← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 160

Sashe 84

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Rufemun baki." Yakatsa mata tsawa had'e da ficewarsa.

Lokacin da Rashida kuwa tafito ta samesu tsaitsaye ammie nabasu haquri akan abunda yafaru don taji komai da kunnenta, haquri tasake ba Rashida sannan tace.

"Son yakamata suje sugano umma kafin suwuce."

"No... ammie tun d'azu suka wuce asibiti ita da baba saidai idan munqara dawowa."

"Ok son kuyi haquri don ALLAH kasaki fuskarnan taka, bana son inganeku cikin damuwa kinji ko 'yatah kuyi haquri." Murmushi sukayi kusan atare sannan sukayi mata sallama zukatan kowanensu ba dad'i kafin su shiga mota subar gidan, motarsu nafitowa daga cikin gate napep d'insu baba nawutowa sun dawo daga asibitin, kusan saida sukayi clashing da juna sannan napep d'in ta ajiyesu sukuma suka wuce.

🤪 *Target bend*🏃🏻‍♀️

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___63💎

Tunda suka hau titi babu wanda yacewa wani uffan har suka isa gida, kowanensu ya lula duniyar tunani akan yanda rayuwa zataci gaba da tafiya dasu bisa linzamin qaddarar da suke akai, musamman Dr nura da yake ganin gaba d'aya cinmutuncin da matar mahaifinsa tayi akansa yaqare, don haka akwai buqatar ya d'auki matakin yiwa abun tufqa tunkafin yayi tsayi.

Gaba d'aya sai sukajidaren ranar yazo masu abai baice, hatta 'yar firar da suka sabayi a kowane dare kasawa sukayi kowane ya shige part d'insa ya kwanta, haka ma da safe kusan yanda suka kwana haka kowane yatashi fuskarsa babu wata walwala har suka zauna wajen karyawa ba wanda yace wani abu bayan gaisuwa, miqewa Rashida tayi bayan tagama nata Karin zata wuce d'akinta taji muryar Dr yace.

"Koma kizauna maman boy ina son zamuyi magana dake."

Bamusu takoma ta zauna yayi gyaran murya had'e da cewa.

"Ina mai baki haquri bisa abunda yafaru jiya, da nasan hakan zata kasance wallahi da ban d'aukeki nakaiki gidan muba, gashi hakan da nayi na neman sauya walwala da kuma farincikin gidannan gaba d'aya, naroqeki kimanta da abunda yafaru domin haka zaisa rayuwarki taci gaba da inganta kamar yanda tafaro, tabbas Bata kyauta ba data cutar dake ta hanyar munanan kalamanta batare da tasan koke waye ba! kuma ko kad'an batayi maki adalci ba a matsayinta na uwa da tasan irin zafin da akej idan aka aibatawa mutum d'a, Amma duk da haka Ina nema mata afuwa a matsayinta na matar mahaifina, ina tabbatar maki da hakan bazata sake faruwa ba in sha ALLAH kinji."

"Uncle kenan! bazance banji komai araina ba akan abunda yafaru jiya kasancewar yazamo silar jefaku cikin halin da tunda nake zaune daku ban tab'a ganinku acikin koda makamancinsa ba, ba ina damuwa bane akan abunda tayi mani ba, kawai damuwata tabayyana ne adalilin yanayin da nake kallon fuskokinku aciki, kalamanta abune da babu tushe, asali ko kuma inganci aciki da har zan damar da kaina. amma shi b'acin ranku da kuma damuwarku tamkar wutace dake cin zuciyata idan Ina ganinku acikinsa wanda natabbata bazata dena ciba har sai lokacin da naga farinciki yabayyana fuskokinku, kuyi haquri domin nima nazamo sila wajen sa ajefeku da kalaman da suka cutar da zukatanku."

Kallon Fatima Dr yayi had'e da cewa.

"Kijifa abunda take fad'a!, taya za'ayi tazamo silar cutuwar zukatanmu bayan laifin ita akayiwa."

"Hakan nafaruwa kuwa Dr, musamman ga zukatan da basu fiye son kansu ba kuma suke kallon damuwar wasu amatsayin tasu, don haka damu da ita mu manta da komai mu fuskanci gabanmmu."

