Sashe 92
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana fitowa ta hangesa zaune a corridor kan sofa ya dafe kai da hannu bibbiyu.K’arasawa ta yi da hanzari da d’an mamaki, ta zauna a kusa da shi kafin tace”Ina kwana”sai kuma ta d’aura hannunta a kan nasa tace”Ya Yash”.
Cikin kasala ya bata iko ta zame hannuwan nasa da take k’ok’arin yi, daga kansa, kafin ya juyo ya zuba mata ido kawai ba tare da ya ce komai ba.
Sai da gabanta ya fad’i sakamokon yadda ta ga idanuwan nasa sun yi jazir…tashi d’aya tausayinsa ya rufe ta sannan gaba d’aya ta shiga jin babu dad’i dan ta san itace silar wannan yanayin da yake a ciki…ta san ba ya iya d’aukar kwanaki masu tsawo ba tare da ya rab’e ta ba.
Haushin kanta ma ta soma ji dan haka cikin inda inda tace”Ya Yash dan Allah ka yi hak’uri,ka san ba ni da lafiya shiyasa…”
“It’s fine”d’in da ya ce mata cikin katseta ne ya sa ta yi shiru.
Tashi d’aya ta ga ya mik’e,yace “idan breakfast ya kammalu ki kawo mini,bari in d’an kwanta, kaina yana mini ciwo,idan na tashi zan ci”
Daga haka ya wuce ya shige cikin d’akin.
Sukuku! haka ta had’a masa abincin, jikinta da ranta duk babu dad’i, ga kuma zazzab’i. babu yadda Yasira da gwaggwo ba su yi da ita a kan ta kawo su taya ta ba amma tace musu”ba komai,za ta iya”dan haka Yasira ta yi mata sai anjima ta wuce office, Gwaggo kuma ta ci gaba da had’a nasu.
Abinci kala uku ta yi
masa da coffee, ta d’auka ta nufi saman, ta je ta ajjiye a cikin d’akin,ta so ta zauna a tare da shi amma tana zuwa sai ta ga yana bacci gashi d’azu ta ji yace mata kansa na ciwo, shiyasa ba ta tashe sa ba ta ajjiye a dining table d’in d’akin, ta yi wanka a hankali yadda ba zai ji ba ta fito ta rufo masa k’ofar d’akin.
Tana fita ya bud’e ido ya bi k’ofar da kallo…
‘a yadda ta ga yanayinsa in da ace ta damu da shi ai da ta tsaya a tare da shi’
Ya aiyyana hakan a cikin ransa.
A d’akin da Siyama take ta tarar da su Yusra suna hira itama Siyaman ta na d’an biyesu ba laifi…
Sai da Manu ta zauna tukunna suka gaida ita kafin Yadira ta mik’e tace”bari ta je ta d’ebo mata abinci”
Ba yadda ba ta yi da ita akan ta barshi ba amma ta k’i ta fice ta tafi deb’owa.
Tana fita Yusra tace”jiya ma kuwa muna rabuwa Mommy ta kira tana so ta ji ya jikinki, ba ta so ta kiraki direct kuma gudun kar ta tasheki dan ba ta sani ba watak’il ko har kun yi bacci,bari in kirata yanzu sai ku yi magana”.
Murmushi Manubiya ta yi kafin tace”barshi ni in kirata da layi na”
Murmushi Yusra itama ta yi tace”anya kuwa kina da sabon layinta?barshi dai in kira”
Daga haka ta kara wayar a kunnenta bayan ta yi dialing…
Bugu biyu a na uku Mommy ta amsa, sai da suka gama gaisawa tukunna tace”ga Adda Manu d’in ta sauk’o, jikin nata Alhamdulillah, amma ga ta dai ki ji muryarta.”
Tashi d’aya Mommy ta fahimci they are up to something, dan haka ta ce “ok ba ta wayar”
Kawai.
Yusra tana mik’awa Manubiya wayar ta tsink’e.
