← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 160

Sashe 11

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai umma nifa inada ilimin arabi, taya zakice d'aya muke da wannan abar dako tsarki batayi balle tasan farillan arwala dana sallah kuma har kice saita fini gata wai don d'ai banida ilimin boko, nidai don ALLAH kubarni bana son karatunnan wlh nafison aure akansa" awannan karon kasa cewa komai mahaifiyar tata tayi harna tsawon wasu lokuta maganganunta kad'ai take ji nayi mata yawo a k'wak'walwa, a inda take tadawo tarik'o hannuwanta ta zaunar da ita sannan itama ta zauna suna fuskantar juna tace "Rashida kifad'amun gaskiya, meyasa kike son ayi maki aure ba tare da kinyi la'akari da wud'annan qananan shekarun da kike dasu ba."

"Umma nima ban sani ba, kawai ji nakeyi ina tsintar kaina a wasu lokutan cikin yanayin sha'awar son yin auren."

"Rashida kin kuwa san me kalmar aure kenufi?"

"Eh malamin islamiyarmu yace mana shine kasantuwar mace da namiji a inawu d'aya bayan angabatar da sadaki da kuma waliyai da shedu, sannan yace ashari ance shine idhalu shai'i fishshai'i wato shi..." Saurin dakatar da ita umma tayi gabanta nafad'uwa had'e da cewa

"Ya isa Rashida na yarda kina da ilimin arabiy kuma ke ba daqiqiya bace kamar yanda muke fad'a amma da kin amince dayin karatun bokon ma koda secondary ne saboda shi yana taimakawa wajen iya zaman takewa da mutane, ayanda kikayi bayani aure baya kasancewa har saida samuwar namiji da mace, to ke yanzu ina namijin da kika tanada ayi maki auren."

"Umma akwai wani Rabe d'an gidan mai koko dake sona idan kuma bakwa sonsa zaku iya zab'amun duk wanda kuke so"

Wata irin ajiyar zuciya iya ta sauke don tasan abun da kamar wuya mahaifin nata ya amince da auren yaron saboda rashin cancantarsa, tashi tayi ranta adagule taci gaba da aikace aikacenta batare da tasake bita kanta ba.

Adaren ranar kasa bacci mahaifiyar tata tayi saboda tunanin maganganun 'yarta, in banda juye juye babu abunda takeyi domin tasan mahaifinta bazai yarda yayi mata abunda take so ba kuma ab'angaren yarinyar tafahimci kalamanta da gaske takeyinsu har cikin zuciya, tanajin tsoron kada rashin yimata abunda take son ya jefata cikin wani mugun hali ko iftila'in rayuwa da zai kaita yabaro ko kuma yatab'a mata mutunci da kuma kimarsu, fashewa tayi da kukan da yasa baba farkowa daga baccin da yakeyi a tsorace had'e da cewa "subhanallahi maman Rashida lafiya kike kuka awannan tsohon daren haka, me akayi makine, meke faruwa dake ne?"

Cikin shesshekar kuka tace

"Babu komai malan, kawai Ina sone don ALLAH kabar yarinyar nan tayi aure shine alfarmar da zan roqa awajenka amatsayina na mahaifiyarta." Tsaki yayi had'e da jan mayafinsa ya komawarsa yakwanta yana fad'in dama wannan maganarce ta zaunar dake kina kuka?, To wlh kinji na rantse bazanyi mata aure yanzu ba dole sai tayi karatun da nake so."

"Kada kace haka don ALLAH, bamusan awane yanayi take acikiba wanda yasa ta furta hakan, katunafa mu iyayene daya kamata ace 'ya'yayenmu na alfahari dasu, kuma kada kamanta su amana ne da ALLAH yabamu ahannayenmu bai kamata ace munwofantar da buqatunsu da ALLAH yad'ora akanmu ba, don ALLAH tunda bata son karatunnan kayi hak'uri muyi mata auren tunda bamusan abunda ALLAH kenufi ba."

