Sashe 23
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Jinjina Kai Baba Larai ta yi kafin ta ce “Khadijah! Ba ki kaini tsanar Yarinyar nan ba inaga,
sannan baki kaini k’in auren nan ba amman ya zama dole mu hak’ura, dan ba zan b’oye miki ba bamu da yadda za mu yi, babu yadda zan yi dan babu abunda zan iya sake yi! Kuma ko ba ni d’in ba ko ina za ki je Wallahi sai dai a ci kud’inki…ƙarshen basirata na k’arar amman ki duba ki ga jinkiri kawai aka samu.
Ki yi hak’uri tunda ta nace akan sai ta shigo gidan mu barta ta zo ɗin, inshaaAllah sai ta fita da k’afarta…
barin ma yadda muka samu Yash d’in ya fara jan mu a jiki ai an samu riba kuma komai zai zo mana da sauƙi!!…
Ki duba fa ki ga yau har durk’usa miki ya yi, sannan ya nuna miki girmanki da matsayinki a wajensa, kinga kuwa wannan ai babban nasara ne, dama garin ƙoƙarin buɗe wata ƙofar wata take buɗuwa lura ne kawai da ba a yi…
Dan haka daga yau, inaso tun daga kanki har izuwa kan Yadira kowaccenku kawai ta nuna tana son auren, bama so amma mu nuna masa muna so d’in, idan aka yi aka gama sai a san abunyi..”
Da sauri Mommy ta ce “Ta ya zan bari a yi auren bayan kin ce in har su ka kasance tare har hakan ya janyo ta rayu da mu to nakasata ta zo kenan”
Cikin tarar numfashinta Baaba Larai ta ce “Kinga da farko dai ba za mu bata damar yin dogon zangon zama a cikin namu ba ta hanyar hanasu kasancewa a tare ballantana har nakasar taki to tabbata, zaman da za ta zo ta yi kamar na baƙunta haka nan za ta zo ta yi shi ta tafi.
Ki kwantar da hankalinki, kin ji ko, in sha Allahu ba za a bata damar kasancewa a tare da shi ba, ballantana wata matsala ta taso ko kuma har su yi shaƙuwar da za su kasa rabuwa ko kuma ta samu abunda zai iya janyowa ta yi dogon zangon…”
Cikin tarar numfashinta Mommy ta ce “in aka riga aka shafa fatiha Larai ta zama matarsa fa a idanun duniya da koina kenan, kinga kuwa ai sun gama kasance tare ko”
Wani ɗan guntun murmushi Baaba Larai ta saki, kafin ta ce “Mommy, dan an yi aure tsakanin Mace da Namiji ba shi yake nufin Mata da Mijin sun kasance tare ba..Yash dama chan shi ga yadda ya ke, kuma akwai abunda zan ƙara akai, dan haka ba za a bari su kasance taren ba!”
Ta ƙarashe maganar tana mai ƙurawa Mommy wadda itanma ta ƙura mata idanu….
Sun ɗan jima a hakan kafin Mommy ta ɗauki haske, dan haka ta sauƙe wata nannauyar ajiyar Zuciya tukunna ta ce “na fahimta”
“Madalla”
Shine abunda Baaba Larai ta ce kafin ta ɗaura da cewa “dan haka mu bari a ɗaura Khadeejah, sannan daga yau, inaso duk ku daina fushi da shi, sannan ko goya su Yahanasu zai yi wannan ma babu ruwanku, a tak’aice dai duk wani abun da zai janyo saɓanin fahimta ko fushi a tsakanin ku da shi ku gujeshi,
A iyaka maganarsa ta yanzu na lura kuma na fahimci
Idan har muka yi hakan to za mu samu kanshi cikin sauk’i, kinga kuwa idan muka samu kanshi komai zai zo mana da sauk’i kenan, dan inshaaAllahu kafin ma amaryartasa ta gano steering da za ta kama ta tuk’a rayuwar gidan nan da shi kansa Yash d’in tuni sai dai ta ji ta a waje.”
…
Sosai hud’ubar Baaba Larai ta ratsa Mommy, dan haka washegari da safe suka tara su Kausar suka yi musu bayani, kowa ya yarda ya amince amma banda Kausar…
babu yadda ba a so a fahimtar da ita ba amman furr ta birkice musu k’arshema barin d’akin ta yi ta banko musu k’ofa bayan ta cewa Mommy
“ai dan ba ita ta haifeta ba shiyasa ta k’i bawa abun mahimmanci, gashi yanzu har za a yi aure, kuma a haka suke so ta kwantar da hankalinta, tana ji tana gani Yash ya auri wata su tare kenan ko ya su ke nufi???…..”
Ganin duk sunyi mata shiru ne ya sa kawai ta fitan, ta bar musu d’akin.
