Sashe 59
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ku kuma”
yayi maganar yana nufin a su Yassira yace”kar in ji bakinku,
har ya gama magana.”
Wato dai a gaban Yaran nan za a yi masa haka! alk’alanci kenan Daddy zai yi musu shi da k’annensa….
“Ina jin ka mana!”
Ya ji muryar Daddyn a d’an zafafe.
A hankali ya d’ago ya kalli Daddyn yace”Ba su kula ta ba.
Kaff cikin su, saida na yi magana tukunna Yadira ta gaida ita‘’
Da takaici Mommy tace
“Saboda ba su gaida matarka ba shine ka koro su daga gidanka??’’
Cikin son fahimtar da ita yace
‘’Mommy saboda sun rainani, kuma sun ki su yi abunda nace a gabanta sun nuna min ban Isa ba, shiyasa na koro su..
Bayaga haka Mommy ta ya za su je har gidanta su k’i su kulata?
sannan kuma ni da kaina in ce su yi su k’i yi!
Maatata ce fa!’’
Ai ko da ace ba za su gaida ita ba da ko ‘Hi’ ya kamata su ce mata…..”
Cikin tarar numfashin sa Ya’isha tace
‘’Daddy cewa ya yi duk sai mun gaida ita, har Yasira da Kausar. kuma fa ita ma bata kula mu ba, how yake tsammanin mu mu gaida ita?.”
Throw pillow Daddy ya jefawa Ya’isha, cikin fad’a yace
“Ba na ce bana son jin bakin kowa ba?”
Da b’acin rai sosai ya juya ga Yashjub ya ce
“Yashjub’’
Ahankali Yash ya kalle sa ya ce
‘’Na’am Daddy’’
Cikin bada umarni da fahimtarwa Daddy ya fara magana
‘’kamar yadda na fad’a d’azu..
ba zan bari giyar soyayyar da ka sha ta lalatamin zumuncin dake a tsakanin ku ba!
Ba zan bari wata mace ta shiga tsakanin ku ba, dan baka san yadda muka sha fama ni da mahaifiyarku wajen ganin mun daidaita kanku ba!”
Ahankali Yash ya lumshe ido yana mamakin yadda su Daddy suka d’auki laifi gaba d’aya suka d’aurawa Manubiya…ta yaya Manubiya za ta shiga tsakanin sa da su Yasira, shi kuma ya yarda..
Dan mai ya sa tun farko idan irin haka ta faru a tsakanin su ba’a d’abbak’a abun sai yanzu da yayi aure?
Kuma shi rainin da suka yi masa a gabanta ne ma ya sake harzuk’a shi har ya koro su!! a
tunanin sa ya Isa da su.
Inda ace ci musu fuska ya so yi ai da a gaban Manubiyan zai fatattake su…Ita Manubiyan ma da suke ta cewa ‘za ta shiga tsakanin su’ bama ta san da case d’in korar sun da yayi ba.
Ahankali tunanin sa ya dawo cikin parlourn jin Daddy yana cewa “Inaso ka sanar da Manubiya, idan kuma ba za ka iya ba to ni zan sanar mata cewa
‘Yadira da Yusra za su gaida ita wannan dole ne!
Amma
tun daga kan Ya’isha har zuwa kan Yassir har Kausar ita ce zata gaida su tunda duk sun girme ta.’”
Da mugun sauri Yashjub ya d’ago sosai ya zubawa Daddy idanuwansa.
“Kwarai kuwa”Daddy yace shima yana kallonsa, kafin ya d’aura da cewa
“Ba wai nace dole idan sun had’u sai ta gaida su ba, ruwanta ne idan taga dama ta kula su in bata ga dama ba karta kula su,
amman kasancewarsu yayyu a gareta ya sanya ba zai yiu ace su su fara gaida ita ba.
Idan ta kula su ta gaida su su amsa
Idan kuma bata kula su ba to
wannan alhakin yana a kanka
na ganin ka daidaita alak’ar dake a tsakaninta da su!