Fita batunta yayi yaci gaba da baccinsa tanata faman basa hak'uri da rok'onsa, tun yana jinta har yadena bacci ya d'aukesa, data fahimci hakan taje ta d'auro arwala ta tada sallah tana fad'awa ALLAH daya sauko da zuciyar mijin nata ya amince da yima 'yar tasu aure,

Haka yatashi da asuba ya sake tadda ita tana kukan, shiru yayi yana kallonta na tsawon mintuna kafin yayi tsaki had'e da mik'ewa yabar d'akin, arwala yayi lokacin har antada sallah anan masallacin dake kusa dasu yafice da sauri, be dawo gidan ba har saida rana tafara fitowa nan ma sake iskota yayi tana kukan, tsaki yaja sannan ya zauna agefen gado yana kallonta yace,

"Yanzu wannan kukan da kikeyi tun jiya fisabillahi bai isheki ba?"

"Taya zai isheni bayan fargaba da tsoron halin da 'yata zata shiga ciki yana dasqare azuciyata," girgiza kai yayi had'e dayin wani tsakin na ba adadi kafin yace "to yanzu ya kike son ayi?."

"Kayimata abunda take so tunda bai sab'awa shari'a ba."

"Ita fa rantsuwar da nayi?."

"Zan fidda maka da kono."

Kallonta yayi cike da tausayin yanayin data koma tsakanin jiya da yau, macece ita mai hak'uri da kuma juriya, iya kyautatawa da kuma biyayyar aure tana yimasa, ko kad'an bata son taga ransa yab'aci shiyasa shima bayason ganin nata b'acin rai, matuqar yin hakan zaisa tayi farinciki kamar yanda take faranta masa to zai amince da buqatar yarinya, nisawa yayi sannan yace taje takirawo masa ita, mik'ewa tayi duk jikinta ba k'wari taje takirawota, bata jima da dawowa ba sai gata tashigo, gaidasu tayi suka amsa mata sannan tanemi waje tazauna,

Gyaran murya mahaifin nata yayi had'e da cewa, "Rashida naso inbaki ilimin dako bayan ranmu zai amfaneki kuma kiyi alfahari dashi amma hakan ya cutara saboda wani buri da kike dash a ranki, mahaifiyarki nagartacciyar matace da tasan dukkanin haqqoqan zaman takewa da bazan iya jurar halin dana ganta daga daren jiya zuwa yau ba, don haka bisa roqo da tayi nahak'ura da ra'ayina na amince da naki kuma zanyi maki abunda kike so saboda wanzuwar farincikinta amma Ina so kisa aranki kuma kirubuta ki ajiye azuciyarki cewa ilimi shine gishirin zaman duniya da bawa kan ribatu dashi adukkanin tsawon rayuwarsa kuma ko yaushene zaki dawo da kanki kinemesa" Shiru yayi na wani d'an lokaci sannan yace,

"Don haka idan kinada wanda kike so na amince ki sanar dashi cewa yaturo iyayensa."

"Baba kayi hak'uri amma ni banida wani masoyi sai Rabe na gidan hajia mai koko." Dariyar takaici yayi sannan yace, "wannan baiyimun ba kicanza wani, domin yaron duka duka shekarunsa basu wuce ashirin ba taya zai aureki har ya iya kula dake, yanzu haka yana can makarantar kwana aji biyar shi yaje yanemi ilimin, to ta ina yaga inda zai ajiyeki."

"To shi kad'aine ke sona baba Amma zaka iya zab'amun duk wanda kaga ya dace." Cike da mamaki yake kallonta kafin yace, "kinsan me kike fad'a kuwa."

"Eh baba nasani kazab'amun ko waye zanyi masa biyayya kuma zan zauna dashi."

"Shikenan tashi kitafi." Yafad'a yana murza hannayensa daya had'e waje d'aya,

Bayan tafita yakalli mahaifiyarta yace "Kingani abunda nake son kigane kenan, tadami mutane da aure take so amma gashi takasa fiddo da wanda zata aura, ina tausayin rayuwarta saboda nasan SANNU SANNU bata hana zuwa..., ba baki nayi mata ba amma duk daren dad'ewa inada yaqini akan sai taga illar rashin tsayawa tayi karatunnan, kiduba fa ko had'a haruffan hausa bata iyayi taya rayuwa zata zauna ahaka."

