← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 152

Sashe 84

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata bahaguwar ajiyar zuciya Kausar ta sauk’e kafin ta d’an matsa garesa tace’’ Bari kaji abunda baka sani ba! Ko da ace Mommy bata tab’a shiga aji ba,wallahi ba zan yi kaffara ba itama ta d’an fahimci wani abun,sakamokon yadda ka dinga k’ok’arin tonawa kanka asiri tun a crime scene d’in,har sign na dinga yi maka da ido amma sam ka kasa fahimta…..
Shiyasa ka ga hankalina ya tashi raina ya b’aci, ga kuma rashin lafiyar da take damuna,’’

Ahankali ta sake taku d’aya ta kamo hannunsa ba tare da ta zagaya gabansa ba ta ci gaba da cewa’’ranar a d’akinka na gaya maka ina tare da kai a ko yaushe, Yassir tunda har na iya danne zuciyata na had’a ka da Munirat inaso ka san na d’auki mission d’innan (aikin nan) da mahimmanci, duk da na san cewa kashe Yashjub ba ya cikin tsarinmu amma idan har ka gaya mini dalilinka zan goya maka baya, kai ko da ace ba za
ma ka gaya mini dalilin naka ba Yassir zan goya maka bayasaboda ina sonka kuma ina so in ga ka yi nasara akan komai, kai kuma a ko da yaushe kamar baka yarda da ni ba shiyasa ban san ta ya zan nuna maka ina son naka ka yarda da ni da gaske ba, da ace na san taimakon ka da muka yi da ni da Mommy zai janyo mini haka daga gareka da ban yi ba tunda na lura tun lokacin da na d’an ja baya da kai saboda mu samu a fasa aurenmu a k’ara maka share har gobe baka yarda da ni ba Yassir’’
Ta k’arashe maganar tana mai durk’ushewa a wajen ta fashe da kuka.

Ahankali Yassir ya sauk’e ajiyar zuciya, tashi d’aya ya fara ganin rashin kyautarwar sa,ta ya ma zai kasa yarda da Kausar bayaga dukkan abubuwan data gayamasa da irin gogayyar da take yi wajen ganin ta taimaka masa,shi sai yanzu ma kwakwalwarsa ta d’au charji amma kwanaki da d’azu gaba d’aya duk kishi ya rufe masa ido, tabbas everything is fair in love and war!’they are at war’ dan haka komai is fair kamar yadda ta fad’a dan ta had’asa da Munirat saboda su samu su cimma abunda suke so bai kamata ya dasa ayar tambaya a kanta ba wanda hakan ne farkon zargin nata da ya fara,tunda in komai ya yi daidai ya tafi yadda suke so ai sune da nasara.

Ahankali ya juyo yana jin tsananin tausayi da k’aunarta suna ratsa sa ya ce ‘’stand up’’
A ranshi yana mai cewa “inshaaAllah zai yi k’ok’ari ya goge tunanin’watak’il Kausar tana son Yashjub’ daga cikin zuciyarsa. Amma a karo na ƙarshe akwai abunda yake son ya tabbatar ta yadda zai yarda da ita d’ari bisa d’ari.
Ganin ta k’i tashi ne ya sanya shi ya durk’usa ya kamota ya d’ago da ita tashi d’aya ya sakata a jikinsa yana mai bubbuga bayanta alamun rarrashi,sun jima a haka sai da ya ji ta yi shiru tukunna yace “Kausar tambayar da zan miki na ƙarshe….na ga kina kuka sannan na ga hankalinki ya tashi kuma muna shiga da kika ga Yashjub da Manubiya kika juya za ki fita wanda hakan yana nuni ne da ba za ki iya jura ba ba zaki iya ganin su a haka ba kenan!,inaso ki faiyyace mini dalilin reaction d’inki ta yadda komai zai tafi daidai a tsakani na da ke.”

