← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 160

Sashe 92

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Don haka sukaje suka kama d'aya daga cikin shanun baffa Ali suka sayar batare da yasani ba aka biya salele kud'insa sannan akayi masu tsakani da ita, sauran kud'in kuma baffa yakai masa, baffa Ali sai faman wasar baki yakeyi duk d'aukarsa a banza aka bashi kud'in, Saida yagama murnarsa sannan baffa Usman yafad'a masa yanda aka samu kud'in, wayyo ranar yini baffa Ali yayi yana d'ebe masu albarka tare da zunduma masu zagi, yaran gida duk Wanda ya matsosa saidai yaji ya falla masa mari yana d'ura masa ashar, daga qarshe da yaji rad'ad'in yaqi d'ebe masa yasa muneera d'aki yasata yayita jibgarta yana tsina yana fad'in sai yafidda kud'in naggensa ajikinta.

Baffa Usman dake zaune yana shan fura yayi dariya had'e da cewa

"Oho dai, inma kasheta zakayi ka kashe ai 'yarka ce, ayanda kake marar hankalin nan da tunani babu abunda yakamata ace kayi illa kanunawa duniya cewa nagge tafi 'yarka muneera awajenka, shasha kawai, mudai bazamu doku ba awajenka, ubangiji ALLAH kashiryar mana dakai kada baqincikinka yasa murasa rayukanmu

*BAYAN SHEKARU ASHIRIN DA BIYAR*

Abubuwa da dama sunfaru wud'anda duk wani mumuni ya ishesa d'aukar darasin duniya matuqar babu ta'bewa da 'bata acikin rayuwarsa....

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___67💎

Da gudu Rashida tashiga part d'in ammie tana kiran fatima.

"Aunty, aunty.." da kad'an sunyi karo da ammie dake qoqarin shiga kitchen, d'an ja da baya tayi cike da farinciki kafin tasake matsowa kusa da ita tarungumeta tana fad'in,

"Ammie kitayamu murna auntynah zata haihu."

Murmushi ammie tayi cike da mamakin irin sakewar da Rashida tayi dasu tsakanin jiya da yau sab'anin yanayin da take ganinta abaya, tabbasa iyaye wani jigone da rashinsu kan kawowa 'ya'ya tawaya maigirma arayuwa,

"Iyyeeeeee....to ina tayaku murana kice little yakusa zama big zai samu d'an qane.."

Ko qarasa maganar ammie batayi ba Rashida ta saketa tanufi bedroom d'in ummie don tasan tana ciki tunda bata ganeta a falo ba, girgiza kai ammie tayi tana kallon Dr nura da yabi Rashida da kallo cike da mamakin tsantsar farincikin da yaga tashiga, juyowa yayi suka had'a ido da ammie yace.

"Gaba d'aya ta canza tsakanin jiya da yau, kinga farincikin dake tattare da ita ammie sai kace wacce aa biyawa makka."

"Haba son!, ai dole tayi farinciki, iyaye fa rahamana sosai ga kuma wannan batun data tsinta alokaci d'aya, matuqar ita d'in masoyiyar kuce dole kaga fiye da wannan farincikin atattare da ita, ni yarinyar na burgeni sosai saboda sanin yakamatar ta"

"Ehm..gaskiya hakane, Rashida kam akwai hankali."

Da gudunta taqarasa shiga cikin d'akin tafad'a jikin fatima dake zaune bakin gado ta tallafe fuskarta da tafin hannuwanta guiwowinsu na akan cinainanta.

"Yeeew...auntay na congrat, agaskiya Ina cikin farinciki marar misaltuwa ayau, bayan duk wasu fad'i tashi da suruttan mutane yau ALLAH zai bamu namu d'an, Ina farinciki sosai auntynah ALLAH ya inganta yaraba lafiya."

Duk wannan surutun da Rashida keyi cikin farinciki Babu abunda Fatima keyi in banda kallonta, d'aga mata idanuwa Rashida tayi tana juya hannunta had'e da cewa.

"Me akayi ne aunty?"

Rungumeta tayi tajawo hannunta ta d'ora akan cikinta tana fad'in.

