Sashe 11
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar bayan mintuna sha
biyar da fitar su Yasmeen Baaba Larai ta shigo….
A yadda
su Yasmeen suka fita suka barta a haka ta shigo ta sameta.
Kusa da ita ta nemi waje ta zauna kafin ta ce “yi haƙuri, sun sameni ina girki ne…Ummi na tarar za ta yi masa girki wai an sallameshi Yassir ya tafi d’auko shi, shine na samu na k’arba, da kyar kuwa ta barmun kin san halinta’’.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin ta ce ‘’Kin kammala abunda kika fara ne?’’
‘’Eh! Ai shiyasa ma na karb’i girkin’’
Baba Larai ta bata amsa a cikin ranta tana addu’ar ‘’Allah ya taimakesu, su samu nasara a kan Yashjub, dan abun nasa kamar gado ya yi, saboda shima ɗin ko me aka yi masa to fa ko an ci sa’a ya kamasa ba ya yin wani tasiri kuma baya dad’ewa ya ke karyewa.’’
Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin ta ce “Sannu y’ar uwata’’
Sai da Baaba Larai ta gama nazartarta tukunna ta ce “mai ya faru kuma?’’
Ta yi mata tambayar tana gyara zama.
Sai da Mommy ta sake sauk’e ajiyar zuciya tukunna ta ce ’’Gobe za’a kai kaya, ayi tambaya a yi komai.
Daddy sai shirye-shirye yake, har yanzu banga alamun fasawa ba, anya Baaba ana yin komai yadda ya kamata kuwa? Dan ni naga har yanzu kamar ma rura wutar ake yi.’’
Ahankali Baaba Larai ta ce ’’da izinin Allah za mu yi nasara. inshaaAllah ba za’a d’aura ba, ke dai kawai ki zuba min ido kamar yadda na gaya miki’’
Numfashi Mommy ta fesar kafin ta ce ‘’sai maganata ta biyu…
Mun yi tunanin Yara fa Baaba, mun gaza mu yi lissafi mai kyau, ba mu auna cewa tsaf shaid’an zai iya tunzura Yashjub aje Yarinyar ta samu ciki ba ko da kuwa ba ayi auren ba!
Kinga kuwa idan akwai ciki to bamu isa hana aure ba ko da ace ma mun hana d’in to munyi ta banza ne.
Na san Yashjub ba shi da neman mata amma akwai shed’an, ita kuma Yarinyar a nata b’angaren na san a yadda Yashjub yake da kud’i kyau da kwarjini ba ko wacce Mace bace za ta k’i amincewa da shi dan in akayi rashin sa’a akaje ba nutsatstsiya bace sannan gashi tana ganin an kusan auren su kinga ai komai mai iya wakana ne.
yanzun fa Yasmeen
ce min ta yi ta fi mintuna talatin a bakin k’ofar d’akin da yake d’azu tana knocking amman basu bud’e mata ba,
Me kike tunani???
Ina amfanin tarwatsa aure in ta riga ta samu ciki?? Dan na san kafin mu samu mu raba su ko mu san abunyi akan cikin asiri na ya gama tonuwa…..’’
‘’Tabbas ba mu yi wannan tunanin ba’’
Baaba Larai ta fad’a tana mai sake gyara zamanta, kafin ta d’aura da cewa ‘’zan san abunyi, matsalar shine sunan Yarinyar da har yanzu bamu gama sani ba, Yassira ta ce kamar Manubiya ko Maryam ta ji Yahanasu tace ko?’’
sai kuma ta yi shiru kamar mai tunani, kafin ta fesar da iska tukunna ta ce “inshaaAllah komai zai yi dai-dai’’.
Ruk’o hannunta Mommy ta yi kafin ta ce ‘’Baaba na gaji,
zuciyata ba za ta iya sake nad’ar wani sabon bak’in cikin ba..’’
Cikin son kwantar mata da hankali Baaba Larai tace “kar ki damu, komai zai tafi cikin tsari..