Da d’an fushi sakamokon tuno mata da abunda ya fi komai d’aga mata hankali da yayi tace “Yassir bani da lafiya, amai nake ji shiyasa na yanke shawarar in tafi”
Kallon ta ya yi kafin yace’’amai kuma?….wanne irin rashin lafiya kike yi da zai baiyyana kishi da b’acin rai a kan fuskarki?ko dai ba zaki iya jurar ganinsu…’’

Turesa ta yi da dukkannin ragowar k’arfin da take ji tukunna ta juya a fusace ta nufi toilet…bin ta shima ya yi dan bai gama da ita ba tukunna.

Tana d’auko pts d’in ta juya za ta fita suka yi kicib’is da shi, kallon sa ta yi ta kamo hannunsa ta damk’a masa still tana kallon cikin idanunsa tace
“Bani da lafiya!”

Had’e girar sama da k’asa ya yi
kafin ya d’ago abunda ya ji ta saka masa a cikin hannunsa,sai da ya kai hannun nasa saitin fuskarsa kafin ya
janye idanunsa
a cikin nata
ya mayar kan tsinken.
Da mamaki k’arara kwance a kan fuskarsa yace
“What!!”
Sai kuma ya kalleta yace
“Tayaya?”

Cikin fushi tace
“Kut!!!tambaya ta ma kakeyi
‘Tayaya??’.“
Tsabar takaici kasa ma cigaba da tsayuwa tayi dan haka ta bangaje sa ta wuce.

Lumshe idanunsa yayi ya furzar da iska, kafin ya bud’e ya juya da sauri ya bi bayanta.
Har ta kusan kaiwa bakin k’ofar d’akin nata, dan haka ya bi bayanta da d’an gudu ya cafkota ya juyo da ita.

Takaicine ya sanya ta fashewa da wani sabon kuka gwanin ban tausayi.

Tashi d’aya jikin Yassir ya sake yin sanyi,bai ma san lokacin da ya janyota ya sake rungume ta ba,yana mai jin tausayi da k’aunarta.
Cikin muryar rarrashi
yace “Haba Kausar,sai kace wata k’aramar Yarinya?
kar ki damu kanki mana, kawai kamar na wanchan karon wannan d’in ma za mu san yadda za mu yi da shi,plss ki daina kukan nan.”

Cikin kuka tace”Yassir ka cuceni!
Shikenan ni na zama sarauniyar zubar da ciki kenan???
kaf gidan nan
a kaff cikin y’an uwanka mata
ko ɓatan wata babu wadda ta tab’a yi amman ni k’iri k’iri ka maidani karuwar k’arfi da yaji!!
saboda ni ba y’ar uwarka baceba ko?
Idan nace ‘A’a’ kuma
ka dasa ayar tambaya a kaina.”

Kamar zai yi kuka yace
“Not at all Kausar,kawai dama ina tunani ne….”
shiruu ya yi
sai kuma yace
“Shikenan
Na yarda dake yanzu na fahimci komai komai kuma ya wuce,na yarda da ke daga yau inshaaAllah”

Turesa ta sake yi
tana kuka kamar ranta zai fita
da kyar ta iya cewa “Yassir
Me kake zargina da shi a da ɗin?”

Sake ruk’ota yayi
cikin sigar lallashi yace
“Na fad’a miki ki manta kawai”

A karo na uku ta sake turesa itama tukunna tace
“Dole fa sai ka gaya min,
me kake tunani a kaina da! Bayaga tunaninka na bana sonka ba na kishin ka?akwai wani abun, menene shi?”

Runtse idanunsa yayi ya d’an sunkuyar da kansa
tukunna ya d’ago ya furzar da iska ya bud’e idanuwan nasa sannan yace
“Okay fine!
Da Ina tunanin kamar kina son Yashjub ne.”