"Maman boy I can't believe so soon zan haifa maki baby, thank you so much for supporting me, haqiqa babu abunda yakai qarfin addu'a tasiri arayuwa, nagode bisa addu'o'in da kika d'orani akai da kuma wud'anda kikeyi mani ba dare ba rana, tabbas anasamun warakar kowace irin matsala tahanyar jajir cewa dayin addu'a, ALLAH ne yace anemi maganin kowace irin matsala amma ana samun warakane bisa qarfin addu'o'inmu agaresa, maman boy kinzamo wani haske acikin rayuwarmu da bazamu tab'a iya mantawa dake ba, yanda kika faranta mana kema ina roqon ALLAH daya faranta maki acikin dukkanin lamurrank, Ina miki albishir da cewa idan ALLAH ya saukeni lafiya zamuyi maki takwara da yardar ALLAH idan aka samu macce, wannan shine tukuicin zamowarki sila wajen tsaida hawayen da muka dad'e suna yimana kwaranya a idanuwa." Taqarasa maganar had'e da riqo hannayen Rashida ta d'ora saman idanuwanta dake fitar da qwalla.

"Kai aunty meye haka kikeyi?, Haba ya isa kidena wud'an maganganun don ALLAH, dukkaninmu ALLAH yakamata mumiqa godiyarmu agaresa, inada tabbin dama lokacin da zaki haihu yayi koda kuwa banbaki wud'an nan addu'o'inba, kawai sun zamo silane bisa wanzuwar qudurar ALLAH agareki, don haka kidena damuwa akan wannan, koda babuni acikin rayuwarku zaki haihu kamar yanda ALLAH ya tsaro, ita addu'a da kike gani ai makami ce babba da idan bawa yariqa duk nisan lokaci zai riskesa da yardar ALLAH."

"Zancen yimani takwara kuwa ALLAH ban yarda ba, sunan yazama local, ni kaina dariyarsa nakeyi wani lokaci."

"Commonnnn..." Fatima tafad'a tare dakai mata d'an duka agefen hannu tanaci gaba da cewa.

"Waya fad'a maki sunanki local name ne, ai sunan Rashida da kike gani sunane mai girma, is drive from the one names of ALLAH dt's (AL-RASHID), Ma'ana mai shiryarwa, asalin sunan ubangijine sai akayi amfani dashi ta hanyar qara harafin (a) yazama (RASHIDA) sai ma'anarsa ta tashi daga Mai shiryarwa zuwa shiryayyiya, don haka kiyi alfahari da sunnki akoda yaushe, domin sunane da bazai kusuba ga wud'anda sukasan asalin ma'anar inda aka ciro sunan, hikimace kansa iyaye nasakawa 'ya'yayensu ire iren wud'annan sunayen saboda fatan ma'anar dake tattare dasu tad'ore akan 'ya'yan masu."

"Laaa...kinsan ALLAH aunty! Hankalina bai tab'a kawomun wannan tunanin araina ba, atak'aice ma mantawa nakeyi da akwai sunan acikin jerin sunayen ALLAH da har zan iya tsinkayo ma'anar dake tattare da sunan nawa, kawai nidai tunda banji ana yayin sakawa jarirai sunan ba to sunan dane agurina, d'ai d'ai kune acikin yaran dake tasowa nake ji da irin wannan sunan, amma yanzu tunda kinfahimtar dani ma'anarsa da inda aka samo asalinsa Ina alfaharin kasantuwa ta da sunanan RASHIDA."

Gyaran murya ammie tayi abkin qofa tana fad'in.

"Agaida qanwar aunty, dama aikoki baban naki yayi shine kikazo kikayi zaunenki?"

"Laaa.... ALLAH na manta ammie, bari naje nafad'a ma uncle."

"Zauna abunki, ai ummanki data shigo tayamu murna tafad'a masa gashican har yafita."

"ALLAH shaf ni namanta sai yanzu bari naje nabashi haquri daga nan nayi masa ALLAH yakiyaye."

Tana gama fad'ar haka tamiqe tafita, ammie tace,

"Kinga mutuniyarki tasaki jikinta sosai yanzu ko?"

"Eh wlh ammie kuma naji dad'in hakan sosai, kinga kafin sutafi zata qara koyamun wasu addu'o'i sosai."

"Wlh ammie tun watan da kika aikamun da wannan ganyen guava kikace mudinga sakawa cikin ruwan tea muna tafasawa muna sha kafin muci komai da safe tun alokacin nafara jin canji da kaina ajikina, ranar muna zaune nida ita sai take cemun akwai wasu addu'o'i acikin alqaur'ani da yakamata na dingayi wud'an annabawan ALLAH sukayi da bai basu haihuwa ba kuma daga baya yabasu, hakan zai taimaka wajen sanya maganin duk da nake amfani dashi yayi tasiri ajikina sosai saboda qarfin addu'a, ammie kamar da wasa ta nunnuna manisu acikin alqur'ani nafarayi, yanzu kimanin watanni biyar inyinsu kenan sai gashi cikin yardar ALLAH ijaba tasauka, tabbas ammie ilimi nada dad'i aduniya kuma yawane dashi da bazaya tab'a qarewa ba sai randa bawa yakoma ga mahaliccinsa, Kuma duk yanda kake taqama dashi sai kaga wanda yafika shi."

