← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 160

Sashe 91

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru baba balarabe yayi kafin yace to yabari sud'an shawarta tsakaninsa da sauran 'yan uwansa da suka zo tare, hakan yasa dady miqewa shida dr sukabar d'akin, bayan sun fita baba balarabe ya tambayi 'yan uwan nasa had'e da kirawo Yaya Maryam da aunty marwiyya dake can shiyar ammie da yake suma wan saheken rasuwar suka iso suda matan baba balarabe sannan yasa aka kirawo suma su umma sukayi shawara, nan take kowa ya amince da hakan don alkhairin da yayi masu bazasu iya hanasa wannan 'yar qanqanuwar alfarmar ba, umma kuwa dama cewa tayi duk shawarar da suka yanke akai tayi daidai batada ja, don haka koda suka nuna amincewar tazauna d'in batayi musu akaiba asalima yanzu tafijin garin aranta saboda mijinta dake ciki fiye da wancan garin da suka baro, gaba d'aya yafice mata arai batada sauran sha'awar komawa cikinsa.

Sosai dady yaji dad'in amincewarsu da buqatarsa yayita yimasu godiya tare da fatan ALLAH ya saukesu lafiya, har bakin motocinsu gida biyu dake wajen gate yarakasu sannan suka wuce shi kuma yadawo gida yana mai jinjinawa qoqarinsu akan amincin da suka bashi.

••• ••• •••
Baffa da baffa Usman kuwa basusan abunda kefaruwa ba har akayi zaman ukkun baba basuda labari akan rasuwar tasa sai bayan kusan sati biyu sannan suka sani, baffa yayi kuka sosai akan mutuwar aminin nasa wanda d'an uwansa yakasa sanar dashi saboda wata 'yar rashin fahimta data shiga tsakaninsu, babu abunda yafi qona masa rai irin ace ALLAH yasa har ansan inda suka tafi amma akaqi sanar dashi har ta ALLAH ta faru akansa, yamatuqar jin zafi da Kuma rad'ad'i azuciyarsa fiye da abubuwan da suka faru abaya, hakan yasa yaqudurce aransa bazaya koma waiwayarsu baba balarabe ba akan maganar da tasa suka yanke ganawa tsakaninsa da aminin nasa idan har suna tunanin hakan tafarune da son ransa ko kuma da had'in bakinsa har sai lokacin da ubangiji yatashi bayyanar da gaskiyar al-amarin, duk da wannan matakin daya d'auka hakan bai hanashi had'a waau daga cikin 'yan uwansa mata ba da wasu abokanansa da 'yan uwansa maza kusan mota biyu sukaje har gida suka yowa baba balarabe gaisuwa, aranar baba balarabe yaji kunyar da bai tab'a jiba aduniya, so yake yakeb'ance da baffa suyi magana amma tsananin b'acin ran dake zuciyar baffa yasa ko bari bayayi su had'a ido dashi balle suyi wata magana, gaisuwa dai ce takawosa kuma yayi masa fatanshi d'aya ALLAH yajiqan aminin nasa kuma ya lullub'esa da rahama, haka sukabar gidan batare daya samu keb'ewa dashi ba ko kad'an, wannan abun yaqara saka baba balarabe cikin nadama da dana sanin abunda yayi don yatabbata shima baffa yayi fushi akan zancen rasuwar da ba'a sanar dasu ba,

Su baffa nafita nan suka nufi gidan Yaya Maryam da aunty marwiyya suka yomasu gaisuwa, nanma baffa bai nuna masu komaiba banda gaisuwar da sukaje yimasu ba sannan suka koma gida.

Suna isa gida baffa yanemi waje yakwanta sboda wani irin zazzab'i daya rufesa, kallonsa matarsa nusaiba tayi had'e da cewa.

"Baffa don ALLAH kafidda damuwar wannan abun aranka, karka manta duka mai rai mamacine, koda kasan da maganar ganinsu bazaka iya hana mutuwarsa ba tunda lokaci yayi, haka kuma koda ansanar dakai zancen rasuwarsa dawuri bazaka iya canza komai ba akan abunda yafaru, don haka kayi haquri muma nan duk ita muke jira, babu wanda kezuwa har sai lokacinsa yayi, su day suka tafi basuyi gaggawa ba mukuma da bamu tafi ba bamuyi jinkiri ba, ubangiji ALLAH kasa muyi kyakkyawan qarshe."