••••
Abun har mamaki yake bawa Mutane, yadda jikin Inna ya ware,
dan tun watanni biyu baya da suka wuce take tashi ta zauna da kanta, wanka ma
Manubiya za ta kama ta ta kaita band’aki ta sanya mata kujera ta fito ta barta ta yi abunta, dukda ba fita take yi ba amma a wannan lokacin likitar tace “a barta ta dinga gwadawa, shima wani exercise d’in ne”
Sannan magana d’aya biyu tana kwatantawa cikin ikon Allah, har waya ta karb’a dukda
maganar tata bata fita sosai haka ta yi wa Yashjub godiya dan ba kad’an ba ta jinjina masa akan yadda ya tsaya tsayin daka, dan ba kowa zai
Iya abunda ya yi ba…
har wasu magunguna likitan ta rubuta shi kuma ya siyo mata masu mugun tsada, wanda akace ta dinga sha safe rana da dare.
aikuwa ba ta sha na kwana hud’u ba
ta k’ara jin dad’in jikin nata matuk’a, kafin wata d’aya kuwa tsaff Inna ta ware gar kamar wadda ba ta tab’a samun stroke a rayuwarta ba, sai dai y’an abunda ba’a rasa ba.
Haka nan ƴan gidansu Manu su ka kasance cikin farin ciki, abinci suna samu jikin Inna kam Alhamdulillah.
Jidda ma har ta fara first semester exams d’inta na level one a northwest yayinda Manubiya kuma ta gama first semester level 3 a buk.
A yau ne za su karb’i lefen Manubiya wanda yayi dai-dai da sauran kwanaki 7 d’aurin auren kenan, shiyasa gaba d’aya suketa hada hada isu isu tun shekaran jiya…..
BULAMA ✍️
0903 441 3252.
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 12*
Ya Musbah ma ya samu aiki a wani company wanda Yash ya nema masa, har makaranta ya koma (ta manya) dan inda Yash d’in ya nema masa dole sai da karatu, dukda yana gane aikin ba wai ba ya ganewa ba amma yana buk’atar k’ari.
Har ya murmure kuwa, dan wajen ana samun alkhairi
sosai….
A cikin watannin da basu kai uku ba har d’aki da band’aki ya gina musu, a filin da ke jikin d’akin nasu wanda yake mallakinsu, da shi da Muhsin suka koma ciki da zama dan mai sunan baba ya koma wajen mahaifiyarsa.
………..
Watanni uku da suka wuce su Mommy sun fi kowa farin ciki, amma a yanzu kam sun fi kowa shiga cikin tsananin tashin hankali dan abun bai zo musu da sauk’i kamar yadda suka yi tunani ba.
A b’angaren Kausar kuwa, gani takeyi kamar ta fi kowa shiga matsala da tashin hankali, shiyasa take jin haushin kowa da komai musamman ma su Mommy, dan a ganinta inda ace sun bar ta ta kashe Manubiya tun farko da ba’a zo nan ba…k’iri-k’iri suka hanata ko da tab’a Manubiyan ne, hakanan ta amince ta yi yadda suke so bayan sun yi mata alk’awarin mara mata baya akan Yashjub, amma kalli yadda yanzu tashi d’aya suka chanja tunani suke so ta bari a yi auren sannan tsabar cin fuska ita gani take ma kamar farin ciki suke yi da auren, dan da su taga ake yin komai, ita kuma sun manna mata hauka sun tattara sun ajjiye gefe!
Bayan da farko plan d’insu shine
‘Duk runtsi ba za su bari Manubiya ta shigo cikin gidan ba’, amman kalli yadda suka sauya shawara tashi d’aya, babu wanda ya damu da ra’ayi ballantana mahangar ta.
Shiyasa gaba d’aya ta shiga cikin bak’in ciki! Takaici da haushi, tana jin kamar ta had’iye Zuciya ta mutu, ta rasa Ina za ta saka Kanta ta ji sanyi.
A b’angaren su Yassira kuwa, ba k’aramin k’ok’ari suke yi ba wajen danne kansu da
nuna farincikin da take tunanin na gaskiya ne.
Yau kam duk yadda suka so danne kansu abun na neman ya gagara, sakamokon akwatunan lefen Manubiya da su Hajiya Mama suka jere a parlourn k’asa tun safe, shiyasa duk suka gaza sukuni.
Sun shirya tsaf tun d’azu amman kuma sun kasa sauk’a k’asan.
A karo na biyu Ummi ta yi knocking k’ofar d’akin Mommy, bata shiga ba ta tsaya a wajen ta ce ”Hajiya Mama fa tun d’azu ku take jira, an kawo sark’ar, ku fito mu tafi.”
Tana gama fad’in haka ta juya ta koma k’asa zuciyarta fal cike da sak’e-sak’e.