← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 160

Sashe 42

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haba Yaya hawwa meyayi zafi haka keda d'anki, ai idan kikayi kuskuren yimasa baki damuwar akanki zata fad'a, don ALLAH da girmansa kiyi hak'uri kibar yaronnan tunda yana son matarsa, yaran zamani da kike gani bad'ai suke dana da ba zaifi kibarsu suyi rayuwarsu yanda sukesu ke Kuma iya naki kibisu da addu'a," Inna Bilkisu tafad'a tana kallon Yaya hawwa cike da girmamawa.

"Bilki."

"Na'am Yaya hawwa."

"Bilki." Yaya hawwa ta sake fad'a akaro nabiyu tana kallonta, itama ta sake amsa mata kamar d'azu.

"Ya isheki haka babu ruwanki da d'ana, kifidda bakinki a wannan maganar saboda ba huruminki bane, ni nahaifi d'ana baruwanki ko yankasa zanyi shishshigin naki ya isa haka kina jina, idan kuwa ba haka ba zan zageki tass awurinnan nayaga maki rigir mutunci ba abunda yadameni, ke kike da abun fad'i agari bani ba don haka bar wajen nan tun wuri kinaji na ko?"

"ALLAH yabaki haquri." Inna Bilkisu tafad'a tare da barin wajen zuciyarta cike da tausayin Nuraddeen, wata irin gud'a Inna ruqayya tasaki had'e da cewa, "su uwar gulma andaiji kunya idan ansanta, sai aja tsomakaran qafafuwa asani inda akayi yau shishshigi baiyi rana ba." Bata tankata ba tawuce abunta Yaya hawwa tajuyo tana kallon gefen da Inna ruqayyace take tace.

"Ai kece babbar uwar gulmar kuma zan dawo ta kanki."
"Kai nadawo gareka zaka saketa ko kafiso sai naga walaqantata agidannan."

"Innar mu don ALLAH kada kirabani da Rashida Ina matuqar sonta."

"Maida son akan waccan mai idanuwa kamar na mujiya koba komai 'yar uwarka ce" Yaya hawwa tafad'a tana nuna muneera dake jingine ajikin k'arfen rumfa ta takure waje d'aya, wani irin shu'umin murmushi Inna ruqayya ta saki tana ayyana abubuwa aranta, cikin katsa tsawa taji tace masa.

"Ka saketa nace.." duqewa yayi agabanta yana fad'in "innar mu kiyi hak'uri bakina bazai iya furta wud'annan kalaman agareta ba."

"Bazaka sake tab'a saina tsine maka?." Tafad'a tana qoqarin bud'e baki ta tsine masa, da gudu Rashida dake lab'e tafito ta durqushe agabanta itama tana hawaye.

"Don ALLAH kada ki rabamu innarmu, kifad'i duk abunda kike so zamuyi amma kada kirabamu ko don albarkacin abunda ke cikina."

Rashida tafad'a tana kuka, wani irin mugun kallo yaya hawwa tabita dashi tana kallon yanayinta da d'an cikin daya taso kad'an ajikinta kafin tace....

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___32💎

Buhun uba mezan gani haka?, Munafukan ALLAH dama cikine dake ake yimani rufa rufa agidan nan? tirqashi to idan tunaninki yabaki cewa wai cikin dake jikinki nada wata kima ko daraja awajena da har zai iya dakatar dani daga qudurina to kinsha qarya, dake har wannan abun dake cikinki bana sonku bana qaunar ganinku, don haka kai kasaketa kaji nafad'a maka kafin raina yab'aci" Yaya hawwa tafad'a cikin zaro idanuwa tana kallon Nuraddeen da izuwa yanzu gaba d'aya qasusuwan jikinsa sunyi sanyi, ga wani irin zazzab'i daya ji yana shirin taso masa, a hankali ya d'ago kai bakinsa na rawa yace. "Innar mu kidubi girman ALLAH kada kirabani da Rashida, wlh zan iya mutu idan kika rabani da ita, nayarda bakya son Rashida amma abunda ke cikinta bai kamata ki k'isa ba saboda jinin kine kuma jinina."
Tana bud'e baki tayi magana taji muryar baffa da tun d'azu yake yaqar zuciyarsa dake Shirin mutuwa ta sanadiyar raunin daya samu tamaidasa marar amfani aduniya, bayan da rayuwarsa ba mutuwa yayi ba cikin qarfin hali da jajircewa da kuma miqa dukkanin yaqininsa ga ALLAH akan zai iya abunda yasawa ransa yafara qoqarin rarrafawa yana dafa bango, addu'a yake maimaitawa azuciyar yana ambaton dukkanin sunayen ALLAH abakinsa yashiga bin bango yana fad'uwa yana tashi, wani azababben ciwo yakeji na qara taso masa tun daga kan qugunsa har zuwa tsakiyar qasan tafin qafafuwansa amma haka yaci gaba da takawa saboda rad'ad'in da yakeji da ciwo azuciyarsa yafi ciwon da yakeji yanzu atattare dashi har ALLAH ya kawosa inda zasu iya ganinsa, fad'uwa yayi zaune zufa na tartsikke masa tako ina ajikinsa yana fitar da lumfashinsa sama sama, ji sukayi cikin d'aga murya baffa yace.

