← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 160

Sashe 10

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai tsaye gida ya nufa, yana shiga ya hangosu uncle h tare da Abba rik'e da little hassan zaune saman wasu kujeru dake can gefe cikin wata 'yar rumfa, parking yayi sannan yafito cikin motar yanufi inda suke ya gaishesu sannan ya sanar dasu zancen Dr. N.I da batun zuwansa anjima, aikuwa nan mahaifinsa ya titsesa da tambayoyin a ina yasanshi?, waya sanar dashi cewa cikakken likitane da har zai kwashi jiki yaje wajensa bayan bashida tabbacin cewa shid'in likitan k'wak'walwane ko akasin haka, nan yaciro compliment card d'in daya basa ya mik'a masu, sosai Abba yaji dad'i kuma ya amince Dr yazo saboda ahalin yanzu ko qanqanen yaro yakawo masa magani ko kuma wanda zaiba 'yarsa magani tawarke zai karb'esa hannu biyu matuqar ya tabbatar da nagartarsa balle d'an gida da bazaya tab'a cutar da ita ba...

*_WAI WAYE (TUSHEN LABARI)_*
_WAYE ABU SUMAYYA_ 'Dah ne tilo awajen mahaifinsa malan Idris Aliyu, ya had'u da mahaifiyarsa awani k'auye da ake kira k'auyen yarimawa dake cikin garin kano alokacin an turasa makarantarsu wajen koyarwa, kasancewar shi mutumne da baya son ganin anbar d'alibinsa ko d'aya abaya ta fannin karatu yasashi maida hankali gaba d'aya wajenta saboda rashin son karatu, Rashida Basharu shine sunan mahaifiyarsa takasance batason karatu ko kad'an tun tana 'yar qanqanuwa har takai 'yar kimanin shekaru goma sha biyar Amma babu abunda yacanza, tsabar repeating d'in da akeyi mata yasahar awud'annan shekarun nata take a matakin aji biyar primary shima d'in daqyar da sud'in goshi akasamu takaisa, social studies shine darasin da take d'aukarsu kuma gwargwado d'alibban nasa suna fahimta inbanda Rashida da akoda yaushe batada wajen zama irin kujerar baya tana sharar baccinta, yafahimci hakanne ta dalilin yawan tambayoyin da yakeyiwa d'alibansa kuma suna bashi amsa daidai gwargwado amma ita saida tazuba masa idanuwa, gashi kusan tafi duka d'aliban ajin be nasu girma, hakan yasa ranar da abun ya fara bashi haushi ya maidota sit d'in gaba inda monitor d'insu yakeyi, cikin b'acin rai dajin takaici yace da ita "as from today this is your sit, I don't wanna be see you sitting back again you here me ko?." yaqarasa maganar cike da fad'a tare da rik'e kunnensa d'aya alamar jamata kunne, Rashida da batasan komai yafad'a ba tana ganin yariqe kunne da sauri tamik'e takama kunnuwanta cike da tsoronsa saboda ganin yanda ya d'aure fuska, gaba d'aya 'yan ajin suka sa dariya har dashi, saida yayi mai isarsa sannan yajuya yabar ajin dama period d'insa yaqare, tana ganin haka ta d'ago kanta had'e da cewa

"Malan in tashi?" Juyowa yayi had'e da cewa,

"Dama ai bani na saki ba ke kikasa kanki, don haka zaki iya tashi idan kin gaji."

"Malan kaifa naga kayi mani na kurmaye kace nakama kunnuwa na." Dariya yayi sannan ya girgiza kai had'e da cewa monitansu "na'ima tashi kifad'a mata abunda nace." Ai kuwa na'ima cikin irin zaqewa d'innan tamik'e tana fad'in "cewa yayi daga yau nan shine mazauninki baya son yakoma ganin kin zauna abaya kiji ko?" da sauri rashida ta d'aga kai tana fad'in "yes" suka sake kwashe mata da dariya hadda monitor d'insu dake yimata gwalo,

"Keep quiet" yafad'a in a serious tone kafin nan kowanensu yakama bakinsa, harara ya maka mata had'e da cewa, "shemless thing to you" washe baki tayi had'e da cewa "thank you sir" cike da jin haushi yabar wajen yana tunanin ta ina zai fara saitata akan layi.

