Sashe 25
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasancewar akwai 'yar tazara tsakanin garuruwan guda biyu wato qauyen yarimawa da kuma bebeji yasa su baffa suka roqi alfarmar abasu amaryarsu suwuce da ita don tuni suka zo da motocinsu k'waya biyar da za'a d'aukar amaryar, ko kad'an baba bazasu iya yimasu musu b saboda tsananin girmama juna da sukeyi don haka sukace abasu mintuna ashirin za'a fito da amaryar su baffa nata godiya tare da yaba karamcin da suka yimasu...
*_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU👏😭_*
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶♀️🚶🏻♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻♂️🚶♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️
Page___20💎
Bayan sun tafi Inna bilkisu tadawo tare da tsayawa tsakar gidan saitin da matar baffa Ali ke zaune ta rangad'a wata uwar gud'a tana fad'in.
"Alhamdulillah ALLAH kaine abun godiya, ita dai hassada ga mai rabo takice kuma duk hassadar mai hasada bai isa ya canza abunda ALLAH ya qaddaro ba sannan shi son kai baya tab'a kai mutum ga nasara, sannan kuma tabbas shi naka sai naka amma dad'in zama sai bare, yarinya dai tashigo gidan mijinta kuma ko ba'aso dole akirata da matar Nuraddeen, uwar gidansa kuma uwar 'ya'yansa suruka a wannan gida, masu had'e had'e da kuma qulle qulle sai su canza dabara domin ruwa kam ya riga daya qarewa d'an kada..sai ayi sauri acanza dabara, yarinya dai ALLAH ya mallaka mata Nuraddeen a matsayin miji domin shi tariqe tun farko kuma shi zai tayata fad'a su ko 'yan baqinciki sai dai su mutu don nagaba yariga da yayi gaba."
Tana gama fad'ar haka tawuce d'akinta tana jin wani sanyi aranta, koba komai tasamu zuciyarta ta rege nauyin da tayi mata akan maganganun da suka ta cab'a mata ita da Yaya hawwa.
Wani irin mugun ashar matar Baffa Ali ta lailayo mata had'e dayin kukan kura tanufi wajen qofar d'akinta tana rafkar mata gambu.
"Bilki, Bilki, Bilki tsakanina da ALLAH tun wuri ki kama kanki ko in tata maki rashin mutunci, ki kama bakinki kafin inyi maki wankin babban bargo agidannan, yo da kike zancen ruwa ya qarewa d'an kada ai bakiga k'arshen wasan ba, in dai nice ruqayya matar Ali gadanga tunda kika shigarmun hanci wlh saina nasa zaman gidannan ya gagare ki dake har 'yar koron taki da aka kawo, kwad'a yayyiyar banza da wofi anga yarinya masu maiqo shine za'a maqale mata, to daga ke har ita sai nasa kun kuka da kanku."
Tana gama fad'a ta banka gambun qofar da qarfi cike da jin haushin rashin tanka mata da batayi ba tajuya tabar wajen, Yaya hawwa najinsu daga kwancen da take taja tsaki had'e da cewa.
"Sakarkarin banza duk kuyi ku gama zan dawo takanku, don da d'ai d'ai zanyi maganinku acikin gidannan."
Ita dai Rashida tun tana kukan har ta dangana ga ALLAH tayi kwancen tana tunanin wannan sabuwar rayuwar da zata fara a d'aya b'angaren tana sauraren firar dasu salame da kareema keyi, muneera ce tafad'o cikin d'akin ko sallama babu tayi tsaye qiqam tana raba idanuwa batare da takalli wud'anda ke wajen ba da alama itama rashin mutuncin tazoyi saboda yanda take bud'ar hanta, sudai su salame na kallonta basuce da ita uffanba ta rab'a tagefensu tanufi uwar d'akin, kallon kareema salame tayi ta d'auke fuskarta tana kallon muneera dake qoqarin hankad'a labulen ta d'aure fuska had'e da cewa,
"Ke malama Ina zuwa?"
