← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 160

Sashe 89

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasa bacci baba yayi, inbanda juye juye babu abunda yakeyi, da zaran yarufe idanuwansa babu wacce yake tsinkayowa sai Yaya hawwa da suka gani a cikin tv d'azu, tambayar kansa ya shigayi.

Shin meke faruwa da matar aminin nasa kuma surukar 'yarsa?, shin gaskiyane ita d'ince idanuwansu suka gane masu acikin tv ko kuwa?, Idan har gaskiya ne itace meye silar fad'awarta a cikin wannan mummunan halin da gaba d'aya duniya ta shaida shi,

Ganin yakasa samun amsoshin tambayoyinsa ya yanke shawarar isko aminin nashi da shikad'aine zai iya bashi amsarsu, miqewa yayi yafito daga cikin masallacin lokacin qarfe ukku saura kwata yanufi fanfunan dake jikin masallacin yayo arwala sannan yanufi sashensa saboda hasken wutar d'akin daya hango wanda shine ya tabbatar masa da cewa har yanzu su umma basu kwanta ba.

Knocking yayi abakin qofar d'akin Rashida tagwalo idanuwa waje tana kallon umma da gaba d'aya jikinta yayi sanyi akan labarinsu Dr da take bata na rashin haihuwarsu da soyayyar da suke nunawa little Nuraddeen, yanda tayi da idanuwa yaba umma dariya don kana gani kasan tsorone kwance fal a qasan zuciyarta, jin baba na sake bubbuga masu qofar ahankali muryarsa qasa qasa yana fad'in.

"Maman Rashida wace irin firace haka kukeyi har qarfe uku takusa kuna zaune, da haka kutashi kufuskanci ubangiji mana kufad'a masa buqatocinku inaga yafi wannan b'ata daren da kukeyi a banza" Yasa umma saurin cewa.

"To malan dama yanzu nake tunanin haka."

"Yawwa to ai yafi, kutashi."

Baba yafad'a tare da juyawarsa yakoma masallaci yana mai fuskantar ubangijinsa yana mai godiya tare da sake miqa d'imbin buqatunsa agaresa.

Haka ta b'angaren aunty marwiyya tsabar farinciki hadda sadaka tayi lokacin dasu Yaya maryam suka isa gida suka sanar da ita zancen had'uwarsa dasu umma da sukayi acan garin, rawa tadinga kwasa tanayiwa ALLAH godiya, duk da bata san taya had'uwar tasu ta kasance ba itama harda k'walla tayi.

A b'angaren baba balarabe ma bacci yayi yana tunanin ko meye gaskiyar abunda yafaru ga iyalin baffa?, Kenan maganar da d'an uwansa yafad'a masa ba gaskiya bace? Idanko haka ne yatabka babban kuskure abunda yayi masu,

Tsaki ya dingayi naba adadi yana ALLAH waddai da zuciyar data tunzurasa yakasa banbance qarya da gaskiya tsakanin maganganun da su baffa suka fad'a masa da kuma wud'anda d'an uwansu yafad'a masa.

Matsuwa baba yayi safiya tawaye don yad'au alwashin komawa garinsu saboda sanin halin da aminin nasa keciki, a iya saninsa yasan shi da kansa yace masu susa asako yaya hawwa da d'an uwan nasa da kuma matarsa, yana tsoron kada ace garin d'aukar matakine ya jefa iyalin tasa cikin wannan halin.

Tunda akayi sallar asuba baba yagama karanta azkar d'insa ya hau shirye shiryen tafiya, kasancewar dady part d'in ammie yake yasa bayan ya kammala shirinsa yace umma taje ta sanar da ammie yana son magana da dady idan yatashi bacci, yanda yace haka umma tayi sannan tadawo tana goye da little Nuraddeen tace.

"Wai malan lafiya naganeka kamar cikin damuwa? Ga alama ko bacci baka samu kayi ba jiya, Kuma yau tunda sassafe kahau shiri, meke faruwa da kaine kuma Ina zakaje?"

Taqare maganar damuwa kwance a fuskarta, ganin haka yasashi d'an murmusawa had'e da cewa.

"Babu komai maman Rashida, zancen bacci kuwa ai bani kad'aine banyi ba...."

"To naji basai ka qarasa ba, amma ina zakaje? Ko yau zamu koma."

