← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 160

Sashe 16

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kai baffa Usman yayi had'e da kallonsa kafin yace "Yanzu kai Ali meye amfanin abunda kayi, karkamanta yaronnan d'anka ne bai kamata kana yimasa abubuwan da basu dace ba gudun kada yadena ganin girmanka da kimarka, kaga daga lokacin fa girma yafad'i."

"A'a meye rashin dacewa anan, gaskiyafa nafad'a masa, zamu saki yaron namune sagaga alalata mana shi acan"

"Ikon ALLAH, yanzu Ali aganinka har abun yakai ga mata ke lalata maza?"

"Ahaf nawa akayi, ba shiyasa qara mutum ya nemawa d'ansa mata acikin dangi ya huta ba, Amma meye amfanin kwashe kwashe awaje."

"Oho!.. yanzu nagane inda zancenka yayi, wlh kaji tsoron ALLAH kabar yaronnan yazauna lafiya da mahaifiyarsa, meye amfanin sonkai Ali?, Tunda yaron nan yakawo wacce yakeso don me da baza'a haquraba abarsa?" "Mtssss..." Baffa Ali yaja tsaki tare da barin wajen yana suruttansa.

Malan Idris kuwa duk da yana cikin damuwar maganganunda baffa Ali yayi masa hakan bai hanasa fad'ad'a fara'ar saba alokacin daya iso makarantar, Kai tsaye ajinsu Rashida yanufa saboda yanda yake mararin ganinta, duk da itama tana son ganin nasa hakan bai hanata b'uya a qarqashin kujeraba alokacin data hangosa saboda yanda take son samawa kanta mafita tahanyar yakicesa aranta, dube dube yafarayi lokacin daya iso qofar ajin batare daya damu da malamin dake ciki yana yimasu mathematics ba yayinda itako banda fad'uwa babu abunda gabanta keyi,....

*_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU👏😭_*
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___14💎

Cikin rashin amincewa da zancen malamin Yaya hawwa tace,

"Haba malan, cike fa da yarda da aminci muke kawo buqatunmu zuwa gareku, sai kuma ace da kanku zaku wargaza wanan yardar da muke da ita akanku, wlh no bana son ya auri yarinyar nan don ALLAH kasake dubawa ko akwai yanda za'ayi" jinjina kai ya shigayi yana kallon gefe gefensa kafin yafara kiran wasu kalar sunaye, yajima yana suruttansa kafin yasake baje duwatsun dake gabansa, d'ago kansa yayi fuskarsa a d'aure yace da ita "d'auki d'aya" hannunta narawa tad'auka ta mik'a masa ya jawo wani tray dake cike da qasa ya ajiye agabansa, tsakiyar tray d'in ya aza dutsin tare da yin rubutu saman qasar, ya kwashe fiye da mintuna biyar yana abu guda sai faman zufa yakeyi, can ya shafe rubutuna yayi tare da d'ago kansa yana nuna Maya qasar dake cikin tray yace, "duba nan kigani"

Tana dubawa taga hoton Nuraddeen shida Rashida lokacin daya riqe kunnuwa yana bata hak'uri, da sauri tadafe qirji tana fad'in "nashiga uku ni kuluwa, malan kaga abunda yaronnan keyi agabanta tun ba'aje ko ina ba, don ALLAH malan kayi wani abun, bazan iya jurewa ganin haka ba"

Murmushi malamin tsibbon yayi kafin yace "fiye da haka sai kingani, kawai kitashi kitafi, bayan auren kidawo masan abunda zamuyi amma wannan bazamu iya komai ba" Babu yanda zatayi dole tamiqe jiki ba k'wari taji yace

"An buqaci ki ajiye kud'in sadaka kafin kitafi"

