← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 152

Sashe 96

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Baba, Yashjub wanda k’arasowar sa kenan sai su Ya Musbah sojojin suka yi wa bayanin arresting Yusuf ɗin da aka yi……
…..”A cikin wayar black snake suka hararo Yusuf ta hanyar bibiyar chat d’insu da suka yi, an gano yana d’aya daga cikin manya manyan yaransa masu tayashi safarar kwayoyi da y’an mata, dan yanzu haka ma a halinda ake ciki a wannan ranar ba dan an kamasa ba to suna shirye shirye ne a kan shi Yusuf d’in zai taimaka a sacewa Black Snack wata Yarinya ‘Mannubiya’…..”
Dan haka za su tafi da shi, kuma babu bailing, har sai sun gama interrogating d’insa, daganan idan suna so za su iya d’aukaka k’ara zuwa kotu kafin a yanke masa hukunci….

Suna ji suna gani aka datsawa Yusuf ankwa wanda yake ta turje turje aka wuce da shi, shi dai Baba bai gama gasgatawa ba amma su Ya Musbah da Yashjub wanda yake ji kamar ya bisa ya fara nad’a masa shegen duka tun a nan saboda tunanin sace masa mata ma da ya yi,duk sun yarda.

Kaka mallan kam har da kukan sa a take ya nemi adaidaita sahu ya nufi gida yana tafe yana kiransu Baba Habu a waya…..

Limamin ne ya matso ya yiwa Baba jaje kafin yace “yanzu a yi sanarwa Akan an fasa d’aurin auren kowa ya watse kenan? ko za a d’aura ko babu shi?”
Murmushi ya Nafi’u ya yi ya kalli Baban Al’ameen wanda ya k’araso yanzun yace”za a yi d’aurin aure yanzu amma ba da wanchan Angon ba,an chanja sabon Ango.”

Jinjina kai Baba ya yi yana jin wani nauyi yana sauk’a daga kan k’irjinsa , dan har ga Allah da ya d’aura auren nan yau da bai san ta ya zai kalli Jidda ba,cike da kwarin guiwa ya kalli Limamin yace”sunan sabon Angon Muhammad Al’ameen Muhammad.”

Murmushi mahaifin Al’Ameen ya yi a fili yace “Alhamdulillah”
Daga haka suka d’unguma izuwa cikin masallacin.

Jidda ne kawai da Siyama sai Muhsin wanda shima ya yi jigumm a cikin d’akin….
Kamar a mafarki ta ji ana sanarwa a loudspeaker”An d’aura auren Muhammad Al’ameen Muhammad da Maijidda Musa akan sadaki naira dubu d’ari biyu lakadan ba ajalan ba….
Wani irin bahagon numfashi ta fesar ta sake kwantar da kanta a kan cinyar Siyama wasu zafafan hawaye suka shiga gangaro mata a ranta tace”shikenan na zauce!!gashi dai k’iri k’iri da Yusuf aka d’aura auren nan na riga na sani amma sunan Ya Al’Ameen nake ji…..”
“Jidda kin ji abunda kunnuwana suka ji kuwa???”

Shiruu ta yi kafin ta tashi a mugun zabure ta mik’e ta zauna sakamokon abunda ita da Siyama da Muhsin suka ji an sake fad’a ana kuma maimaitawa a loudspeaker, dai-dai nan su Anty Umma suka shigo, Anty Umma tana shigowa ta rungume ta haka ma Aisha wadda take waya da Nafi’u domin ta tabbatar….
Sai da ta yanke wayar tukunna ta sanar da su komai abunda ya faru…
Nan waje ya kaure da murna Jidda kuma ta fashe da kukan da kowa ya san na farin ciki ne…
Har cikin d’akin Ammi ta shigo ta rumgume Jidda ta sake neman yafiyarta tukunna tace”Bari ta tafi ta fara shirye shiryen tarbar amarya…”
Tare suka tafi ita da Mama domin su je su d’anyi shirye shirye….Zuwa yanzu Mama ta tabbatar Yashjub dai d’an gidan Imam Manubiya ta aura, dan tana ganin su Yusra ta ga kamanni, ta dad’e da yi wa kanta alk’awarin fita daga harkar Imam da zuri’arsa amma kuma tana so ta ji ya Yahanasunta take,dan haka ta tsara a kan za ta ke tambayar Manubiya halin da y’ar tata take ciki ba tare da ta bari ita kanta Manubiyan ta fahimci wani abun ba….

