← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 152

Sashe 131

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matar ce ta bawa Gwaggo Suwaiban addu’o’i, kuma ta ce ta dage da Azkar da sallolin dare..Aikuwa da taimakon Ubangiji cikin ikonsa yanzu Mijinnata har islamiyya ya barta ta shiga, sannan yanzu kam ana iya zuwa wajenta kuma wannan tsangwama ta kyarar duk babu, ba shi ma da lafiya ya kwanta jinya….
Ko da ta tambayesa zata zo ta ga Inna an yi auren su Jidda duk ba ta zo ba! Nan ma sam bai yi yunk’urin hanaawa ba, dukda ba ya so amma shi kansa ya san yanzu kam surk’ullensa sun daina tasiri a kanta…hakanan ta taho kano ita da d’aya daga cikin y’ar mak’oftan nasu mai suna Hadiza bafulatanar Yarinya mai shekaru 17 kyakkyawar gaske siririya doguwa fara sol gashi har gadon baya.
Tunda suka zo da Ya Musbah ya kyalla ido ya ga Hadiza itama ta gansa suka kamu da k’aunar juna, abun kamar had’in baki.
Satinsu biyu ya ga dai ba zai iya daurewa ba ya amayar da abunda ke zuciyarsa itama kuwa Hadiza ko irin d’an jan ajin nan na mata da kunyar fulani gagara kwatantawa ta yi tashi d’aya tace masa ‘Yes!!’

Dama su Inna sun fahimci take takensu, ai kuwa Yarinyar tana gayawa Gwaggo Suwaiba suka hau murna, itama kuma Inna Ya Musbah ya gaya mata, ba kad’an ba Inna ta ji dad’in had’in shiyasa Murna ta zame mata biyu, ga farin cikin ganin y’ar uwarta ga kuma farin cikin had’in Hadiza da Ya Musbah da Ubangiji ya had’a!
Hausawa sun ce ba ‘a yabon d’an kuturu sai ya shekara da yatsu amma tabbas ita kam za ta yabi Hadiza saboda Yarinyar tana da hankali, ga ilimin addini, ga son mutane da girmama na gaba da ita,sannan gwaggwo Suwaiba ma da suka yi watanni goma sha uku tare da su ta bada kyakkyawar shaida a kanta, kuma itama ta ji dad’in had’in matuk’a.

Dama su Inna so suka yi a b’oye abun sai an saka rana komai ya kankama tukunna a fito da maganar, ba dan komai ba sai dan saboda Baraka…
amma Allah da ikonsa tun kafin kowa ya ji ma ita Barakar ce ta fara ji kamar wata mai duba…aikuwa nan da nan ta kunno masa wutar bala’i ta koina, ba ta tashi masifar ta sai dare ya yi idan ya zo bacci, nan za ta hanasa bacci sai dai su kwana idanunsu biyu..amma har gobe shi nuna mata ma yake yi bai san a kan me take bala’in nata ba!!!shi inama ya ga lokacin yin wata budurwa???…
Dukda hakan bai sa Baraka ta hak’ura ba, kuma bai sa ta bar Hadizar ta zauna sakayau ba, dan yanzu tun safe har dare a wajen su Inna take wuni! dukda idan ta shiga wajen nasun fuskarta kullum kamar ta shanu sannan hakanan za ta yi tai musu kallon hadarin kaji, amma kuma hakanan za ta zauna a tsakiyar su ta na ta yada maganganu a Hadizan har ma da su Inna! ko a jikinta.
kuma zuwa yanzu hakanan ta hana Ya Musbahn keb’ewa da ko Innar ne, wai duk dan gudun kar ya samu lokaci da momment da Hadiza.

Kamar mai gadin sa haka ta koma, ta kafa ta tsare, haka nan za ta yi ta zaman jiransa a side ɗin su Innar…yana dawowa daga aiki kuwa zata fara hamma har sai sun tafi. ko wajen Baba ya je haka za ta yi ta safa da marwa a bakin k’ofar parlourn nasa ta baya har da lab’e, har sai ya fito sun wuce tukunna hankalinta zai kwanta.