Cikin jin zafi da takaici tabud'e jikkarta taciro naira dubu uku ta ajiye masa sannan tafito kamar zata tashi sama tana fad'in, "wannan ai shi ake kira da asara, maqaryacin banza da wofi meye bazai yuyu ba aduniya, ai wlh banda wancan shashan Aliyun daya kwatanta mani wajenka kuma yace aikinka sha yanzu magani yanzune babu abunda zai kawoni nan don nasan dama bakomai irinku suka iya ba, malan bakada imani shiyafi dacewa da wannan aikin nazo nan nayi asarar kud'ina ga banza." Har ta isa gida fad'a takeyi tana qarawa saboda jin zafin kud'inta da aka amsa ga banza kuma ba'ayi mata aikin da take so ba, nafef na ajiyeta tabud'e jikka taciro kud'i taci karo da baffa Ali daya fito daga masallaci, yana hangota ya washe baki had'e da nufo inda take yana fad'in "sannu da zuwa Yaya hawwa" rufe jikkarta tayi had'e da banka masa wata irin muguwar harara sannan tace, "kasallami mai napep d'in nan acikin kud'ina" tawuce abunta, babu yanda ya iya tunda ta tafiyarta dole yaciro wata damuqaqqar d'ari biyar ya miqawa mai napep d'in yace, "ungo bawan ALLAH cire kud'inka kabani canji" mai napep d'in na amsa yatada kekensa had'e da cewa "ai ahaka na d'aukota."

"'Darin d'in."

"Eh wlh, don ma bance da hamsin ba wannan tsayin da aka sani." Yana gama fad'a yaja kekensa yabar wajen, da sauri baffa Ali ya cimmata daidai qofar shiga gida yana fad'in "Yaya hawwa wud'an ne kud'i kuma kike biyata da kika sani asarar miqa kud'in da nake dasu gaba d'aya, shi kuma tsabar rashin mutuncin wai har nera d'ari ya karb'a, kuma wlh ita kad'ai ce gareni yau ina zancen nakai ad'an silala mana wake da mai sai gashi anrabani da ita."

"Ai ni be burgeni ba don ba haka naso ba, so nayi ya karb'i d'ari biyu a hannunka, idan kahanashi ciko yacire hularka yaje da ita"

"Yaya hawwa meyayi zafi haka?, ALLAH baki haquri, yanzu dai mu ajiye wannan maganar, ya kikaga malamin inadai komai angama ko?" Kallonshi tayi had'e da yaqe hauru hakan yasa shima yasaki murmushi azatonsa andace, ji yayi tace

"Anko dace Ali, ai har an rabasu yanzu kawai ka qaddarama har ya auri 'yarka ya gama"

Sake washi baki yayi yayi had'e da cewa "ai nafad'a maki aikinshi Sha yanzu magani yanzu, dako kinata faman kunfar baki ga inda za'ayi maki maganin matsalarki cikin sauqi." Saida tad'aure fuska sannan tajuyo tana kallonsa ido cikin ido ranta ab'ace tace,

"Eh nako gani Ali, amma ina tabbatar maka da cewa nima cikin sauqi nima zaka biyani kud'ina da kasa nayi asararsu ga banza ga wofi, saboda rashin mutuncin Ali ni zaka yaudara, ka turani wajen matsiyaci talaka da baisan komai ba akarb'e mani kud'i ga banza kuma ace abunda nake so baze yuyu ba, to wlh kaji narantse maka kud'ina ko sisi bazaiyi ciwon kaiba saika biyani" tana gama magana tawuce abunta, tsaye baffa Ali yayi yana kallonta cike da mamaki kafin yayi hanzarin bin bayanta, "Yaya hawwa nifa ban fahimci me kike nufi ba"

"Oho! Ni ba abinda ya dameni kaji nafad'a maka saika biyani kud'ina ko in d'ibesu ajikin waccan gwalmammiyar 'yar taka kona rage zafi."

