← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 160

Sashe 88

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh ammie, kawai yanxu baccine ke yawan damuna."

"To may be rankon wanda bakiyi bane kwanakin baya, Ina son take?"

"Yaje tahowa dasu Yaya maryam."

"Au har sun iso? Bari make muqarasa aikin kafin su iso, Rashida kinemi kud'in da zakifa biyamu kafin mugwada maki maigida naga sai warar idanuwa kikeyi kina bid'ar inda zaki hangoshi."

Cike da tsokana ammie tafad'ima rashida haka sannan tafice tana dariya.

Koda su Dr suka iso su ammie na a harabar gida ita da dady suna jiran isowarsu ita kuma umma nacan tagama shishshirya abincin da sukayi tana gyarawa little daya qara wayau yayi kyau sosai, tawai tashiga yimasa tana fad'in.

"Maigida mai raki, d'an Fatima mai kukan yaye, mijin hajiya mai babbar kyauta."

Baba kuwa dake gefe zaune yana kallonsu sai faman dariya yakeyi, shima little d'in dariya yakeyi harda qyaqyatawa riqe da marfin mai yana wasa dashi.

Cike da farinciki su ammie suka tarbesu had'e da yimasu iso zuwa part d'in nata, bin gidan su baba balarabe sukayi da kallo suna jinjina ki had'e da mamakin yanda suka fita daban acikin masu arziqi wajen girmama d'an Adam da kuma karrama shi har suka iso cikin falon, Yaya Maryam kam kusan lumfashinta d'aukewa yaso yayi saboda irin qamshi da sanyin a.c daya bugi fuskarta, ji tayi jiri na neman d'ibarta da sauri tariqe hajia Aisha matar baba balarabe, juyowa tyi takalleta had'e dayin murmushi cikin murya qasa qasa tace.

"Yawwa Yaya riqeni, nima nan jiri d'ibata yakeyi ina neman fad'uwa"

"Bari Aisha! wannan shi ake kira da aljannar duniya, anbasu duniya kuma ga dukkan alama lafira ma zasu samu"

Bayan sun zazzauna ammie taje da kanta ta d'auko masu ruwan swan masu sanyi a tire tana jero masu sannu, bayan ta ajiye masu ruwan takoma ta d'auko wasu had'e da kofuna tanufi d'ayan parlon da dady yaja su baba balarabe, Saida ta ajiyema kowanensu agabansa sannan tanemi d'aya daga cikin kujerun tazauna tana gyara mayafinta dake qoqarin zamewa fuskarta asake.

"Sannunku da zuwa, ya hanya?"

Saida mijin Yaya Maryam ya ajiye cup d'in daya tsiyaya ruwan yasha sannan suka had'a baki shida baba balarabe suna fad'in.

"Yawwa hajia, hanya Alhamdulillah, mun sameku lafiya?."

"Lafiya klw wlh, ya kuka baro mutanen gida."

"Kowa lafiya klw hajia, since agaisheki sosai da d'awainiya ALLAH yasaka da alkhairi."

"ALLAH sarki ai Bakomai yiwa kaine, "
"Hakane gaskiya angode sosai, yau ALLAH yanufa kun ganemu agarinku waccan rangon saurayinnan naku ya taddomu cikin wannan rana saboda rakinsa sai kace ba namiji ba."

"Aikuwa dai ya kyauta tunda gashi yasa anyi zumunci."

"Hakane gaskiya, tofa angode da d'awainiya sosai Ubangiji ALLAH yabiya kuma yasaka maku da mafificin alkhairi."

"Amin ya ALLAH."

Ta amsa masu had'e da miqewa tanufi wajensu Yaya Maryam ta barsu nan tare dasu dady suna qara gaggaisawa.

"Hajiya sannunku fa da hanya, don ALLAH kuyi haquri nabarku zaune ko?" tafad'a lokacin da take qoqarin shigowa inda suke.

"Ai babu komai hajia, ya gida munsameku lafiya."

"Lafiya klw Alhamdulillah."

"Ya 'yan yaye sarakunan raki da jiki, muna zaunenmu yatado damu muda angwayenmu saboda rakinsa."

"To ayi haquri hajia, ba raki bane kewarku ce tayi masa yawa shiyasa shi zazzab'i, gashi kuma tunda kuna son maigidan kun rugo ko kuwa?"

"A'a indai mazan rakine mun barmiki namu sun ishemu, mukam dai albarkacin 'yarmu mukazo gani ba shiba." Yaya Maryam tafad'i hakan tana dariya.