Duk iya dubarar daya kamata yayi wajen ganin itama tamaida hankali wajen fahimtar karatu kamar sauran d'aliban yabi amma abun ya cutara, yabi mata tahanyar yawan yimata tambayoyi ko zataji haushi tamaida hankali amma taqi, yayi zaunar da ita yakoya mata ita kad'ai shima ta gagara fahimta, hakan yasa aka kirawo masa ita a office d'insa don ba qaramin tausayawa rayiwarta yakeyi ba, bayan tazo tagaishesa ya amsa cikin natsuwa sannan yace,

"Rashida meyake damunki" shiru tayi har saida ya sake cemata, "meyasa kike son wahalar da mahaifinki bakyason karatu?" Cikin amsar da baiyi be tsammanin jinta daga bakin taba yaji tace, "Malan ni bana sone kuma bana ganewa shiyasa."

"A'a Rashida baki sawa ranki zaki gane bane, Amma inada yaqini akan idan kika jajirce Kuma kika maida hankali da SANNU SANNU zaki iya."

"Bazan iya ba malan."

"Saboda me kikace haka?."

"Saboda aure nake so malan!"

Bata qarasa rufe baki ba yayi saurin zamewa daga riqe da fuskansa da yake da hannu ya tokare ga bencin dake gabansa yana mamaki, yajima bai sake cemata komai ba yana nazarin kalamanta masu ban al-ajabi har bayan wasu mintota kafin yace,

"Amma Rashida kinsan meye aure kuwa, kinsan illar dake cikin jahilci da rashin ilimi acikin rayuwar d'an adam da kika zab'awa kanki shi?."

"A'a ko d'aya, Amma nidai kawai natsinci rayuwata abisa turbar son aure, wannan kawai shine dalilina."

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke sannan yace, "Shikenan tashi kitafi, ALLAH yakyauta yazab'a mana mafi alkhairi?."

"Amin malan" ta amsa masa sannan tamik'e zata fita, har takai bakin qofa ya tsaida ita had'e da cewa "menene cikakke sunan mahaifinki Kuma awace anguwa kuke da zama?"

"Sunansa malan bashar mai takalma, anan anguwar muke kusa ga masallacin juma'a dake nan gefen makarantar nan." Jinjina mata kai yayi sannn ita Kuma tafita abunta hankali kwance....

_don Allah kutayani turawa a groups, gaba d'aya nayi missing nawa kafin komai yayi settling up_👏🏻

*_ALLAH KAJIK'AN IYAYEN MU👏🏻😭_*
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___9💎

Yana barin wajen saiga Rashida tafito zataje islamiya, kallo d'aya tayiwa mahaifin nata dake faman fad'a yana suruttai ta d'auke kai saboda sanin halinsa, ta gabansa tabi zata wuce ya daka mata tsawa yana fad'in, "shashashar yarinyar zo nan." dawowa tayi agabansa ta durqusa kanta sunkuye ak'asa yaci gaba da cewa, "wane d'an iskan malamine kika turomun har gida ya titseni yana nema yafad'a mani maganganu akanki." Cikin rashin sani tace, "malami kuma baba?, Wlh ni ban turo maka kowa ba." Aharzuqe yayo kanta yana fad'in "wato baki san ko waye ba ko? Maza shiga cikin gida idan jikinki yafad'a maki zakiyi bayani daqiqiyar yarinya kawai da batasan abunda takeyi ba."

"Baba makarantar islamiya zanje fa." Tafad'a tana turo baki had'e da ja baya daga durqushen da take, ganin yayo kanta yasa ta tashi tanufi cikin gida da gudu, bayanta yabi yana cigaba da fad'an har ya shiga cikin gidan, hangota yayi tab'uya abayan mahaifiyarta dake shara tsakar gida tana fad'in, "don ALLAH Baba kayi hak'uri ni bansan kowaye ba."