"Gaskiyane malan amma mubita da addua shiyafi, yaran zamanine kahaifesu baka haifi halin suba"

Anan ya zauna yana bata labarin abunda yafaru jiya tsakaninsa da malamin makarantarsu d'aya iskosa akan matsalar rashin gane karatunta sannan yafad'a mata shawarar daya yanke akan mijin da zai aura mata, fatan alkhairi umma tayi had'e da fatan Allah yasa wanda aka zab'a mata d'in ya amince da ita....

_Note_
_A wannan gab'ar yakamata iyaye su fahimci cewa duk wani kalami da 'ya'yansu zasuyi yakamata ace sun natsu kuma sun zauna sun fahimcesa kamar yanda mahaifiyar Rashida tayi domin kowane yaro yanada k'wak'k'warar hujja da dalili akan kowace irin kalmace da zai fad'a Wanda sune zasu iya banbance mai kyauce ko kuma akasin haka, kamar dai Rashida ga bayanin data zauna tayiwa mahaifiyarta duk mai hankali yasan cewa zancen auren da take fad'in tana so har azuciya ne bawai abaki kad'ai ba, kuma kowane yaro da yanayin qaddarar da Allah ked'orasa akai tun yana qanqaninsa wacce iyayene solar tabbatuwarta akansa, don haka iyaye mudinga natsuwa muna nazartar kowane harafi kuma kowace kalma tare da kowane muradai na 'ya'yanmu don sama masu mafita akan abubuwan da zasu iya jefasu da uma mu cikin nadama da dana sani nahar abada, ilimi nada amfani sosai amma idan jiran asamesa zai iya jefa rayuwar 'yarki/ka cikin wata matsala za'a iya jinginesa har sai bayan an kauda waccan matsalar sai aci gaba da nemansa, ubangiji ALLAH yasanya muradanmu na alkhairi su daidaita dana 'ya'yanmu domin tabbatuwar farincikinmu da kuma samuwar ingantacciyar rayuwarsu, ba abun mamaki bane abunda Rashida ta aikata domin yasha faruwa ga wasu 'yan matan kuma yakanci gaba da faruwa, wasu kan furta da baki wasunsu kuma kannuna alama, amma sai kaga iyaye sun kasa fahimtarsu tare da kauda idanuwansu akan abunda suke son (aure) sai kaga sun lalace daga qarshe ma sun jawo masu abun fad'i aduniya wal iya zubillahi ALLAH kashirya mana zuri'armu_

*_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU👏😭_*
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___8💎

Bin bayanta yayi da kallo har saida tafice sannan yayi ajiyar zuciya, azahirin gaskiya yayi mamakin yanda Rashida ta iya bashi amsa kai tsaye batare da tayi shayin komai ba, amma azuciyarsa yaga nagartar da kuma ingancinta data iya bayyana abunda ke cikin zuciyarta wanda da yawan 'yammata irin wannan nadamunsu amma sai su gagara furtawa balle har asama masu mafita, Wanda kuma yin hakan kuskurene dake haifar masu da jefawa cikin halaka, koda yake mafiya lokuta iyaye sune sila saboda rashin sauraren 'ya'yan nasu da wani dogon buri da suka d'orawa kansu, mik'ewa yayi tare da d'aukar littafin dake gabansa yanufi ajin da yake da darasi da d'alibansa.

Yinin ranar abu d'aya ya dinga tunani shine kalaman d'alibar tasa, bayan yayi nazari da Kuma dogon tunani ya yanke shawarar iske mahaifinta yauidan an tashi makaranta, ana tashi kuwa ya hangota bakin gate ita da abokananta zasu fita da sauri yaturo wata d'aliba be takira masa ita.

"Rashida malan Idris nakira ki" yarinyar tafad'a had'e da ficewarta don dama gida tanufa, kallon Rashida meenah qawarta tayi sannan takalli sauran friends d'insu had'e da cewa,

"Anya rashida malan Idris ba sonki yakeyi ba?"

"Wlh Nima haka nake zargi shamsiya" duka takaimasu had'e da cewa,

"Bana son sa'ido, ni malaminane babu komai tsakanina dashi"

"Hmm mudai bari muwuce kya cimmana"
Chapter 11 · 0% Book details