"Haba Yaya hawwa, meyakawo zancen 'yata anan, don ALLAH kiyi shiru kada afahimci abunda ke faruwa." "Meya dameni ko anji, d'a dai nawane kuma nace bana buqatar wacce za'a aura masa amma anqi afahimceni, to Ina ruwan mutum da duk matakain dana d'auka, kaga ni kaje duk yanda zakayi kahad'o mani kud'ina in koma wajen malan bakada imani, nasan shi kad'aine ke iya maida abunda bazai yuyu ba ya yuyu."
( _wal iya zubillah, yya haww kam kinyi nisa kina buqatar addu'a, duk wani mai sab'o yakan b'oye baya son kowa yasani amma ke qarara kike nunawa mutane ke bakya tsoron ALLAHn da yayiki ma balle d'an Adam, ubangiji ALLAH ya shiryeki da duk masu hali irin naki_).

••• ••• •••
Da gudu taqarasa cikin zauren nasu tare da tsayawa tana fitar da nishi ahankali, murmushi tayi had'e dasa hannuwa tasake rufe fuskarta, "Alhamdulillah" tafad'a tare da sake leqowa tana hangosa daidai lokacin daya miqawa yaron ledar sannan ya juya yakoma tahanyar da suka biyo, da sauri takoma itama cikin gida tana fad'in "wai kodai mafarki nakeyi?" Daidai lokacin ta k'araso tsakar gidan umma najin me take fad'a tace "meye kuma kike tambayar ko mafarki kikeyi." Cikin farinciki taqaraso inda take zaune tana gyaran wake tace, "Babu komai ummata"

"Anya Rashida?, gaskiya da walakin goro acikin miya wannan farinciki da naga kinayi" kafin tarufe baki sai ga yaron da malan ya aiko yayi sallama had'e da cewa, "wai gashi inji malan idris yace abawa Rashida" kallon yaron umma tayi sannan tamaido kallonta ga Rashida data sunkuyar da kai qasa, murmushi umma tayi sannan tamik'a hannu takarb'i ledar had'e da cewa, "kace angode." Har yajuyazai fita umma takirasa ta warware hab'ar gefen zanenta taciro naira hamsin tamiqawa yaron tace, "kace masa angode kaji ko."

"Kibarsu umma ai har yawuce nagode." Yaron yafad'a tare da ficewarsa da gudu"ikon ALLAH, kaga yaro mai tarbiya, ubangiji ALLAH yai maka albaraka kaji.!" Acan cikin zauren ya amsa da "Amin" sannan yaficewarsa, juyowa umma tayi tana kallon Rashida dake duk'e tana tayata tsince waken, tanaji zatayi magana da sauri tamik'e tana cire jikkarta dake kafad'arta tashige d'aki don tasan babu abunda umman tata bata sani ba, ita dai umma abunma dariya yaso yabata wai yau Rashidar tace dajin kunya, "ALLAH ka sake shirya mana" tafad'a sannan taci gaba da gyaran wakenta, acan cikin d'aki kuwa Rashida kasa tsaida kanta daga murmushin da takeyi tayi tafad'a akan katifarta tare da mulmulawa tajawo pillow tarungume tana dariyar da umma bazata iya jiba ta runtse idanuwanta had'e da furta "I luv you malamina, I luv you Nuraddeen"

Saida tagama sabbatunta tukuna ta tashi tacire uniform d'inta ta sanyo doguwar riga tafito don taya mahaifiyarta aiki, sosai umma ke kallie da sauyin walwalar da 'yar tata ta samu tare da farincikin da take ciki wanda bako shakka tasan abunda take tsammanin rasawane akwanakin baya tasamu tabbacin samunsa, dariya tayi cikin tsokana da nuna cewa bata san abunda ke faruwa ba tace

"Rashida nikuwa wai meye tsakaninki da wannan malamin naku daya aiko maki da saqo d'azu, gashican ma akan kujera na ajiye har babanki yadawo" Saida tayi dariya sannan tace

"Kai ummata ai kunsan komai?"

"A'a nikam ban san komai ba amma dai yanzu abani labari insha, don naga alamar farinciki ya banbanta ranar yau data sauran ranaku ukun da suka gabata, fad'amun meye sirrin 'yatah." Dariya ta sakeyi had'e da cewa.

"Kai ummata, nafahimci komai nakeyi kina sane dashi qyalewa kawai kikeyi."
Chapter 16 · 0% Book details