"Koma waye shi ni bai isa ya canjamun ra'ayi ba, karatune sai kinyi ko bakyaso har gaba da secondary in Sha ALLAH, don haka idan zaki dage kimaida hankali kiyi karatu ki dage donni bazan aurar dake yanzu ba har sai kin kammala degree."

Bubbuga qafa Rashida tafarayi tana kuka yayinda mahaifiyarta da baba sukayi tsaye suna kallon ikon ALLAH cike da mamakin wai meyake damun tane da gaba d'aya ta zubar da kunyar da aka san 'ya mace da ita agabansu tana kukan aure take so, wani irin takaici ne yarufe baba ya karb'e tsintsiyar dake hannun mahaifiyar tata yafara zabga mata jiki tasa ihu tana tsalle tsalle tana fad'in, "wayyo baba kayi hak'uri, ni ban turo kowa ba wlh, malan Idris kad'ai ne ya tambayeni a ina ne gidanmu na fad'a masa amma daga haka bance masa komai ba, wayyo umma kice yadena dukana da tsintsiya fa babu kyau" kad'an yarage ita da baba suyi dariyaganin yanda take tsalle kabar d'an biri, cikin gimtsewa baba yace "Ai k'wanda nadukeki da ita ko kyabar wannan zancen banzar da kikeyi kinatsu kiyi karatu."

"Ni bana son karatun nan baba wlh..." Bata qarasa ba umma tayo kanta da sauri tarufe mata baki gudun kada tajawo mata abun fad'i a makwabta, jefarda tsintsiyar baba yayi yafice gidan yana wani huttai sai kace namijin zaki yabar umma da ita tana yimata fad'a.

"Haba Rashida! Haba Rashida! wannan abu dame yayi kama, don ALLAH meyasa bazaki natsu kiyiwa kanki fad'aba, yanzu meye illar mahaifinki don yace kiyi karatu?, 'yafa mace kike kuma haihuwa zakiyi, da wane ilimin kikeso kiyiwa naki yaran tarbiya idan har bakiyi karatu yanzu ba?." Ita dai banda dudduba jikinta da shacin tsintsiya duk yabi yakwanta mata babu abunda takeyi, asalima ba sauraren umma take yiba balle tasamu amsoshin tambayar da take yimata, "umma dubi yanda baba ya fasamun jiki da tsintsiyar nan bacin yasan duka da ita babu kyau?" Tafad'a hawaye kwance a fuskarta tana kallon umma, tsabar takaici yasa umma mik'ewa had'e da zungureta tabar d'akin tana fad'in, "ai shikenan ke kika sani tunda bakisan ciwon kanki ba sai kije kiyi abunda kike so, ana yimaki magana don kin raina wayon mutane kin maidani mahaukaciya nakiyi kikeyi, in akwai abunda yafi aure kije kiyi idan kina iyawa, shidai ilimi da kike gani garkuwane acikin kowace irin rayuwa tad'an adam, wanda kuma duk baya dashi babu banbanci tsakaninsa da dabba." Acan cikin d'aki Rashida tace

"Haba umma, haba umma dabba fa kikace, ALLAH dai yatsareni,"

"Eh dabba mana, meye banbancin tunda bazai iya fahimtar duk abunda rayuwa take ciki ba balle ya banbance tsakanin baqi da fari acikin al'ummar dake zagaye dashi, matuk'ar baki sauka akan dokin naqin da kika hauba kika natsu kikayi karatu to tabbas kema d'in bakida banbanci da wannan akuyar da kike gani d'aure" tak'arasa maganar tana juyawa akuyar k'asarin dake gabanta, d'ago kan da zatayi taga Rashida tsaye agefen k'ofar d'akin kumbure da fuska tak'urawa akuyar idanuwa, harara ta cillama ta sannan tace, "ki kalleta dakyau kigani k'ilan har saita fiki gata saboda ita babu mai takura mata kuma dole abata abinci taci batare da zagi ko duka da tsangwama ba Amma kefa? Wayasan me gobenki zata haifar maki."
Chapter 10 · 0% Book details