← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 160

Sashe 149

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mezai hana idan bakayi qasa da guiwaba wajen zuwa gareta."

Da qarfi Dr yajuyo yana kallon mahaifinsa yace.

"Taya baffa!, Nasan cewa hakan zaiyi mani wuya don babu tantama ayanzu tana aqarqashin inuwar wani. Sanin cewa anganeta bayan tafiyata da nayi yanzu da kuma jin cewa tana raye cikin qoshin lafiya, da damar had'uwa da d'ana data bani kawai ya wadatar basai naje na haddasa mata damuwa ba agidan aurenta, qaddarata kenan arayuwa wataqil rasata da nayi shine hukuncin da ALLAH zai yimun akan abunda na aikata." Ya qarasa maganar yana goge hawayen da suka zubo masa ya ajiye Yaya hawwa gefe tare da miqewa yabar d'akin, qofar part d'in da sukayi zama ya nufa yayi zaune yan kuka tamkar wani qaramin yaro, shikenan yanzu yajawa kansa rasata sanadiyar nisanta kansa da yayi da ita, wannan wace irin rayuwace da akoda yaushe jarabawa mai nauyin gaske ke biye da ita

Kallon little baffa yayi shima ya kallesa sukayi murmushi sannan sukabi bayansa, daidai lokacin baba nusaiba ta shigo fuskarta cike da farinciki taci karo dasu Inna Bilkisu dake tsaitsaye suna jimamain yanayin da Dr yafito ya shiga ciki, nan fa tashiga tambayar Ina Nuraddeen d'insu da akace ya dawo, kafin tabata amsa yayi saurin d'ago kai yana goge qwalla aka shiga gaggaisawa, kan kace me tuni gidan ya cika da masoya da abokanan arziqi na gaskiya da muna fukai ana taya baffa murna, Inna Bilkisu kuwa ba'a magana yanda kikasan ta tashi sama, farincikinta biyu dawowar Dr Nuraddeen da little daya bayyanar mata ita alokacin a matsayin d'ansa, Wanda hakan ba qaramin dad'i yayi mata ba cewa tuni anga Rashida ashe harda abunda ALLAH ya arzuttasu dashi, anan ta zage tana tayasu murna tare da yiwa Dr bayanin kowace baba nusaiba awajensa da kuma 'ya'yanta da suke matsayin qanne agaresa d'aya bayan d'aya, yaji matuqar dad'i sosai kafin yafara tambayar mutanen gidan inda nan aka sanar dashi rasuwar Inna ruqayya da auren muneera, yayi jimamin mutuwar Inna ruqayya sosai tare da nema mata gafara, ad'aya b'angaren kuwa yayiwa muneera murnar aurenta da tayi bata tsaya jiransa ba, ana hakane sai gasu baba balarabe dasu Yaya Maryam sun iso don tuni labari yakai kunnensu saboda kafafen yad'a labarai babu ta inda bai jeba, tsananin farinciki yasa suka kasa haquri suka biyo hanya don tabbatarwa kansu abunda sukaji tare da roqon baffa yafiya bisa laifin da sukayi masa na b'oye masa ganin Rashidar da akayi da kuma nura d'ansa, musaman Yaya Maryam da tafi kowa nadamar hakan don dama tuni su baba balarabe da aunty marwiyya su sun zubar da makaman yaqinsu, tayi kuka sosai tare da nadama akan yanke hukuncin da tayi bisa rashin sani don gaba d'aya taji bayanin da baffa Ali yayi a qafafen yad'a labaran da 'yan jaridun da gidan redio da talevision sukayi.

Murmushi kawi baffa yayi had'e da cewa "babu komai tsarin ALLAH ne duk da dai itama tayi haquri tuni an had'asa da jikansa, kawai ba'a bayyana hakan bane don kada taji har zuwa lokacin da ALLAH zaiyi ikonsa kuma gashi SANNU SANNU ALLAH yakawo lokacin."

Kallon baba balarabe tayi yayi saurin noce kai qasa yana sosa qeyarsa, murmushi tayi had'e da cewa.

