawo cikin anguwar, ko gyara tsayuwar motar beyi ba ta b'alle marfinta ta ruga aguje tanufi qofar gidan tana kiran "umma, ummaa."

Turus ta tsaya ganin qofar rufe da kwad'o gabanta na tsananta fad'uwa, juyowa tayi jiki ba k'wari tace.

"Uncle ya naga gidan arufe?." Tana qarasowa inda suke a firgice.

Maqwabcinsu ne taga yazo wucewa zai shiga gidansa kafin dr yace wani abun tabi bayansa da sauri tana fad'in. "Baba, baba na kande!."

Da sauri ya juyo yana kallonta cike da mamaki yaja da baya, ya matuqar tsoratar ganinta awannan lokacin ba zato ba tsammani, matsawa ta sakeyi kusa dashi jikinta na rawa tace, "baba nakande nice fa Rashida, nice Rashidar umma fa, don ALLAH baba kada ka gujeni ka tsaya kafad'amun Ina su umma da baba sukaje, Ina son nagansu baba nakande, Ina matuqar kewarsu, kafad'amun ina ne suka tafi don ALLAH."

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke cike da ta'ajibi yace. "Rashida!"

"Na'am baba nakande."

"Rashida ke ce?"

"Eh baba, Ina su ummata suka tafi?"

Jinjina kai baba nakande ya farayi kafin yafashe da kuka yana fad'in. "Wayyo ALLAH na Rashida sai dai kiyi haquri..."

Bata qarasa jin abunda zai fad'a ba tsabar fargaba da tsoron abunda take tunanin zai fad'a yasata fad'uwa wajen, da gudu su Dr. Suka qaraso wajen Fatima taduqa ta tallabota tana kiran sunanta, Dr nura dake riqe da little ya miqama baba nakande hannu dake kuka yace.

"Assalamu alaikum, baba meye kafad'a mata halama haka?."

"Yaro kaine?" Baba nakande yafad'a yana share hawaye don ya wayesa,

"Eh baba."

"Dama tana hannunka?"

"Eh baba,"

"To meyasa bak sanar da ita komai ba?, Gashi yanzu tun kafin infad'i abunda zan fad'a tasome."

Ganin halin da take ciki yasa Fatima takoma cikin mota ta d'auko gorar ruwan swan d'in dake ciki ta yayyafa mata had'e da shafa matasu ga fuska,

Ahankali Rashida tabud'e idanuwa tare da fashewa da kuka tana fad'in. "Nashiga uku aunty don ALLAH kada kucemun iyayena sun mutu sun barni.."

"Haba Rashida, waya fad'a maki cewa iyayenki sun mutu?, Iyayenki na raye amma bamusan inda suka dosa ba, sun bar garinnan kwata kwata saboda b'atanki.."

Kan baba nakande yarufe baki tuni sukaga Rashida tafara fizge fizge idanuwanta sun kakkafe."

Da sauri Dr yace Fatima takarb'i little da sai faman kuka yakeyi ya tallabi Rashida yasa cikin mota, "baba don ALLAH idan ka amince kazo muje asibiti dakai, nasan bazaka rasa sanin wasu daga cikin dangin taba."

Duk da baba nakande najin tsoron halin mutunen duniya tausayin Rashida yasa bai tsaya tunanin komai ba yashiga motar ya bisu, da gudu Dr nura ke taka motar har suka isa asibiti, cikin gaggawa aka karb'i Rashida kasancewar wajen aikinsa ne ba tare da antsaya wani b'ata lokaci ba, ba'a jima ba likitan daya shiga dubata yafito had'e da tambayar Dr nura cewa dama tanada hawan jini (hypertension)?.

Nan yabashi amsar cewa tana dashi lokacin data haihu amma yayi tsammanin cewa wannan is normal yariga ya wuce,

"Noo..gaskiya ba haka bane, yanzu hakan shine ya tsar mata, sai dai baiyi mata worst sosai ba za'a iya shawo kansa da yardar ALLAH, inaga ko yanzu saboda bata jima da haihuwa bane hakn tafaru, amma in sha ALLAH komai zai dai daita don Babu wata matsala bayan shi, yanzu haka anyi mata allur bacci ne saboda tasamu isashhen hutu"

"Alhamdulillah Dr. Ngd sosai."

