← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 160

Sashe 97

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dady ne yatambayi umma ko lafiya yaga tayi tsaki, tace kabarni da yarinyarnan marar kunya wai ni take fad'awa na kunna tv tashar BBC ana fira da mijinta inba tsabar rashin ta ido ba sai kace mijin nata yadamu da itane, dariya yayi tare da matsawa ya d'auki remote d'in tv dake kunne yana fad'in, to meye abun kunya aciki, idan bata fad'a maki ba wa kikeso tafad'awa?, ko Qaryane tafad'a shid'in ba mijinta bane? yaqare maganar daidai lokacin da yakamo tashar BBC, juyawa tayi zatabar wajen don batasonma ganinsa gaba d'aya dady yariqo hannunta had'e da cewa don ALLAH tsaya suji ko zasu samu wata hujja acikin firar da akeyi dashi wacce tahanasa dawowa, dama tuni ita umma tafara jin haushinsa tun lokacin da suka tsinci labarin cewa yace bazai dawo qasar ba yafiso yayi zamansa acan, shene abun yaqona mata rai har take ganin kamar yayine don yacutar mata da yarinya data kafe kai da qafa saishi duk da yashafe shekaru masu yawa acan batare daya tab'a tunanin waiwayo taba.

Babu yanda ta iya dole suka zauna suna kallon fira.

Gaba d'aya b'angaroran biyu sun shagala da irin firar da akeyi dashi har zuwa lokacin da ake tambayarsa dalilin daya hanasa komawa qasarsa yabada gudun mawarsa duk da zamowar gwamnatin qasarce ta d'auki nauyin karatunsa da komai nasa har zuwa lokacin daya kammala, yajima shiru yana tunanin amsar da zai bayar amma daga qarshe yace bayada wani dalili, kawai yafi sha'awar yayi zaunensa acan ne, da aka sake tambayarsa cewa ko yayi hakanne saboda kud'in da can qasar za'a bashi anan qasar baza'a tab'a iya bashi koda makamancinsu bane amma bud'ar bakinsa sai cewa yayi koda qasar bazata biyashi ko sisi ba yafiso ya zauna acan, shi kawai baisan abunda yasa hakanba amma yafi son zama acan har iya qarshen rayuwarsa fiye da yakoma qasarsa.

Tirqashi! Nan take Rashida taji wani dimmmm! akanta tanajin gaba d'aya duniyar tayi mata nauyi saboda maganganun da taji suna fitowa daga bakin wanda zuciyarta tagama bashi aminci da yarda, d'ago kai tayi tana kallon irin yanda yake b'ata rai da nuna damuwarsa qarara afuska adaidai wannan gab'ar wanda farkon fara firar dashi ba haka yake ba duk da akwai sauyesuyen da tagani atattare dashi alokacin na rashin walwala da sakin fuska da ada Bata sanshi daau ba, amma da akazo daidai wannan gab'ar sai taga sauyin yasake lunkuwa atattare dashi, nan take jikinta yayi sanyi tashiga jerowa kanta tambayoyi akan me hakan kalamansa ke nufi?, shin ko yamanta da ita ne?, meye ma'anar zai zauna acan har abada?, Shin a Ina ya ajiye auren nasu?, Idan kuma zancensa ya tabbata meye makomarta?, Meye makomar rayuwarta?, wane hali zata kasance aciki?.

Kafin ta lalubo amsar wud'annan tambayoyin sai taji ansake jefo mata wata tambayar da tayi daidai da d'ai daga cikin tambayoyin da tayiwa kanta, shin kamar yanda kafad'a kafi son kazauna acan qasar nahar abada to ya zancen iyalinka da kuma sauran ahalinka?, Sai daya murza goshinsa da yatsun hannuwansa na tsawon daqiqu biyu sannan ya d'ago kansa idanuwansa sunyi jawur yana kallon wanda keyi masa tambayoyin yace iyali? Ahali?, Kamar ya?,

Abokin firar nasa yayi d'an murmushi yana jujjuyawa akan kujerar da yake zaune akai sannan yace Ina nufin matarka da 'ya'yanka, iyaye harma da 'yan uwa, bud'ar bakinsa ba abunda yace sai iyaye, 'yan uwa? bansani ba, yaqare maganar cikin yanayin ko inkula.

