Sashe 33
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasa bashi amsa ta yi sakamokon tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki yanzunnan, da kyar ta d’an juya ta kalleshi, a hankali ta ce “to, gamu nan zuwa”.
Bakinta kawai ya bi da kallo, kafin da kyar ya ce ”ok”
daga haka ya wuce ya nufi motarshi ya shiga ya zauna.
Ita dai Siyama za ta iya cewa tunda take a rayuwarta bata tab’a had’uwa da wanda tashi d’aya ta tsaneshi kamar Yassir ba, gashi dai kyakkyawa kuma d’an gayu amman sam bai mata ba!
Ta lura da yanayin kallon da yake yi wa mutane wanda duk wanda ya gani kai tsaye zai san ba na Allah da Annabi bane sab’anin na sir Najeeb…wanda ana ganinsa dama an san ya fi sa hankali.
Shiyasa yana wucewa Siyaman ta kalli Jidda ta ce ”sai dai fa ke ki shiga motarsa, dan na san idan na shiga ni to kafin mu k’arasa tsaf zan iya tsinka masa mari in gaggaya mishi magana! Na tsani Namiji mai kallon iskanci….”
Jin Jiddan ba ta ce mata komai bane yasanya ta kalleta sosai kafin ta ce ”Jidda!”
Firgigit ta ga Jiddan ta yi, kafin ta d’an juyo ta kalleta sai kuma taga ta sake juyawa ta maida idanunta ga balcony d’in gidansu Al’ameen, a ranta tana mamakin “anya shi ta gani kuwa! ko dai gizo ya ke yi mata..yaushe ya dawo…ko nemanta bai yi ba”
da sauri kuma sai ta kawar da tunanin…amma dukda a zuciyarta sai da ta sake cewa ”ko ma ya nemeni ni kam dama ba kulasa zan yi ba”
Da mamaki Siyama take kallonta kafin ta kalli inda ta ga ta tsurawa ido tukunna ta ce ”Jidda! Ki shafawa kanki lafiya, ki rufawa kanki asiri…”
Kasa cewa komai Jidda ta yi tana mai jin yadda kwallah take k’ok’arin zubo mata dan haka ta yi sauri ta ce ”ki zo mu je kawai, Aisha in ta fito sa tafi da wanchan”
Ta yi maganar tana mai yin gaba abunta….Tabbas ta san ko da ace tanason ta b’oye sannan ta share al’amarin to ba lalle ta iya ba!
Dan ba kad’an ba ta ji tsananin ciwon abunda Al’ameen yayi mata, har fa aiki yayarta ta yi a gidansu duk ata sanadiyyarsu amman shine ko sak’on ‘hi’ bata samu daga garesa ba bayan ya dawo kuma ta san ya ji komai.
Tana k’arasawa ta bud’e gaban motar ta shiga ta zauna ta runtse idanunta…k’ok’ari
kawai takeyi ta ga ta hana kanta kuka.
Tun d’azu ta lura da yanayinshi da yadda yaketa faman shishige mata, shiyasa
yanzun ma ta ƙi yarda ta tsaya opposite d’inshi ko kuma kusa da shi, ba ta son shiga motar Yassir har ga Allah to amma d’ayar motar kuma ta sir Najeeb d’in ce, shiyasa ta tsaya tana wasu-wasi akan ta bi bayan Jidda ne ko kuma
ta tsaya Aisha ta zo su wuce tare a motar Najeeb d’in…..ba ta gama tunani ba ta ga ya tunkaro ta.
Tashi d’aya ta diririce ta kuma fara da na sanin k’in bin Jidda da ta yi….har ga Allah fargaba ta ke ji idan ya matso kusan ta.
Yana k’arasowa dai-dai Aisha tana fitowa rik’e da robar capulas wadda ke d’auke da turaren wuta, coal har da kasko da ashanarta.
