← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 160

Sashe 151

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yabata amsa yana kallon yanda duk yanayinta ya sauya.

"Kar dai kice mun kin tsoratane?."

"Sosai wlh."

"Ki kwantar da hankalinki kinji ko, in sha ALLAH zamu Isa lafiya."

Sannan ya tada motarsu sukaci gaba da tafiya, har suka iso cikin kano batool bata sake cewa uffan ba gudun kar maganar da zatayi ta d'aukar masu hankali don ta matuqar tsorata fiye da tunani, shi kuma dayaga hakan sai bai cemata komaiba fata dai su isa lafiya.

Suna kawowa daidai wata roundabout motar data d'auko Dr Nuraddeen na wucewa zasuyi yuton ta d'ayan titi ta jami'an da suka biyota baya ta shigo aguje lokacin little shi kuma ya shigo sai batool ta saki wata irin qara wacce ita tasa little rud'ewa saidai yaji sun bugi motar jami'an tsaron,

Da sauri Dr Nuraddeen da har motar da yake cike ta juya ta d'ayan titin ya hango abunda yafaru ya tsaida drivernsa.

Nan take go slow ya cika wurin don gaba d'aya gaban motarsu little data buga data jami'an tsaron ya molaqe Amma su babu abunda ya samesu, don little qoqarin ma bud'o gambun motar yakeyi yafito, d'an ja da baya motocin suka shigayi sannan aka taimaka masa yafito had'e da d'an dafe goshinsa daya bugu ya da sauri ya zagaya inda batool take, ita kam da alama somewa tayi da sauri wani mai keke napep ya miqo ruwan leda aka yayyafa mata ta farfad'o tana fad'in.

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, Abbana."

Murmushi little yayi sannan yariqota tafito daga cikin motar wanda daqyar ta iya takawa saboda qafafuwanta da suka kumbura, adaidai lokacin Dr Nuraddeen ya qaraso shida drivernsa yana fad'in.

"Subhanallahi, injin ba abunda ya sameku?,"

Juyowa little yayi da sauri don bazai manta muryar wannan mutumenba, sai da Dr Nuraddeen yakusa fad'uwa saboda wani irin jiri daya d'ebesa lokacin da idanuwansa suka sauka akan fuskar little dake fad'in.

"Ko kad'an Alhamdulillah, ALLAH ya tsare." Nan ma gabansa ne ya sake fad'uwa tuna wannan muryar wanda yarage masa hanya ne jiya da daddare a jahar borno, Abu mafi qololuwar ban mamaki dashi shine yanda sak fuskarsa irinta Rashidarsa, to wannan wane mutumne dake bibiyarsa tun jiya, yana wannan tunanin ne yaga suna qoqarin barin wajen da sauri batool tajuyo had'e da dawo wajen motar tana fad'in.

"Abu sumayya su hassana fa."

Sai alokacin shima yatuno dasu da sauri ya qarasa ta gaban motar ya bud'e lock d'in daya danna tin tasowarsu don kada suyi yunqurin bud'e gambun tunda basaji, sannan ya dawo ya bud'e bayan, ga mamakinsa sai yaga gaba d'ayansu sun fad'o qasan sit d'in d'aya ta taushe d'ayar kuma baccinsu sukeyi, hamdala yayi tare da d'auko ta saman wani ya karb'eta sannanya d'auko d'ayar yana duddubata, haka batool ta qaraso wajen batare da taji nauyin cikin dake jikinta ba takarb'i ta hannun mutumen Wanda gaba d'ayansu sun tashi baccin sai faman murza idanuwa sukeyi da hannu suna kallon mutanen da sukayi cincirindo wajen, kallo Dr Nuraddeen yabi yaran dashi, ahankali ya furta subhanallah, saboda tsantsar kamarsu daya gani da wannan mutumen daya taimakesa jiya, Kai ko baka tambaya ba kasan 'ya'yansa ne, banbancin kawai shine hasken fatar da yaran suka fishi Wanda da alamu na mahaifiyarsu ne dake d'auke da tsohon ciki.

Gaba d'aya rud'ewa Dr Nuraddeen yayi ya rasa tawa zaiyi cikinsu, ta jami'an tsaron da wasu daga cikinsu sun fad'o sun d'anji rauni kota wud'annan ahali dake da matuqar yanayi da habibty d'insa.