"Dama hakane 'yata, koda kuwa wanda baikai darajarka bane ko kuma yafika zakaga yasan wani abun dakai baka sani ba, duk da nasan wasu daga cikin addu'o'in 'yata kifad'a mani sauran naji domin inada wata qawa yanzu kusan shekaru talatin kenan bta haihu ba, kuma tana matuqar son haihuwar kamar taqwato, babu gwaje gwajen da batayi ba, qasashen waje kuwa sunje ba iyaka amma har yau ba'a dace ba, kuma duk da hakan bata gaji ba har yanzu tana kan neman magani cike dasa ran wata rana zata dace, zanji matuqar dad'i idan tasamu irin wannan farincikin da ayau muke ciki kuma hakn zaisa nayi alfaharin tarayyata da ita nahar abada."

"Ai kuwa ammie bari nafad'a maki don gab d'aya nahardace su akai, ba ita kad'ai ba, ina fatar duk wanda kecikin irin wannan matsalar ya amfana dasu domin samun waraka kusa kusa matuqar zai dage dayinsu cike da yaqinin ALLAH zai amsa masa."

"To bara nad'auko biro da takarda narubuta 'yata, kinsan qwaqwalwar taku da tamu yanzu ba d'aiba."

Takarda ammie ta d'auko Fatima tafara karanto mata addu'o'in daki daki kamar haka.

( _Rabbi laatazarni fardan wa'anta khairul warithiyn,_)
( _Rabbana hablana min azwajina, wazurriyaatina, qurrata a'ayunin, waja'alna lil muttaqina imama_)
( _Lillahi mulkussamawati wal'ardi, yakhluqu maa yasha'u, yahabu liman yashaa'u inasan, wayahabu liman yashaa'uzxukur.._)
( _Rabbi habliey minladunka zurriyatan d'ayyibatan, innaka sami'uddu'ah_)
( _Wa'inni khiftul mawaliya minw waraa'i wakanatimra'atiy aaqiran fahabliey minlladunka waliyya_.)
( _wayumdidkum bi amwalin wabanieyn.._)
( _wamaa tahmilu min unsaa wala tada'u illa bi ilmihi.._)
( _izhaa qada amraan fa'innama yaqulu lahu kun fayakuun.._)
( _qala kazalika qala rabbuka huwa alayya hayyinun waqad khalaqtuka min qablu walam taku shai'a_)
( _Yaa zakariyya Inna nubashshiruka bigulaminismuhu yahya lam naj'allahu min qablu samiyya_)
( _Rabbi habli minasswalihieyyn_).

'Dago kai ammie tayi had'e da cewa. "'yatah har yanzu addu'o'in basu qareba, naga har nacika takardar nan.?" Saida Fatima tayi dariya sannan tace.

"Dayawa ko ammie?, Ai dama mai bid'a dole sai ya daure, balle ace d'an mutum kake so ai Dole sai an nace kuma anjajirce kafin akai ga gaci, ni ada nake ganin yawan addu'o'in amma daga baya da ALLAH yataimakeni na haddace wasu wasu kuma ina dubawa ga takardar dat rubuta mani wallahi sai nadena jin wahalarsu, kinsan ammie abun sa kaine, idan kad'auka da sauqi sai yazo maka cikin sauqi, duk yawannan nasu da kike gani idan natashi da daddare nayi raka'a biyu na sallame nakan maimaitasu fiye da sau goma wani lokacin kuma nakanyi ko sau d'ayane bayan nayi istigfari da washi zuwa ga ubangiji sannan nayiwa annabi salati tare dayiwa ALLAH godiya bisa wasu ni'imomin da yayi mana nadaban. Idan na kammala sai nakoma bacci, wani lokacin tare ma dashi mukeyi gaba d'aya idan anyi sallar asuba rana tafito sannan mukoma bacci, wani lokacin ammie ko sallarma bamayi, arwala kad'ai mukeyi muzauna muna bitar addu'o'in har bacci yana d'an fizgarmu wani lokaci."
Chapter 92 · 0% Book details