Da k’arfi tace
“What(me)?”
sai kuma ta sake fashewa da kuka
kafin ta sa hannu ta kamo sa sai da suka isa k’ofar d’akin ta murza key ta bud’e tukunna tace
“Get out Yassir! (Fice min a ɗaki Yassir)
Tunda dak’ik’in tunaninka
da kishi sun rufe maka ido,
ba na jin akwai abunda zan gaya maka kuma ka yarda da ni.ka je ka yi tunanin duk ma abunda ka ke so, ban damu ba, tunda duk bayanin da na yi maka ranar a d’akinka ba ka yarda ba!!.
Hatta sirrin da Mommy ta gaya mana wanda ba kowa ake so ya ji ba duk sai da na gaya maka..amma shine still ba ma ka yarda da ni ba??
shikenan!!
Ba komai.”

Ahankali yace “Kausar”

Cikin fushi tace
“trust yana da matuƙar mahimmanci Yassir….
taya ma za ka yi wannan tunanin a kaina?.
Baka san yadda ka ɓata mini rai yau ɗinnan ba!.
Ka fice mini daga ɗaki kawai”

Matsowa ya yi da sauri yai hugging d’inta yasa k’afa ya tura k’ofar ya rufe.

Ba yadda ba ta yi da shi ba
amman sam ta kasa kwatar kanta,dan haka ta sake sakin wani kukan kawai…

Lallashinta ya shiga yi a chan k’asan zuciyarsa kuma yana daya sanin zarginta da yayi…

Sai da ya ji ta d’an yi shiru
tukunna ya cikata ya ce”na yi laifi, a karo na farko gashi na yi yarda na karɓi laifina kuma na yarda na yi miki laifi, ki yi hak’uri.
InshaaAllah ba zan sake ba,
sannan daga yau ba zan sake dasa ayar tambaya a kanki game da komai ba I promise!.
Duk abunda kika yi kawai zan yarda dake ne, ko ma menene.
Pls Kausar ki yafe min”
Ya fad’i hakan ya na k’ok’arin durk’usawa.

Da sauri ta rikesa ta d’an girgiza masa kai…sake yunk’urawa yayi zai durk’usa dan haka tace
“Ya wuce, ba komai”

Ahankali yace “thanks love..sosai sosai”
Sai kuma ya d’an kalli shafaffen cikinta yace”mu zauna sai mu yi magana ko?”

Jinjina kai kawai ta yi
daga haka ta wucesa ta isa
bakin gadonta ta zauna

Tana zama shima ya zauna
Ba tare da b’ata lokaci ba yace
“Yaushe kike so mu je asibitin??”

Sai da ta d’an d’auki lokaci tukunna tace”ba zan je asibiti ba,idan cikin ya kai wata biyar sai in fara zuwa awo
InshaaAllah”

Da sauri yace “Kausar pls
kar mu yi haka da ke mana!
Wacce irin magana ce wannan??”

Girgiza kai ta yi kafin tace
“Yassir ba zan iya yin wani abortion d’in ba fa,ai ka ji dai da kunnenka abunda Doctor yace mana the last time ko?…ko kana so mahaifata ta lalace tun kafin na fara tara iyali??
Bayaga haka ma
ai ni na sha gaya maka dama a ko da yaushe ba son rabuwa da babyna nake yi ba, hak’uri kawai nakeyi ina biyeka.”
A hankali ta kamo hannunsa ta d’aura a kan cikinta tace
“wannan babynmu ne,
kasancewarsa jininka ya sa na ji Ina matuk’ar k’aunarsa ,
saboda tsananin son da nake yi maka, ba zan iya rabuwa da shi ba,wallahi ban tab’a jin so da k’auna bayan wanda nake yi maka ba sai a kan cikin nan!”

Damk’e hannunta ya yi da k’arfi dan ba kad’an ba
maganganunta sun shige sa sun yi tsananin tasiri sun kuma ci galaba a kansa.
Ya jima maganganunta suna ratsa sa kafin a hankali cikin kwantar da murya yace
“Kausar!!
Daddy will kill me
Mommy ma Allah kad’ai ya san mai za ta ce…me”

Cikin katseshi tace
“Kanka kawai ka ke dubawa??”
Chapter 84 · 0% Book details