"A'a fa hajia, karfa yazo kugansa kuce baza kubi su alhaji ba ku kunga wurin zama inda maigidanku yake."

Rashida kuwa tunda taji muryar su Yaya maryam take qoqarin fitowa Fatima tariqeta had'e da cewa tabari sugama gaisawa tukuna suma sufita gaishesu.

Muryar ammie sukajiyo tana qwalawa Fatima kira da sauri tamiqe had'e da amsawa sannan tacewa Rashida tazo sutafi.

Tare suka fito da gudu Rashida taruga qiris kad'an ta ture fatima tana fad'in "oyoyo gwaggona nayi kewarki sosai."

Dariya duk suka aza mata Yaya Maryam nafad'in.

"Oh ni maryama ko yaushe Rashida zakiyi hankali."

"Kai gwaggo da hankalina fa, kawai dad'i nakeji naganku, ina su baba?"

"Gasucan awancan d'ayan falon ammie tabata amsa tana mamakin irin sakewar da tayi, amma d'azu gaba d'aya tabi duk ta takura, sai alokacin Rashida ta tuna da ashe ammie nawajen cike dajin kunya tamiqe tanufi inda su baba balarabe suke cike da farinciki.

Murmushi Fatima tayi lokacin da take qarasowa wajen tana girgiza kai tare da duqawa tagaishesu tana yimasu sannu da zuwa.

Bayan sungama gaisawa ammie tace.

"'yata jeki kikira umma tazo takawo masu Nuraddeen, naga matan nan nasa sai hararata sukeyi."

Gaba d'aya sukasa dariya suna fad'in.

"A'a hajia indai wannan maigidan nakine mai kukan yaye mun barmiki kiyita kaya basai yazo ba."

Suna rufe baki umma nashigowa d'auke dashi yana wasarsa cike da gwalamniya, kasancewar taqofar baya tashigo yasa Rashida dake qoqarin fitowa daga wajen su baba balarabe tana dariyar labarin da suke bawa dady nata lokacin da aka yayeta tayi ido biyu dasu, kasancewar bataga fuskar umma daidai ba saboda tajuya tana yimasa wasa should kad'ai tahango gasu ammie a tsakiyarsu tasan bazata rasa ganinta ba yasa tayi saurin sadda kanta qasa, can kamar an tsinkaleta tayi saurin d'ago kanta tunawa da gefen fuskar wacce tagani, turo idanuwa tayi ganin wai ummanta ce agabanta d'auke da little, jitayi lumfashinta na neman d'aukewa da sauri tace.

"Um..um..ummah.." tana nunata da hannu,

Da qarfi umma ta d'ago kai jin muryar 'yarta tilo da bazata tab'a mantawa da ita ba, yayinda gaba d'aya su ammie suka miqe suna kallon abunda ke shirin faruwa,

Ganin umma na neman sandarewa a inda take tasaki little yasa Fatima qarasawa da sauri takarb'esa tana kallon ikon ALLAH,

Rashida da tuni hawayen farinciki suka jiqa mata fuska tafara takowa cikin rashin kuzari jikinta har wata tsima yakeyi cikin rawar murya tana fad'in.

"Um..mata ni..ni..ce Rashida, nice Rashida 'yarki data b'a..b'a.ta."

Kafin taqaraso tuni qafafuwanta suka kasa imata tafad'i qasa tana kukan da babu shakka zata iya cewa na farinciki ne, haka umma gaba d'aya kasa motsawa tayi saboda qafafuwanta da suka yimata nauyi Saida taji su Yaya Maryam sunce.

"Aisha.." atare sannan tasamu wani irin qwarin guiwar qarasawa wajen 'yar tata dake jan qafafuwa tana neman isowa inda take ta rungumeta tana wani irin kuka mai cike da ma'anoni kala kala,

"Ina kika tafi Rashida kika barmu, munyi kuka mun shiga damuwa marar adadin duk ta dalilin rashinki, Ina kika tafi baki nememu ba kika sa gaba d'aya mukabar kowa namu Rashida saboda rad'ad'in rashinki akusa damu?."

Kasa amsawa Rashida tayi sai sake naniqe mahaifiyarta takeyi cikin jiki tanajikamar lumfashinta zai fita saboda tsabar farinciki, daqyar tasamu cikin wata irin murya mai ban tausayi tace.