"Ba damuwa dr.nura, ALLAH yabata lafiya."

"Amin Dr"

Nuraddeen yafad'a yana kallon baba nakande dake zaune yayi tagumi.....

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

_ASSALAMU ALAIKUM, GAISUWA DA FATAR ALKHAIRAN ALLAH AGAREKU MASIYANA, INA BAKU HAQURU AKAN RASHIN AMSA MAKU IDAN KUNYI COMMENT😅 KUYI HAQURI IN SHA ALLAH DAGA YAU ZAN GYARA, KUNA QORAFI AKAN HAKA ASHE ABUN SON KAINE WATO WANZAM BAKA SO GA KANKA,🤣 YO IDAN HAKAN NA BATA MAKU RAI ME KUKE TUNANI AGARENI NIDA NAZAUNA NAYIMAKU TYPING DON KU NISHA'DU SAI ACE ANWAYI GARI KO THANKS BAZAN SAMU AWAJENKU BA BALLE COMMENT, DUK DA DAI NI NASA KAINA AI KUNSAN BABU DADI DON NA TABBATA KUNA KARANTAWA, SHIYASA NIMA NA SHAREKU DON KUJI IDAN ABUN KWAI DA'DI😂 BUT TUNDA KUN QARA, TO ZAN GYARA KAMAR YANDA NAKEYI ADA, INA FATAR KUMA ZANGA CHANJI AWAJENKU TA HANYAR DA'DA'DAN COMMENT 'DINKU👏 NGD SSAI_

Page___55💎

Tuni baba balarabe da Yaya maryam dasu aunty marwiyya suka isa asibitin cikin daren sanadiyar wayar da baba nakande yayiwa baba balarabe ya sanar dashi zancen dawowar 'yar d'an uwan nasa shi kuma yakira Yaya maryam takira aunty marwiyya ta sanar da ita, kowanensu cike da farinciki yake a zuciyarsa naganin 'yar tasu duk da dai a yanayin da take ciki na nema ya gusar masu da farincikin,

Little kuwa yayi kuka har ya gaji saboda tsabar yunwar da yakeji, goyashi fatima tayi bacci ya d'aukesa shi kuma Dr nura ya koma gida don ya d'auko masu abunda zasu iya buqata kafin gobe don yasan bazasu wuce gobe ba shiyasa koda su baba balarabe suka iso asibitin Fatima kad'ai suka tarar sai baba nakande, ita tawuce dasu d'akin da Rashida take kwance tare da yimasu bayani ataqaice kafin Dr ya iso.

Jugum jugum ya tarar dasu kamar wud'anda k'wai ya fashewa cikin ciki ya wuce ciki ya ajiye kayan dayazo dasu yana kallon gefen da Rashida ke kwance hannunta laqe da drip sun kusa qarewa sannan yajuyo yanufi inda baba balarabe ke zaune shida mijin Yaya maryam,

"Assalamu alaikum." Yafad'a yana miqa masu hannu suka gaggaisa kafin baba nakande yayi masu bayanin cewa shine mutumen da yazo da Rashida, cike da girmamawa suka sake gaishesa kafin ya nemi waje yazauna yana fuskantarsu, matsowa su aunty marwiyya sukayi wajen suma suka gaisa sannan Dr nura yagabatar masu da kanshi ataqaice yaqare maganar yana nuna masu Fatima.

"Waccan kuma iyalina ce."

"Masha ALLAH." Baba balarabe yafad'a sannan yace.

"Ni sunana malan balarabe, qane ga mahaifin ita waccan yarinyar Rashida, ita Kuma wannan sunanta Maryam wato Yaya agaremu nida mahaifin Rashida, wannan qanwar mahaifiyar tace sunanta marwiyya sai kuma shi wannan mijine ga ita yayar tamu wato alhaji ubale."

