Sashe 1
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[8/17, 10:16] Billy S Fari: 🚶♀️🚶🏻♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻♂️🚶♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞
*DOMIN FARINCIKIN KINE SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO (OUM AFFAN)*❤️
_ALHAMDULILLAH INA GODIYA GA RABBIL IZZATI WAL JABARUD DAYA BANI IKON SAKE DAWO MAKU DA WANNAN SABON LITTAFI NAWA DAKE CIKE DA 'DIMBIN DARUSSA DA NAKE FATAN SUZAMO TSANEN DA ZAMU IYA TAKAWA WAJEN GYARA KURA-KURANMU, WANNAN LITTAFI GABA 'DAYA QIRQIRARSA NAYI BISA LA'AKARI DA WASU ABUBUWAN DAKE FARUWA ACIKIN RAYUWARMU TA YAU DA KULLUM DON HAKA IDAN KAGA YAYI KAMA DA RAYUWAR KA/KI TO AKASINE KAWAI, SAI MUYI QOQARIN GYARAWA, FATANA ALLAH YA YAFEMUN KURAKURAN DA ZASUZO DAGA CIKINSA KUMA YASA DANI DAKU MUYI TARAYYA ACIKIN LADAR DA ZATAZO ACIKI👏🏻, HAR ILA YAU BAZAN MANTA DA ADDU'AR FATAN ALKHAIRI AGAREKU BA *YA HAJJA CE* DA KUMA TAWAN *SALMA ABALI (LITTLE PRINCESS)* INA ROK'ON ALLAH DA YATABBATAR MAKU DA ALKHAIRANSA KUDA AHALINKU ADUK INDA KUKE, *MLF*_💋👏🏻
Page___1💎
Tafe suke cikin wata kyakkyawar mota k'irar BMW da kallo d'aya zakayi mata kasan cewa sabuwace dal da ba'a dad'e da fiddota acikin ledar taba saboda yanda take faman sheqi da qyalli, cikin natsuwa matuqin motar ke tuqinsa yayin da wacce ke zaune agefensa da tsohon cikinta dake nuna alamar ko meye aciki neman fitowa yakeyi akoda yaushe, muskutawa tayi sannan tajuyo cikin zaquwa had'e da kallonsa tana cewa,
"Abu sumayya wai wannan wace irin tafiya ce kakeyi haka?, Don ALLAH kataka motar nan da sauri, wlh namatsu naganeni agaban Abbana da kuma ummata." yanayin yanda take maganar kad'ai tana faman kashe murya shi zai tabbatar da cewa ita d'in matarsa ce, cikin k'warewa da iya tuqi ya juya sitarin motarsa ya shiga kwanar dake gabansa tare da d'an qara gudun motar kad'an sannan yace,
"Gimbiya! haka yayi maki?." Yafad'i hakan batare daya d'auke idanuwansa daga kan titin da yake kallo ba "kad'an qara mana." tafad'a tare da juyawa ta sit d'in bayansu tana kallon yaransu 'yan mata su biyu dake kwance bacci ya d'aukesu, kallo d'aya zakayiwa yaran katabbatar da cewa 'yan biyune saboda tsantsar kamar da sukeyi da junansu, wata kyakkyawar ajiyar zuciya tayi had'e da shafa tulelen cikin dake jikinta tace,
"Alhamdulillah, Abu sumayya namatsu mu isa gida naga farincikin da zai bayyana a fuskar Abbana idan yaganeni tare da wud'annan kyawawan jikoki da ALLAH ya albarkacesa dasu bayan rabuwarmu dashi na tsawon shekaru bakwai, ga kuma wata kyautar agefe tare dani wacce nake fatar Allah yasa takwaransa ne aciki, natabbata hakan zai qara sakasa cikin farinciki sosai, Kuma yasake gusar masa da abun da nayi Masa azuciya"
"To ALLAH ya saukeki lafiya gimbiya kuma yabamu abunda muke fata don cikar burinmu da kuma tabbatuwar farincikin Abban da kike hasashe."
