← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 152

Sashe 99

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ikon Allah ne kawai ya kai Yashjub asibitin, dan shi kansa gani kawai ya yi har ya iso, amma ya ma manta ta Ina da Ina ya bi.

Yana shiga ya tarar da su carko carko a reception, da sauri Hajiya Mama ta k’araso tana zuwa yace”menene yake damunta??”
Ya yi mata tambayar yana addu’ar ya ji tace zazzab’i ko wani abun amma sai kunnuwansa suka jiyo masa sautin muryar ta taana cewa”ciwon ciki ne yake damunta…”
A hankali ta sake cewa”yanzu kuma ta fara bleeding!.”

Wani kalar mahaukacin bugawa k’irjin Yash ya shiga yi, bai san lokacin da ya durk’ushe a wajen ba kamar wani zararre….babban abunda zai tarwatsa shi a halin yanzu ya burkitashi shine idan aka ce cikin nan ya zube! Allah kad’ai ne ya san kalar tsantsar so da k’auna da kuma yadda ya kwallafa rai a cikin nan…..

Dai dai nan Dr ya fito ya kalli Hajiya Mama yace”pls follow me!”
Daga haka ya wuce ya nufi office d’insa.

Da kyar Hajiya Mama ta iya kamo hannun Yash ta rik’e sa ta mik’ar, suka nufi office d’in har da Ummi, aka bar Munirat ta shige wajen Manu.

Suna shiga likitan ya kallesu one by one kamar ya ce Yash ya fita dan ya san maybe shine Mijin, sai kuma kawai ya zab’i ya yi maganar a gabansa dan haka ya kalle su yace”have a seat”
Saida duk suka zazzauna tukunna ya ajjiye takardar da yake rubutu a kai a gefe, ya cire glasses d’in idanunsa ya kalli Hajiya Mama yace”ke grandma d’inta ce?”
A hankali Hajiya mama ta jinjina masa kai alamun”eh”.

tsura mata ido ya yi, kafin chan ya sauk’e ajiyar zuciya ya fara magana”ya kamata ku da kuke manya, ku dinga saka idanu a kan y’ay’ayenku da jikokinku..ku dinga gaya musu abunda ya dace da wanda bai dace ba..yanzu gashi saboda kyaliyarku da rashin kula Yarinyar nan ta je ta yi ta shan maganin zubar da ciki kuma mai k’arfi,we lost the Baby!!(cikin ya zube!!), but ni babban tashin hankalina anan ma shine ba lallai ta k’ara haihuwa ba! saboda maganin da ta dinga sha yana da k’arfi kuma ta sha sa over ne….

A hankali Yash ya tura kujerarsa baya, ya mik’e, ya juya ya fice….kamar wanda kwai ya fashewa a ciki haka ya fita daga asibitin ya hau titi ya kama tafiya ba tare da ya ma san inda zai je ba………….

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 34*

Ya yi tafiya mai nisa sosai, dan sai da ya kusan k’arasawa gida ma tukunna ya tari Napep ya shiga ganin jiri yana shirin zubar da shi.

Yana shiga gidan dai-dai su kuma su Mommy suna fitowa, har da Yassir domin zuwa asibitin.
Ba su kula shi ba shima bai kulasu ba, dan sun riga sun fito shi kuma napep Tana ajjiyesa ya afka cikin gidan.
yanayin sa ba k’aramin dad’i ya yi musu ba, dan ko ba’a fad’a ba sun san cikin ya zube ne shiyasa ya zama haka.

Direct side d’insa ya nufa,
yana zuwa ya rufe ko’ina ya turawa Siyama message ya ce ‘Manubiya ba lafiya’
Daga haka ya kashe wayoyinsa ya rufe ko’ina ya kwanta ya yi shiruu….

