← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 152

Sashe 102

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cizan labb’a Najeeb ya yi, bai jira ya kai aya ba ya katsesa ta hanyar cewa”Tabbas Yash ba don na san gigin giyar kishi ce take d’awainiya da kai ba wallahi da sai na rufe ka da duka!
Bari ka ji abunda ba ka sani a kan Abbakar ba…za ka iya tuna ranar da ka zo ka same ni akan mu je gidan su Manu kanason magana da ita urgent muka kira Abbakar ya yi mana kwatance,bayan y’an mintuna ya sake kira yace mana sun tafi k’auye?”
Bai jira jin me zai ce ba yace”to k’arya yake yi, dan a ranar ma sai da Manubiya ta yi exams, kuma ai kaga abunda ya faru next na case d’in black snake wanda hakan yake sake nuni da babu inda ta je tana cikin garin amma ya yi mana k’arya, saboda son da yake yi mata sam ba ya so ka rab’eta!.
A ranar da na bashi katin ka, na yi masa bayani nace ya bata tun daga ranar na fahimci son ta yake yi, ban gaya maka ba saboda gudun irin wannan abun da ka aikata da kuma gudun dasa zargin ma shi kansa a tsakaninku, Ashe na yi ta banza tunda gashi Yaro k’arami ya juya maka lissafi!…
Saboda ita fa ya nemi transfer, dan tunda aka fara maganar aurenku ya gudu, aashe kwanciyar kura yayi, ya je ya yi sabon shiri! ya dawo da niyyar tarwatsa ku!.
A gaskiya Yash ka bani kunya, dan ban yi tunanin za ka yarda da …..”

Cikin tarar numfashinsa Yashjub yace”Najeeb I saw there chat!
(na fa ga chat ɗinsu)”

Kamar Yahanasu za ta rufe sa da duka tace”kuma sai ka yarda ita ta yi?”

“To wa ya yi? Wayarta ce, kuma numberta, na gani..da dp da komai duk nata ne sannan ga chats nan na gani, waye ya yi idan ba ita ba?bayaga haka ba wai iyaka chats ba na ji da kunnena tana waya da shi tana cewa,sai da na fita tukunna ta samu damar yin wayar….da asubah! Sannan kusan kullum yana kiranta ina gani ba ta d’auka a gabana…”

A hankali Najeeb yace”me ka gani a chats d’in?”

Sai da ya share hawaye tukunna yace”Najeeb shiyasa tun farko da ka tambayeni na ce muku ban yarda ba!saboda i can’t believe wai Manubiya zata yarda ta yi maganata da shi, sannan har ya yi mata prescribing maganin da za ta sha ya zubar mata da ciki na da ke a jikinta.”

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Najeeb da Yahansu suka ce a tare, kafin Yahanasu ta matso ta zauna a gefen sa ta kamo hannayensa tace “Yash kalleni nan!”
Sai da ya juyo ya kalleta, tukunna ta ce ”da ka ji Manu tana waya da asubah, ba da kowa take waya ba da ni ne!”
Da mamaki ya kalleta wanda hakan ya sa ta jinjina masa kai tace “tabbas…na yi wa Manubiya alk’awarin ba zan fad’a maka ba, amma yanzu kam ya zama dole in fad’a maka….”
Tiryan tiryan ta zaiyyano musu komai game da yadda Manu tace mata ‘…ta taimaka mata suma su yi bada gudummawa a case d’in estate d’insa, ba za ta nad’e hannu ta zuba ido ana wasa da rayuwar mijinta ba!..’
Da binciken da suke yi akan case d’in, da kud’ad’en da Manu ta bayar, duk dan a yi bincike duk sai da ta gaya musu komai ba ta b’oye ba tukunna ta d’aura da cewa”wallahi ka godewa Allah Yash, dan samun mata irin Manu ba kowa ba, Manu mace ɗaya ce tamkar dubu!
Allah ya zab’e ka, kar ka yi masa butulci.
Maganar chats da shan magani kuma, ni na san aikin su waye!!Amma ba zan fad’a maka ba saboda wani dalilinawa. kawai Ina so ka tsananta bincike a kai, ka duba cctv ai akwai a gidanka, ka yi bincike sosai, ta nan ne za ka gano waye ya d’auki wayarta, waye yake saka magani a abunshanta ko cin ta duk za ka gani.”