"Amin." baffa yafad'a yana kallon d'an qaramin cikin dake jikinta yataso kad'an, murmushin da yafi kuka ciwo yayi yanajin wani irin zugi aransa, anan yaqudurta azuciyarsa idan ALLAH yasauketa lafiya matuqar namiji tahaifa zaiyiwa aminin nasa takwara, ganin yanda takafesa da idanuwa kamar zatayi kuka tana fad'in.

"Baffa kayi haquri kaji." Don haka take kiransa har yanzu, yayi yayi da ita tadena amma taqi, hakan yasa yaqaqaro murmushin qarfin hali had'e da cewa.

"Nusaiba to me akayi naga kina b'ata fuska, ai dole nahaqura tunda yariga ya tafiyarsa, amma inajin rad'ad'in rabuwata dashi sosai,"

"To kayi masa addu'a,"

"Zanyi masa nusaiba amma kema zakiyi masa takwara idan kika haifi namiji?"

Cike da yarinta tasa hannuwa tarufe fuskarta, don har lokacin bata cika shekaru goma sha shida ba aduniya kuma ALLAH ya albarkaceta da samun ciki wata hud'u kenan ynzu da kwanaki, yana matuqar jin dad'in zama da ita duk da zamowarta yarinya da mafiya al-amurranta shirme sunfi yawa, amma takan nuna damuwarta aduk lokacin data ganesa cikin damuwa kuma tana bashi kulawa daidai iya qarfinta naqaramar yarinya dad'in dad'awa ma ladabi da biyayyar da take yimasa badon 'yan matsalolin dake tattare dashiba dake hanasa samun cikakkiyara natsuwa da yace gaba d'aya bai tab'ajin dad'in rayuwar aure ba sai yanzu, qaramar yarinyace mma tanada kiyayewa sosai wajen iya zama da miji bisa turbar da yake koyar da ita, hakan yasa duk yanda damuwa tayi masa yawa idan yaga hakan zai haifar da tasirinta wajen cutar da yarinyar yake dannewa, hakan yayiko yanzu yadanne duk abunda yakeji yashiga zolayarta tana dariya.

Bayan kwana biyu baffa yaje can gidansu baffa Usman ya isko 'yan sanda sunyi cirko cirko aqofar gidan wai zasu kama muneera akan tafasama wani saurayi dutsi a ijiya har saida ta tsiyaye gaba d'aya.

Inspector najida yagani a tsaye jikin motar fuskarta ba walwala tana jira ashiga akamo muneerar, wajenta yanufa tana ganinsa tasaki fuskarta had'e da qarasawa wajensa kafin ya iso, d'an russuna kai tayi tagaishesa had'e da cewa.

"Baba ya gida ya kwana biyu?"

"Alhamdulillah 'yata injin dai ko lafiya?."

"Lafiya lau baba, yaron kune yafasawa wani ijiya shine aka kaimana qararsa."

"Subhanallahi wakenan."

"Muneera baba, yarinyar nan batajin magana sau biyu kenan ana kaimana case d'inta amma saboda kai sai nasa asulhunta abun, amma awannan karon dole mukai case d'in kotu."

"Haba 'yatah, don ALLAH karkice haka ai shi taimako ba'a gajiya dayinsa."

"A'a baba! Haka ya isa batajin magana da yawa, koda zamuyi wani abun dole sai munje kotu da ita."

"Shikenan!, 'yatah ALLAH ya kyauta, zamu biyo bayanku in Sha ALLAH muji yanda za'ayi."

Har inspector najida tajuya zata tafi sai kuma tasake juyowa ta tsaida baffa tana fad'in.

"Baba nikam nace wai yabatun tsohuwar matarnan taka Yaya hawwa, injin tasamu sauqi?."

Saida Baffa ya sinne kai yana d'an sosa qeyarsa saboda nauyin maganar da yaji sannan yace.

"Ehmm! Da sauqi zamuce, Amma har yanzu tana kware anaci gaba da bata kulawa aqarqashin jami'an lafiya."