Baisan lokacin da yaba drivern umurni yaje yayi qoqarin fiddo motarsu little data shige cikin ta 'yan sandan ba shi kuma yabi su little dake qoqarin komawa gefen titi yana fad'in.

"Sannunku ko.?"

"Yawwa" little yafad'a yana qoqarin amsar hassana a hannun batool bayan ya ajiye hussaina qasa.

"Am don ALLAH nace daga jahar borno kuke ko?"

"Eh, Amma kamar jiya kaine muka ragewa hanya da daddare zaka sauka hotel ko."

"Exactly! 'yatah."

Dr Nuraddeen yafad'a cike da mamakin yanda tagano shi yana miqawa little hannu.

"Bawan ALLAH baka ganeni bane, nine fa wanda kuka taimakawa daren jiya da taxxi d'in data d'aukoni ta samu matsala, Katina.!"

"Eh maigida natuna.." little yafad'a yana d'an dafe goshinsa inda yabugu, da alama wajen zafi yake yimasa,

"To barka da arziqi, kuzo mana ga mota can kada kutsaya abakin titi ga rana sosai, ga motar mucan kushiga kafin afiddo waccan d'in ko don yarannan."

Yaqarasa maganar jikinsa har rawa yakeyi yawuce gaba yanayi yana waigowa yana kallon su, idan ya kalli little ya kalli yaran har suka isa jikin motar ya bud'e masu suka shiga, 'yan jarida kam ba magana ga labaran da zasu iya bugawa amma tsananin go slow da taron mutane yahana tunda motacinsu nacan baya.

Anyi anyi aciro motarsu little amma taqi tashi balle asa ran za'a cirota don haka sai Dr Nuraddeen yace suciro kayansu sai su ajiyesu gida idan yaso daga baya in ancire motocin ajikin wajen sai yadawo ya d'auka, duk da little baiso hakan ba haka yayi haquri sukaje shi da drivern daya d'auko Dr Nuraddeen suka kwaso kayan aka zuba a boot, sannan yaba wani jami'i cikin jami'an tsaron da baiji ciwoba maquddan kud'i yace, a d'auki mutun ukun da sukaji rauni akaisu asibiti, sauran kuma suraba in Sha ALLAH zai biyo bayansu.

Sannan suka d'auki hanyar zuwa anguwar su batool, shi dai Dr Nuraddeen baisan ko Ina ba acikin garin asalima sai kalle kallen yanda garin ya sauya gaba d'aya yakeyi don komai ya canza badon ana rubuta wasu abubuwa da wurairai ba zai iya rantsewa yace ba'a cikin kanon daya sani yake ba, drivern kawaine daya san waje ke tuqinsa cikin natsuwa da kwanciyar hankali har suka isa anguwar, ita kanta batool taga wasu canje canje da dama tunda shekara bakwai ba wasa bane, hatta gidan nasu data hango ancanza masa tsarin wajen qofar shiga da fenti sai wasu sabbin gine gine data gani acikin anguwar tasu, ana kaiwa bakin qofar gidan drivern yayi horn saboda abud'e gate a tsammaninsa zasu shiga ciki ne Dr Nuraddeen yace a'a ya tsaya waje tunda wucewa zasuyi basai an bud'e ba.

Abba dake tsaye yana faman safa da marwa lokacin angama saukar alqur'anin ana addu'a suna jin horn gaba d'ayansu sukace Alhamdulillah tamkar an sanar masu da cewa su d'inne, da sauri su uncle da Abba sukayo waje jikinsa har rawa yakeyi yana qoqarin fad'uwa amma haka yaci gaba da nufatar bakin gate d'in da sauri da sauri, daidai lokacin mai gadi ya hangame gate d'in batool tafito ita da little suna rirriqe da gambunan motar, wani irin farinciki ya lullub'eta lokacin data hango mahaifinta kyakkyawan dattijo da gaba d'aya gashin kansa izuwa na fuskarsa yayi fari saboda tsufa, Amma hakan bai hana ka hango kyawonsa da hasken fatar da ALLAH yayi masa wanda adalilinsa ake kiransa da alhaji umar fari, ahankali take takawa izuwa garesa don bazata iya rugawa ba idanuwanta na zubar da qwallan farinciki, yayin da shikuma yafad'i qasa had'e dayiwa ALLAH sujudushshukur, su uncle ma tsaye sukayi suna dariya had'e dasa hannuwa suna goge qwallan da suka zubo masu yara da manya kuwa sukayo ruu wajenta suna yimata oyoyo. daqyar ta iya samu suka barta taqaraso wajen mahaifinta da alokacin ya d'ago daga sujadar da yayi, wani irin kuka ta kucce dashi had'e da durqushewa agabansa ta dafa qafafuwansa tana fad'in.