A hankali Siyama ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya
wadda har sai da duk su biyun sukaji, dariya ya d’an yi kafin ya ce da Aishar “kin barmu a rana”
Kallonshi kawai Aisha ta yi a ranta tace “ikon Allah”
ita yake yi wa magana amman idanunshi na akan Siyama, shiyasa kawai sai ta yi murmushi tukunna ta ce ”ku yi hak’uri”.
Siyama ce ta ce mata
“ga Jidda chan, bari in je mu tafi tare, ke
kwa taho”.
Da sauri Aisha ta ce ”a’a, bari ni in je mu tafi tare da su, ku kwa taho ku biyu.”
Tana gama fad’in haka ta yi gaba, dan ita har ga Allah had’in nasu ya burgeta, gashi Najeeb d’in nutsattse dashi daga gani…..ko bai fad’a ba ta san yana ciki ne da Siyama shiyasa ta basu sarari ta barsu su biyu, ita kuma ta nufi motar da akace mata Jidda tana ciki mai uban tint!
Ita kanta Jiddan sai da ta shiga ma tukunna ta lura da tint d’in tsabar b’acin ran da take a ciki.
Ko minti uku batayi da zama ba Aisha ta bud’e gidan baya ta shiga, dan haka Yassir ya kunna motar bayan sun gaya mishi inda za su je su kwashi kayan daganan su wuce gidan amaryar…
sam Yassir bai so
Aisha ta shigo ba, so yayi a bashi chance da guda d’aya kawai musamman ma Jiddan
dan shi a rayuwarsa dama yana
matuk’ar son mace fara fat! Ga ta wannan ga shape ga kyau ga ta da Yarintarta…
Kuma zuwa yanzu ya lura tana da hankali da nutsuwa gata very innocent dan ba ya jin ta yi magana sau uku tun
daga farkon ganinta da yayi har izuwa yanzu..
Ba dan yaso ba ya kunna
Motar yayi gaba yana tuk’in yana satar kallon Jidda yana mamakin abunda yake shirin sakata kuka.
Aisha tana wucewa,
Najeeb ya lura da yanayin Siyama…dariya ya yi ganin yadda ta yi da fuska kafin ya ce
“Savior d’in taki ta tafi ko?”
Shiruu ta d’an yi kafin ta d’an girgiza kai kawai.
Murmushi yayi yace “ki fad’i abunda ke ranki fa”.
Shirun da ta yi ne yasa ya sake cewa “to tunda ba za ki fad’a ba, bari ni in bada hak’uri dan
ni kaina na san na takuraki, ki yi haƙuri nima na kasa hana kaina ne, shiyasa, ayi min afuwa…um..?”
Ya fad’i hakan yana had’e hannuwanshi alamun rok’o.
Kamar ba zata yi magana ba sai kuma tace”ba komai fa”.
“Really?to ya naga sai faman had’e rai kike yi, musamman ma a wajen hoto?”
Ya fad’i hakan cikin tarar numfashinta.
Kamar za ta ce masa
Yassir ne bataso, sai kuma ta yi shiru dan sun fahimci Yassir k’anin Yashjub ne, kar ta je ko shima sunada dangantaka da Najeeb d’in sosai apart from
Abota ta je ta kwafsa..
Wucewar motar su Yassir ɗin ne ya sanya shi cewa ”mu bi bayansu
kar mu b’ata, kin d’auke
hankalina
Like seriously banma san lokacin da ya kunna motar ba.”
Ya fad’i hakan yana kallonta
sannan ya d’an matsa ya nuna mata hanya da Hannunshi.
Wucewa ta yi, shi kuma ya bi ta a baya yana mai jin wani shauk’i da annashuwa suna ratsashi….tun a asibiti ya kamu yau kam ya sake kamuwa katamau ya fad’a tsundum!
Adduar shi d’aya ‘Allah ya sa babu wani, sannan Allah ya sa ta amince da shi,’
dan shi kam ya ga mata, kuma inshaaAllah sai ya samu, da izinin Allah.