Akwai tafiyar da Al’ameen zaiyi zuwa Dubai nan da sati d’aya, shiyasa ana gama d’aurin auren Mahaifinsa ya cewa Baba”sai nan da sati d’aya tukunna za su d’au amarya inshaaAllah daganan direct sai a wuce da ita airport”
kamar ya sani sai ya d’aura da cewa”amma dai za su fara magana da Angon yanzun duk yadda suka tsayar zai kira sa.”
Aikuwa albishir yana zuwar ma Al’ameen bayan ya gama kukan farin ciki ba kunya ba tsoron Allah ya ce shifa kawai a kawo masa matarsa yau su zauna a nan kafin su wuce”
Dariya su Ammi suka yi suka kira su Inna suka sanar musu….k’arfe takwas dai dai aka kawo amarya Jidda side d’in Al’ameen da ke cikin gidan.
Sai da kowa ya watse tukunna ya shigo…farin ciki da tsantsar nishad’i masoyan suka tsinci kansu a ciki mara musaltuwa….tunda ya shigo ya yi hugging d’inta suka yi shiruu da kyar ya cikata suka yi nafila suka d’anci abinci daga haka ya ja ta ya sakata a jikinsa yana sauk’e ajiyar zuciya yana hamdala suka kwanta…..Jidda har ta fara fargaba..ganin awa d’aya awa biyu bai yi yunk’urin yi mata komai ba ya sa ta kwantar da hankalinta tana mai sauraron yadda k’irjinsa yake bugawa da k’arfi har zuwa wannan lokacin,a haka suka kwana ranar kamar wanda aka cewa wani zai zo kwace masa ita ne,ita kam Jidda jikinta har ya fara tsami tsabar yadda ya ruk’umk’umeta…..

Tun a wajen kai amarya Yusra ta kira Ya’isha tace”to fa babu abunda aikin Baba larai ya yi, dan ga Najeeb da Siyama nan kamar za su cinye juna!”
Dabass!!!haka Ya’isha ta zauna a kan kujerar parlourn Mommy sai kuma hawaye suka fara bin fuskarta…
Da mamaki Mommy da Baba larai waenda suke cikin tsananin farin ciki suka shiga kallonta don yanzunna ta dawo daga ganin Abbakar take ce musu”Da farko ya d’an so ya yi zurfin ciki, amma daga baya ya amince d’ari bisa d’ari it’s like ya ma fi su son mutuwar auren Manu da Yash d’in,kuma yace’ba ya buk’atar sisin kobo kawai su kular masa da mahaifiyarsa su biya duk wasu kud’ad’en asibin ta’.”
Hakanan suna ta murna ita da su to kuma me ya saka ta kuka tashi d’aya haka…
Mik’ewa Mommy ta yi ta k’arasa inda take ta shiga tambayarta,da kyar ta iya ce mata”ai Najeeb da Siyama aka
gani tare har yanzu suna tare ba su rabu ba….”
Sai kuma ta mik’e ta fice da sauri tana kuka.
Shiruu Mommy ta yi ta fad’a duniyar tunani,har ga Allah tana mutuwar son Najeeb ya auri Ya’isha gashi abun na Y’an matan nata zuwa yanzu shima ya fara damunta..Jiya ta ga d’aurin auren d’an k’awarta wanda suka shirya ita da k’awar tata a kan za a had’asa shi da Yasira,tsabar abun da munafurci ko gaiyyatar ta bikin ma ba a yi ba sai kawai d’aurin aure ta gani….
“Ki kwantar da hankalinki,inshaaAllah duk za su yi aure,Najeeb kuma shima ki barni da shi, bari mu fara gamawa da Manubiya tukunna”
Muryar Baba ta katse mata tunaninta.
A hankali tace”Baba larai idan kuma ya kai kud’i kafin a gama da Manubiyan fa?”
“Kar ki damu ba zai kai ba,ai ita Manubiya inaga ba lalle ta k’ara sati biyu a cikin gidan nan ba fa! Komai a shirye yake, kuma yana tafiya a kan tsari ga kuma wanchan Yaro d’an albaraka Abbakar shima yana side d’in mu, dan haka kawai ki kwantar da hankalinki a kan komai…kar ki damu Najeeb zai dawo sannan shima wanchan na Yasirar ko a ta biyu ne za ta shiga inshaaAllah……”
“Allah yasa”
Kawai Mommy tace, daga haka ta yi shiruu haka itama Baba larai.

Bayan sati biyu!.

Satin su Jidda d’aya a Nigeria suka wuce Dubai ita da Al’Ameen, dan cikin sauk’i ta samu visiting visa.

Najeeb da Siyama abu ya yi k’arfi, da shi da Yashjub har sun je sun nemi izinin zuwa zance a wajen su Baba Habu wanda hakan idear Baba ce,yanzu haka kuma maganar kawo
Kud’i da saka rana ake yi…..

Yusuf kuwa babu shi babu labarinsa an hana ma ganinsa,sai dai hakan kamar ya sake ruru wutar bala’i tsakanin Baba da y’an Uwansa ne, a cewarsu”tsabar mugunta a gabansa shi da Yashjub aka tafi da Yusuf amma ba su yi komai ba maimakon bin bayansa kuma su d’aurin aure ma suka ci gaba da yi.”

Ya’isha Yassira da Yusra kuma suna gidan Manu har yanzu, sun kafa sun tsare!
da farko ba sa samun damar yin chatting da Abbakar ta wayar Manu kamar yadda suka tsara, sai da aka yi sati d’aya suka samu Siyama ta tafi tukunna….sai sun daidaici ta tada sallah za su d’auki wayartata su yi abunda suka ga dama su goge su ajjiye mata wayar kafin ta idar, dama shima Abbakar ya san time d’in da suke samun chance shiyasa a ko da yaushe ya ke available……Ana gamawa za su goge gudun kar ta gani shi kuma Abbakar yana chan yana tarawa a tasa wayar.
Chapter 96 · 0% Book details