← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 160

Sashe 80

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hakane nura! Kaci gaba da haquri kana kwantarwa da iyainka hankali, da SANNU ALLAH zai duba lamurranku ya share maku hawayenku, akoda yaushe addu'ar mu natare dake."

"Dady, ammie nagode da kulawar da kuke bamu tare da addu'o'inku, koda ALLAH bai bamu aihuwa ba ku kad'ai kun isa farinciki agareni domin babu abunda yakai samun nagartaccin iyaye aduniya muhimmanci, sune kad'ai farincikin da idan katuna zaya dad'a sanyaya maka zuciya."

Daidai lokacin umma tafito daga kitchen don tagama kammala komai zata koma part d'insu, "umma gafa d'anki da d'azu nake fad'a maki cewa yana kan hanya ya iso."

Dama tuni umma tadawo wajen hajia fareeda da aiki kamar yanda dady ya umurta kuma tanajin dad'in aiki da ita sosai don kusan komai atare sukeyi cikin girmamawa, sab'anin hajia nafeesa da saidai ta nad'e qafafuwa tana bada umurni, murmushi tayi had'e da qarasowa wajen tace.

"Sannu da zuwa.." Bata qarasa ba sakamakon juyowar da yayi suka had'a ido, cikin i'ina tace.

"Kaine?"

"A'a baba kece anan kuma.?"

Yafad'a yana nuna baba da hannu, binsu da kallo su ammie sukayi cike da mamakin ganin sunsan juna, nan Dr nura yabasu labarin ynda yasanta har yana qarawa da tambayarta cewa.

"Baba ina wanda naganku tare."

"Yana can shagon da alhaji yabashi yariqa kulawa dashi, ai shi d'in mijinane"

Tafad'a akunyace tare da komawa kitchen,

Dariya su dady sukayi kafin sushiga bashi labarin zuwansu ataqaice amma basu fad'a masa cewa sanadiyar b'atan 'yarsu sukazo garin ba.

Dawowa tayi d'auke da wani qaton try da suka shirya masa abincin da yafiso ita da ammie wato tuwon semolina da miyar kub'ewa d'anye, da sauri ammie taje tariqo mata tana fad'in.

"Kai umma ai dabari kikayi nazo na d'auko masa." Sannan ta ajiye abincin agabansa, yana bud'awa yaga best food d'insa ba shiri yature jikkar gabansa yana qoqarin fara zubawa yaci, d'an mangararsa ammie tayi aqeyar kai tana fad'in.

"Bazaka bari kafara watso ruwa ba.?"

"Awshh....ammie bara nagama cin abinci tukuna, ALLAH yawuna har sun tsinke."

Yafad'a yana shafa inda ta mangaresa, dariya umma dake tsaye tana kallonsu cike da burgewa tayi tana goge 'yan hawayen da suka zubo mata tunawa da tata 'yar sannan tabar wajen.

Bayan ya kammala cin abincinsa yaje ya watso ruwa sannan yaje wajen hajia nafeesa matar babansa ya gaisheta daga can kuma yawuce wajen malamin da yake karb'o maganin Little Nuraddeen awajensa ya karb'o sannan yadawo gida lokacin kusan qarfe biyu na rana yawuce kai tsaye d'akin ammie tana zaune tana tilawar alqur'ani, Saida takai aya sannan tarufe taje ta d'auko wata leda cikin drower d'in madubi tadawo inda yake zaune gefen bedside d'inta ita kuma ta zauna agefen gado.

"Ungo wannan ka kaimata, don ALLAH kace takula da shansa tunda safe kafin taci komai, shi wannan ganyen koba don haihuwa ba yanada kyau adinga tafasashi ana sha da ruwan tea kafin aci komai da safe, yana wanke duk wata datti dake cikin jikin mutum har zuwa mara, hakama yana wanke dattin mahaifa sosai, hatta wannan tumbin da kake ganin kafara azawa idan kuna shansa tare zaya rage sosai, don haka kukula, shi magani da kuke gani dace ne bamusan ta ina ALLAH zaisa adace ba, ALLAH yabamu rayayyi masu albarka."

