← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 160

Sashe 78

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Daga mata kai tayi sannan tajuya zata tafi tana d'auke da little.

"Au! yau babu rakiya maman boy?"

Ta juyo tana kallon rashida dake qoqarin tasowa alokacin. Har bakin mota ta rakata tare da yiwa Dr.nura godiya sosai tamiqa mata Little sannan suka wuce...

_Darasi: 'yar uwa ki guji aikata laifi komai qanqantarsa domin bakisan iya adadin mutanen da Zaki iya cutarwa ba ta dalilinsa, wanda hakan kad'ai na iya zamowa dalinlin tsanantar hukuncinki awajen ALLAH, domin shi mai yafe haqqinsane amma banda haqqoqan rayukan da kika cutar, laifi d'aya yaya hawwa ta aikata akan rashida amma mutane da yawa sun cutu adalilinta, ciki kuwa harda qaramin yaro (yusuf) dake fuskantar damuwa da kuma barazana ta dalilin hakan._

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___58💎

Shiru Yaya Maryam tayi na tsawon daqiqu uku kafin tace.

"Hakan shine daidai, dama abunda nayita qoqarin lurar dakai kenan ka kasa ganewa, to amma batun cewa za'a mayar masu da yaro don yanke duk wata alaqa dake tsakaninmu kabarta don ni gaba d'aya bana buqatar jinmu yakoma zama atare dasu tunda basa da zuciyar imani."

Sun jima suna tattaunawa kafin yabar gidan har lokacin yanajin d'aci akan maganganun da baffa Ali yafad'a masa.

••• ••• •••
Baffa nagama waya da malan balarabe yakalli d'an uwan nasa ya sakar masa murmushi cikin qarfin hali sannan ya juyar da kansa gefe, yana maimaita innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun aransa.

Dafa kafad'arsa baffa Usman yayi had'e da cewa.

"Meke faruwa ne Yaya?"

"Abunda Nuraddeen yayi gudun faruwarsa." Yabashi amsa had'e da juyowa suna fuskantar juna.

"Kayi haquri Yaya, dama dole hakan zata faru, mu auna kanmu a matsayinsu mugani, don haka dole zamu lallab'asu har su fahimcemu, ayanayin yanda damuwowi sukayi masu yawa kamarmu, abune mai wahala su iya riqe fushinsu alokacin da sukaji labarin tafiyarsa musamman idan sun jine daga bakin daya kasa yimasu kyakkyawan bayanin da zayasa sufahimta, shi kuwa rashin bayani acikin kowane al'amari shike haifar da husuma da kuma aikin dana sani, don haka dole muyi haquri har zuwa lokacin da zasu fahimcemu."

"Shikenan Usman, amma duk da haka mufara jaraba zuwa wajensa idan mun sauka."

Awa hud'u ta d'aukesu kafin su isa kano, ana ajiyesu tasha suka sake shiga motar da zata kaisu qauyen na yarimawa, cikin qananan daqiqu suka isa sukaci sa'a kuwa yana zaune bakin gida yana arwala suka yimasa sallama, bai amsa ba har saida ya gama arwalarsa ya d'aga kansa sama yayi addu'ar da akeyi bayan gama arwala sannan ya kallesu fuskarsa a sake ba yabo ba fallasa ya amsa masu salamar.

"A'a malan Idris, malan Usman sannunku da zuwa yanzu kuke tafe?." Yafad'a yana qoqarin ajiye butar da yayi arwala agefe, kallon baffa Usman baffa yayi kafin suji ya sake cewa.

"Kai Hassan kushiga ciki ku kawo ruwa a butoci magrib taqaraso ana batun tada sallah."

"Am sannunku da zuwa bari naqarasa masallaci kafin ku iso liman na batun tayarwa."

"To shikenan!"

Baffa yafad'a cike da mamaki a fuskarsa.

Basu sake Shan mamaki ba sai da suka fito sallah suka tarar da tabarma an shimfid'a a qofar gida da kwanonin abinci,

"A'a malan Usman ya akayi kukayi tsaitsaye? bisimillah kuzo kuzauna mana,

Gaggaisawa suka shigayi kafinsu baffa sufara qoqarin canza maganar izuwa asalin wacce takawosu, Amma ga mamakinsu sai sukaga kawai yajawo kwanoni abinci yana fad'in bisimillah malan idris muci abinci ko."