Juyowa tayi cikin ba'acin rai itama had'e da cewa "to sa'idanawa masu barci da ido d'aya Ina ruwanku da inda zani, Ina dai amaryar nan ba 'yar uwarku bace balle kuce zaku hanani shiga"
"Bashi aka tambayeki malama ba, amsa zaki bamu ba rashin kunya ba don kinsan nan gidanta kika zo" kareema tafad'a a tsattsaye, tsaki muneera tayi had'e da kutsawa tashiga cikin d'akin Rashida na kwance saman gado fuskarta lullub'e da mayafin da aka rufo mata tasa hannu ta yayeshi da qarfi, da sauri Rashida tamiqe zaune tana kallon muneera dake riqe da mayafinta data cire, idanuwa muneera ta qura mata tana kallon gashin kanta daya zubo har gadon bayanta sanadiyar jawo mayafin da tayi ribon d'in ya cire, kyakkyawar fuskarta ta qurawa Ida kafin can kamar an tsunkureta ta zabura had'e da cewa,
"Au yihakuri fa na manta ke amarya ce Saida lallab'awa.." mere baki tayi sannan tafara takawa tana qarewa d'akin kallo kafin ta maido hankalinta gareta,
"Dama kece ya nurana keso? kece ya zab'o a matsayin mata bayan yasan Ina qaunarsa, dama kece kika zamo katangar data shiga tsakanina dashi Kuma har kika datsemun duk wani mafarki da kuma burin mallakarsa dana dad'e inayi, kika wargazamun farinciki tare da sani zubar da k'wallah acikin kowane dare?, Hmmm to kinyi kuskure yarinya a wud'annan qananan shekarun naki baki kai matsayin da zaki mallaki ya nura naba kuma na hak'ura, domin na d'au alwashin shid'in mallakina ne ni kad'ai, kid'auka wannan auren jeka nayi kane kukayi saboda dole kirabu dashi ko kina so ko bakyaso, mallakina ne shi Kuma ki kalleni da kyau kigani nice daidai shi saboda nid'in 'yar uwar sace kuma jininsa don haka d'an uwa sai d'an uwa badai bare ba."
Taqarasa maganar tana wani kallon sama da qasa irin ita wayayyiyar nan , sai alokacin Rashida ta d'ago kai cikin mamaki tana qarewa muneera kallo wacce tun shigowarta data kalleta ta aza itama cikin matan gidanne saboda yanda taganta ajeme cikin wata kod'ad'diyar atamfa wacce duk da itama a qauye take bazata iya ko gugar leda da ita ba, sak kamar muneera irinta 'yan matan qauyennan ne da suka jima basuyi aure ba ga wasu uban qassan wuya da suka taso mata fuska cike da jar foda, kallo d'aya zakayi mata kasan cewa ba yarinya bace zata kai shekaru 20 aduniya ga matsalar qauyanci da rashin wayewa da suka taru suka sake jemeta waje d'aya sai kace wacce tashekara aru aru d'in nan, watanni ne tsakaninta dasu kareema wanda hakanne yasa babu wata girmamawa tsakaninta dasu sai reni, shiyasa da sukayi mata magana bata sauraresu ba hakan yasa salame tamiqe taje d'akinsu ta d'auki wayarta takirawo Nuraddeen ta sanar dashi abunda ke faruwa dama yana bakin gida baiyi nisa ba sai gashi ya shigo da sauri, yana shiga kareema na qoqarin shiga uwar d'akin saboda yanda taji tana yab'a mata maganganu da sauri yariqo hannunta yace tawuce, abakin qofar shigowa taci karo da salame tadawo zata shiga tariqe hannunta tana fad'in.
"Muje salame ai yayan yadawo, barta dashi." Wucewarsu d'akin mahaifiyarsa da tagama had'a masu 'yan abubuwan da zata basu tana fad'a suzo suwuce gidajen mazansu dare yayi don har ankira sallar isha'i, nan suka fara bata labarin abunda kefaruwa tace.
