← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 152

Sashe 132

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kausar dai is one of the reasons Yash!
ko har ka manta message d’in da ka turo mini da Hannunka??”
Muryar Hajiya mama ta katse sa tana mai k’arasowa inda suke, kafin ta zo ta nemi guri ta zauna, tana mai fuskantar sa tace”Yash an baka sarari kamar yadda ka buk’ata, Kausar is no longer your wife! Dan haka menene dalilinka na k’in komawa Nigeria, ko kanada waenda suka fi mu ne da ba za ka gaya mana matsalarka ba sai su?”

Hawayen da ya zubo masa ya sa Hannu ya goge kafin ya ce ”barin maganar nan shine mafi alkhairi ga kowa Hajiya mama, bana son yinta…”

Sake gyara zama ta yi da zaman gilashin idanunta, ta fuskancesa sosai tace”ni kuma yau na nace sai na ji komai, dan haka the sooner you talk the better,,dan ka san ba zan tab’a hak’ura ba ko?.!”

Jinjina mata Kai ya yi, dan haka tace”perfect..muna sauraronka!”

Sai da Yashjub ya d’auki sama da mintuna goma, ya yi shiruu kawai…
kafin chan ya zaro wayarsa ya kai musu inda videos d’in Yassir suke, ya mik’awa Hajiya mama, ya yi sauri ya mik’e ya fita……
….
Sai da hawan jinin Hajiya Mama ya tashi! Abhi kansa sai da ya yi Hawaye ba sau d’aya ba….ba su iya b’oyewa Daddy komai ba hakanan suka sanar da shi komai, wanda shima ɗin sai da suka yi da na sanin fad’a masa ɗin da suka yi ta waya! dan sosai ya gigita ya kad’u matuka da al’amarin, da kyar Ummi ta taushe sa aka samu ya sha magani ya yi bacci bayan sallar asubah dan throughout ranar ba su runtsa ba.

Da kyar da mugun kyar suka lallab’a Yashjub, aka samu ya yarda zai zo Nigeria! dan ba k’aramin Takaici ya ji ba da ya ji sunce har sun turawa Daddy, saboda shi har ga Allah ba hakan ya so ba…
sai da Hajiya mama ta zaunar da shi ta yi masa fad’a ta nuna masa illar yin shiru da kuma guduwar da ya yi, tukunna ya yarda da kyar ya amince ba dan ya gamsu ɗari-bisa-ɗari ba.

Sai da suka yi sati d’aya, tukunna suka samu zuwa…
Yashjub Manubiya Abhi da Hajiya mama…
Manubiya kanta Hankalinta a masifar tashe yake, dan tunda Yash ya sanar da ita komai ta fahimci yau case ne a gidan, shiyasa ta nemi alfarmar ‘ya bari su Ya Musbah su zo su d’auketa a airport, ta yi missing su Inna dayawa, bata samu ta yi musu sallama ba, gashi har gwaggo Suwaiba itama ta zo.’
Ya fahimci zillewa take son yi, kuma shima baya son a yi a gabanta, shiyasa ya amince….tun kafin su yi boardn ta sanar da su Ya Musbahn, ai kuwa a airport d’in su suka fara gani shi da Ya Nafi’u kafin su Junior suma su ka k’araso.

……Ba daban Yassir ba ya cikin gidan ba to da tuni Daddy ya dad’e da d’aukar mataki a kan sa, dan ya tafi Abuja tun last week bayan ya cewa kowa ya je yin business ne…
Da farko da Daddy ya ji zancen masifa ya shiga, da tashin hankali mai tafe da tausayin Yassir d’in..yanzu kuwa haushi da tsanar Yaron yake ji maƙura!!
Baya jin ma zai iya kallon fuskarsa.
Ba ya son jin ko da sunansa ne….