Kai ne za ka nuna mata cewa yayun ta ne su ɗin kuma ta dinga gaida su saboda a samu a zauna lafiya, a raya zumunci….
Sai kuma magana ta biyu
‘Daga yau har gaban abada idan su Yasira za su je gidanka a rana sau goma to baka da iko sannan baka Isa ka kore su ba!
Na san gidanka ne, na san kai ne ka siya ka zuba furnitures ka yi komai da kanka amman ni kuma nine ubanka!
dan haka in dai ni na haife ka, to Yassira,Yahanasu,Ya’isha,Yadira,Yasmeen,Yusra,Yassir kai har ma da Kausar duk za su je gidanka a duk lokacin da suke so!
Idan ma hutu suke so su yi to za su je su yi har sai sun gaji dan kansu tukunna su dawo amma kai dai baka da ikon koro su…in har kuma kace za ka yi taurin kai to zan sa ka had’omin spare key na kaff gidan naka in rabawa ko wanne a cikinsu….
Ban d’aura auren da zai tarwatsamin kan ƴaƴana ba wallahi.!”
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya ce
‘’a kiyaye” daga nan ya wuce sama.”
Shiruu Yashjub yayi, ya ma kasa cewa komai…
Har sai da Mommy tace
“Sai magana ta uku! Yadira ta had’a kayanta tun d’azu. Idan kun zo tafiya ku wuce da ita,
za ta zauna a gidan naka for sometimes.”
Saida ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya ce
“To Mommy ba damuwa, amma jiya na gaya miki za mu tafi Cyprus..mai zai hana a bari sai mun dawo t….”
Cikin tarar numfashinsa tace
“Ka wuce da ita,idan kun zo tafiya sai ka dawo da ita, in kuka dawo sai ku koma tare da ita”
Ahankali yace”Mommy, jibi ne ai…”
Cikin fushi tace
“Ka san Allah Yashjub idan ka gwada min taurin kai idan bance ku tafi honeymoon d’in tare da ita ba ka chanja mini suna..”
Shiruu ya yi kafin ahankali ya ce “Shikenan Mommy..ki yi hak’uri”kafin ya kalli Yadira ya ce “Ki d’auko jakar taki yanzu zamu wuce. Bari in yi wa Daddy sallama”
Ya fad’i hakan yana mai hayewa sama.
Murna a wajen Yadira ba a magana…tashi d’aya itama ta yi wuff ta haye ta je d’auko kayanta.
Ko da Yashjub ya je wajen Daddy basa hak’uri yayi sosai
tukunna dakyar ya samu ya d’an sauk’k’o bayan zazzafan warning d’in da Daddyn ya zuba masa akan “indai har yanaso su zauna lafiya da shi tou ya ja k’annensa a jiki…duk ranar da aka ce ya mutu shi ne Uba!…kar ya biyewa Mace ta rabasu tun yanzu.”
“InshaaAllah”kawai Yashjub d’in ya ce daganan yayi masa sallama suka rabu lafiya,
A ranshi yana mamakin yadda Daddyn yayi masa sannan yadda suka d’auki laifi kachokam suka d’aura akan Manubiya wadda bata ji ba bata gani ba!
It’s like kamar ma Daddyn har ya fara jin haushinta ne tun kafin a je koina, kawai dai bai nuna masa bane, amma ya fahimta, dan tunda har Daddy ya ce “har Kausar sai Manubiya ta gaida ita”
To fa abun babu sauk’i sam! dan duk mutumin da Daddy zai yi favoring (zai fifita) Kausar akan sa to yakamata ayi gaggawar gyara tsakanin su..
Shiyasa kawai ya hak’ura yake ta basu hak’uri…ya san su iyaye ne fushin su garesa masifa ne, sannan kuma yasan yanzu yana yin taurin kai ko ya yi wata maganar to Manubiya zai sake janyowa bak’in jini a wajensu.