"Dukkaninmu da kake gani abu d'aya muke babu banbanci, Kuma mukad'aine iyayen Rashida acikin wannan garin, munyi baqin ciki sosai alokacin da muka rasata wanda sanadiyar hakanne ya haifar mana da shiga matsanancin damuwa kala kala har yakai ga su iyayenta da suka haifeta sun kasa jurewa rashinta sunbar garin bayan doguwar jinyar da sukayi a asibiti."

A yanayin bayanin da baba balarabe keyi yasa Dr nura gamsuwa akan cewa su d'in shaiqanta ne na jini don haka yasaki jiki sosai dasu had'e da yimasu bayanin yanda suka tsinceta dalla dallah da irin wahalar da yaronta yasha wanda shine sanadiyar da yasa basu nemesu ba tun wuri, duk da dai yayi qoqarin ganin yasamu iyayenta alokacin Amma ALLAH bai yarda ba, gaba d'ayan su kuka da tausayin halin da Rashida tashiga ita da yaronta suka shigayi suna Mai godewa ALLAH daya miqata ga hannun mutane nagari masu d'imbin karamci da halacci, a daidai lokacin little dake goye a bayan Fatima ya tashi yafara mutsu mutsu yana neman yin kuka Nuraddeen yamiqa mata hannu ta sancikke masa shi, miqasa yayi hannun malan balarabe had'e da cewa.

"Wannan shine abunda ALLAH ya albarkaceta dashi wanda muka rad'a masa suna Nuraddeen bisa yardarta da kuma amincewarta."

Hannun baba balarabe na rawa ya karb'esa yana qare masa kallo don wajen d'auke yake da hasken wutar lantarki kamar rana, tabbas ko ba'a fad'a ba wannan yaron jinin sune don kamarsa sak da d'an uwansa wanda itama mahaifiyar tasa wato Rashida dashi take Kama, wasu zafafan hawayene suka zubo masa yana maijin inama d'an uwansa bai tafi ba yaga irin kyautar da ALLAH yayi masa ta hanyar dawo masa da 'yarsa da kuma jikansa a hannunsa.

Rungume yaron yayi yanaji tamkar d'an uwan nasa ne kafin yaji hannun Yaya maryam data kasa dangana tana qoqarin karb'arsa.

Murmushi tasaki alokaci d'aya hawaye nasake suko mata saman fuska itama lokacin data karb'i yaron tana fad'in.

"ALLAH mun gode maka daka dawo mana da Rashida lafiya daga hannun bayinka salihai masu kyakkyawar zuciya, ya ALLAH ka lullub'esu da tarin ni'imominka tare da yalwataccen farinciki marar yankewa acikin zukatansu da kuma fuskokinsu,"

Taqarsa maganar had'e da d'ago yaron tana sumbatarsa.

"ALLAH ka isarwa mahaifiyarka Nuraddeen ita da iyayenka, yayi maka sakayya kaida mahaifinka ga muguwar kakarka data nemi salwantar maku da rayuwa kida mahaifiyarka, ALLAH..."

Katseta mijin nata malan ubale yayi tahanyar cewa.

"Haba Maryam, menene haka? Keda yakamta kigodewa ALLAH sai ki koma kinayiwa bayinsa mummunar addu'ah? Shin ashe hakan ya kamatan ceki kiyi bayan kinsan ALLAH maiyin sakayyane ga bayinsa wud'anda aka zalunta?."

Shiru tayi had'e da miqawa aunty marwiyya little itama takarb'esa, shafa kansa ta shigayi cike da qaunarsa tana yaba kyawon da ALLAH yayi masa da yanayin jikinsa mai cike da ban sha'awa.

Ganin gaba d'ayansu sun shagala yasa Fatima komawa cikin d'akin da Rashida ke kwance, tana zuwa ta isko tafarka daga allurar baccin da akayi mata lokacin kusan qarfe d'aya saura mintota nadare, da sauri Fatima ta matsa kusa gareta tana jero mata sannu, qoqarin tashi zaune tayi ta dakatar da ita tana fad'in "a'a komawarki ki kwanta maman boy."

Tana dafa kafad'arta had'e da qoqarin maida ita kwance,
Chapter 73 · 0% Book details