← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 160

Sashe 63

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba'a sauya tsarin duk wata qaddara da ALLAH yarubutowa bawansa, don haka malan Idris Ina roqonka da kaje kajanye wannan qarar daka kai ta iyalinka da d'an uwanka, yanzu muyi haquri tunda mai faruwa tariga da tafaru bazamu iya canxa komai ba saboda abun da duk akace ya had'a da sammu ko asiri to saidai ayi haquri abisa da addu'a domin itace makarinsa, indai ta b'angarenane malan Idris nayafe masu, _wa'ufawwidu amri ilallah_ inasa tsammanin ko yaushene ubangiji zai sake had'amu da 'yarmu kafin rai yayi halinsa, kaima Nuraddeen kayi haquri, nasan kaima kanada damuwar da dole ta d'ara tamu ko suzo d'ai, amma haqurin da addu'ar su zakayi kaima saboda sune kawai maganin wannan al'amarin." gaba d'aya kasa cewa komai baffa yayi, baisan wane irin karamcine baba take son kashesa dashi ba bayan halaccin daya yimasa na bashi 'yarsa, miqewa yayi yabi hanyar fita har yana harhad'a hanya Wanda da kad'an yafad'i saboda wani irin jiri daya d'ibesa, da sauri Nuraddeen yaje yakamasa, shi kuma baffa Usman tsayawa yayi yana taba su baba haquri tare da tabbatar masu da cewa yanzu haka yau hukuma zataje kaima bokan samame aka mosa kuma da yardar ALLAH za'aganeta.

"Hmmmm!" Kawai aunty marwiyya tafad'a tana jijjiga qafa tana hurar hanta alamun da sake d'innan, russunar da kai baffa Usman yayi agabanta yana kallonta yace, "ayi haquri, tabbas ba dad'i kuma ba'a kyauta maku ba, Amma insha ALLAH za'a bimata haqqinta yanda yakamata."

"A'a Usman Wai banace abar zancen ba, kuje asake bayin ALLAHn nan don giraman ALLAH." Baba yafad'a yana maitabbatar masa da abun har cikin zuciyarsa.

Daidai lokacin Nuraddeen yadawo bayan yakai baba daketa aikin sharar kwallah cikin mota, guiwowinsa ya ajiye qasa agabansu had'e da bud'e baki zaiyi magana amma sai kuka yaci qarfinsa, kallo umma kad'ai da yayi yasa yaji duk guiwowinsa sun sare, qwarin guiwar daya zo da ita yarasa haka kalamn daya tanada don qara basu haquri da nuna masu irin halin da take ciki duk sun kuccema bakinsa, ganin haka yasa wud'anda sukazo tare suka tashi suka fara fita d'aya bayan d'aya suna goge k'walla, a yau sunyi dana sanin sanin Yaya hawwa bisa wannan ta'asa data aikata, yau sun tabbatar da hukuncin da baffa yayi mata ya cancanta da ita koma fiye da haka.

Ganin kukan nasa yai qarewa yasa baba balarabe yace "haba Nuraddeen, kayi haquri muyita addu'a, wannan kukan bayada amfani, kaduba kaga yanda kabi duk ka lalace, karame kayi baqi tamkar ba nuran da muka sani ba, shin idan kai kayi hakan, muda muka haifeta ya kakeso muyi?"

Cikin dasashshiyar murayarsa da bata fita sosai yana sheshshekar kuka yace, "umma, baba, don ALLAH kuyafemun bisa wannan sakaci da nayi, kuyi haquri kuyafemun." Sai alokacin umma tad'aga ta kallesa tace.

"Bakomai Nuraddeen, ba sakacinka ya janyo hakan ba, son zuciyar mahaifiyarka da babu yanda zakayi da ita, banga laifinka ba ko kad'an don duk wanda ya kalleka yasan kana cikin irin yanayin da muke ciki banbancin kawai cine namu ya bayyana afili, amma kai nuqurqusarka yakeyi acikin jiki, tabbas muna kewar rashin Rashida da alhinin inda qaddara takai mana ita, to yazamuyi? Zafa mu iya rasa rayuwarta gaba d'aya koda tana agabanmu ne, basai ta b'ata ba, don haka muyi haquri har zuwa lokacin da ALLAH zai bayyanata kaji ko?."