Tsabar bala’in da ta sakawa kanta ko girki ba ta iya zama ta yi, ballantana gyaran gida!
koina ya yi datti…gashi ba girki, gida duk tsami kuma a da Baraka kam tanata tsafta gwanin ban sha’awa.

Sai dai kullum idan ta gama gadin nasa suka koma b’angaren su yace mata’ta d’an saka turaren wuta ta kimtsa gidan yana kyankyami’ shi kuma ya fita ya je ya siyo musu gurasa da nama…abunda Baraka ba ta sani ba shine idan ya yi fita siyan gurasa da naman ne yake samun ganin Hadiza, dan sam ba shi ne yake zuwa siyowa ba, almajirin su mai wanki da sharar gidan yake bawa shi kuwa ya dawo ciki ya wuce wajen Hadiza inda suke had’uwa kullum wajen wanke wanke ta baya.
Yana lura da sa idon da Baraka take yi masa, dan ko fitar zai yi sai ta lek’o ta tabbatar ya fita d’in tukunna take komawa ba ta san yana kallonta ba.
A yadda yake son Hadiza ba ya so a samu matsala a aurensu, kuma zuwa yanzu ya fahimci Baraka ta hau Buzu, shiyasa ko su Inna da suke ta cewa ya fad’a mata idan auren ya rage saura sati biyu jin su kawai yake yi, dan sai ya samu kansu tukunna zai nutsu ya zauna ya yi musu bayani sosai..domin shi kam inshaaAllah sai dai kawai Baraka ta ga Hadiza a d’akinsa matsayin matarsa ko kuma ta ji ana d’aura aure.

A b’angaren Baraka kuwa har yau ba ta kama Hadiza da Mijinta ba, amma dai ta san akwai abunda ya ke wakana a tsakaninsu, gashi wayarsa koina password ballantana ta yi masa bincike…Bokan ta ne ya fara sanar mata, yanzu kuma ya sake d’aga mata hankali ta inda yake ce mata ai maganar aure ma ake yi…
dama chan Baraka a cikin masifa take sakamokon yadda komai ya k’i tafiya yadda take so, Ya Musbah ya k’i ya dawo mata kamar da! Sam ta gagara mallakesa kwata-kwata, sannan so take a raba gidan biyu ko a sayar da gidan a sayi wani su rabu da su Inna amma abu ya ci tura!!!
Gashi gaba d’aya ta rasa soyayyarsa kuma ta gagara dawo da hankalinsa gareta, kuma sai yanzu ita kanta ta fahimci masifaffiyar k’aunar da take yiwa mijin nata musamman ma da ta ji zancen maganarsa da wata….shiyasa ta tashi ta tsaya tsayin daka! Ta ƙudiri aniyar ‘wallahi indai ta haifu, to Ba’a isa a yi mata kishiya ba, kuma Inna da take zugasa ta hana ruwa gudu ta toshe mata duk wata hanya wallahi sai ta haukatar da ita, ko kuma ta maida ita kamar yadda take farko ta hanyar kwantar da ita, ta yadda za ta zama da ita da gawa babu maraba!’
saboda Bokan ta yace mata”Inna ce take yin addu’o’i ba dare ba rana, babu ji babu gani, shiyasa komai nata ba ya ci, komai nata yake tab’arb’arewa.”