InshaaAllah ba zan zuba ido Ina ganinki cikin damuwa ba…’’
Daga haka ta shiga lallab’ata tana bata Baki tare da bata tabbaci….. Tukunna da kyar Mommy ta samu ta d’an nutsu, dan ba kad’an ba ta tsorata matuk’a kuma hankalinta ya tashi kwarai.
….
A bakin k’ofar shiga side d’in Yashjub Yassir ya yi parking,
shi da kanshi ya taya shi shigar da jakar computersa da kayan dubiyar da aka kawo mishi
tukunna ya yi mishi sallama ya tafi.
Gwaggo da Ummi ne suka kai mishi abinci, daganan suka tambayeshi ko akwai abunda yake buk’ata ya ce ‘’ba komai’’
dan haka suka mishi Allah ya kare gaba ya k’ara sauk’i, suka tafi domin ya samu ya huta…
Ai kuwa bai huta d’in ba, dan duk sai yau masu gadi suka samu zuwa dubiya saboda ta’aziyya da suka tafi na driver kuma
dama shima ya ce kar a gayawa waenda ba su saninba asibitin da ya ke.
Wannan ya shigo wannan ya fita haka masu gadi da drebobi har ma da na mak’ofta da maƙoftan da kansu aka dinga sintiri, har dare! dan haka ciwon Kai sai ya sake turnik’e shi.
Ya na sane da su Mommy, kaff cikinsu
Yadira ce kawai ta shigo ta duba shi, itanma ya lura kamar fushi take dashi amman kana ganinta ka san ta damu sosai!
Da yake Yarinyace itan shiyasa ya yi saurin b’aro jirginta.
Hakanan ta yi mishi ya jiki
harda d’an dessert d’inta ta had’o ta kawo masa.
Sam fuskarshi babu annuri haka ta yi ta tafi dukda kuwa ya ji dad’in zuwan da ta yin amma ya kamata ya koya wa Yaran nan hankali, shiyasa d’azu ma ya ƙi sakarwa Yasmeen!
Ba zai yiu su yi fushi da shi a sanda sukaso ba tare da wani kwakkwaran daliliba sannan in sunga dama su kulashi a lokacin da suke so, ba. Sam ba zai d’auki wannan iskancin ba…in the first place ma (ai tun farko ma) ba su Isa yin fushi da shi ba ko ma me ya yi ai shine Babba shine a matsayin ubansu, ko da ace
shine bashi da gaskiya ba zai basu damar yi mishi wannan rashin ɗa’ar ba! Ballantana kuma shike da gaskiya…..
..wannan tunanin ne ya sanya ciwon kan nasa ya sake hauhauwa, dan abun ya b’ata masa rai sosai musamman ma ta b’angaren Mommy, ya ji zafi kwarai, a ganinsa bai kamata ta biyewa Yara ta k’i zuwa duba shi ba, ya riga ya san halinta da
mugun tirjiya shiyasa kawai ya share ya yi k’ok’ari ya rarrashi kansa da niyyar zuwa wajen ta anjima inshaaAllah ya bata hak’uri kamar yadda ya shiryawa yi tun a asibiti….Daddy ya yi masa magana, haka ma Manubiya, sannan shima a karan kansa baya son irin zaman da suke yi da ita har cikin zuciyarsa amma ita take janyo komai, Mommy tanada wani halin da sai wanda ya zauna da ita ne kad’ai zai iya sani,
tanada shiru shiru tanada hak’uri amman kuma ba ta da dad’in zama kwata-kwata,
shiyasa duk wanda ya ga irin zaman da sukeyi ita da shi sai ake ganin kamar shi ne ba ya kyauta mata bayan ita take tab’o sa.
A hankali ya fesar da iska ya lumshe idanuwansa tashi d’aya tunanin dayake ta yi da rashin sanin abunda ya kamata ya yi game da rasuwar drivernsa ya taso masa…dan haka ya d’au waya ya kira Manubiya akaro na uku daga dawowarshi zuwa yanzu, dan tabbas yana buk’atar shawara.