Kallonta kawai Nuraddeen keyi yana auna girman imaninta da kuma yaqininta ga ubangiji, sai yakeji inama ace tasa mahaifiyar haka take, nasihohi suka shiga yiwa junansu na muhimmancin yarda da qaddara da kuma haquri alokacin jarabawa, inda nan baba balarabe yajawo masu qissar annabi yusuf da mahaifinsa annabi yaqub har qarshe, gaba d'aya sunji sun samu natsuwa aransu amma tsakanin baba da Nuraddeen kowane da abunda yake qisawa aransa don mancewa da zancen b'atan Rashida agaresu abune da bazai tab'a yuyuwa ba.

••• ••• •••
A 'bangaren boka kuwa tuni komai y tsaya masa saboda yanda al'amurransa suka hargitse kuma suka lalace masa, duk wani siddabaru da surqulle da yakeyi yanzu ko yayi basayi, gashi shed'anun aljanun da yake huld'a dasu gaba d'aya sun qone lokacin daya turasu wajen Rashida saboda qarfin addu'o'in data dingayi, kullum cikin tashin hankali yake da fuskantar fushin miyagun iyayen gidansa da suka b'atar dashi suka tab'ar dashi don ko yaushe cikin saukar qur'ani almajiran da baffa yasa suyi masa addu'a suke, shiyasa tun ba'aje ko inaba ALLAH yafara gwada masa ikonsa ta hanyar tarwatsa duk wani laqaninsa na tsafi da Kuma qarfinsa, hatta iri b'acewar da yakeyi ada wacce itake qara qayata masa bokancinsa yanzu ta gagaresa, fitama wahalar yimasa takeyi saboda tsoron abunda kan iyazuwa ya dawo, ga yunwar cikinsa ita kad'ai ta ishesa saboda duka aljannun sundena yimasa hidima, Yauma yana kwance duk ya qanjame ya qara naqashewa akan wacce yake da ita yaji wata irin gumza da qara na nufato 'yar bukkar da take ciki, arazane ya tashi zaune don ya tabbata wannan qarar ta mugun aljaninsa ne daya tura ya hallakar masa da Rashida, da sauri yafito yana waige waige kafin cikin wata irin wahalalliyar murya yaji mugun aljanin nafad'in

"Sunnqonaniiiii, sun halakaniiiii, sun naqasa mani rayuwaaa kuma dole zaann d'au fansaaaa, hnnnnnmmmmmmm" gumza yakeyi sosai irin wacce ke nuna tsantsar wahalar da yake cikinta. Cikin wani irin qamari yariqo boka bargaji da ahalin yanzu bayada qarfi ko ikon ganinsa ya dinga bugasa jikin itatuwa yana jefosa qasa, bai qyalesa ba saida yaga yasome sannan yayi wata irin muguwar qara yana girgiza, so yakeyi ya shiga jikin bokan amma ji yake Sam bazai iya rayuwa ajikin saba, hakan yasa ya quduri zaman jiran dakon biladama nafarko da zaya fara takowa cikin jejin zuwa inda suke don ya d'auki fansa tahanyar shiga jikinsa..

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___48💎

Jiniyar motocin 'yan sanda kawai ketashi aguje saman titi kusan mota uku, gaba d'aya cike suke da zaratan 'yan sanda majiya qarfin da babu alamar tausayi atattare dasu ko misk'ala zarratin, yanayin fuskokinsu kad'ai idan ka kalla zai tabbatar maka da ashirye suke dasu fuskanci kowane irin qalubale ne indai akan aikin da suka fitoyine, motar su inspector najida itace agaba, sai wacce aka d'auko Yaya hawwa tare da wasu 'yan sanda su biyar tana biye dasu a tsakiya sannan ta ukun data biyo bayansu wacce ke d'auke dasu blessing da wasu 'yan sanda su uku abaya, tafe suke yaya hawwa najin wani irin tashin hankali na ziyartota saboda tunawa da yanda takwashe da boka bargaji a wancan karon, Babu babban tashin hankalinta irin kar suje bokan yaqi bayyana tunda b'acewa yakeyi bala'i yaganta a hannun 'yan sandan nan data tabbatar basuda sauran Imani azuciyarsu, idan ko har haka tafaru ta tabbata a wannan karon wannan arniyar mai qirar samudawa kasheta zatayi, tana wannan tunaninne taji ankai mata wani mugun naushi abaki, kufron Jamil ne da ahalin yanzu babu d'igon tausayinta ko kad'an a ransa yana kallonta cike da tsana, Wanda yayi mata hakanne dama don jin motar su inspector najida dake gabansu data tsaya had'e da cewa.