Yahanasu ma ta yi sabon saurayi mai suna Egnr Doc Kamal sumaila vice governor d’in Kano state…sun had’u da shi ne ta sanadiyyar tsaya musu da ta yi a matsayin mataimakiyar lawyer su na shar’iar da suka yi ta fafatawa yau kusan shekara d’aya kenan akan mulkinsu da aka yi musu almundahna, to yanzu dai Alhamdulillah komai ya daidaita sun hau kan mulki wanda sai a lokacin ne ya fito mata da k’udirinsa!
Ya fi wata d’aya yana binta tana cewa a’a, shi ya d’auka ma ko saboda kasancewarsa babban mutum amma bai tab’a aure bane ya sanya tace masa a’an, sai da ta fito masa ta basa labarinta tukunna ya fahinceta…cikin ikon Allah shima d’in hakan ce ta yi ta faruwa da shi, dan sau hud’u ana samun matsala a batun aurensa (ana fasawa) dan haka yace mata ta yi hak’uri ta daure su bawa alaƙartasu chance inshaaAllah wannan karon daga shi har ita za su dace…
Da kyar da taimakon su Manubiya da ta gayawa suka dinga bata shawarwari aka samu ta amincewa Alhaji kamal, yanzu dai ya zo sau biyu jiya kuma sunzo shi da Abokinsa sun gaida Daddy.

Hatred, tsagwaron tsana da tsantsar takaicin Mommy ne ummul’aba’isin kwanciyar Daddy rashin lafiya, ga kuma damuwa daban-daban, gashi Yashjub ba ya kusa.
Last week Abhi ya zo ya dubasa, sam bai ji dad’in yadda ya ga jikin nasa ba, dan ba don yana da aiki ba ma to da ba zai koma gida ba….
Hankalinsa duk ba a kwance ba, Hakanan ba dan ya so ba ya wuce Uk…tun a jirgi ya kira Yashjub yace”yana son ganinsa a Uk idan ba damuwa.”
Ya san suna waya da video call da Daddyn, amma ya kamata ya je ya gansa gaskiya.

Bayan kwana uku da dawowar Abhi su Manubiya suka zo ita da Yashjub d’in…ta yi fari k’all, ta yi k’iba ta yi fresh ta k’ara kyau abunta amma babu ciki babu alamun sa a tare da ita, wanda hatta su Hajiya mama sai da suka d’an ji d’arr!! Amma kawai sai suka basar, suka ci gaba da murnar ganin juna.

Abhi kam ya ma fi su Hajiya mama damuwa, har ga Allah fa wannan yana daga cikin confidential reasons d’insa(ɓoyayyen dalilinsa) da ya sa ya so ace Yashjub yanada mata biyu ne, ba wai Kausar ba! A’a, bayan ya sake ta(kausar ɗin), ya so ace Yash ɗin ya auri wata saboda ba zai yiu ace Yash ya k’are rayuwarsa a haka ba, duk wannan uban dukiyar ace shege ne kad’ai zai juyata………
“Abhi Ina wuni!”
D’in da Yash ya ce masa ne ya katse masa tunani…

Ahankali ya ke kallonsu shi da Manubiyan, kafin ya d’an yi murmushi ya amsa gaisuwar tasu tukunna ya d’aura da cewa “duk kun yi k’iba kun yi kyau abunku tubarkallah!”
Sunkuyar da Kai Manu ta yi cikin tsananin jin kunya, yayinda Yashjub ya d’an sosa k’eyarsa yana murmushi….

Ciki su Hajiya Mama suka wuce da Manubiya bayan an gama gaishe gaishe..suna wucewa Abhi ya gyara zama ya kalli Yash yace masa
“yaushe za ka je ka dubo mahaifinka??”

Tashi d’aya yanayin fuskar Yash d’in ta chanja, idanunsa suka d’an fara kad’awa.
Sai da Abhi ya sake jeho masa tambayar a karo na biyu, tukunna da kyar ya samu yace”ba rana!”

“Saboda me??”
Abhi ya tambayesa cikin tarar numfashinsa.

Wata nannauyar ajiyar zuciya Yash ya sauk’e kafin yace”Abhi pls, dan girman Allah ka bar maganar kawai.”

Jinjina Kai kawai Abhi ya yi, daga haka ya d’auki waya ya danna kiran Hajiya mama tana d’auka yace
“Mama sai fa kinzo saboda ya k’i gaya mini.”

Runtse idanu Yash ya yi da tafukan hannunsa, kafin ya cika ya d’ago ya kallesa yace”Abhi saboda Kausar ne fa, dan Allah kawai ka bar…”
Chapter 131 · 0% Book details