Bayan sun gaisa ne ya nemi ta bashi shawara akan ‘ya yi bincike akan rasuwar driver d’insa, ko kuma ya barshi’
saboda ya san ba accident bane, dukda ya yi
alk’awarin d’aukar d’awainiyar iyalin Mutumin daga nan har abada inshaaAllah,,to amma kuma yana gani kamar bai kyauta ba idan ya bari mutuwar sa ta tafi a banza saboda ya kare kanshi
daga sakamakon da binciken zai bayar, wanda ka iya tarwatsa shi gaba d’aya.
Bata tsananta bincike ba, ta daure ta cije sosai tukunna ta bashi amsa iyaka ta dai dai abinda ya tambayeta….
Cikin son fahimtar da shi ta yi masa nuni da yadda idan ya yi binciken kuma ya je sakamakon ya tarwatsa kamar yadda ya ke zato shin waye zai ci gaba da kula da Iyalan mutumin??.
abu mafi dacewa da zai yi wa mutumin shine ya kular masa da iyalansa, shari’ah kuma a barwa Allah subahanahu wata’ala, shi zai bi masa hakkinsa.
Ya ji dad’i kwarai kuma, ya samu relief dan dama so yake a hanashi yin binciken.
Sun d’an tab’a hira, yau ɗin ya ji dad’i dan babu mita babu complain haka suka sha soyayyarsu kafin su yi sallama ya katse kiran suna jin kamar kar su kashe wayar.
Suna gama waya, ya mik’e ya nufi cikin gida.
Yana shiga side d’in Daddy ya wuce, suka hau shirye-shiryen gobe, ya dad’e sosai a wajen Daddy kafin su yi
sallama ya tafi…
Ba k’aramin dad’i Daddy ya ji ba da ya ga hatta cokali Yashjub ya riga yayi order, ya sayi komai!
kuma gidan ma ya tsara komai,
ya had’a komai, ga lefe shima Yahanasu tana kan had’awa…
Ya san inda ace Yassir ne to da zuba ido zai yi ya naɗe Hannu a yi masa komai….
Yashjub yana fita side d’in Mommy ya wuce, sai dai yana zuwa k’ofar d’akinta ya ji a rufe….
Ya so su tattauna ya bata hak’uri su fahimci juna, amman yadda ya yi ta faman bugu ya ji shiru ne ya tabbatar masa da ta yi bacci..
Haka nan ba dan ya so ba ya juya ya tafi ya barwa gobe.
A b’angaren Mommy kuwa, a
lokacin da ya zo tana parlournta, ta fara jiyo muryarshi yana magana da Yadira wadda take masa sai da safe..
dan haka ta yi sauri ta afka d’akinta ta rufe da wuri saboda ba za ta iya fuskantar Yashjub a halinda take ciki ba! Dan ta san tsaf zata iya shak’e sa!!!!!
Haka kurum, tashi d’aya! Yaro ya tsund’umata a cikin bal’ai da tashin hankali, rabonta da ta yi bacci fiye da na awa biyu har ta manta…haka kurum ya je ya d’auko musu mayya!Yo mayya mana, idan ba mayya ba wacce iriyar Yarinyace haka da za’a yi ta yin aiki a kanta amman a banza?.
Ba abunda ya fi sake d’aga mata hankali kamar d’azu da ta lab’e ta ji Daddy yana waya da Abhi wai yana hanya ya taho, ta tabbata kenan gobe za a kai kaya a saka rana, dukda Baaba Larai ta ce ‘’ta jira ta ga goben tukunna in an kai to shine sun yi failing(sun faɗi)’’
Amman ita a yadda ta ga anata shirye-shirye gadan-gadan ta san an riga an kai ma an gama, saidai su nema wani alternative d’in(wata hanyar)…