Sashe 117
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin kowa jigum ya sa shima ya nemi waje ya zauna ya yi
shiru….sam ya k’i yarda ya kalli inda Yassir yake ma sakamokon wani haushi da takaicinsa da yake ji.
Numfashi Daddy ya fesar kafin ya kalli Junior yace”ya bayanin
result d’in???”
Mik’ewa Junior ya yi , kai masa takardun da ya shigo da su na results d’in a envelope tukunna ya koma ya je ya zauna sannan yace” irin na d’azu ne, cikin kwanansa 12 dai dai..na yi kwakwaran bincike yadda ya kamata,sai da na je ma na sake d’aukar jinin nata na yi binciken komai kamar yadda ka ce, ga kuma scanning d’in shima.”
Dubawa Daddy ya yi, ya bawa Abhi shima ya duba.
Shiruuu parlourn ya kasance daga nan kafin Yassir yayi gyaran murya
yace”Daddy idan ba damuwa ni na yarda zan auri Kausar!!!
Akan dai ta fita ta tonawa family d’innan asiri sannan kuma
ta d’auki d’an d’anuwana ta tafi dashi tayi masa raino da tarbiyyar single parent(Mace)..
Ni Na ji na gani zan aureta,
tunda dama ina sonta.”
Cikin katseshi Daddy yace
“Yassir I’m sorry, kawai ka bar maganar nan,ka san cewa Kausar ba za ta yarda ta aureka ba,tunda har mahaifiyarka ta fad’amawa watak’il ba ka sani ba ne amma ta nuna ta kuma ce ba za ta tab’a aurenka ba don ba ta sonka…k’iri k’iri ta bijirewa aurenku kwanakin baya dan haka inaga yanzu ba lokacin fa ya dace ace za ayiwa Kausar dole ba,
ta burkice, ba ta ji bata gani dan ina ganin babu abunda ba za ta iya aikatawa a halin yanzu ba….kuma tsaf za ta iya tafiya d’in kamar yadda ta fad’a sannan na tabbatar sai ta yi amfani da wannan Yaron against Yashjub, bayaga haka bai kamata mu bari ta tafi da Yaro ya rayu a hannunta ita kaɗai kamar yadda ka fad’a ba.
Sannan akwai abunda ta shirya, tunda har ta fara maganar tafiya dan Kausar d’in da na sani ba za ta yi abunda ta yi yau ba tare da ta tanadi kwakkwaran plan ba….ai ta ga ta samu ciki dan haka tana ganin tanada makami, shiyasa ya zama dole mu kuma mu yi mata shigar sauri kafin ta yi b’arna.
Sannan Yassir ko an yi aurenka da Kausar ba za ku zauna lafiya ba, ta dinga taso da fitintunu dan zatace an yi mata dole ne,again kamar yadda ka
fad’a kana sonta so za ta ke juyaka ne kawai!
In zan baka shawara ka d’auka dan Allah ka hak’ura da Yarinyar nan har abada.
Cikin d’an uwanka ke a jikinta,
haba mana kwab’ar kar ta yi yawa.
Sannan ba zan ji dad’i ba
Ni kaina idan aka ce ka d’auki nauyin abunda ba laifin ka bane ba.”
Da k’arfi gaban Yashjub ya yanke ya fad’i dan a kaff cikin maganganun Daddy tun kafin ya fito ya fad’i abunda yake ransa ainun ya fahimci inda zancen zai dira, dan haka ya runtse idaunsa da mugun k’arfi yana sauraron Daddy da ya ci gaba da cewa”some facts cannot be denied!!(akwai abubuwan da ba zai yiu a iya chanjawa)…
kasancewar ba na son Kausar ba shi zai sa in rufe ido in k’i gaskiya ba!sannan ko babu komai nima y’ay’a mata ne guda shidda a gabana,idan wani ya yi musu haka ba zan ji dad’i ba!
A al’amarin nan Abu na farko da zan so ka saka a kanka Yashjub shine ba zan bada goyon baya a zubar da ciki ba, saboda haramun ne.
Sannan ka yi hak’uri Yashjub, kaima na san ba laifin ka bane ba amma itama ba laifinta bane ba, saboda kamar yadda ta fad’a da gaske ne maganar da Likita ya yi akan mahaifarta lokacin na ji zancen dan haka ka ga ba za ta so ciki da gangan ba tunda ba zata yarda ta zubarba, kuma ba za ta so ta haihu babu Miji ba.
Ta yiu tricking d’in naka ta yi da gaske, amma tabbas na san ba ta yi tunanin za ta samu ciki ba.
Abunda nake so ku fahimta a nan shine k’addara ce ta fad’o mana…. idan muka ce Kausar ta zubar da cikin nan bayan kuma mun san yanayi na lafiyarta da halinda take ciki to mun zalunceta, kuma ba zan ma bari a zubar da cikin ba. idan kuma aka ce ta haihu babu Miji shima mun zalinceta kuma na san ma ba za ta yarda ta zauna da mu ba….kuma duk daren dad’ewa kowa ya san Yaro na Yashjub ne dan gaskiya ba ta b’uya.”
Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e kafin ya kallesu ɗaya bayan ɗaya tukunna yace”hakan ya sanya na yanke shawarar abunda ya kamata a yi a rufawa kowa asiri.
Yashjub k’addara ta riga fata, kuma an zo wajen da dole sai ka yi hak’uri ka danne zuciyarka an rufawa juna asiri..ni Mahifinka ne, har abada ba zan yi abunda zai cutar da kai ba sai dai in yi wanda ba zai cutar da kai ba, wanda zai rufa maka asiri. Ka dai ji dalilan da na bayar kuma na san ka fahimta…dan haka ka auri Kausar!