"Kuyi haquri, kuyu haquri umma, son zuciya da biyan buqatar rayuwa tasa aka rabani daku, akanisantani da farinciki na aka nemi salwantar da rayuwata batare da andubi halin da nake ciki ba, saidai tsananin addu'arku agareni ya kubutar dani ga shiga duk wani irin gararin rayuwa, ya haskakamun dukkanin lamurrana, ya damqani a hannayen da babu son zuciya balle son kai acikin al'amurransu, d'ago kai umma tayi fuskarta jiqe da hawaye tariqe fuskarta tana goge mata hawaye da manyan 'yan yatsunta.

"Kidena kuka 'yata, muyi godiya ga ALLAH daya sake had'a fuskokinmu ba tare da yad'au rayukanmu ba, haqiqa dukkanin bawan da yayi Imani kuma yayi haquri ubangiji bazai tab'a bari ya tozarta ba."

"Hakane umma, nayarda da ALLAH shike jarabta rayuwar bawansa kuma yayi masa mafi qololuwar sakayya alokacin daya maida dukkanin al'amurransa agaresa, nayi kuka mai yawa lokacin dana koma agareku ban taradda kuba, saidai yau dukkanin kukana yaqare umma tunda gani gaku."

Tare suka juya suna fuskantar alqiblah had'e dayin sujudush shukur sannan suka juyo Rashida ta sake rungumeta tana fad'in.

"Ummahhh nayi kewarki"

Murya suka jiyo a bakin qofa ana fad'in,

"Ummanki kad'ai kikayi kewarta bada abbanki ba 'yata?."

juyowa Rashida tayi daqarfi jin muryar mahaifin nata dake tsaye fuskarsa jiqe da k'walla yana takowa izuwa garesu yana bin 'yan uwansa daya gani a tsaitsaye da kuma 'yar tasa tilo da tuni yagama fidda ran cewa zasu sake had'uwa,

"Babaaa..!"

Rashida tafad'a tare da rugowa da gudu tayi tsalle ta hayesa had'e da rungumesa, wani irin sanyi taji aranta da yasa ta runtse idanuwa tsabar jin dad'i hawaye naci gaba da kwaranyo daga cikin idanuwanta.

"Nayi kewarka baba.."

"Kika ce?"

"Nayi matuqar kewarka sosai babana."

Murmushi yayi cike da farinciki yasa hannu ya goge hawayen dake zubowa daga cikin idanuwansa, sake rungumeta yayi sosai tamkar wanda za'a k'wacewa itama tashige jikinsa tanajin wani farinciki marar misaltuwa atattare da ita.

Wannan al'amari da yafaru ba kad'an yasa dukkanin wud'anda ke cikin falon hawaye ba, musamman baba balarabe da Yaya Maryam da sukafi kowa jin dad'in faruwar haka idan aka cire Rashida aciki.

Ganin taqi saukowa daga jikin baba yasa baba balarabe da tuni duk suka hallara afalon jin abunda kefaruwa ya qaraso wajen yad'an tulli bayanta kad'an had'e da cewa.

"To cikamun d'an uwana haka kada kiqarasamun shi."

Lokaci guda duk sukasa dariya kowane nagoge qwallan da suka zubo masa, rungumesa baba balarabe yayi yana fad'in.

"Meyasa d'an uwa?."

Baba daya kasa tsaida hawayen farincikin dake yimasa zarya a fuska yace

"Tsarin alqalamin qaddara d'an uwana." D'agowa baba balarabe yayi had'e da cewa

"Baka kyauta ba ko kad'an kuma kada kasake yin hakan?, ko kamanta cewa mu muna buqatarku idan har ku bakwa buqatarmu da har zaku yanke hukuncin guduwa kubarmu batare dakun fad'a mana inda kuka jeba?"

Duk da shine Yaya akansa hakan bai hanashi bashi haquri ba, Yaya Maryam kuwa koda yanufi wajenta d'an marin fuskarsa tayi hawaye nazubo mata had'e da cewa.

"Zaka sake?" Kafin yabata amsa tasake kaimasa wani d'an marin agefe d'aya tana fad'in.

"Zaka sake guduwa kabarmu.?"

Cikin kukan farincikin irin son da suka nuna masa yace.

"Kiyi haquri Yaya Maryam bazan sake ba." Yasa hannu yagoge mata hawayen farincikin dake kwance a fuskarsa.

Nanfa dady yayi gyaran murya had'e da cewa.

😅 *HOPE YOUR MISSION IS ARCHIVED?*

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___66💎
Chapter 88 · 0% Book details