Kaff gidan zuwa yanzu kowa ya san Daddy yana cikin b’acin rai! On top of na farkon da yake a ciki da kuma rashin lafiyarsa, shiyasa kowa ya sha jinin jikinsa harda Mommy wadda ta fara shirye-shiryen yi masa bori ata dalilin kwata-kwata ya daina raba musu kwana ita da Ummi, dukda ko da chan d’in ma tana zuwa dama yake korarta, amma dai ai ya fi mutunci da daraja akan yanzu da ya had’ewa Ummi kwanakin gaba d’aya kaff.

Jirginsu Yashjub ya sauk’a da safe around 6:00am na su Yassir kuma ya sauk’a around 6:40am, Shiyasa ya zamana sun shigo cikin gidan kusan a tare dan su Yashjub suna gama shiga shima ya shigo.

Side d’insa ya fara nufa ya je ya yi freshening up!
Daga haka ya fito a gurguje dan ya yi misssing Kausar over!!
Dukda wajen sabuwar budurwarsa da suka had’u a instagram ya je ya gwangwaje abunsa, amma da kewar Kausar yake kwana yake tashi, har ga Allah shi kansa bai san wanne kalar so yake yi wa Kausar ba.

Ita kuwa Kausar tana chan, ta shiga damuwa..dan mutanen sun ce mata ‘ba za su tona Yassir ba, dan ya cika alƙawarin da ya yi musu ta inda ya dad’e da taimakawa oganninsu suka gudu.’

Ba k’aramin tashin hankali Yassir ya shiga ba da ya fara jiyo kamar muryar Yash suna magana shi da Ummi a baki bakin k’ofar.

Aikuwa yana shigowa da shi ya fara cin karo! ya juya baya yana magana shi da Ummi….
Tashi d’aya hankalinsa ya tashi, ransa ya yi masifar b’aci, zuciyarsa ta fara tafarfasa….wani irin sabon haushi tsana da k’iyyayyar Yash d’in suka yi masa k’awanya..

“K’araso ciki Yassir!!”
Muryar Abhi ta katse masa tunani, a dake!.

Kasa juyawa Yashjub yayi, sakamokon wani irin yanayin da ya tsinci kansa a ciki.

Yassir d’in kamar ba zai kula sa ba, sai kuma ya d’an matsoshi yace”sauk’ar yaushe?”
Bai jira jin amsar sa ba yace”welcome”
Daga haka ya wuce ciki dan he can’t stand him.

Parlourn taff cike yake, daga Mommy sai Kausar wadda take ta uban bacci ba ma ta san sun dawo bane kawai babu.

Shiruu kowa ya yi, har su Yadira da basu san me ke faruwa ba!

Yayinda su Daddy suka tsura masa idanu kawai.

Cikin nutsuwa Yassir d’in ya k’araso, ya nemi guri ya zauna ya fara kallonsu one by one dan zuwa yanzu kam ya san tabbas akwai matsala.

Gyaran murya Abhi ya yi kafin ya kalli su Yasmeen yace “ku d’an bamu guri”

Girgiza kai Daddy yayi cikin tarar numfashinsa ya ce ”ka barsu Abhi,Ina buk’atar shaidu.”
Bai jira d’aukar lokaci ba ya kallesu ɗaya bayan ɗaya yace
“ina so duk ku zama shaidata!
Daga yau har gaban abada babu ni babu Yassir!!!”
Sai kuma ya kalli Yassir d’in yace
“mintuna arb’ain kawai na baka! Ka tartara ya naka ya naka ka bar mini cikin gidana!!!!”.

Da mugun sauri Yashjub ya juya ya fita, Yayinda su Yusra suka kaure da kuka suka shiga rok’ar Daddy suna basa hak’urin ya taimaka ya bar Yassir, ko me ya yi bai chanchanci hakan ba!….dan Allah ya janye maganarsa.