"Shikenan ALLAH yaqarawa zukatanmu haquri kuma yabasu girman d'auke duk wata jarabawa da kuma gwagwarmayar rayuwa."

"Amin ya rabbi."

Suka fad'a tare suna murmushi, nan suka dasa rankon sabuwar firar da basuyi ba jiya,

Bayan wata uku little yaqara wayau Rashida ta yanke shawarar yayesa saboda ganin irin girma daya taso masa kuma babu abunda bai iya ciba. Ana saura sati d'aya tayayeshi suna zaune ita da fatima tace.

"Aunty nifa wani sati cire yaronki zanyi amama, ALLAH nagaji da tsutsannan da yakeyimun."

"Kai maman boy, shekararsa d'aya da wata d'aya fa kenan?"

"ALLAH nagaji aunty zalina yakeci sai yayita cizona da haqoransa masu kaifin tsiya sai kace reza." dariya Fatima tayi had'e da cewa.

"Aikuwa baki isa ba, sai yayi 2years tukuna, haquri kawai zakiyi kema wayasan yanda ummanmu tayi fama dake."

"ALLAH sarki umma, ai da zaku had'u kika tambayeta Allah zata fad'a maki bata wani sha wahalar renona ba saboda da kanta take fad'a cewa ni 'yar baiwa ce."

"ALLAH!?" Fatima tafad'a tana dariya hadde da zaro idanu, gwaggo mai aiki dake goye dashi tana mopping tace.

"Gaskiya hajia ta yaye yaron nan tunda ya iya cin komai, tubarkallah qato dashi gayanan yana neman karyamun baya,"

"Laaa...gwaggo har dake?, Zo kawomun yarona indai goyone daga yau yadena son naki."

Qarar wayar rashidane data jiyo rurinta ad'aki ya katse firar tayi saurin miqewa don ta d'auko gwaggo tace

"A'a Bari nad'auko maki, Amma cin hancin yaye d'an hajia ne zan baki."

"Aikuwa angama gwaggo." Rashida tafad'a tana dariya

"Ai sai kuyi bari abbansa yadawo zan fad'a masa ai."

koda gwaggo takawo mata wayar har tayi missed call, murmushi tayai ganin lambar Yaya Maryam da kullum saita kira idan bataji takirata ba taji ya lafiyarau take ita da litte, saurin kiranta tayi don kada tasake kiranta bugu d'aya ta d'aga.

"Rashida ya kike? kuna lafiya."

"Lafiya klwa gwaggo ya wajensu baba balarabe?"

"Kowa lafiya Rashida, Ina maigida."

"Gashinan ya hayewa gwaggo mai aiki baya, dama yanzu nake zancen zan yayesa da aunty saboda mugun tsotsans."

"Kul! Karki fara, kibari koda wata biyar ne nan gaba yad'an qara qwari kinji nafad'a maki ko?" 'bata fuska tyi kamar zatayi kuka had'e da cewa.

"Kai gwaggo kinga yanda yazama wani tulele dashi, ALLAH bazan iya da tsutsar saba."

"Cit d'inki, kenan ummanki sau uku tana zancen yayeki amma saboda qulafucin nono saita fasa har saida kika shekara biyu cif sannan ta yayeki, shima d'in haka kika dingayi kamar zaki mutu duk kikabi kika tada mana da hankali."

"Nid'in gwaggo!?" Tafad'a tana kallon fatima dake jin duk abunda Yaya Maryam kefad'a tana gumtse dariyar dake neman kucce mata.

"Ked'in fa, some some nawa kikayi?, Banda ALLAH yayi zakinfita ai da yanzu saidai labarinki, don haka kibari sai nan da wata hud'u idan ALLAH yasa munada rai."

"Shikenan gwaggo, ya labarinsu ummana?"

"Kiyi haquri Rashida har yanzu bawani labari akansu, amma munanan muna addu'a ALLAH ya karkato hankalinsu sudawo gida."

Wata gauruwar ajiyar zuciya tayi kafin suyi sallama tana dubon inda Fatima ke zaune, kashe mata ido d'aya tayi had'e da d'aga mata gira tana dariya tace.

"To 'yar baiwa ya akeyine?."