“Ki yi magana mana kin yi shiru”Yusran tace.
“Ai naga kamar ya tsink’e ne”
Cewar Manubiya.
“Oh God!I forgot fa!wayar tawa ban yi recharging ba!akwai kud’i a wayarki?Yadira ta fita kuma ban san password d’inta ba….”
Yusra ta fad’i hakan ta na mai mik’ewa ta k’arasa kan Manubiya ta tsaya tana jira ta bata wayar.
Siyama har za ta ce ga tata nan a kira dan kamar ta fahimci akwai wani abun, sai kuma ta tuna babu kud’i a wayarta dan haka ta fara k’ok’arin cin bashi da sauri dan a samu a kira Mommyn da wayartata amma sai ta ji Manu tana cewa”Eh akwai gashi”kafin Siyama tace wani abun har ta danna password d’inta ta bud’e ta mik’awa Yusran wayartata, ita kuma ta sa hannu ta karb’a tana cewa”Bara in saka miki sabuwar number tata in yi saving,ai ta dad’e da daina amfani da wachchar….
Zuciyar Manubiya d’aya, dan ba ta yi tunanin akwai abunda Yusran za ta iya yi daga karb’ar wayarta da making call ba..cikin jinjina kai tace”tabbas kam dan ko na kirata wani zubin ta shiga ba ta d’auka ba, wani zubin kuma ba ta shiga.”
“Yeah a saloon aka sace, ita kuma ba ta samu ta yi welcome back ba har yanzu”
Ta fad’i hakan tana kwafe number da ta ga anyi ta kiran Manubiyan da ita a jiya ba ta d’auka ba dan gashi ta ga time ɗin da adadin calls ɗin sannan ta ga 090 kamar yadda Yadira ta fad’a, dan haka ba ta da tantama itace ta gayen.
Sai da ta gama kwafewa ta adana a wayarta tukunna ta yi copying sabuwar number Mommyn daga wayartata ta loda a wayar Manubiya ta danna call ta mik’a mata tana murmushi.
“Lucky morning!na ga password na kwafe number.”
Yusra ta fad’i hakan a cikin ranta.Kafin ta juya ta wuce ta koma wajen zamanta ta zauna.
Da kulawa suka gaisa da Mommy har da Baba larai,suka tambayeta ya jikinta tace “Alhamdulillah”daga haka suka yi sallama dai-dai nan Yadira ta shigo mata da abinci.Babu yadda ba su yi da ita ba amma ta k’i ci, Siyama ma ta ji dad’in k’in cin da ta yi dan itace ma ta fara yi mata signal da ido saboda yadda suka dage ya sa suka fahimci in ba da kyar ba sun mata abu a cikin abincin ne…shiyasa ta k’i yarda ta ci iyakaci ta d’auki ruwanta na bohole da ta d’ura a gora jiya wanda taga har ya yi k’ank’ara k’ank’ara ta bud’e ta yi bismillah ta kai baki..kalar ruwan bai chanja mata ba hakama taste d’in shiyasa hankali kwance ta sha sosai ta ajjiye tana sauk’e ajiyar zuciya…
Murmushi Yusra ta yi a ranta tace”in kin san wata ai ba ki san wata ba!”.
Ba su fi minti ashirin da zama ba, Inna ta kira Manubiya ta sanar mata halin da ake ciki tace”nan da 11 za a d’aura aure”
Daga Manubiya har Siyama duk kuka suka saka…gashi sunata kiran Jidda ta ma k’i d’agawa.
Sama Manubiya ta je ta sanar da Yash halin da ake ciki dan haka ya mik’e yace “bara ya shirya sai su tafi”
shima duk hankalinsa a tashe.Ba yadda ba ta yi da shi ya tsaya ya karya ba amma ya k’i yarda yace”su je da wuri kawai ba su da ishashshen lokaci, ya san idan ya yi wa Baba magana inshaaAllah zai d’aga k’afa”
A gaggauce ya yi wanka ya shirya cikin wata had’add’iyar b’akar jallabiya daga nan suka d’auki hanyar gandun albasa gaba d’ayansu har Yusra da Yadira.