"Kayafeni Abbana natuba, nayi nadamar duka abubuwan b'acin ran dana saka ka aciki, nayi tir da halina da nazamo bijirarriyar 'ya agareka bayan duka soyayyar daka nunamun, haqiqa inuwar iyaye da kuma alfarmarsu da 'ya'ya suke samu awajensu tafi qarfin wofantarwa da kuma fifita ra'ayin zukatansu akanta, Abbana..."

Bata qarasa ba da sauri Abba ya duqa ya d'agota shima yana hawayen sannan yasa yatsunsa akan fuskarta yana goge mata itama hawayen dake zubowa afuskarta.

"Ya Isa haka Batool, duk da laifin nakine amma kuskuren nawane, mezai Hana iyaye sudinga fahimtar 'ya'yansu da kuma kwatanta yimasu adalci, tabbas ni nahaifeki Amma banida ikon sarrafa rayuwarki da kuma zuciyarki tayanda zance lallai sai kinyi abunda nake so, ALLAH nagode maka, kaine maji roqon addu'ar bayinka ya ALLAH, Ina godiya agareka daka iso mani da 'ya 'yana lafiya."

Yaqare maganar tare da rungumota ajiki yana maijin wani irin farinciki,

Kallon little dake tsaye dasu uncle h ana gaggaisawa yayi bayan yayiwa Dr Nuraddeen godiya yara sunciro masu kayansu sun wuce, a hankali ya bud'e masa d'ayan hannunsa yana fad'in.

"Zo mana yarona, ko har yanzu baka haqura ba fushi kakeyi da abunda abban naku yayi maka?."

Da sauri little yaqarasa wajensa cike dajin kunya yad'an russuna yana gaishesa, cikin hawayen nadamar abunda yatab'a yimasa randa yadawo da batool gida ya saketa tayi wajensu uncle tana gaishesu shi kuma yasa duka hannuwansa biyu ya rungumo little sosai ajiki yana fad'in.

"Haba Nuraddeen, nifa abbanku ne, don me zaka nesanta kanka agareni? kai da batool matsayi d'aya kuke dashi yanzu agurina, don ALLAH kayafemun duka abunda nayi maka abaya ko da sau d'ayane ka amsheni amatsayin mahaifinka kaima."

Shidai little baice komai ba don yanzu shima hankalinsa na wajensu baffa, ya matsu yaje garesu da albishirin mahaifiyarsa tabashi damar zuwa garesu tare da zuwa qasar da mahaifinsa ya tafi ya nemosa, Wanda ya tabbata hakan zai yiwa su baffa dad'i sosai, muryar Abba daya ji yana fad'in ko sai naduqa qasa zaka yafemun laifina d'ana had'e da qoqarin duqawar tasashi sairin fitowa daga tunanin da yake shima ya rungume abban yana fad'in.

"Abba duk abunda zakuyi mana aduniya kunfi qarfin duqawa agabanmu domin soyayya takansa kuyi mana hakan, wancan abun daya faru Abba yariga daya wuce, ka yafemana bisa damuwar da muka saka ka aciki domin mun dad'e da fahimtar hakan kuskurene."

'Dan juyawa yayi tacan gefen gate ya hango su hassana sun b'uya suna leqo mutanen gidan, don kam yanda sukaga ana koke koke bazasu d'auka na farinciki bane dole suyi takansu tunda d'an banzan wayone dasu, Abba ga matanka can sun b'oye wataqil fushi suke baka tarbesu ba.

Daidai lokacin ya hango shurahbil ya nufi wajensu don tun d'azu batool ke nuno masu irin 'yar b'uyar da sukeyi suna leqowa su koma ana dariya shine yatafi wajensu shima yana dariyar.

Hannu ya miqa masu har hassana zataje, hussaina tajaye hannunta tana fad'in.
Chapter 151 · 0% Book details