Su Yassir suna ɗaukar hanya, ya turawa Kausar message kamar haka”Yashjub yana gidan Daddy yanzu haka, alamun rauni, rashin kuzari da tashin hankali duk sun baiyyana a tare da shi, dan haka wannan shine lokacin da ya fi dacewa ki tunkaresa…get ready.”

Hajiya Mama da Ummi suka tarar a d’akin, Manubiya tana kwance tana barci dan tunda aka fito da ita ba ta bud’e ido ba.

Hajiya Mama ba ma ta san sun shigo ba, dan ta yi zurfi a tunani matuk’a…
idan akwai abu guda da za ta iya rantsuwa a kai shine ‘Manubiya ba za ta tab’a shan kwaya domin ta zubar da cikin jikinta ba’ sannan tunda har Doctor ya ce magani ta sha cikin ya zube tou kuwa maganin ta sha ba tare da ita kanta ta san tana sha d’in ba, bi ma’ana drugging d’inta aka dinga yi har cikin ya zube!…
Daga ita sai Yasira, Yusra da Yadira a cikin gidan sai gwaggwo sai Yashjub…
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun rajiun” ta shiga maimaitawa a cikin ranta dan waenda ta zarga su Yasira ne!
Tabbas Mommy ta cucesu ta cuci jikokinta muddin hakan ta tqbbata, dan ta san ita ce ta koya musu wannan muguwar dab’iar.
“Maama Ina wuni,ya mai jikin?”
Muryar Mommy ta katse mata sak’e-sak’enta.
D’agowa ta yi kawai ta zuba mata idanu, wanda hakan ya sanya ta sha jinin jikinta ta hau dibi dibi…kallonta kawai Hajiya Mama ta ke yi tana sakewa… a ranta tana mamakin ‘tayaya Mutum ɗan Adam zai iya zama wannan mugun mugun Azzalumi har haka!?’
Tun tana Uk take mugayen mafarkai akan su Yasira da Manubiya, shiyasa tunda ta zo aka ce mata suna gidan sam hankalinta bai kwanta ba, amma kuma dukda haka bata tab’a kawowa za su iya aikaata wannan mugun abu da take zarginsu da shi ba!.

Da kyar ta iya cewa”lafiya Alhamdulillah.Jiki da sauk’i.”

Shiruu duk suka yi, suna so su tambaya su tabbatar da cikin ya zube ne, amma kuma suna shakkar kar Hajiya Mama ta gano wani abun, dan iyaka kallon da take yi musu kad’ai ya sa sun sha jinin jikinsu,shiyasa suka ja bakunan su, suka yi shiru.

Baba Larai ce tace”itakam wannan cikin nata mai laulayi ne, Allah dai ya raba su lafiya!”.

Sai da Hajiya Mama ta d’an k’ura mata ido kafin tace”Ciki kam wanda ya bayar ya karb’a, sai dai mu yi addu’ar Allah ya kawo masu albarkaa, Allah ya sa wannan d’in mai ceto ne.”

Guntun murmushin da Ya’isha ta yi da kuma ajiyar zuciyar da Mommy ta sauk’e sai da Hajiya Mama ta gani ta kuma ji!! dan haka ta sunkuyar da kanta k’asa kawai ta hau salati a cikin ranta kanta yana wani irin juyawa..Tabbas an zo gab’ar da ya zamo mata dole ta shigo
rayuwar cikin gidan Daddy ta san abun yi, Mommy rub’abb’en seed ce da ya zamo mata dole ta b’intike ta tun kafin ta fara kisan gilla!…ta riga ta cucesu tunda gashi ta yi poisoning (ta gurɓata) tunanin su Yasira, ta kafa musu muguwar d’abia a cikin kansu!! Dan haka ta yi yaɗo kenan a cikin gidan ɗanta da ita da muguwar ɗabi’arta!
Amma bata makaro ba! Tana da yak’inin in sha Allahu za ta iya gyara jikokinta muddin ta samu ta ɓintiƙe Mommy aka samu ta yi nesa da su.