Wata irin razana Rashida tayi had'e da miqewa tana girgiza kai tana ja da baya, tsaye tayi cak lokacin da taji yana cewa mata da 'ya'ya shi bayada ko d'aya bayan ansake jefa masa wata tambayar akansu, durqushewa tayi wajen tare da fashewa da kuka tana fad'in, Kada kayi hakan malamina, iyaye,
mata, 'ya'ya, ahali duka kana dasu, idan har zaka manta dani baici kamanta da iyaye da kuma d'anka da muka rabu ina d'auke dashi, safe, rana, dare soyayyarka bata tab'a fita azuciyata ba, idan kuwa zakayimun halacci ban cancanci kamanta dani ba balle har kafurta babuni acikin rayuwarka gaba d'aya, duk iya shekarunnan narayune da igiyoyin aurenka akaina batare da nadamu da qananan shekaruna ba ina dakon jiran dawowarka agaremu, na b'ata duka lokacina wajen baka yardata da kuma soyayyata amma acikin qananan mintuna gaba d'aya ka rosamunsu.

Wani irin kuka tasaki tare da rugawa tashige d'akinta tasa makulli, adaidai lokacin little Nuraddeen yadawo daga makaranta, ya isko su Dr da gaba d'aya sun kasa motsawa daga inda suke zaune yayi sallama, ganin hawaye daga idanuwan Fatima da tausayin mamansa yasata kuka yasa ya jefar da jikkarsa abakin qofar shigowa falon yazo ya duqa agabanta yana goge mata hawayen tare da tambayarta meyasata kuka, riqo hannunsa tayi tana shafa kansa had'e da kallon tv tana hango kamarsa acikin fuskar Nuraddeen da ake concluding firar da akeyi dashi, tabbas jini jini ne duk da kamannin little gaba d'aya na mahaifiyarsa ne amma akwai na mahaifinsa kad'an atare dashi, ganin tana kallon tv yasa shima yamaida hankalinsa ga tv, qurawa Nuraddeen idanuwa da ake nuno qaton hotonsa had'e dayin d'an taqaitaccen sharhi akan bayanin da yayi cikin firar da akayi dashi, maido kallonsa yayi ga fatima had'e da cewa, wayeshi mama?, Meya samesa naga ana nunosa kina kuka?, Kasa amsa masa tayi saidai Dr nura yace yamaza yaje yacire uniform d'insa yayi wanka sai yazo yaci abinci.

A lokacin little nada shekaru goma sha biyar aduniya kuma yana matakin aji na hud'u a makarantar secondary.

Umma kuwa murmushin da yafi kuka ciwo tayi had'e da kallon dady tace kagani, kawai ita kad'aice ke hauka akansa, gaba d'aya ya manta da ita balle abunda ke cikinta, dafari na d'auka yanda suka nuna damuwa akanta koda tabbaci suka samu akan tamutu bazasu manta da itaba, nayi tunanin son da suka nuna mata zaisa susamu tawayar farinciki atatattare dasu don nuna damuwarsu akai, amma sai gashi cikin wannan yanayin da ake ciki yasamu qwarin guiwar barin qasar, naji ba dad'i lokacin da aka sanar damu amma marigayi yalurar dani na fahimci hakan ba laifi bane, sai gashi akaro nabiyu da ranta bata mutuba sun wofantar da ita kuma nasan cewa dole zasusan cewa anganeta daga wajensu balarabe da sauran mutanen gari, hakan da sukayi shima babu kyautawa aciki, sai kuma gashi anxo mana da labarin yace bazai dawo qasar saba alokacin da tagama sa burin cewa zai dawo zuwa wajensa, shima d'in banji dad'i ba araina don Babu uwar dake burin ta zauna tana kallon 'yarta agabanta kuma da sunan tanada aure musamman yanda ake sheganta mata yaro, amma kazauna ka lurar dani cewa ba lallene abunda aka fad'a yatabbata ba, ka hana zuciyata ta gasgata zancen sai gashi yau agabanka, da kunnuwanka ka gani kuma kaji abunda yafad'a da bakinsa, Wai bayada mata da 'ya'ya gaba d'aya saboda rud'in duniya da abun duniya daya d'ebesa, alhaji shin shima wannan ba gaskiya bane?, shima suruttaine it na mutane kada I gasgata?,