A mota Yusra ta yi chatting Yassira ta tura mata har da number Abbakar…Ya’isha Yasirar ta kira ta tsara mata komai yadda za ta yi kafin tace”idan ya k’i yarda ta kira ta za ta san abun yi”.
A b’akin gate d’in gidan suka tarar da Baba Ya Nafi’u da kaka mallan da wasu mutane su uku.Da mamaki su Ya’isha suka shiga kallon juna ita da Yusra dan basu san sun chanja gida ba kuma za su iya dafa Al’Qurani akan cewa Yashjub ne ya basu gidan!tabb!aikuwa yanzu ba sai anjima ba za su gayawa su Mommy, dama sun san irin haka ce za ta yi ta faruwa,gashi kuwa har an fara….
Suna wannan tunanin suka k’arasa suka gaida su Baba, daga haka ya Nafi’u ya ce bari ya bud’e musu gate su shiga da motar amma sai Yash yace ya barshi bari ya bar motar tasa a waje kawai.
Shi ya bud’ewa su Manu k’aramar k’ofa suka shige ciki daganan suka juya wajen su Baba da shi da Yash.
Manya manyan flat house ne guda biyu iri d’aya gate d’insu da compound d’aya, ko wanne yana d’auke da 4 bedroom da 2 parlours da kitchen da dining area,ga babban tsakar gidan da ya ji interlock wanda atleast sai a gina irin gidajen uku a cikinsa.Har da d’akin mai gadi a kusa da gate d’in.
Ba kad’an ba gidan ya burge su Manubiya tashin hankalin da suke a ciki ne ya sa ba su tsaya santin gidan ba suka afka b’angaren da suka ga k’ofarsa a bud’e.
A chan waje kuwa sai da Yash ya tsaya tukunna ya fahimci limaman masallacin area d’in ne Baba yake tare da su…
Sai da suka gama suka yi sallama suka wuce tukunna Yash ya yunk’ura da kwarin guiwa zai lallab’a Baba amma instead sai Baban ya rigasa ya shiga had’a sa da Allah yana neman alfarmar indai ya d’aukesa a matsayin uba kuma yana ganin girmansa to kawai ya bar maganar ya yi wa su Jidda addu’ar samun zaman lafiya.
Sai da Baba ya tabbata ya d’aure Yash da jijiyoyin jikinsa tukunna ya barshi jiki a sanyaye…..
Tun daga nesa da ya taho!
Ya Nafi’u ya fara murmushi, dan ba kad’an ba ya ji dad’i a cikin ransa matuk’a!
Dama d’azu da sassafe da ya je ya yi masa magana a take ya yi masa alk’awarin ‘inshaaAllah zai zo,’
kuma dama tun a d’azun ya lura wannan karon ya Musbah ya ji fad’an da ya yi masa sosai, shiyasa tun a lokacin ya ji sanyi da dad’i a ransa dukda kuwa uwar ramar da ya ga
Abokin nasa ya yi.
Sai da ya gama parking mashin d’insa tukunna Baba ya lura da shi ya gane sa…..k’uraaa masa ido ya yi gaba d’aya tashi d’aya sai tausayinsa ya lullub’esa, dan ana ganinsa an san yana cikin matsananciyar damuwa.
A hankali Baba yake jin duk wani takaicin Ya Musbah da ya k’unsa yana warwarewa sakamokon fahimtar da ya yi tabbas ba yin kansa bane kuma shi kansa ba ya jin dad’in abunda yake yi d’in, dan gashi gaishe da shi yake yi amma sam ya kasa kallon cikin idanunsa kamar ma kuka yake son yi.
Ahankali ya had’iye wani k’ululun abu da ya tokare masa mak’oshi yace”Alhamdulillah Musbahu”still yana kallonsa yana karantarsa.