"Karka kuskura kasaki matarka Nuraddeen ko bana raye aduniya, ke kuma d'anki ne bazan hanaki kiyi duk yanda kike so dashi ba amma Ina so kisani aduk lokacin da kikayi nasarar sa Nuraddeen yasaki matarsa to kisani ranar nima babu aure tsakaninmu kije kema na sakeki." Afirgice yaya hawwa ta d'ago kai tana kallonsa jin kalaman dake fitowa daga bakinsa cike da mamaki, shikuwa Nuraddeen duk da babu wani qarfi ajikinsa da gudu yataso yayo wajen mahaifin nasa da shed'arsa kefita sama sama batare daya tsaya fahimtar maganganun dake fita daga bakin saba, fuuuu.. Yaya hawwa tayi tawuce sashenta ranta ab'ace, ko kad'an bata damu da yanayin data gansa ba balle tayi tunanin taya akayi yazo wajen, amma gaba d'aya yara da manya dake gidan sunyi mamakin ganin baffa a wurin batare da kowa ya riqosa ba, kansa suka taru hadda muneera dasu Inna ruqayya ana yimasa sannu duk da Inna ruqayya bakad'an taji zafin bayyanarsa awajen ba saboda yanda ya b'ata mata masu tsarin, Rashida kuwa tunda tajuyo takalli baffa daga durqushen da take shima yana kallonta tayi murmushi lokaci d'aya kuma hawaye na yimata kara kaina a fuska kasa tashi tayi har saida Inna Bilkisu tazo ta riqata ta tashi tana mai godiya ga ALLAH daya hana faruwar abunda Yaya hawwa taso faruwarsa.

Wajen suka nufa lokacin Nuraddeen ya rungume Baffa yana kuka cike da tagwayen farin ciki da suka lullub'e masa zuciya, na farko ganin akaro na biyu ALLAH yasake bawa mahaifinsa damar sake taka qasa da qafafuwansa na biyu kuma yanda ALLAH yakawo masa ginshik'in daya shiga tsakanin hana faruwar rabuwarsa da masoyiyarsa, shi kansa baffan kuka yakeyi Amma nasa na takaici da baqincikin irin matar da ALLAH ya jarabcesa da ita, d'ago kansa yayi yana shafa kan Nuraddeen yace.

"Kayi hak'uri dukkani tsanani yana tare da sauqi, Alhamdulillah wama sha'a fa'ala."

'Dago kai Nuraddeen yayi yana jin wani sanyi azuciyarsa ya kalli Rashida da har lokacin kuka takeyi ya girgiza mata kai alamun tayi shiru tare da sakar mata murmushi, hannu tasa tagoge hawayenta itama tana mayar masa da nata sannan tajuya tashiga sashensu ta d'ebo ruwa a joke, duqowa tayi tana karanta addu'o'in data iya had'e da tofawa tabawa baffa, murmushi yayi yakarb'a ruwan yana saka mata albarka yasha sannan ya miqawa Nuraddeen sauran yace ya shafa masa a qafafuwansa, bayan mintuna kad'an baffa ya gwada qoqarin tashi da sauri Nuraddeen ya miqa hannuwa zai riqosa ya dakatar dashi, su dai mutanen gida duk suna nan tsaye cirko cirko suna kallon ikon ALLAH, duk da baffa najin zugi da zafi atattare dashi hakan bai hanasa gwada miqewar da kansa ba yana cije baki saboda zugi da rad'ad'in da yakeji har ALLAH ya taimakesa ya miqe da kansa, rufe idanuwa Rashida tayi hawayen dake cikin idanuwanta suka samu damar zubowa sannan tabud'e tana fad'in "Alhamdulillahillazi bini'imatihi ta timmusswalihat, ya mujibudda'awat, Alhamdulillah kathiran."