Babu yanda suka iya saboda yanada matuqar muhimmanci agaresu da bazasu iya yimasa musu ba, wanke hannayen su sukayi sukasa suka fara cin abincin tare har suka qare,

Bayan sun kammala, baffa yace.

"Don ALLAH malan balarabe kayi haquri ka sauremu, nasan an aikata maku ba daidai ba, amma kuskurene da babu wanda ya isa ya kauce masa, tabbas Nuraddeen yabar qasarnan saidai bada son ransa ba, nine natirsashi ganin yana shirin ruguza rayuwarsa, kuma dama ce wacce yasamu tun kafin wud'annan matsalolin su faru, ganin ba lallai bane ya sake samun wannan damar ba kuma ga yanayin da yake ciki yasa daya tirje akan babu inda zaije saboda yana tsammanin dawowar matarsa garesa wanda abune gaibi akan dawowarta yasa natilasta masa zuwa koya fita daga cikin halin damuwar da yake ciki."

"Hmmm malan Idris kenan!, Ai bance kunyi wani laifi ko kuskure ba, meye laifinku don kunyi qoqarin inganta rayuwar d'anku?, Meye laifinku don kunyi abunda zai sakaku cikin farinciki?, Ba kuda wani laifi don haka kumanta da komai, fatana d'aya muma ALLAH yabamu ikon d'aukar darasin da kuka koyamana muma mu inganta rayuwar 'ya'yanmu kamar yanda kukayi koma fiye da hakan.?"

Duk iya qoqarin da sukayi wajen ganin sun lurar dashi ya fahimci gaskiya hakan ya cutara daga qarshema cewa yayi.

"Don ALLAH da girmansa malan usman mubar wannan magana kada tajawo rugujewar sauran mutuncin dake tsakaninmu, d'anku dai ALLAH yabashi ilimi mai albarka mukuma ALLAH yatsare mana 'yarmu aduk inda take yabata juriyar shanye duk wani abu da zai nemi duqufar mata da farinciki."

"Amin" suka amsa masa dashi bayan sun sake bashi haquri sannan suka wuce zukatansu a dagule.

Bayan suntafi yakira Yaya Maryam lokacin tana zaune itada Rashida tana bawa little da sai qara wayau yakeyi nono,

"Na'am balarabe ya akayi? Duk lafiya dai kuke ko?"

"Lafiya klw Yaya, dama iyayen yaronnan mijin Rashida ne sukazo bada haquri...."

"Kaga rufemun babinsu bana son ji, ai Ina mumuka haifi aburmu kuma muka bashi aurenta ko! don haka yanzu mun raba, ko suna so ko basa so yazama dole yabawa Rashida takardar ta, bazata koma gidansa ba ko mutuwa zaiyi, shashancin baza da wofi." Yaya Maryam ta katsesa tana masifa,

Wata irin zabura Rashida tayi had'e da miqewa tsaye da kad'an little yafad'i, Yaya Maryam tayi saurin riqosa had'e da kashe wayar tana binta da wani mugun kallo mai cike da tarin tambayoyi, hankalinta atashe takalleta tana fad'in

"Mekike fad'a haka gwaggo!," da yake da haka suke kiran sunanta sannan taci gaba da cewa.

"Wai wa ake zancen zai sakeni?, Duk fa iya adadin kwanakinnan dana d'auka zuciyata cike take da mararinsa, idanuwa da kunnuwana cike suke da son ganinsa da kuma jinsa, kawai nayi shirune saboda kada kuga rashin kunyata tayi yawa amma Ina son na had'u da mijina, shine kuma kuke cewa sai ya sakeni?, Meye laifinsa?, Wne zunubin ya aikata da za'ayi yunqurin rabashi da ni?"

"Ungo nan marar kunyar yarinya." Yaya Maryam tafad'a had'e dayi mata daqquwa tanaci gaba da cewa.

"Ke wane zunubin kika aikata da uwarsa ta rabaki dashi, kin ganemun shashashar yarinya da batasan ciwon kanta ba, to bari infad'a maki wlh munfiso kimutu atare damu muyi maki sallah murufeki da mumaidaki gidansa uwarsa ta sake halakar mana dake, don haka tunwuri kiciresa aranki matuqar kina son muzauna lafiya dake kinji nafad'a maki."