"Amin Abu sumayya." tafad'a tare da d'ora kanta saman kafad'arsa, shirune yabiyo baya na tsawon mintuna biyar kafin tasake cewa, "Wlh gani nakeyi kamar bama tafiya, hanyar tamkar ana qaramata tsawo, wataqil don na jima ban bita neba?." murmushi yayi had'e da cewa
"Kai gimbiya d'oki dai ne kikeyi, Amma ai ba laifi ina tafiya sosai, kiyi hak'uri, ai sannu a hankali zamu isa in sha ALLAH kilometers biyar ne yarage mana, kinji hausawa nacewa SANNU SANNU bata hana zuwa...." Kafin yarufe baki yaji tace, "Sai dai adad'e ba'a kai ba, kuma ni shine bana so." taqarasa maganar tana turo baki had'e da mik'ewa zaune daidai, "Abu sumayya naji marata tad'an murd'a." Rage gudun yayi had'e da cewa,
"Subhanallah Gimbiya ko abun yazo ne?." Yafad'a tare da juyowa yana kallonta a d'an firgice, yatsina fuska tayi sannan tace,
"Bana tsammanin hakan, saboda idd na sai next month on 13 yanzu kuwa kaga muna 25 ne dis month."
Tana rufe baki wata qatuwar mota tayo cikinsu aguje tare da gittawa agabansu, ji kakeyi qiiiiiiiiii...gigigigif..karaf, tabugi motarsu tafad'a jikin wata motar dake tafe bayansu itama tana k'ok'arin kaucewa ta d'ayan gefen, sosai yake qoqarin juyar da staring motar da dukkanin k'arfinsa da kuma gwanewarsa amma da yake duk qaddarar da ALLAH yatsaro akan bayinsa ko suna so ko basa so sai wannan alqalamin da aka dad'e da rubuta qaddarsa ya tabbatar da ita agaresa, duk iya qoqarinsa kasa iya sarrafa motar yayi balle ya samu nasarar tsaida ita waje d'aya, ganin haka yasashi qoqarin riqo matarsa da tuni kanta ya bugi glass d'in motar yafita tacan waje yayin da gangar jikinta na acikin motar, cikin yanayin fad'uwar gaba da kuma firgici yafara k'ok'arin jawota sai ji yayi sun bugi wani abu da yasa motar tasu tsayawa cak, daidai lokacin shi kuma kansa yabugi dashboard d'in motar da k'arfi wanda yasa nan take yaji gaba d'aya na'urorin dake aiki a sassan jikinsa sun tsaya cak, hatta jinsa da ganinsa ji yayi suma sun d'auke alokaci d'aya, cikin tashin hankali mutanen da suka tsaitsaya akan titin suna salati ganin yanda wannan tashin hankalin ke faruwa sukayo kansu ganin motar ta tsaya don kawo masu d'auki, gaba d'aya motar ta nad'e waje d'aya sanadiyar wani makeken dutsi da suka buga, kallo d'aya zaka yiwa motar ka rantse baza'a samu rayuwar ko d'aya daga cikin mutanen dake cikin taba, ganin jini na malalowa tak'ark'ashin motar ya sanya mutanen himmatuwa wajen b'alla gambun motar ta kowane gefe, shi suka fara jawowa kafin suyi nasarar fiddo da matarsa fuskarta gaba d'aya jini ya wanketa ta yanda bazaka iya gane ko wace itaba, cikin tashin hankali suka ida fiddo da ita daga cikin motar tamkar gawa saboda ko motsi ba tayi, hankalinsu bai tashi ba sai lokacin da suka lura da tulelen cikin dake jikinta sai faman motsi abunda ke ciki yake ga kuma jini d'aya b'alle mata na faman kwararowa daga k'asanta, cikin rud'ewa wani daga cikinsu ya d'ago kai yana kallon wud'anda ke kan mijin nata yace,
"Matarnan tana buqatar taimakon gaggawa." Bai rufe baki ba mijin nata da tun d'azu ake faman yayyafa masa ruwa ya farfad'o tare da bud'e ido, ko kad'an babu alamar k'warzane ajikinsa da zai nuna yaji ciwo wanda hakan yaja hankalin mutanen akan doguwar sumace yayi suka fara yayyafa masa ruwa, k'ok'arin bud'e baki yayi yayi magana amma yakasa saboda lumfashinsa da yakejin yana qoqarin fin qarfins, yana gani aka tallabi matarsa aka nufi cikin wata motar da ita don ceto rayuwar abunda ke cikinta don gaba d'aya alokacin bata rayuwarta suke ba saboda ganin yanda cikin nata ke motsi kamar zai fasa cikin ya fito, sake yunqurawa yayi zaiyi magana idanuwansa na hawaye yana kallon yanda cikin nata ke motsi amma yakasa, kamar wanda aka tsikara da qarfi yajuyo ya maido kallonsa awajen motar tare da d'aga hannu yana nuna masu, da k'yar yabud'e baki yace, "'ya'yana..." Bai k'ara saba jini yafara fitar masa abaki tare da sakin hannunsa ya fad'i qasa, da gudu wasu suka d'aukesa suka nufi motar da akasa matarsa aciki lokacin har ana qoqarin barin wajen aka sakashi shima cikin motar tabar wajen dasu aguje, yayin da wasu suka nufi wajen motar suka fara qoqarin b'alla gambunanta na baya, koda sukayi nasarar b'alle gambunan motar basu ga komaiba a saman sit d'in sai da suka leqa a k'arqashin motar sannan suka hango qananan yara a qarqashi, gashi motar ta molak'e waje d'aya babu isasshen wajen da za'a iya jawosu hakan ya matuqar tayarwa da mutanen wajen hankali saboda rashin sanin makomar yaran da kuma sanin ko awane hali suke ciki awajen.