"Haqiqa kayi Abu mai kyau, wannan shine banbancin hankali da kuma tunanin dake tsakanin mace da namiji, badon haka ba natabbata da abubuwa marasa dad'i sun faru da yawa, kayi qoqarin riqe zumuncin d'an uwanka bashar ALLAH yajiqansa Kuma ya saka maka da alkhairi."

Sun jima ana fira cikin farinciki da kuma kewar juna da akayi, wanda anan ne Dr Nuraddeen yaji rasuwar mahaifin habibty d'insa tare da tabbacin cewa ashe batayi wani aure ba tun daya tafi, wani irin tausayinta ne ya rufesa tare da qaunarta mai tsanani, wannan wane irin halaccine da karamci tayi masa arayuwa, gaba d'aya ta qarar da quruciyarta azaman jiransa shi kam dame zai ska mata aduniya.

Jan little yayi agefe bayan ya kauda idanuwan mutane ya shiga tambayarsa labarin habibty d'insa wanda sai alokacinne little ya tuna da gaba d'aya baiyi waya da itaba tunda suka iso saboda wayarsa nacan ya baro a can cikin motar da sukayi accident, da sauri yaje ya anso wayar baffa ya daddanna lambobin wayarta yakirata, Rashida dake zaune cikin d'aki lokacin tagama sauraren firar da akayi da Dr Nuraddeen da baffanninsa tasha kuka har tagaji, Saida tasa hannu ta goge hawayen da suka jiqa mata fuska sannan tamiqa hannu ta d'auko wayar had'e da d'agawa, kallon Dr Nuraddeen yayi had'e dayin murmushi sannan yace.

"Assalamu alaikum, gwaggona barka da marece.." cikin muryar dake bayyana mata tsantsar farincikin da yake ciki,

'Dan Jan majina tayi kad'an had'e da goge hancinta ta daidaita muryarta don kar yafahimci tasan wani abun don ta tabbata yasan da komai yanzu matuqar ya isa wajen sannan tace.

"Wa'alaikissalam d'an gidan mamansa, sai yanzu kake kirana?, Ina kashige ne nayita kiran wayarka baka d'aga ba duk kabi ka d'agamun hankali, Saida nakira 'yatah take fad'amun ai kin Isa lafiya amma sau biyu kuna qetare rijiya da baya da baya?"

"Ina tuba gwaggo, wayar nacan acikin motar na manta da ita, wlh kam kingin qiris mukayi."

"To ALLAH ya tsare gaba, su umma ma da dady dasu uncle sunyita kiranka basu samu ba, kayi qoqari ka kirasu duk da nasan bazasu rasa yin waya da batool ba, ALLAH yahutar da gajiya kadai ci abinci ko?"

"Eh gwaggo.sosai ma, ammm gwaggo nace kiriqe waya zanyi maki wani surprised."

Tanajin yafad'i hakan ta kashe wayarta, sake kira yayi ta d'aga yace.

"Gwaggo nazo wajensu baffa ne, kuma na had'u da mah.."

Bai qarasa ba taruntse idanuwa had'e da kashe wayar gaba d'aya ta ajiye tanaci gaba da wani irin kuka data kasa banbance shin na farinciki ne ko akasin haka..

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

_Assalamu alaikum warahmatullahi wabara katuhuun, bakina bazai gaji da gode maku ba tare da miqo gaisuwata had'e da fatan alkhairi agareku ba masoyana, tabbas shi mutum rahamane aduk inda yake, wlh namatuqar jin dad'in kiraye kirayenku ta waya kuna yimani ya jiki da addu'o'in samun sauqi kuma Alhamdulillah naji sauqi indai jikin yabi haka, Ina godiya ga dukkanin wanda yakirani da masu turo saqo through inbox na messages ko na WhatsApp, ngd ngd ngd sosai jaxakumullahu bikhair, bazan manta dakuba wud'anda sukayita turo addu'o'insu ta group musamman 'yan group d'ina na amanata😅wato SANNU SANNU FANS GROUP 1&2 Kuma kun nunan qauna ALLAH yasaka maku da mafi qololuwar alkhairansa duniya da lahira._👏

Page___102💎

Jin wud'annan kalamai nata yasa Fatima dasu Dr da basuma san da tana wajen ba juyowa da qarfi, tashi yaransu dake tare dasu zaune sukayi sukabar falon cikin tausayi Fatima da alokacin da ita har Dr suka tabbatar da cewa mutumen daya gama magana yanzu a tv shi d'inne mijin na Rashida kamar yanda suke tunani tayi had'e da zuwa inda take ta d'agota daga durqushen da take qasa ta dawo saman kujerun da suke zaune ta zaunar da ita zakiyar inda take zaune da Dr sannan cikin sanyi murya yace.