"Haba gwaggo! Haba gwaggo wannan wani irin tsattsauran hukuncine zakuyi mana, inada yaqini akan tunda wannan jarabawa tasameni shima t yake cikin irin tashi jarabawar, don ALLAH kada kura bamu kodon yaronnan." Taqarasa maganar tana kallon little dake hannun ita Yaya Maryam d'in had'e da fashewa da kuka, har ga ALLAH Yaya Maryam taji tausayinta, Amma Babu yanda ta iya, wannan ita kad'aice hanyar da zasubi su kub'utar da 'yarsu daga sharrin uwar mijinta, wacce itama tanacan cikin mummunan yanayin da basuda labari akai, cikin dakewa da qarfin hali tace.

"Rashida kawai kuhaqura da juna, yaro kuma Allah shizai rayashi ko bakwa tare don haka kibi umurninmu kizauna lafiya."

Wani kukan ta sake fashewa dashi had'e da durqushewa qasa tana fad'in.

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, astagfirullah ALLAH natuba kayafemun laifukana, ya ALLAH ka sauqaqamun wud'annan jarabawowin rayuwa kada sufi qarfin zuciyata susa na sab'a maka," kallon yya matram data kauda kai tana goge 'yan guntayen hawayen da suka zubo mata tayi.

"Gwaggo baifa sakeni ba, taya zaku rabamu?, Karku manta dani harshi zamu iya sake ahiga wani hali idan kuka yimana haka, kunada iko akaina ammashi sam bai kamata kununa iko akansa tahanyar tirsasashi ya sakeni ba."

"Kedai zaki shiga wani halin keda kike ganin bamu isa mutirsasaki akan abunda muke ganin shine alkahiri arayuwarki ba, amma bandashi tunda har ya iya mance awane irin hali zaki shigaba keda abunda ke cikinki ba ya tsallake qasarnan ya tafiyarsa duk da yasan abunda yafaru dake Amma saboda ya gyara rayuwarsa kuma ya farantawa iyayensa yatafi yabarki acan duniyar da bai masan inda kike ba don ya inganta gobensa, ba kekad'ai da ba kyanan ba hatta mu iyayenki da yasan muna nan ya wofantar damu ta hanyar tafiyarsa batare da saninmu ba, wannan shi kike tunanin har zai shiga wani hali idan aka rabaku.? Tir da wannan banzan tunani irin naki" tana gama fad'ar haka tafice d'auke da little da yayi bacci a hannunta

Tunda tafara magana Rashida ta dasqare a inda take tsaye, shin Anya maganganun da gwaggon tata ke fad'a gaskiya ne ko a'a?, Ko kwanto tashigayi akan cewa habibyn nata zai iya tafiya acikin yanayin da ake na b'atanta kuwa?, Inaaa hakan bazai yuyu ba , tabama kanta amsa had'e da miqewa tana goge hawayenta, dole yau sai tahad'u da mijinta koda hakan na nufin za'a rabata da lumfashinta ne, dole ta qaryata d'ayar zuciyarta dake neman gasgata kalaman da gwaggo tafad'a mata.

'Dakin da anan ne aka bata tashiga ta d'auko mayafinta da sauri tanufi qofar fita gidan, kota halin qaqa yau tanada buqatar zuwa ta had'u da masoyinta kuma mijinta, sand'a tafarayi gudun kada taganta ta hanata zuwa har ta isa bakin qofar gidan

Tana fitowa taci karo da Fatima aqofar gida ita da Dr ya kawota.

Cikin farinciki Fatima tarungumeta tana fad'in "'yar halak ina zakije ne ko kema kinyi kewar tamune kamar yanda mukayi?"

Ganin yanda idanuwanta sukayi jajir saboda kukan da tayi yasa Fatima cewa.

"Subhanallahi, maman boy meyake faruwa?" Hakan yasa Dr fitowa daga cikin motar yana kallonta had'e da qoqarin rufe marfin motar, qarasowa wajensu yayi kafin yace.

"Maman boy lafiya?" Yanda sukaga ta sake fashewa da wani kukan yasa Fatima riqo hannunta zata shiga cikin gidan da ita da sauri taja baya tare da tirjewa.
Chapter 78 · 0% Book details