← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 152

Sashe 35

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yassira, Baba larai sai Yadira da Yusra ne suka tsaya a bakin motar, suna jiran fitowar Yahanasu dan wallahi yau ba za su raga mata ba, rainin wayon nata ya yi yawa! Matar da ta ce musu ba ta san kwatancen gidan ba shine suna zuwa suka tarar da ita a bakin gate tana jira a bud’e mata….

Yahanasu kuwa ba k’aramin dad’i ta ji ba da taga su Aisha, dama tunda su Yasira suka je suka tambayeta ta san su da naci shiyasa hankalinta bai kwanta ba tace bari dai ta zo ta tabbatar da ba su zo d’in ba…..da farko da ta ga motocin su Yasirar a bayanta hankalinta ba k’aramin tashi ya yi ba ta shiga lissafin yadda za ta yi ta taka musu burki amman da suka shigo ta ga su Aisha sai ta ji wata nutsuwa da kwanciyar hankali sun rufar mata ga shi har da sir Najeeb! Ta san duk bala’in su ko ma menene suka zo yi ba su isa su yi a gaban sir Najeeb ba, ga kuma Ummi a hanya itama wadda ta tsaya yin waya da ita ne ma shiyasa ba ta fito daga cikin motar ba har yanzu…
….d’azu da Ummin ta ga su Yassira sun fito ne ta fahimci gidan za su zo, shiyasa ta ce su jira ta ta d’auko mayafi itama tana so ta zo gidan amman tana fitowa sai wayam ta gani! Sun ta fi sun barta, shine a take ta kira Yahanasu ita kuma ta yi mata kwatance, yanzu kam da suka yi wayar ma tana bayan layi….

Su Baaba Larai suna tsaye suna jiran fitowar Yahanasu suka ga su Aisha sun tunkarasu.
Baba Larai ji ta yi kamar ta koma cikin motar dan ta tsani
Yaran dama tun kafin ta gansu, sam ba ta k’aunar Manubiya da duk wani ahalinta….
Ba yadda ta iya haka ta tsaya dan ga Najeeb ya tunkarosu ta san shima gaida ita zai yi ba dan hakan ba wallahi da tuni ta koma cikin motar.

Aisha ce ta fara gaida Baaba Larai kafin su Siyama.
“Alhamdulillah” kawai tace, daga haka ta d’auke Kai, Yasira kuma ta yi sauri ta kara waya a kunneta ta matsa gefe gudun kar ma su yi gigin kulata.

Still Aisha ce ta cewa su Yadira “sannunku”

Kamar ba su ji ta ba haka suka yi mata.

Still Aishan ce ta kuma cewa Baba larai”ya taro?Allah ya sanya alkhairi”

Sai da ta juyo ta kalleta kafin tace“Ameen”daga haka ta zubawa Jidda da Siyama jajayen idanuwanta.

Ita Jidda har ga Allah tsoro matar ta bata, ga kuma Al’ameen da shege Yassir da suka kunno ta, ga shi taga ana amsa musu dakyar, su Yusra kam ko kallo ma ba su ishesu ba. Shiyasa kawai sai ta juya ta ce “Siyama, ku taho mu wuce ciki”

Kamar dama jira Yusra take, sai cewa tayi ”Atleast ai kya tsaya ki yi kyakkyawar gaisuwa da y’an uwan wanda kike k’ok’arin shigewa cikin gidan nasa”
Ta fad’i hakan tana murmushin
da Mutum zai kasa gane rashin iya magana ne koko dai rainin hankali ne.

Cike da mamaki Najeeb ya ce “Yusra! Languagee!”
Ya d’an ja k’arshen yana mai d’age gira sannan yad’an motse Baki.

Juya ido kawai ta yi ta kalli sama dan haushinsa dama gaba d’ayansu suke ji.
Ganin abunda ta yi ne yasa kawai ya d’auke kansa ya kalli Baaba Larai ya ce ”Ina wuni
Baaba ya hidima?