"Hmm! ALLAH dai ya kyauta, Amma ni wlh har yarinyar nan tafara bani tausayi, koni nan dana girmeta nesa ba kusa ba ya naqare da matsalar Yaya hawwa da ruqayya da kuma rashin kunyar yaransu inba Nuraddeen da Yusuf ba, sukad'aine nake jin sanyinsu amma kaf gidannan babu wanda keda ragi, sudai iyaye kishi suke dani gashi kowacenmu da mijinta balle ace ai saboda haka, sukuma yaran iyayen ke lalatasu shiyasa Amma banda haka har ina za'ace muneera ta isko matar yayanta tana yimata rashin kunya, zumuncine da yariga ya lalace saidai ALLAH ya kyauta."
"Hakane inna, amma kema da alifinki? Kidena biye masu balle shiga harkarsu, inaji d'azu kin dawo kina maidawa Inna ruqayya da maganganu ai kinga hakan bai dace ba, ka kyale mutum duk abunda zaiyi tunda dai kasan adoke bai isa ya dokeka ba amma saikiyita biye masu ana fitina." Kareema tafad'a ranta a d'an b'ace, shiru Inna Bilkisu tayi tana nazarin kalamanta don tasan gaskiyane tafad'a kawai dai abun da ciwone shiyasa bazaka iya haquraba wataran, muryar salame taji itama tana fad'ar.
"Eh Inna ALLAH gaskiya kareema tafad'a don ALLAH kidena biye masu, kinsan abun fad'i agarinnan baya k'arewa, kuma mu kece mutuncinmu da kimarmu agidajenmu, da wani abun yafaru agidannan akaji dasa bakinki ba zamuji dad'i ba, don ALLAH kiqara haquri dasu wata rana sai labari"
"Shikenan, ALLAH yaganar damu kutashi kutafi" tabasu amsa atak'aice.
Acan sashen Nuraddeen kuwa tsaye yana qoqarin shiga yaji maganganun muneera sun dakar masa kunne a lokacin da take cewa d'an uwa sai d'an uwa badai bare ba da sauri ya qarasa shigi ciki tare da fizgota ya jefota falo yana fad'in "uban waye ya fad'a maki d'an uwa sai d'an uwa, itama yanzu 'yar uwace awajenmu tunda na aurota na kawota a gidan nan don haka maza kifice kibani waje ko in tattaka ki awajennan wawiya kawai da bata iya magana ba" turo baki tayi tana susar kai had'e da cewa,
"Kai ya nura nizaka yiwa walaqanci akan wannan 'yar yarinyar.." kanta yayo da gudu tafita ta tsaya bakin qofar d'akin tana cigaba da fad'in
"Wlh ALLAH ya nura ni bazan yarda ba ai kasan ina sonka sosai shine kaje ka auro wannan abar.." Bata rufe baki ba cikin tak'a biyu ya cimmata a bakin qofar d'akin had'e da sakar mata wani mugun rank'washi akai, ihu ta saka tare da dafe kanta tabar shiyar aguje tana kuka, rumfar d'akinsu ta shige tafad'i qasa tana murje murje da qafafuwa tana wayyo Inna zai kasheni, aguje tafito d'akin tanufi wajenta yanajin haka ya koma Uwar d'akan Rashida na zaune a gefen gado kanta qasa idanuwanta na zubar da hawaye, durqusawa yayi a gabanta tare da tara hannusa hawayen dake neman saukowa daga idanuwanta suka sauka akai, cikin rashin jin dad'in abubuwan da suka faru yace,
"Habibty kuka kikeyi?" Shiru tayi tare dasa hannunta akan hanci taja majina sanna a hankali ta d'ago kai tana kallonsa, ganin yana qoqarin saka idanuwansa acikin nata yasa tayi saurin maida kan qasa, magana yaci gaba dayi cikin tattausan lafuzza,