A hankali ta d’ago kanta ta kalli Mommy wadda sai a lokacin tace”To Allah ya kawo masu albarka”
Ita da su Yasira.
Cikin rashin son ganinta tace”ki tafi ki je wajen Yashjub! yana da buk’atar ki, za mu kula da Manubiya.”
Babu musu tace”to shikenan Hajiya Mama”dan itama so take ta gudu, saboda ta san tshoho duk inda yake ya fika wayo shiyasa take so ta yi nesa da ita gudun kar ta gano wani abun game da su..dan wannan kallon da taga tana yi mata ta san ba na lafiya bane ba.
“Allah ya k’ara sauk’i.” Tace, daga haka tayi musu
sallama, suma su Baba larai suka yi wa su Hajiya Mama sallama, daga nan duk suka fice zuciyoyinsu fess! kamar an yi musu bushara da gidan Aljannah.

Hatta Ummi sai da ta dasa ayar tambaya a kansu, itama ta fara zarginsu, dan yadda suka yi da yadda suka nuna halin ko in kula gameda batun zubewar cikin, dole abun ya saka duk wani mai hankali a shakku.

Shiruu d’akin ya d’auka bayan fitarsu,kafin daga baya Ummi ta ce”Bari in je in yi girki kafin ta farka.”
“Sannu Ummi, Allah ya yi miki albarka”
Hajiya mama tace dan gaba d’aya jikinta ya yi sanyi, ta kad’u kwarai.

Jaka Ummi ta d’auka, daga haka ta fita itama jiki babu kwari.
Baya ta fara dubawa dan ya ci ace Munirat ta kammala shanyar kayan Manu da suka  tafi yi, ga mamakinta sai ta ganta ta fito daga lab tana tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, sai da ta zo daff da ita tukunna ma ta lura da ita. Da mamaki ta tsaya take kallon idanunta waenda suka kumbura kamar wadda ta sha kuka..”Ummi za mu wuce ne?”
Ta yi mata tambayar ba tare da ta had’a idanu da ita ba.
“Kuka ki ka yi?”
Itama ta jeho mata da tata tambayr.
“Cleaner d’ince ta d’an watsa mini hypo a ido garin wanke zanin Manu shine na je lab d’in suka duba mini, sun ce ba komai, bai ma shiga idon ba.”

Wata bahaguwar ajiyar zuciya Ummi ta sauk’e saboda da har ta fara tunanin wani abu na daban…..

Sai da itama ta sake duba mata idon tukunna suka nufi gida.

Ummi tana fita, Hajiya Mama ta kira Daddy a waya tace”ya zo yanzunnan tana da buk’atar ganinsa.”

Suna gama magana Inna Siyama da Muhsin suka shigo,har da Sir Najeeb wanda ya je zance ne ya ji zancen, dan haka aka taho har shi, shine ɗin ne ma ya kawosu.

Cike da girmamawa suka gaida Hajiya Mama, ta amsa da kulawa, kafin suka shiga jaje da tambayar jikin nata.
Cike da alhini Hajiya Mama take sanar dasu ‘ai cikin ma ya zube har sun yi mata wankin ciki…’
gab’a d’aya shiruu aka yi jiki da zuciya duk ba dad’i.
Hawaye kawai suka ga yana bi ta k’uncin Manu wadda shigowar su Inna ne ya farkar da ita, su ba ma su sani ba.
Numfashi Hajiya Mama ta fesar kafin ta  tura kujerar ta dai-dai saitin kan Manubiya, a hankali ta shiga rarrashinta tare da yi mata nuni da ta karb’i k’addararta Hannu bibbiyu, Allah ya na sane da ita shi zai sake bata wani.

Da kyar ta samu ta iya bud’e idanuwanta waenda suka yi mata nauyi, tukunna da taimakon Siyama da na Hajiya Mama aka samu ta tashi ta zauna, still hawaye sun k’i su daina sintiri a kan fuskarta.
Chapter 99 · 0% Book details