Ihu yaran gidan suka fara suna tsalle ganin yanda baffa yafara tafiya ahankali yana dafa bango batare da anriqasa ba, juyowa Nuraddeen yayi ya rungume Rashida agaban kowa yana fad'in.

"Ke alkhairice arayuwata da kuma ta mahaifina, ya ALLAH kada kabani damar shaqar lumfashi a inda babu habibty d'ina."

Cike da jin kunya Rashida ta notar da kanta qasa tana murmushi tare da d'an turesa daga rungumar daya yimata ta juya tabar wajen cike da farinciki azuciyarta."
Juyawa yayi shima yabi bayan yaran dake biye da baffa suna tafi da ihun murnar ganin ya samu lafiya,

Suna barin wajen inna ruqayya taja wani irin dogon tsaki cike da takaicin Rashidar babu babban baqin cikinta yanzu kamar cikin da tagani ajikinta wanda tamada yaqinin shizai qara zamowa shamaki kuma katangar da zata rugujewa 'yarta samuwar nata farincikin, cike da son muzanta Rashida daidai lokacin da ta aza k'afarta zata shiga sashenta tace "Aikin banza da wofi, zuri'ar 'yan tsibbu da mayu da gani anyo gadon buge bugen qasa."

Tsaye cak Rashida tayi tana sauraren kalaman da take jifarta dasu kafin tashigewarta batare da tajuyo ba balle ta tankata zuciyarta fad'a mata kada ta tab'a damar da kanta don tace mata haka, dama shi d'an adam haka yake duk abunda yake aikatawa sai yayi tsammanin kowama yana yinsa, konkad'an baici ta damar da kanta ba tunda tasan sunan da tayi mata da ita yafi dacewa ba itaba.

Da gudu muneera tabiyo bayan Rashida har zata aza qafarta ta shiga sai tatuno jan kunnen da ya nura yayi mata.

"Rashida" muneera takira sunanta cikin sanyin murya, juyowa tayi tana kallonta, ganin tana son yimata magana amma takasa shigowa tace. "Aunty muneera shigo mana."

"A'a bazan shigo ba ya nura na iskoni sai ya maidani tamkar jaki yasha Kara."

Murmushi Rashida tayi tare da dawowa bakin qofar inda take tsaye tace, "to gani aunty muneera" susar kanta tashigayi kafin tace, "naji Inna tana cemaki wai zuri'ar 'yan tsibbu saboda kinyi wani abu aruwa kinba baffa yasha yawarke har yana tafiya, don ALLAH da gaskene shi kikeyi?" Murmushin da bai kai cikiba Rashida tayi tare da gyara tsayuwarta sannan tace "A'a muneera ba gaskiya bane, ni bana tsibbu kamar yanda Inna ruqayya tafad'a maki balle iyayena ko zuriarmu, Amma muna roqon ALLAHn daya halicci cuta kuma yayi maganinta cike da yaqini kuma ya karb'a mana, adduace nayiwa baffa d'azu don yasamu sauqin rad'ad'in ciwon da yakeji sai aka dace da ijaba ta sauka bayan jimawarsa azaune yana shan magani da kuma amfani da addu'o'i Wanda inada tabbaci akan tasirinsu ne yanzu yazamo silar samun sauqinsa bayan natofa masa addu'a aruwa yasha."

"Laaa ashe Inna qarya takeyi, don Allah Nima zakiyiwa ya nura aruwan yasha sai ya aureni." Muneera tafad'a had'e da matsowa kusa ga Rashidar bayan ta d'an sassauta murya,
Chapter 42 · 0% Book details