"You stupid maza kifita anzo wajen."

Juyawa tayi cike da fargaba tana kallon bakin titin da suka tsaya tare da waigawa gefe gefe tana kallon cikin dajin, jitayi gabanta yaqire yafad'i da sauri tadafe qirji tana fad'in. "Wayyo ni ALLAH."

Cike da hasala wata 'yar sanda dake cikin motar tare da ita ta izo qeyarta suka fito tana fad'in

"Idiot, bakiyi wayyo ba, yanzune zaki fara, tana fitowa sauran 'yan sandan suma suka firfito bayan motocin nasu sun tsaya suka zagayeta hannunta na d'aure da ankwa, cikin jarumta inspector najida tafara azo qafarta wajen motar kafin ta ida fitowa gaba d'aya fuskarnan tata a d'aure, d'aga kai tayi tana qarewa dajin kallo tun daga farkonsa har zuwa qarshe sannan tajuyo ta maido kallonta ga Yaya hawwa da kanta ke nad'e da bandeji, hakama hannunta and'aure matashi tare da sagalo bandejen da aka d'auresa ga wuyanta, sai qafarta itama duk an nad'e mata yatun da bandeji ga fuskarta da blessing ta bubbuge mata itama duk ta kumbure, gaba d'aya halittarta ta canza kai bazakace Yaya hawwarnan bace mai shegiyar isa da rashin mutunci, ajiyar zuciya tayi sannan tafara takowa zuwa inda suke tsaitsaye har lokacin idanuwanta nakan Yaya hawwa, tana isa da sauri duk suka qame had'e da buga qafa suka sara mata, sunansu tashiga kira d'aya bayan d'aya suna amsawa da qarfi yayinda Yaya hawwa ta sinne kai qasa tana Dana sanin wannan halin data jefa kanta, musamman yanda taga 'yan sanda zagaye da ita, da qarfi taji inspector najida tace.

"Kowa ya shirya acikinku?"

"Yes sir." Suka fad'a atare.

"Duk kankanku a shirye kuke daku bada rayukanku ga yiwa qasarku aiki?"

"Yes sir." Suka sake fad'a atare.

"Ok ina buqatar kowanenku yacire tsoro ya fuskanci wannan aiki da zamuyi mai suna operation ss, ba gudu baja da baya, duk rintsi duk wuya kada wanda yagudu har sai mun kama wannan azzalumin da duk wani dake tare dashi a wannan jejin kunaji ko?"

"Yes sir."

"Kun shirya?."

"Yes sir." Suka sake fad'a atare cikin d'aga murya har lokacin suna a qaqqame, kallonta tayi had'e da yimasu umurni da hannu data shiga gaba su bita abaya. Nan take blessing kamar jira takeyi ta tasa qeyar Yaya hawwa zuwa cikin jejen, tafe yaya hawwa take tana d'ingishi suna biye da ita abaya, Saida sukayi tafiya mai nisa sannan suka soma shiga ainahin cikin dajin da boka bargaji yake, wata irin qara suka jiyo da kururuwar da tasa nan take Yaya hawwa ta d'iba da nakare wani gefen zata koma baya, taqa biyu blessing tayi ta damqota tare da buga mata qasan kututun bindigar dake hannunta tafad'i qasa, rufeta sukayi da duka, da sauri inspector najida ta dakatar dasu.
Chapter 63 · 0% Book details