Ahankali Najeeb ma ya zauna a gefe, suka saka shi a tsakiya yace”Yash shaid’an ya tsani ya ga ana zaman lafiya, ya tsani ya ga an yi aure ana soyayya tsakani da Allah ,nan za ka ga ya fara saka zargi da abubuwa a zuk’atan maaurata, bayan Abbakar da sharrin zubar da ciki da chats Yash akwai shed’an, dan Allah ka daure ka yi trusting matarka duk rintsi!
Ba fa a aure da zargi, babu kyau! ka daina dan Allah kar ka sake wannan tab’argazar, shi kuma Abbakar ka bar ni da shi sai na ci uwarsa, wallahi zai san Ina ya zo”.

“Ba na jin har yanzu yana da rai, dan dukan da ni yi masa ba lalle ya rayu ba”
Ajiyar zuciya Najeeb ya sauk’e kafin yace”mu yi addu’ar ya rayun dai”
“InshaaAllah ya mutu”
Yash ya fad’a cikin d’aci yana jin wata tsanar Abbakar tana sake taso masa.

A hankali Yahanasu tace”ai yanada magoya baya, dan shi kad’ai ba zai iya aikata wannan b’arnar ba…..”

Shiruu duk suka yi, Hatta Najeeb shima zuciyarsa sisters d’in Yash d’in ta zarga, tunda a baiyyane ba sa sonta, amma kuwa da sun cika dabbobi, dan in har za su iya kashe d’an wansu to kuwa abun nasu Azimun ne! ya godewa Allah da ya rabu da Ya’isha bai aureta ba…….

A ɓangaren Yash ma, yadda Yahanasu ta yi masa bayani da komai da kuma ya tuna yadda Yasmeen tun farko ta ce Manu bata da ciki..babu wasu waenda suka zo kansa sai su Yasira, tunda tare suke da su a cikin gidan. Sai dai kuma duk da yadda komai ya ke masa nuni da su ɗin ne, so yake kawai ya maida zarginsa akan gwaggwo! saboda yanzu haka a cikin tashin hankalin binciken estate d’insa yake, yana jin tsoron sakamokon…shiyasa yake addu’a Allah yasa idan ya yi binciken ya gano gwaggwo ce kawai, ba y’an uwansa uwa d’aya uba d’aya ba.!…

Yahansu ce ta ce”Manu da sunanka ta yi barci a bakinta…ka tashi ka j….”
Tun kafin ta rufe bakinta yace”Bara in je in ganta…..”
Murmushi duk suka yi, cikin tsananin jin dad’i suka mik’e, Najeeb yace”na san ba zaka fad’awa kowa ba amma pls Yash rashin fahimtar nan  da kuka samu da abunda Doctor yace inaso ya tsaya a iyaka mu uku kawqi! Sannan kamar yadda yaha tace ‘ka yi bincike,’
Allah ya sa mu dace.”
Jinjina kai Yashjub ya yi yana jin wani sanyi yana shigarsa kafin yace musu”na gode,sosai”a hankali.

Murmushi duk sukayi suka ce ‘ya dage da addu’a, ya cire komai a ransa’
daga haka suka wuce, shi kuma ya hau sama domin ya d’auko makullin motarsa……
Har wannan lokacin Ya’isha tana tsaye tana jiran Najeeb.

Sallama ya yi da Yahanasu, ta wuce, shi kuma ya d’auke kai ya yi kamar bai ganta ba ya had’e rai sannan ya nufi motarsa da sauri, wanda hakan ya sanya itama ta nufosa da sauri, amma kafin ta k’arasa tuni ya shige ya bata wuta ya yi reverse an wangale masa gate ya fice da mugun gudu.