A samu ta haihu lafiya daganan duk decision d’in da ka yanke ba zan ce komai ba!
Ko wanne family suna da nasu secret d’in, cikin jikinta dududu satinsa biyu dan haka idan aka yi aure za ta haihu ne akan lokaci asirin kowa a rufe, duniya ba ta sani ba.Yaro kuma kai ka san yadda zaka yi a gaba ka fitar masa da hakkinsa ba tare da an kwaresa ba.
Ka yi hak’uri ka d’auki nauyin da yake naka ne,na san ba laifinka bane ba amma duba da yadda Yaron nan zai zo duniya a ganina idan aka barsa da ga shi sai Kausar a inda ba mu sani ba to gaskiya ba mu yi masa adalciba, kuma kai ka san wacece Kausar! ba ta nutsu ba ma ballantana ta yiwa wani tarbiyyar da ta kamata.”
Ajiyar zuciya Abhi ya sauk’e kafin yace”Daddy abunda ka fad’a gaskiya ne! sannan hakan shine kaɗai zaɓinmu mafi sauƙi dan duk wani zaɓin da ba wannan ɗin ba to yana tafe da ƙalubale a bayansa”
Mik’ewa tsaye kawai suka ga Yashjub ya yi….yana jin kanshi yana wani irin juyawa yace”Daddy idan na auri Kausar zan iya mutuwa, amma kamar yadda ka fad’a k’addara kowa da kalar tasa…zan je in samu Manubiya in gaya mata komai, duk abunda tace a yi to shi za a yi…
Wannan rayuwar mu ce,
na ci amanar ta!
A ganina ita ya kamata a barwa wannan hukuncin ta yanke…this should be her decision to make.
Dukda cewa idan na auri Kausar zan iya mutuwa, amma idan har ta bi bayan abunda kuka hango kuka fad’a to shikenan na yarda zan aureta d’in har zuwa lokacin da za ta haihu!.
Idan kuma ba ta yarda ba to
ku yi haƙuri dan ba zan aureta ba.
Daga nan Kausar is free to do whatever the hell she’s planning on doing(in Kausar ɗin ta ga dama za ta iya zuwa ta yi duk abunda ta shiryama ɗin, ban damu ba”.)
Yana gama fad’in haka
ya juya ya fita ko bi ta kan Daddy wanda yake cewa “yanzu zama za mu yi mu jiraku kenan kake nufi?”bai yi ba.
Sai a lokacin Yassir ya d’an samu nutsuwa…
Sosai Daddy ya ji haushi ya fusata…tayaya Yash zai ce sai abunda Manubiya ta yanke tukunna shi za su yi??
A tak’aice dai Yashjub ba shi da zaɓi sai na Manu, su kuma suna zaune suna jira har sai ya je ya tambayota ta fad’i yadda za a yin tukunna ya zo ya gaya musu su
Kuma su yi.!
Ya san dole abun zai tab’ata tunda abune wanda ya shafi Mijinta da wata Macen amma kuma power d’in da Yashjub ya bawa Manubiya a wannan al’amarin ya yi yawa sosai!!…ya san wannan ba shine lokacin da ya kamata ace ya ji haushin Manubiya a kan wannan maganar ba dan tunda cikin jikinta ya zube shi tausayinta ma yake ji sosai, amma tashi d’aya a take a lokacin sai ya ji takaicinta ya rufe sa….ba zai tsaya a mayar masa da d’a boyi boyi ba fa!.
Wato ko abu zai kashe shi kamar yadda ya fad’a indai ta na so to
zai yi kenan! matar da ya kamata ace she’s even greatful da Yash ya aureta aka kawota cikin family d’insu shine amma ta kafa ta tsare ta ke juya musu d’a suma take so ta juya su.
Lissafin da Daddy yakeyi haka nan shima Abhi yake irinshi
Exactly.
Dama shi Abhi tun farko da su ka je kai kud’i sai da ya saka hakan a ranshi, amma daga baya sai ya janye, yanzu kuwa power d’in Manu ya yi yawa gaskiya dole a ja mata layi.
Dan wannan Yarinyar idan ba su yi da gaske ba har Hajiya mama sai ta juya.
Numfashi Daddy ya fesar kafin ya kalli Abhi yace”yanzu me ye abunyi?ni dai ba zan jira sai Yarinya ta yanke hukunci tukunna mu maza mu zartar ba.”
Jinjina kai Abhi ya yi yana d’an lissafi kafin yace”Daddy a yiwa kowa adalci sannan a duba Yaron da bai ma riga ya zo duniya ba…kamar yadda ka fad’a duba da yanayin hanyar da akabi aka sameshi ya kamata ace mun tsaya tsayin
daka mun sadaukar da abubuwa da yawa wajen ganin mun inganta rayuwa da tarbiyyar sa…”
Da sauri Yassir yace”Abhi ni k’anin Yashjub ne, inason Kausar, me yasa ba za ku aura mini ita ba ni???
Wallahi idan kuka had’a Kausar da Yashjub to
kun had’a fitina ne saboda ba sa shiri ba sa so…..”
Cikin fushi Daddy ya katse sa yace”idan ka ƙara magana Yassir Allah sai ka fita a parlourn nan!!!
Mahaukacin banza kawai mara zuciya…
Anya Yassir ka san ciwon kanka kuwa??”
“Hmmm”kawai Junior yace
Wanda hakan ya sa duk sai da suka d’an kalleshi.
Atake jikin Yasssir ya d’anyi sanyi dan sai a yanzu ya fara tunanin kar fa ya kwafsa..to amma shi yanzu ya zaiyi???….ga duka ga hana kuka!inaa!!!ba zai bari auren nan ya d’auru ba fa…