"A'a bana tunanin haka domin idan nace zan koma banyiwa alhaji adalci ba don gaba d'aya amanar sabon shagonsa a hannuna ya damqata, zandai je kano ne Ina son in had'u da alhaji Idris akan abunda muka gani jiya dangane da iyalinsa? Kinga bai kamata ace nagani nayi shiru ba matuqar ita d'ince kamar yanda Rashida tafad'a."

"ALLAH ya kiyaye." Umma tad'an fad'a kamar cikin jin haushi zatabar wajen.

"Dakata mana, Ina Kuma zakije muna magana.?"

"Ai mungama magana tunda kafad'a mani inda zakaje."

"To meya b'ata maki rai aciki maman Rashida naga zakibar wajen rai a b'ace."

"Bakya son natafi ne?"

Shiru tayi batare data tanka saba tana d'an jijjiga little dake mutsu mutsu yana neman tashi, murmushi yayi don yasan dole hakan zata faru, mawuyacin abune ga uwa ta iya manta wanda ya cutar mata da d'a, musamman idan taga ana damuwa da al amarinsa alokacin da shima ya jarabtu sai taga kamar ita annuna rashin so akan nata ne da aka kasa nuna masa haka a lokacin da ake cutar dashi.

Lumfasawa baba yayi had'e da cewa, " kiyi haquri maman Rashida abunda zuciyarki ke tunani ba haka bane, iya sanina matuqar zamuyi koyi da mafificin halitta to bazamu rama cuta da cuta ba domin shi yakan rama cuta da alkhairi ne ga wanda yacutar dashi sannan karki manta da irin d'imbin alkhairin da d'an baiwar ALLAHn nan da mijinta suka yimani, koba komi tunda suka qaunaci 'yarmu sunngama mana komai arayuwa."

"Amma kuma meya biyo baya malan?, Cutarwa da kuma neman salwantar mata da rayuwa, yakamata kafahimci hakan kabarsu suma da tasu jarabawar suji idan akwai dad'i, 'yarmu aka cutar amma rad'ad'in da zafin akanmu yaqare muda muka haifeta, don haka dole suma suji irin wannan zafin alokacin da take cutuwa duk da kuwa basu ke cutuwar ba."

"Ashsha! Kada kibari 'yarki tafiki hankali da tunani, karki manta mu da muka shiga cikin tamu jarabawar ai ba qyalemu sukayi ba, qarfinsu, lokacinsu da kuma kud'insu harma da mutuncinsu duka sunyi amfani dasu wajen nuna mana damuwa akan halin da muke ciki, shine yanzu zakice mu muwofantar dasu saboda sun zamo silar cutuwarmu data 'yarmu?, Kiyi haquri mumanta da abunda yafaru tunda ALLAH ya maido mana da 'yarmu duk da nasan hakan abune mai wahala amma zamu iya matuqar mukaci gama da yawan tuna alkhairansu."

Sosai jikinta yayi sanyi kuma b'acin ran da takeji akansu yad'an rage sosai,

"Shikenan ALLAH yasawaqe yasa kaje lafiya kadawo lafiya."

"Amin ya rabbi, bari naje inaga kiran alhaji ne qilan yafito." yafad'a yana ciro wayarsa dake ruri a gaban aljihu.

Qarasa shiga cikin d'aki tayi shi kuma yanufi sashen ammie.

Sida suka gaisa cikin girmamawa sannan yasanar dashi zancen tafiyar da yake so yayi yau, duk da ko kad'an dady baya son yayi nesa dashi haka yadaure yabashi goyon bayan yin tafiyar tare da ciro dubu goma yamiqa masa yace yayi na mota.

"A'a alhaji da ka barsu wlh, akwai kud'i a hannuna sosai."

"Ai nasani, ka karb'a ni nabaka kaqara, kud'i ai basa yawa ga matafiyi." Karb'a yayi had'e da yimasa godiya sannan yami zaifita, har yakusa kai bakin qofa alhaji ya kirasa had'e da cewa.

"Am..malan bashar me zai hana kabari zuwa jibi sai mutafi tare don zanje sayo kaya, kasan duk kayan namu sunyi qasa.?"

Sosa kai baba yayi had'e da cewa.

"Ai da kabarshi alhaji, so nake yau ko gobe in juyo idan ALLAH ya yardar mana."