"Amin ammie, amma shi wannan ganyen mene ammie?"

"Ganyen guava ne."

"Guava fa kikace ammie!, Wannan guava dai dana sani."

"Eh mana, Ina tabbatar maki idan kuka gane shan tea da ita, bazaku tab'a bari ya tsinke maku va agida, da kanku zaku kirani kusanar dani amfanin da kukaji tayi maku ajiki."

"To ammie shikenan mungode."

"Yawwa ALLAH yayi albarka kuma yakiyaye hanya."

"Amin ngd."

Yafad'a had'e da miqewa ya kama hanyar komawa kano bayan yayi sallama da mahaifinsa.

••• ••• •••
Kimanin kwanaki uku Yusuf ya d'auka kwance yana fama da zazzab'i, baya fita ko ina daga d'aki sai d'aki har ALLAH yasa yasamu sauqi, baffansa nafita zuwa gona ya iske baba Usman a d'aki yana shiryawa zaije gidan baffa zasu koma wajen baba balarabe su sake bashi haquri akan abunda yafaru, dama Inna ruqayya tafita anguwa Inna Bilkisu kuwa tana waje tana share wajen dabbobinta da yayi datti, baffa Usman na gyara zaman hularsa akai yaji anriqo rigarsa, juyowa yayi had'e da cewa.

"A'a Yusuf ka taso? Yajikin naka da sauqi ko?"

"Eh baffa Usman naji sauqi sosai."

"Masha ALLAH, ALLAH yaqara sauqi , to ya akayi ne." Duba gefe da gefe yayi sannan ya leqa ta qofar shigowa d'aki yaga ba kowa ya matso dab da inda baffa yake zaune a gefen gado a kunnensa yace.

"Baffa aunty Rashida matar ya nura tadawo, naganta da idona Amma karka gayawa baffana."

A razane baffa Usman yamiqe had'e da cewa.

"Kai Yusuf bana son shashanci, a Ina kaganta ne?"

Hannu Yusuf yasa had'e da rufe baki yana qwalalo idanuwa ya juya yana kallon qofa,

Furzar da iska baffa Usman yayi had'e da kwantar da hankalinsa ya matso inda Yusuf ya dafa kafad'unsa.

"Yusuf ka kwantar da hankalinka, Babu wanda zaiji kaji ko?, Yimun bayani a Ina kaganeta."

"Bana son baffana yaji yace idan nafad'a nima zai b'addani kuma bazai sake bani abinci ba."

"Bazaiji ba nayi maka alqawari kaji ko?"

Nan Yusuf yayiwa bayanin baffa komai had'e da roqonsa don ALLAH kada yafad'awa baffansa shi yafad'a masa, jikinsa na rawa yabar d'akin shima baffa Usman jikinsa asanyaye yabar gidan yanufi wajen baffa yayi masa bayanin abunda Yusuf yafad'a masa, yayi matuqar shan mamakin cewa wai har yanzu baffa ali na adawa da Rashida, tsanar da yakeyi masu har takai girman da zai sake cillasu awata damuwar, tare suka fito suka nufi gidan lado mai kalanzir suka tambayesa abunda yafaru ranar tsakaninsa da Yusuf na zancen ganin matar da Yusuf ya tabbatar masu da cewa Rashida ce.

Sun samu amsa daidai da zancen Yusuf don haka ba b'ata lokaci suka nufi gidan baba balarabe.

Sai yanzu baffa yasake fahimtar dalilin fushin da baba balarabe yayi sosai, ya tabbata akwai maganganu da baffa Ali yafad'a masa marasa dad'i wud'anda sune suka tunzurasa, haqiqa ko shine malan balarabe zai d'au zafi fiyema da hakan domin d'a baifi d'a ba.