Anan sukayi cirko cirko suna shawarar yanda za'ayi a fiddo yaran, wani mutumne daga cikinsu yabada shawarar tunda akwai wani gari dake nan gaba kad'an aje asamo k'wararrun masu gyaran mota da suka iya kwanceta da had'ewa suzo su kwance motar gaba d'aya a fiddo yaran ko nawane shi zai biyasu, haka kuwa akayi cikin mintuna ashirin wane yaje yazo dasu su biyu d'auke da kayan aiki, nan take suka fara aikinsu cikin k'warewa wanda cikin minti 30 sai gashi sun raba body d'in motar da shimfid'ar qasanta, da sauri aka ciro yaran har lokacin gaba d'ayansu bacci sukeyi, bazaka tab'a cewa daga cikin motar aka fiddosu ba saboda ba wadda tayi ko qwarzane acikinsu inba d'ayar data d'an karce agefen kuncinta ba wanda ga alama wani qarfene ya karjeta, "ALLAHU AKBAR" wud'an ke wajen suka fad'a cikin mamaki da kuma tsoron ALLAH da gasgata ikonsa don gaba d'aya babu wanda yasa ran za'a fiddosu da rayuwa saboda la'akari da yanda motar ta mokad'e waje d'aya, ana hakane suka jiyo qarar waya acikin motar a gefen da aka ciro matar, d'aya daga cikin sune yaje yana bin sautin qarar wayar dake cikin jikkar ya d'auko tare da ciro wayar ya d'aga.
"Assalamu alaikum." Shine abunda yafad'a kafin yaji an amsa masa ta d'aya b'angaren da, "wa'alaikassalam." Cire wayar yayi a kunnensa ya duba sunan dake yawo a screen d'in wayar yaga ansa _ABBANA_ hakan yasa yayi saurin maida wayar a kunnensa yana kallon sauran mutanen dake wajen tare dashi sannan yayiwa mutumen da tun d'azu sai faman tambaya yakeyi ina mai wayar bayanin abunda ke faruwa, Nan take yarud'e yafara tambayarsa adaidai wane wajene abun yafaru, cikakken bayanin yayi masa don akwai buqatar yazo yakarb'i yaran dake wajensu kafin yasan da komai sannan ya kashe wayar,
Kallon wud'anda suka kwance motar mutumen da yasa aka kirawosu yayi had'e da cewa, "bayin ALLAH nawane za'a biyaku?." Gaba d'aya suka amsa masa da "A'a alhaji, kabar kud'inka don ALLAH mukayi, ubangiji ALLAH yatsare kuma yatashi kafad'un iyayen yaran nan," suna gama fad'ar haka suka d'auki kayan aikinsu fuskokinsu cike da tausayin halin da akace masu iyayen yaran na ciki sannan suka wuce, duk mutanen dake wajen godiya tare da addu'ar fatan alkhairi suka yimasu saboda karamci da 'yan uwantakar addini da suka nuna.
Kasan cewar kilometers biyar ne yarage a tsakanin inda akayi had'arin da kuma cikin garin kano inda iyayen wud'annan yaran suka nufa yasa Abban nata d'aukar dogon lokaci kafin ya iso wajen, hakan yasa mutanen duk suka fara watsewa d'aya bayan d'aya lokacin har yaran sun farka sun fara kukan ina iyayensu suke,