Murmushin yak’e ta yi
kafin ta ce ”Alhamdulillah,
Ya gajiyarku?”

“Mun gode Allah” yace,
kafin ya juya ya kalli Yassira wadda ta gama wayar k’aryar ta zo tana gaida shi, da kulawa ya amsa mata daga haka ya juya ya nufi cikin gidan yana mamakin yadda Yadira da Yusra suka yi masa..wato ko kallo ma bai ishe su ba! Tabbas
Yara sun girma kam….

Sir Najeeb yana shiga motar Ummi ta k’araso.
Already su Siyama ko gama gaisawa basu bari sir Najeeb ya yi da su Yassira ba suka matsa da niyyar shiga ciki….Yahanasu ta fito da fara a ta tarbe su kamar za ta goyasu, wanda hakan ba k’aramin sake tunzura su Baba Larai ya yi ba…ita Baba larai
Babban tashin hankalinta ma shine
ta yaya za ta aiwatar da mission d’inta
da waennan jama’un a cikin gidan?..
Lissafin da takeyi kenan suka ga gate ya zuge motar Ummi ta danno kai.

Cikin b’acin rai Yassira ta ce
“Innalillahi!
Tabbas Matar nan ta ci a bata sarauniyar y’an naci,
Mace ace ba zuciya kwata-kwata, a taho a barki amman sai da kika zo? Ko waye ma ya yi mata kwatance oho?!”

“Ba zai wuce angon da kika kira yace ‘mu jira mu taho da y’an d’aukar amarya’ba, kinga
ita da ta fiki ai gashi yayi mata tashi d’aya!”
Yusra ta bata amsa tana mai
wucewa ciki
ranta a mugun b’ace…
…..ta so su Jidda sun biyeta yau da sun ji maganganu wallahi! Ta san
ba class d’inta bane su ɗin
sannan ta san idan ta yi hakan zatayi acting childish (za a ga Yarinta a lamarin nata) amman
wallahi sai dai a kirata da jinjirar k’auye! Ba ta damu ba. Dan tunda ta d’aura idanunta a kansu ta ji ta rasa duk wani haƙuri kawaici da hankalinta tashi d’aya.
Tunda take a rayuwarta bata tab’a jin tsana irin wadda take yi musu ba…gashi ta san dole ta dinga ganinsu tunda sun riga sun had’a y’ar uwarsu da yayanta, watak’il ma a haifo
musu mai kama da su
Innalillahi!!!
wallahi za ta iya mutuwa idan hakan ta faru!…..

Ya zama dole a san na yi da Manubiya dan ba ta da guri da muhalli a rayuwar d’an uwanta!

Ashe dama akan wannan y’ar talakawan Ya Yash ya d’agawa kowa hankali! Dan ganin da ta yi wa su Jidda ya nuna mata cewa Manubiya talakan tukuff ce!…

Babu abunda ya fi sake b’ata mata rai kamar ankon atamfar 6500 d’in da suka yi a bikin d’an uwanta! Kamar Yash ace wai an yi ankon 6500 a bikinsa wannan lalacewa haka har ina?…..
Tana tafe tana waennan saƙe-saƙen Kamar za ta fashe! Haka ta afka cikin parlourn, ko bi ta kan masu goge-goge bata yi ba ta wuce sama…