"ALLAH sarki, ALLAH yabata lafiya, kwanakima nayita neman lambarka awayata narasa lokacin da naga ana nuno yanayin da take ciki a tv, abun yabani tausayi sosai sai natuna da zancen bokan da take zuwa wajensa dake asibiti, shaf namanta nakiraka na sanar dakai cewa bayan angama bashi treatment yafarajin sauqi da sati d'aya ashe shima yasamu matsala aqwaqwalwarsa, abun mamaki koda akayi masa gwaje gwaje sai aka samu qwaqwalwarsa lafiya take Amma yanayin abubuwa irin na miyagun mahaukata dake iya illata kowa, asibitin na shirin sallamarsa sai aka samu ya gudu, yanzu haka zaka ganesa akan tituna tsirara haihuwar uwarsa ko akan juji yanacin lalataccen abinci marasa kyau kamar yanda mahaukata keyi a wani lokacin kuma sai kagansa da sutura ajiki yana bin mutane yana bara abashi abincin da zaici, rayuwa yakeyi gatanan dai, shi ba dabba ba kuma ba cikakken mutum ba, hakan yasa nayi tunanin cewa wataqila matsalarsu d'aya da tsohuwar matarka, Ina nufin qwaqwalwarsu lafiya klw take saidai suna azabtuwane ta dalilin miyagun aljanun da suka shiga jikinsu su sukesa sunayin wud'annan abubuwan dakesa anayi masu kallon mahaukata, shine nayi tunanin kiranka nafad'a maka ko zaku koma gwada maganin musuluncine tunda yanzu kusan shekara d'aya da watanni kenan ana fama dana asibitin ba'a dace ba."

Shiru baffa yayi yana maimaita kalaman inspector najida a qwaqwalwarsa, tabbas maganarta akwai qamshin gaskiya aciki dole yayi nazari akanta sosai ko ALLAH zaisa adace.

"Shikenan 'yata in Sha ALLAH zamuyi tunani akan haka nida 'yan uwana, dama qarfina yafara qarewa akan wannan matsalar tata, kullum cikin kashin kud'i ake, kuma duk da binciken da sukayi akanta suka yad'a aduniya ankasa samun tallafi daga ko ina."

"ALLAH yasawaqe baba, har yanzu ita matar d'an naka ba'a ganta ba ko?"

Saida Baffa yayi ajiyar zuciya sannan yace. "ALLAH kad'ai yasani 'yatah.."

Ananma yake bata labarin rasuwar aminin nasa wato mahaifin matar d'ansa, tamatuqar tausayawa tare da yimasa addu'ar ALLAH yajiqansa da rahama, suna tsaye 'yan sanda suka fito da muneera duk anbubbuge mata fuska saboda taurin kan da tasa wajen kamota, su kansu 'yan sandan sai nishi sukeyi saboda wahalar dasu da tayi suna sake jibgarta da kulaken dake hannuwansu Inna ruqayya nabiye dasu tana d'ura masu zagi, juyowa inspector najida tayi da qarfi jin zagin da takeyi masu, Inna ruqayya naganin haka ta arta dana kare don bata manta irin azabar da tasha ahannun taba, ana qoqarin tura muneera mota tarugo da gudu ta lab'e bayan baffa da yayi tsaye yana kallon ikon ALLAH tana fad'in.

"Wayyo baffa ka ceceni, wlh ba laifina bane, innace tace naje wajen salele na karb'o mata saqo ashe wai iskanci zaiyi dani ya bata kud'i, shine ni kuma na doka masa wani qarfe yafad'a akan wani abu nasamu nayi guduwata, shine akace wai nafasa masa ijiya, don Allah baffa kataimakeni bana son zuwa."

"Yi haquri munneera jeki ku tafi yanzu nida Usman zamu biyo bayanku, Ina shi baffan naki yake?"

"Ya gudu baffa, kuma wlh har dashi ke karb'ewa salele kud'i wai zaya aura mani shi ni kuma bana sonsa, kuma baffa ya..."

"Ashsha muneera yishiru haka jeki kinji zamuzo yanzunnan?"

'Bare baki tayi tana kuka had'e da susar kai 'yan sandan sukazo suka cakumeta tanata tsalle tsalle da ihu suka sakata aciki, yaran anguwa da suka taru sai faman dariya sukeyi, girgiza kai baffa yayi sannan yabar wajen don ya tabbata Usman baya cikin gidan shi Kuma mahaifin nata sakaran wofi da rashin kunyarsa akansu kad'ai ta tsaya yayi guduwarsa...

Daqyar baffa Usman da baffa suka samu sukayo belin muneera batare da anje kotu ba saboda ijiyar yaron batayi komai ba amma yace sai ambiyasa kud'insa.
Chapter 91 · 0% Book details