Duk qoqarin da yakamata su baffa suyi wajen yiwa baba balarabe bayani yanda zai fahimci komai sunyi amma gaba d'aya Sam yaqi saurararsu balle yafahimce su, da suka d'auko masa zancen ganin Rashi da akace anyi kuwa buga kai yayi ga qasa yace shi baima san da zancen ba, Dole suka haqura suka koma gida, kusan ko yaushe cikin kiransa suke awaya da isko shi gida suna son tabbar da zancen amma ko kad'an yaqi barin hanya ko kad'ance da zasu iya gane hakan, musamman suka turo abokanansu da mutanen da suke da kima abashi haquri ko zai sauko yafad'a masu cewa Rashi tadawo.

Amma baba balarabe yakafe akan bashida masaniyar hakan, ayanayin yanda yake sakin fuska da tarbar wud'anda suke turowa yasa bazasuqi amincewa da zancensa ba, gaba d'aya baffa yasake shiga damuwa har ya soma ramewa.

A kullum bayada lokacin kansa saina bin hanyar zuwa gidan baba balarabe, baya can baya gidan Yaya Maryam, hakama aunty marwiyya, duk inda yake sa ran zai samu tabbacin labarin zuwan Rashida yana biye dashi Amma k sunqi bud'e baki sufad'a masa gaskiya.

Duk zafin da aunty marwiyya ta d'auka akan maganar saida yasoma bata tausayi saboda irin yanda taga yana kaida komo gidanta shida d'an uwansa kawai saboda su sani ko Rashida ta dawo amma idan ta tuna cewa fada masu shine zai sake zamowa silar da Rashida zata koma acikin ahalinsu da Babu zuciyar tausayi ko Imani atattare da wasunsu sai taji zuciyarta ta karye, musamman idan ta tuna da rashin 'yar uwarta da tayi akusa da ita ta dalilin haka.

Ganin irin kai da komowar da baffa keyi a tsakankanin gidajen nasu su uku yasa suka yanke shawarar had'a Rashida dasu Dr nura su koma da ita acan borno domin hakan shi zai fimasu kwanciyar hankali tunda sunsan inda take, koba komai itama zata d'an rage damuwar da take ciki tunda har yau taqi sakin jiki kullum cikin qunci take.

Wata nakaiwa qarshe Dr nura sunzo yimasu bankwana yaya maryam takira baba balarabe da aunty marwiyya suka roqesa akan buqatarsu tasu koma da Rashi acan yafi masu kwanciyar hankali indai hakan bazai zamo takurawa agaresu ba har zuwa lokacin da ALLAH zai qaddari dawowar iyayenta,

Sun matuqar jin dad'i yanda suka basu yarda haka tare da amice masu akan 'yar tasu duk da babu wata alaqa inbata musulunci ba a tsakaninsu musamman Fatima da tunkafin Dr nura ya amsa cewa sun amince tace.

"Babu wata matsala sun amince ba komai." Har tana karb'ar little a hannun aunty marwiyya cike da farinciki.

Rashida kuwa babu yanda ta iya domin ta dad'e da tabbatarwa kanta da cewa batada wani sauran iko akanta tunda tarasa iyayenta akusa da ita, komai yanzu sai yanda akayi da ita, sunjima agidan kafin Yaya maryam taje ta har had'o mata kayanta dana little, aranar ma Rashida tasha kukan rashin iyayenta sosai tare da fawwala dukanin al'amurranta ga ALLAH tana mai addu'ar ALLAH yasa wannan qaddarar da zata d'auketa ta maidata garin da tabaro tazame mata alkhairi, ahalin yanzu ko kad'an bata ganin laifin tafiyar Nuraddeen, saidai takanji wani irin zafi da qunci azuciyarta Idan ta tuna dashi wanda batasan dalilin faruwar hakan ba.

Haka sukayita bata baki da rarrashinta sannan suka d'auki hanyar komawa borno ita dasu Dr.

Gidan iyayenta kuwa tuni Yaya Maryam da baba balarabe suka yanke shawarar saka 'yan haya aciki kafin randa ALLAH zai dawo dasu sai suna jujjuya masu kud'in...

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___61💎
Chapter 80 · 0% Book details