Ba kad’an ba ta ji kunya da nauyinsa da ya bud’e mata marfin motar, dan ta san wannan ya fi sa’an su Ya Yusuf ma a shekaru, sosai…..
Sai da yace “bismillah” tukunna ta d’an d’aga kafarta dakyar ta haye motar dan irin ƙirar jeep d’innan ce mai
tudu da fad’i sosai amma ba ta cika tsayi ba.
Sai da ya rufe mata murfin motar tukunna ya juya ya koma side d’inshi, ya bud’e ya shiga ya kunna da sauri da sauri dan ya daina hango Yassir, kuma ya san ba gidan amarya a ka nufa direct ba.
Da kyar kuwa ya hango shi bayan sun fita titin, dan haka ya shiga binsa har ya samu
ya tadda shi, suka jeru…
Sai da ya jeru da Yassir d’in tukunna ya d’an kalli Siyama wadda take ta faman danna wayarta ya ce “ku dai Mata bakwa gajiya da chatting!”.
Kashewa ta yi, ta d’an sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce ”ba chatting nake yi ba, pictures d’in d’azu da na yi da wayar nake
dubawa”.
Kallon hawaii d’in tata ya yi kafin ya ce ”ai mai hotunan zai turomin clear ones…”
ganin ya
samu opportunity yasa ya yi sauri ya mik’a mata wayarshi tukunna ya d’aura da cewa”ki saka min numberki, sai in yi miki sendin ta watsapp idan ya turo”.
Kamar ba zata karb’a ba sai
kuma ta karb’a ta rik’e wayar a hannunta ta shiga jujjuyawa…..da kyar ta gano inane gaba sakamokon hasken da screen ɗin ya yi, sai kuma ta rasa ta yadda za ta yi sliding dan babu alamun touch ko hanyar dake nuna mata ta inda zatayi sliding keyboard d’in ya fito, kuma ita har ga Allah bata shirya basa number ta ba! Bata dad’e da fita daga bak’in cikin ex boyfriend d’inta (tsohon saurayinta) ba, wanda
har ya gama cin amarcinshi ya dawo sai faman naci yake yi mata tsabar ya raina mata wayo. ko me yake nufi da ita oho.
Bata shirya samun wani sabon baƙin cikin namiji ba bayan wanda ta riga ta samu….
had’in su Manubiya aya ne izina ce!
Allah ne yayi had’insa, ita kuwa ba za ta d’aukowa kanta dala babu gammo ba…..
Shirun da ya ga tayi ne ya sanya ya d’an sosa k’eyarsa
kafin ya ce ”okay fine!
Ko zan iya samun numberki? Saboda ina matuƙar buƙata,..ba wai saboda sending pictures ba”
Ya fad’i hakan yana mai yin kalar tausayi da fuskarshi.
Murmushi kawai ta d’an yi..ba tare da ta san ya za ta yi ba ta d’an shafa kan wayar, da
ikon Allah kuwa sai taga ta bud’u, tashi d’aya ta hango
Phone dan haka ta shiga ta juye masa digits d’in nata daga haka ta mik’a masa wayar tana da ta sanin bashi.
“Tnx” yace.
Sai da ya kira ya ji ya shiga wayarta tukunna ya yi saving ya ajjiye wayar ya ci gaba da janta da hira.
Sama-sama ta ke d’an biye shi..ya lura Siyama irin y’an matan nan ne masu jan aji shiyasa tashi d’aya ya fahimci zai sha wahala..sam bai damu ba dan shi indai za ta kulasa to ba ruwansa..tabbas ya san sai yanzu zai fara soyayya! Dan a lokacin da Ya’isha take ja mishi rai k’ulewa yakeyi ya ji haushi amma da ikon Allah ko fushi ya kasa yi anan, duk kalar basarwa da cin maganin da Siyama take ta yi sam ya kasa yin ko da fushi sau d’aya d’an kad’an ne.