K’amewa kawai ta yi a wajen, ta kasa motsi, kafin da kyar ta ja k’afafuwanta ta wuce garden, tun kafin ta gama shiga ta fashe da wani irin kuka.

Junior kam yau ya samu fuska a wajen Yadira ba laifi, dan suna shiga Yusra ta wuce sama su kuma suka zauna a main parlourn…gaba d’aya jikinta ya yi sanyi shiysa ya sameta yau ɗin, ta d’an sake da shi.
wanda murna da farin cikinsa sam suka gagara b’oyuwa.A rayuwarsa yana mutuwar son Yadira, so ba na wasa ba,Allah ya jarabcesa da masifaffiyar k’aunarta.

Ummi tana zuwa za ta d’aura girki, ta tarar gwaggwo har ta kusan kammalawa…
dan haka ta sa hannu har da Munirat itama suka taru suka yi na duka gidan, nan da nan kuwa suka gama.
daga haka suka wuce asibiti kai abinci, bayan ta had’a na Yash  a daban daban ta ajjiye.

Babu yadda ba ta yi da Hajiya Mama akan ta hak’ura ta koma gida ba tunda ga Siyama amma Hajiya maman tace”ba komai za ta kwana da Manubiya, da safe sa chanjeta.”

Yashjub yana hawa sama aka fara kiran sallar Magrib, dan haka ya ga ‘bari ya kama ruwa, ya yi alwallah kafin ya wuce.’
Zuciyarsa ta yi sanyi zuwa wannan lokacin, amma ciwon da kansa yake yi ba kad’an bane ba, yana buk’atar ya sha magaani..
Amma a yadda yake jiri a yanzun ya san idan ya sha babu komai a cikinsa wahala zai sha, gashi a side d’in babu cima, tunda ba zama ake yi a ciki ba, kuma ba zai iya tsayawa cin abinci ba dan ya san yin hakan zai d’auki lokaci…
dan haka ya kira gwaggwo a waya yace”ta had’o masa coffe dan Allah yanzu da sauri, zai sha, yanaso ya sha da magani, kafin ya wuce sallah.”
Lokacin da ya kira ta tana shirin kawo masa abunci ne dama, dan haka ta ce “to shikenan”.
Daga haka ta katse ta ajjiye basket d’in ta shiga had’a masa coffee d’in.

Kausar tana cikin kitchen d’in a wannan lokacin, dama tana ta tunanin ta yadda za ta aiki gwaggon a samu ta ajjiye basket d’in Yash ita kuma ta samu hanyar juye abinda ta k’unso a cikin abuncin nasa, a kai..kawai ta ji ya kira gwaggwon.
Ba k’aramin dad’i ta ji ba da ta ga gwaggo ta fara had’a coffe saboda dama ta riga ta yi
diluting abun kuma ta san idan ta zuba akan farar shinkafa ko miyar agusin da suka yi zai gane, coffee zai fi haɗiye abun lumi ba tare da an gane an zuba komai ba.……

Yana fitowa daga band’akin ya chanza kaya zuwa jallabiya, ya d’auki wayoyinsa ya kukkuna,
sai da ya gwada layin Manu akace masa tana barci, tukunna ya zuba a aljihu ya d’au makullin mota ya nufi k’asa dai dai gwaggo tana shigowa da basket.
“Yauwa sannu gwaggo iyaka coffee d’in kawai za ki zuba mini”
ya fad’i hakan yana mai sauk’owa daga stairs d’in a gurguje.”
Itama da hanzari ta shiga zuba masa, kafin ya k’araso cikin parlourn har ta gama zubawa.

Sai da ya nemi guri ya zauna tukunna ya karb’a yace “sannu gwaggo”
Daganan ya fara k’ok’arin kaiwa Baki.
Chapter 102 · 0% Book details