Sau d'aya kabani gamsashiyar amsa amatsayina na uwa kuma macce dake d'auke da zuciya irin ta d'an adam da batada qashi shin yakamata raina yab'aci kuma naji zafi akan wud'annan abubuwan ko kuwa?,

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___72💎

Shiru Dady yayi gaba d'aya yakasa yin magana saboda yanda jikinsa yayi sanyi akan kalaman da Dr Nuraddeen yayi, yajima zaune yana nazarin maganganunsa dana umma yanaso yagano dalilin da zaisa Dr Nuraddeen yayi hakan, amma duk iya nazarinsa da zurfin tunaninsa kasa samun dalili d'aya yayi da yasa ya aikata hakan, abu d'aya zai iya cewa shine kodai k'wakwalwarsa tasamu matsalane ko kuma rud'in duniya, Amma wane irin abune zaisamu aduniya da sukafi iyayensa da iyalansa da sauran 'yan uwansa aduniya, yatabbata dole dai akwai abunda ba daidai ba acikin wannan al-amarin, wanda qoqarin gyarashi izuwa daidai d'in baqaramar wahala zaiyiba, dole koma meye yazamo d'aya daga cikin wud'anda zasu fahimci rad'ad'in da umma keji aranta fiye da yace zaiyi qoqarin fahimtar da ita kuma awannan karon, domin hakan zai saka mata wani shakku arai tayi tunanin kondon bashi yahaifi Rashida ba tunda ranta yariga da yagama b'aci, Saida ya sauke wata irin gwauruwar ajiyar zuciya sannan ya kashe tv had'e da kallon umma dake sharar qwalla da gefen hannunta yafara qoqarin bata maganada kuma kwantar mata da hankali,

A matsayinki na mahaifiya tabbas nasani dole zakiji badad'i bisa abubuwan dake faruwa domin UWA DA 'DA sai ALLAH, ayanayin daya fitar da lafuzzansa babu kyautawa aciki ko kad'an kuma beyi adalci ba, mussamman ga iyayen da suka haifesa, anan yakamata kiyi tunani,abubuwane marasa dad'i kefaruwa akan Rashida kikaji ba dad'i aranki to mekike tunani ga iyayensa da suka haifesa daya nunama duniya baisan komai akansu ba alokacin da akayi masa zancensu, wannan abu mai girmane da akwai buqatar ace anbinciki qwaqwalwarsa da zuciyarsa kafin a amince da kalaman da yayi, anawa tsammanin indai wud'annan maganganu da yayi dagaskenke yakeyi to tabbas yarasa hankalinsa ne, idan kuma da hankalinsa yayisu to rud'in duniya ne kuma zaiyi nadama akai ko yaushene, don haka Ina so kiyima Allah kicire komai aranki uma ki kwantar da hankalinki muje can garin iyayen nasa muji ko meye kefaruwa don asamu maslaha aciki.

Maslaha! Maslaha dadynsu? Wace irin maslaha za'aje nema awurin iyayen da suka cutar da 'yar wasu kuma suka nemi gyara rayuwar nasu d'an don ALLAH yamayar masu da aniyarsu?, ai shi ALLAH baya zalinci kuma abunda duk kayi sai anyi maka, saboda haka babu inda zamuje tunda hatta su kansu yanuna baya buqatarsu balle suyi darajar da zasu iyayin wani abu akansa, umma tafad'a cikin b'acin rai da nuna tsantsar baqincikin daya tarar mata azuciya, ganin haka yasa dady ya d'auki hularsa dake gefenta had'e da cewa ALLAH yasawaqe yabar gidan don yasan duk bayanin da zaiyi mata alokacin bazata fahimceshi ba, asalima zai dad'a qaramata wani rad'ad'ine azuciya idan ya matsa mata, duk da shima wani sashe nazuciyarsa nafad'a masa Nuraddeen yayi kuskure mai girma amma acan qasan zuciyarsa yahanasa gasgata hakan domin shi mutumne mai yawan yiwa mutane uzuri.
Chapter 97 · 0% Book details