"Ummaaa!.." tafad'a cikin sigar damuwa.

"ALLAH sarki, ummanmu gaskiya baqaramin so da tausayinki take ba, amma ke shine kike so kicuci yaronmu, to ALLAH yakama ki duk naji abunda Yaya Maryam tafad'a, ashe haddasu some some akayi akan nono, oh ni Fatima! gaskiya umma taga jalala." taqare maganar had'e da tintsirewa da dariya tana tafa hannuwa, tayi hakanne saboda tadaqile tasirin damuwar dake shirin ziyartar Rashida akan zancen rashin dawowar iyayen nata da suka gama da Yaya Maryam.

Binta da kallo Rashida tayi tana murmushi, a zuciyarta tana mai addu'a, Allah ya dawwamar da irin wannan farinciki da Fatima ke ciki atattare da ita nahar abada.

Dr kuwa tunda yaji zancen Rashida na Shirin yayen little shima yafara shire shiren nema mata takardun shedar kammala primary, dama sun tab'a maganar karatun da ita tafad'a masa primary ne kawai tayi har take basu labarin yanda tahad'u da abban little a sanadiyar rashin son karatunta sunata dariya, bai wani sha wahalar samun takardun ba saboda yanda komai ya lalace zaka iya samunsu matuqar akwai kud'i atare dakai, kafin kace me har yagama had'a takardun da cike mata form d'in shiga makarantar gaba da primary na wannan shekarar tare da taimakon Fatima batare da sanin Rashidar ba, akoda yaushe Rashida cikin farinciki take natakusa yaye little Nuraddeen tahuta da tsutsa ita kuma Fatima nayimata dariyar maida ita makaranta da suke shirinyi bada saninta ba, wanda ALLAH kad'ai yasan yanda za'a kwashe matuqar har yanzu tana nan akan bakanta na rashin son karatu.

Satin yaye little nakamawa tahad'a gaba d'aya sauran kayansa dake hannunta takaiwa Fatima suna tayi mata dariya ita da Dr.

"Ikon ALLAH, maman boy wannan wace irin korace haka akeyiwa takwara, anharhad'o komai nasa sai kace zai bar gari"

"Uncle sunanta kora da hali, gaba d'aya nayi handing over dashi, gashi ga mamarsa kar akoma cewa ansanni, yabarni inhuta abuna ko d'akina kada yakoma leqawa har sai jinin jikina yadawo."

"E'em kedai! karfa ayi haka bayan kwana biyu kice kinyi missing d'insa."

"Cab! Uncle little d'in?, Ai yanda take addabar rayuwata da daddare babu wani missing d'insa da zanyi."

"Kika ce?"

Tayi dariya kawai had'e da juyawarta tabar falon fatima nafad'in.

"Muna nan dake zakizo ganinsa muma muyi maki handing over."

Randa akayi yayen little kuwa ba qaramar rigima suka shaba duk daya saba kwana wajensu amma sai kace wanda aka fad'awa yayesa za'ayi haka yadinga yimasu kuka cikin dare, sunyi lallashi har sungaji amma yaqiyin shiru, idan tayi tagaji taba Dr shima yayi nashi lallashin amma kamar ana sake sake turashi,

ALLAH sarki Rashida tun tana iya sauraren kukan har takasa tasa pillow ta dad'e kunnuwanta amma bata dena jiba, tashi tayi tayi zaune tsakiyar gadon tanajin kukan nasa har cikin ranta batasan lokacin da itama tafashe da kuka ba, batasan meyasa ba ko kad'an bata iya jurar kukansa gashi bazata tab'a iya fita da sunan taje taduba saba, d'aga hannuwanta tayi sama ahankali tafara yimasa addu'a.

"Ya ALLAH Kai kake karb'ar addu'ar mahaifiya ga d'anta, ALLAH kasa masa dangana, ya ALLAH kamar yanda yabar nono na ayau ALLAH karabashi da duk wani musibar rayuwa tun daga qanqantarsa har zuwa girmansa, ALLAH kasa yazamo mai juriya da haquri acikin rayuwarsa kuma ka albarkaceshi kasa amfani mai tarin yawa acikin wanda yasha na tsawon wannan lokacin."
Chapter 84 · 0% Book details