"To shikenan ALLAH yakiyaye hanya, dama nafi samun natsuwa idan kana kusa lokacin da zan tafi, don ALLAH ka gaishe mana dasu."

"In sha ALLAH zasuji mungode."

Abakin qofa sukaci karo da Dr nura yana qwalawa ammie da dady kira, kallo d'aya zakayi masa kasan cikin farinciki yake saboda wani annuri dake fita a fuskarsa, d'an sunkuyawa yayi yana sosa k'eya ya gaida baba, fad'ad'a murmushinsa yayi had'e da amsa gaisuwar daya yimasa yana fad'in.

"Agaida likita bokan turai kuna lafiya?.."

Bai qarasa magana ba yaga Fatima na qoqarin shigowa itama tajawo hijab d'in jikinta yarufe mata fuska, ganin yayi tarugo da gudu hango ammie nafitowa tafad'a jikinta tana kuka.

"Subhanallahi.. Dr lafiya?"

Baba yafad'a yana kallon Dr nura da shikam sai faman washe haqora yakeyi, gaba d'aya 34 d'insa sun kasa rufuwa, Saida ya d'an sinne kai qasa had'e da kallon Fatima ta wutsiyar ido sannan yace.

"Baba lafiya klw ku qyaleta kukan dad'i ne takeyi, addu'arku da kuka dad'e kunayi ne ALLAH yakarb'a mana shine fa tunda likita yafad'a take wannan kukan."

"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah..."

Gaba d'aya falon tundaga ammie dake faman rarrashinta har baba da dady suka fad'a atare, sai alokacin Dr yaji wata irin kunya tarufesa da sauri yajuya batare daya qaraso cikin falon ba.

Maida jiki gabas ammie tayi had'e dayin sujada hawayen farin ciki nazubo mata tace.

"Lakal hamdu ala maqadait, walakash shukru ala man a dait, tabarakta ya zaljali wal ikram." Sannan ta tofa tashafe a fuska. Dady kuwa Banda murmushi Babu abunda yakeyi, nan take yaqudurta aransa zai yiwa baba dake tsaye wata kyauta a matsayin godiyarsa ga ALLAH bisa wannan ni'imar daya yimasu duk dako ba itace ta farko ba,

Hajia fareeda wato ammie itace matar dady tafarko kuma uwar gidansa tanada yara uku dashi kuma sune manyan 'yayansa agidan, Dr nura shine babban d'ansa sai kuma qanensa faruq, saurayine Amma zaikai shekara ashirin da bakwai haka, sannan qanwarsu Khadija dake da shekaru ashirin da hud'u, tayi aure bayan shekaru uku da suka wuce bayan ta kammala karatunta a fannin lafiya wato (nursing), kuma ALLAH ya albarkaceta da samun yara biyu Shahid da Shahida idan kaganesu zaka d'auka tagwayene amma ba haka bane saboda haihuwar rurrutsa tayi, tana ilorin acan take aure saboda mijinta soja ne basu fiye zama waje d'aya ba, yau in suna wannan garin to gobe kuma suna waccan garin, wannan dalilin ne yasa dady cewa ba itace ni'ima tafarko da ALLAH yayi masu ba.

Tun daga nan ammie bata sake haihuwa ba kuma hakan bai tab'a damun dady ba, acewarsa sukad'ai idan ALLAH ya raya masa sun isheshi, amma da yake ammie macece mai tsananin alkunya da kuma son mijinta ta tirsasa masa cewa dole sai yaqara aure saboda yasamu qarin zuri'a ita kanta tana sha'awar yara qanana gashi ga dukkan alamu haihuwar ta tsaya mata, don haka tayita rarrashinsa har tasamu ya amince ya auro hajia nafeesa, 'ya ga amaninsa da suka tashi tare ya rasu yabarsu su takwas ga mahaifiyarsu, rashin wadatar da suke ciki don shi sana'ar noma yakeyi, sai gashi ALLAH yamasa rasuwa yasa dady ke tsananin tausaya masu kuma yake taimakonsu sosai, daga nan ammie tabashi shawarar ya auri nafeesar saboda hakan zai qara bashi damar taimakon 'yan uwanta sai gashi tazamo butulu ta hanyar walaqanta duk wani dake tare dashi matuqar bayada arziqi, musamman hajia fareeda data d'auka wata maqiyiyarta aduniya.
Chapter 89 · 0% Book details