A d’akin Yahanasu Yadira ta samesu dan haka suka fara shirin tafiya.
Manubiya ce tace “tana so ta je ta yi wa su Mommy da Ummi sallama”dan haka Yadira da Munirat suka tafi rakata.
Suna fita Yahanasu tace
‘Ayi hak’uri Yash,
ayita hak’uri…d’azu Ina kitchen na ji mommy tana waya da su
Yassira, suna ajjiyewa kuma na ji ta kiraka, dama tun daga nan na san akwai matsala, aikuwa da suka tashi shigowa kusan dukkansu da kuka suka shigo!
wai ‘ka kore su, k’annenta kuma suna gidan yanzu haka.’
Dama yadda na ji Mommy da su suna yi wa Daddy bayani, shi kuma yana fad’a na san kawai ya riga ya hau shiyasa ban saka Baki ba.
Na yanzu ya faru sai a kiyaye gaba, dan Allah Yash karka basu k’ofar da za ka janyowa baiwar Allah n nan bak’in jini a wajen Daddy…”
Ajiyar zuciya ya sauk’e daganan yace
“InshaaAllah’’
Ba a wani dad’e ba su Manubiya suka dawo…
Sark’ar gold Ummi ta bata y’ar k’arama wadda ba za ta wuce 600K ba, a cewarta ‘ta ajjiye ne a tunaninta za’ayi bud’ar kai, to
kuma sai ta ga ashe su basa bud’ar kai…’
daga nan ta d’an yi mata nasiha.
Mommy kuwa sallama kawai sukayi daganna suka fito Manubiya tana mamakin yadda yanayin fuskarta ya chanja, dan d’azu sam ba haka ta yi mata ba a gaban Yash.
Yash ya ji dad’in gift d’in Ummi matuk’a kuma bai ji dad’in rashin ganin gift daga wajen Mommy ba, yana sane ko a lefe ma ba ta basa komai ba Mom da Hajiya mama sai Yahanasu ne kawai suka bada…dukda ya san yau d’in ranta a b’ace yake
amman ai dama Uwa tana tanadan gift d’in Amarya a irin wannan ranar ko da ace ta bayar da na lefe, ya san maybe za suce ai ya yi komai ya saka komai amman ai Ana bada gift ne saboda karramawa ba wai dan babu ba.
Har mota Yahansu da Munirat da Yassir suka rakasu su da Yadira da akwatunanta har biyu.
Sai da suka ga ficewarsu tukunna suka nufi main door,
signal kawai Yassir ya yi wa Munirat daga nan Yahanasu bata san inda sukayi ba ita dai ta ganta ta shiga parlourn ita kad’ai.
Kausar tana ganin ficewarsu ta windown d’akinta ta koma ta kwanta ta fashe da wani irin kuka, babu abunda ya fi b’ata mata rai irin yadda yake wani rik’e mata jaka yake bud’e mata murfin mota.
Tana kwance tana ta faman kuka a haka ta ji an bud’e k’ofar d’akin an shigo.
Ta san Mommy ce dan haka tace ‘’I’m fine”
Murmushi Mommy ta yi, ta nemi guri ta zauna a kusa da ita kafin tace”Ki yi hak’uri Kausar,
saura d’an k’an’kanin lokaci..
Na san da ciwo, amman ki k’ara hak’uri…
Ki duba kiga yanzu da ikon Allah Daddy ya fara karkatowa side d’inmu, duk abunda muke so shi yakeyi.
Shima Yashjub d’in ki duba kigani ko b’acin raina ba ya son gani wanda da sam ba haka yake ba.
Ki kwantar da hankalinki, na yi miki alƙawari indai kina da ni to bazakiyi kuka ba…”
Ahankali ta tashi ta zauna tana kallon ta ta ce ”thanks for everything Mommy, amma na ga suntafi da Yadira, kenan ba ranar dawowarta nan gidan kwana kusa kenan?
Idan fa ba ta dawo ba babu ta yadda za ayi mu…”