Daina ji Yassir ya yi na y’an sakanni…
Ya riga ya san duk inda aka je aka dawo su grenade ne Ummul’abaisin wannan mummunan al’amari da ya faru da shi a yanzu, dama ya san ɓata lokacin da ya yi wajen kuɓutar da su dole ya fuskanci hukunci daga garesu, amma kuma a tunaninsa 3 million d’in da ya bayar ta isa ta rufe musu Baki ai.
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
ya shiga ambato a cikin ransa, dan bai ma san mai zai yi ba, ko ya zai yi ba, ko kuma mai zai ce ba!!!!.
Shin da gasken gaske ne wannan al’amarin ya ke faruwa da shi, kokwadai mafarki ne yake yi….zai iya cewa tunda yake a rayuwarsa bai tab’a zama helpless cikin matsanancin tashin hankali ba irin wannan!!
Na farko ya san tabbas an san me ya yi , na biyu kuma yanzu shi idan ya fita ta ina zai fara?
Ba shi da halin da zai iya ciyar da rai biyu, besides da ma ya gama tsarawa ita kanta yanzu kam sai dai ta ci gaba da ciyar da kanta dan last kud’in hannunsa ne ya yi amfani da su ya je Abuja ya dawo……

Da farko zuciyarsa tunzurasa ta fara yi akan ya yiwa Daddyn bori yace”babu inda zai je, sannan yace sharri aka yi masa”
amma kuma indai videos da voice d’in da mutanen suka turo masa shi suka turawa su Daddy tou tabbas bai Isa ya fara cewa sharri baneba..Idan ya yi hakan kamar ya sake tsunduma kansa a wani sabon bala’in ne…dan haka zai fiye masa idan ya kwantar da kai a halin yanzu da halin da yake a ciki.

Cikin fushi ya ji Abhi yace
“we are morethan disappointed in you Yassir, ka bamu kunya!
ban tab’a tunanin za a samu b’ata gari a cikin zuri’armu ba! dan haka tun kafin mu fara yi maka Baki ka b’ace mana daga gani a yanzu-yanzu ba sai anjima ba!.”

Dai-dai nan Mommy ta sauk’o k’asan.

Wani Irin rikicewa parlourn ya yi da koke-koke, hatta Yahanasu sai da ta yi hawaye kafin daga bisani ta mik’e ta shige d’akinta.

Dai-dai nan Mommy kuma tana k’arasowa cikin parlourn, ta tsaya a tsakiyarsu, ranta a mugun b’ace, hankalinta a masifar tashe, jikinta yana wani irin karkarwa, tace
“Ashe dama gulma da munafuci aka shirya, shiyasa na ganku gaba d’aya kun yo family kun zo????”

Bata ga mik’ewar Daddy ba sai k’arasowar da yayi ya d’auketa da wani mahaukacin mari!!
Cikin tsananin fushi hargagi da hargowa yace
“dabbancin naki yau har ta kan Mahaifiyata ya biyo Khadija!!!Saboda ke mahaukaciya ce wadda ba ta san wa ya yi mata gata ba shine a gaban idanunmu za ki furta wannan kalmar??
Waye ya ke yi miki munafurcin??”
Ya yi mata tambayar kamar yana shirin rufeta da duka!

Tashi d’aya Mommy ta sha jinin jikinta, tashin hankalin da take a ciki ya sake hauhawa…Tabbas a yadda ta ga Daddy ya fusata d’innan ta san muddin ta biye masa to fa za ta janyowa kanta matsala….
Shiyasa tashi d’aya ita ta sauk’o, a take ta fashe da kuka ta durk’ushe a wajen cikin kuka tace
“ka yi hak’uri Daddy dan Allah, ka yi hak’uri b’acin rai da tashin hankalin jin abunda kuke ik’irari ga Yassir ne ya janyo hakan, amma ka yi hak’uri da abubuwan da na fad’a ba zan sake ba, sannan dan Allah ka yiwa Yassir adalci, ka yi hak’uri, ko me ya aikata a ganina bai chanchanci hakan daga gareka ba!”

Da mugun sauri Yassir ya mik’e ya fice..inshaaAllah tunda har Mommy ta sauk’o ya san za ta san abun yi.
Chapter 132 · 0% Book details