"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah wannan shine abunda yakamata yafara fitowa daga bakinki gwaggon yara, na tabbata cewa zuwan wannan rana zai zamo wani abun farinciki azuciyar da wannan kukan da kikeyi bai isa ya gasgata hakan ba domin nasan kowa akke, a ma'auni mizani na zahiri Nuraddeen bai kyauta maki ba kuma baiyi maki adalci ba, Amma abad'ini abunda ke b'oye bazamu iya yanke hukuncin yayi daidai hakan daya yimaki ba ko baiyi ba, domin bamuda hurumin sanin gaibi sai abunda ke zahiri, ayau d'innan nayi farincikin yanda ubangiji keshirin dunqule abubuwan da suka wawwatsu waje daban daban awaje d'aya, ayau Ina cike da farincikin ganin mahaifin little yadawo qasarsa, inajin wani shauqi da farincikin cewa little zai had'u da mahaifinsa d'aya buge shekaru kusan ashirin da tara bai tab'a ganinsa ba, to idan har ni zanji irin wannan farinciki azuciyata to me ake tsammani ga wud'anda sune mafi kusanci agaresa? Musamman zuciyar data rayu tana d'awainiya da qaunarsa da kuma dakon zuwansa agareta akowane lokaci?, Nasani akwai rad'ad'i sosai kaga wanda kake tsammanin ya aikata maka kuskuren da bazai rasa hujjarsa tayin hakan ba sai kuma kaga yakasa wanke kansa akan wannan kuskuren daya aikata maka alokacin da kake tsammani, Amma akoda yaushe ana son mutum yazamo mai uzuri da kuma bincike idan wani abun yafaru, Ina so kamar yanda zuciyarki tayi masa uzurin rashin dawowarsa to tasake bashi wata damar tahanyar binciko ko meye dalilinsa na aikata hakan, wannan kukan duka bayada amfani kamata yayi mugodewa ALLAH daya nufi sake had'a fuskokinku, don ALLAH da girmansa kiyi haquri karki d'auki wannan abun da zafi haka.

"Haba aunty!, Haba aunty wane irin bincike zan b'ata lokacina dayi bayan yakasa bayyana gaskiyar daya b'oye agaban duniya, ada zuciyata nafad'amun cewa duk lokacin da zai dawo agaremu zai dawone da cikakkiyar hujjar da zata tabbatar mani da abunda zuciyata ke zargi wanda harga ALLAH zan iya yimasa uzuri akai, Amma ga yanda yadawo da kuma irin amsoshin da yake bawa manema labarai gaba d'aya ban yadda dashi ba, asalima tsoro yabani kwata kwata don bayada wata hujjar data wuce masa son duniya da kuma holewa ta zaunar dashi awaccan qasar.

"Subhanallahi, maman little me kike son fad'a haka?"

Dr yafad'a tare da qoqarin gyara zamansa yana kallonta, cikin kukan da gaba d'aya takasa denawa tace.

"Uncle kayi dubi izuwa yanayin rayuwar da yadawo tsunkensa shi kad'ai, a tsawon wud'annan shekarun da yayo ba ahaka yakamata kamilin mutum yadawo ba, atleast mata, 'ya'ya su suka kamata suzamo abokanan rakiyarsa domin suzasu tabbatar da hujjarsa ta zama waccan qasar har na tsawon wud'an nan shekarun, Amma idan basuba bayada wani dalili ko hujja da zata gamsar dani, son kai, son zuciya rud'in duniya da holewa suka d'aine zan yarda cewa sun zaunar dashi awaccan qasar."

Shiru Dr yayi yana nazarin kalamanta kafin can yace da ita.
Chapter 149 · 0% Book details