Wucewa su Yassira suma suka yi suka nufi cikin parlourn
dan haka da sauri Yahanasu ta ce”mu je ciki muma, idan muka je kowa sai ta kama floor a samu a sassaka turaren wuta ya ratsa ko Ina dan ba lokaci.”
Ko ishashshiyar gaisuwa da introduction (gabatarwa) Yahanasu bata bari Ummi da Munirat sun yi da su Siyama ba, haka nan ta azalzalesu suka shige ciki.
Aisha ta d’an fahimci wani abun, ga kuma yadda y’an uwan Yashjub d’in suka rabu gida biyu da masu hankali da jahilai, shiyasa suna shiga itama ta cewa Siyama ta tsaya ita da Munirat da Jidda su saka turare a k’asan su yi ta
gyaygyarawa.
Ita da Ummi kuma suka yi sama da masu gado,
Yahanasu kuma ta yi chan sama turakar mai gida…inda
d’aki d’aya ne tak a floor d’in sai tafkeken roof top open terrace. Saman farko kuma
d’akuna biyu ne da parlour d’aya, sai wani parlour mai kamar d’aki wanda Yash ya zuba kayan gym a ciki dan haka suka tattara kayayyakin gym d’in Najeeb ya kira wasu a cikin masu gyara gidan suka kwasa aka kai d’akin Yashjub dan akwai wani guri a cikin glass inda za a iya zuba kayan, su kuma suka fara kafa gadon su a nan, Najeeb yana cewa “idan Yashjub ya zo Aisha zai nuna”
Itama tace
“Shi za ta ce ya chanza masa tsarin gida!”
Hakanan suna raha suka shiga had’a gidan.

A tunanin su Aisha sun yi zab’en gado mai kyau da tsada amman sai da suka b’ige da d’an jin kunyar
gadon nasu da suka ga kayan gidan, dan hatta d’akin chan k’asa guda daya na bak’i
Turkish ne a ciki wanda a k’alla sai an zuba miliyan goma tukunna za a sayi gadon.
Kaff gidan Turkish ne, Main parlourn k’asa ne kawai
royal, white da royal blue, colour din mai masifar kyau. shima kuma saboda ansan Turkish zai ɗan yi wa parlourn kad’an kasancewarsa
tafkeken gaske shiyasa aka zuba royal complete set ɗinsa d’urma d’urman gaske mai tafe da set d’in dining table da madubin sa da komai ma….

Kitchen d’inta ma royal blue ne da white, wanda had’uwa girma da tsaruwar kitchen d’in
yasanya Siyama da Munirat suka tsaya a ciki suna ta zancen kitchen d’in da k’auyanci suna yi wa kansu dariya
Dan tashi d’aya tasu ta zo daya gashi har sun saba……

Gidan ya had’u k’arshen had’uwa…
Duk inda aka ware domin deco
da saka tv an yi decorating nashi
da wani had’add’en painting wanda ya ke nan
jikinshi kamar marbles, kuma duk
iri d’aya grey da white wanda hakan kalar marbles d’in gidan yake gaba ɗaya mai masifar kyau, Pop da chandelier kam ba a magana ga toilets da closets suma abun kallo,gida dai ya had’u iya had’uwa babu makusa sai dai ta fannin masu Hassada
….
Shiyasa su Siyama suka dinga jinjina izza da kud’urar ubangiji dan tabbas idan ba Allah ba to babu wanda zai yi hakan,
‘wai nan ne gidan Manubiya!’
Allah mai girma da iko!.
Murna da farin ciki kam sun yi mata bila adadin dan ta samu duniya sai dai ta tashi ta nemi lahira, sannan ta samu Miji mai
tsananin sonta da k’aunarta, ga hutu Allah ya bata matsalar d’aya ce ‘dangin miji’ amman baya ga wannan
Manubiya kam ta samu komai…a ce a d’aukota daga gidansu tashi d’aya a kawota wannan gidan haka
mara makusa ko d’aya!
dan tun daga waje!gate!har compound d’in gidan wanda ya ji interlocking concrete da grass carpet, da garden
a haka ma basu zagaya baya sunga swimming pool ba,
Duk koina babu makusa.
Duk iya kushewar mutum sai dai ya hak’ura in ya shigo wannan gida na Manubiya da Yashjub.
…….
…D’akin bak’i Jidda ta bud’e ta shiga,ita sam ba ta yi tunanin akwai mutum bama sai da ta yi
ido biyu dasu Yasmeen tukunna tashi d’aya ta ce ”Sorry”
daga haka ta juya.
Chapter 35 · 0% Book details