← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 152

Sashe 114

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin kallon fusata da takaici Junior yake jifansa da shi, ya had’e rai da fuska tamau, kafin da kyar ya janye idanunsa daga kan Yassir d’in ya juyo ya kalli su Daddy yace”bai bayarda exact weeks ba amman a yadda na fahimta da k’irgen da na yi banajin ya fi 12 days gaskiya…”

Ajiyar zuciya Kausar da Yassir suka sauk’e a b’oye, yayinda Daddy ya d’an tafi Luu zai fad’i
Abhi yayi saurin ruk’o sa.

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Ummi tace, sai kuma hawaye,
domin itama tun d’azu da ta lura da yanayin Yashjub wani mugun mugun tausayinsa ya lullub’eta, yanzu kuwa ana fad’a yadda ya mik’e ya nufosu yana tangad’i dole ko waye ya ji tausayinsa….ta san ciwon ɗaukar alhakin abunda baka da masaniya a kai, baka kuma da ikon chanjawa…

Yana zuwa a hankali ya shiga tsakanin Daddy da Junior ya rik’e kafad’un junior yace “Junior tsakanin ka da Allah, cikin nan 2 weeks ne??”

Shiruu Junior yayi, yana ji kamar ya kurma uban ihu…..wani irin tausayin Yashjub da tsanar su Kausar had’i da bak’in ciki mai tafe da tashin hankali ne suka rufar masa a lokaci guda….
Tabbas Yashjub bai chanchanci haka daga garesa ba, amma kuma ya zame masa dole shima ya tsayawa kansa sannan ya kare kansa……
Ahankali ya ji Yashjub d’in yace
“Ba haka bane ba ko?
Cikin ya fi 1 month ma, I’m sure of it.”

Da kyar Junior ya bud’e bakinsa yace “Am
Yashjub…cikin nan bai wuce 12 weeks ba I’m sure of it, dan na gwada yadda ya kamata kuma wannan abun ba ya k’arya sabon shig….”

Wata wawuyar shak’a
Yashjub ya kaiwa Junior cikin tsananin b’acin rai yace
“Ya za ka ce abun nan baya k’arya?k’arfen nasara ne fa!!
k’arya yake yi bashi da tabbas,ba gaskiya ya fad’a ba!!”.
Sai kuma ya juya ya kalli Daddy yace
“Daddy,I’m not responsible
i….”
Shiruuu ya yi ganin yadda gaba d’aya mutanen parlourn suka tsura masa ido…a hankali
ya lumshe idanunsa yana jin
duniyar tana juya masa kafin da kyar ya d’aga k’afarsa kawai ya juya ya fice da mugun sauri…bai tsaya a koina ba sai side d’insa na da dan bai shirya fuskantar Manubiya a haka ba.Yana shiga ya zube a kan kujerar parlourn ya fashe da wani irin kuka kamar k’aramin Yaro.

Yashjub yana fita, Hajiya Mama wadda tunda aka fara maganar kwanakin cikin da taga yadda Yashjub ya yi ta shiga tsananin tashin hankali! tace
“kun dai san
Ina da buk’atar a yi mini bayanin komai ko???
Dan kaina ya d’aure tamau tun d’azu, kuma zuciyata ta k’i yarda da lissafin da kwakwalwata ta yi
Gameda yadda Yashjub ya yi yanzunnan.”
Ta yi maganar tana kallon su Daddy.

Ahankali Mommy wadda ta fara kukan munafurci ta matso kusa da ita tace”kar ki ga
laifin Kausar, kuma kar ki ga laifin Yashju….”
Cikin katseta da tsawa Hajiya mama tace”A’a!!!!
A’a sam ba na son jin wannnan maganar!
Bana son jin maganar k’azamiya Kausar da kamulalle Yashjub a waje d’aya,ba na so!
Tun wuri ma ku nemo wani sharrin ba wannan ba!

Ku fad’a mini gaskiya, in je in samesa in yi masa bayani, dan na san yadda ya yi d’innan da kuma abunda kike shirin fad’a mini dole akwai abuunda kukayi wanda ya sa yake zargin wannan shegen cikin nasa ne!”

Ahankali Daddy wanda yake ji kamar ya fashe da kuka yace
“Hajiya mama mu je sama in yi miki bayani”

Wannan karon zabura Hajiya mama ta yi kafin tace”Au kaima??sharrine fa!kar ka yarda da makirci, sharri da asiri…ba batun wata Kausar da Yashjub
ba ma naso in ji wannan batun,
kawai ku gaya mini gaskiya
Inje in fad’a masa a samu ya bar d’aga hankalinsa a aikin banza..”

Ahankali Abhi ma ya matso yace “Hajiya Mama mu je
mu yi miki bayani, wannan duk b’ata lokaci ne!
Ki tsaya ki ji komai dan Allah….”

Shiruuu ta yi kafin ta juya ta shiga watsawa Kausar wani kallon tsana!…..Hajiya mama ji take inama ace babu zunubi wallahi yau da sai ta kashe Kausar
A nutse za ta shiga kitchen ta d’auko wuk’a ta b’oye a cikin rigarta ba za ta bari kowa ya gani ba, sai ta zo daff da ita tukunna za ta zaro ta lulluma mata….
“Mu je Mama”
Muryar Daddy ta katse mata tunanin da take yi.
Juyawa kawai ta yi ta nufi sama

Sai a sannan su Mommy suka d’aga Kausar suka nufi saman da ita.

Yahanasu da Ummi kuma suka bi bayan Yashjub…sun jima suna knocking kafin ya bud’e yace musu”ba komai kar su damu yana buk’atar hutu!”
Yahanasu za ta sake yin magana yace”plss”kawai.
Dan haka Ummi tace mata “su je, su barshi ya huta d’in.”
Daga haka ta ja Hannunta suka wuce suna masu jin tsananin tausayin Yashjub d’in.

Suna kai ta d’aki Mommy tace
“Kowa ya fita!ta na son za ta yi magana da Kausar.”

Suna fita Kausar d’in ta mik’e tace”Ina buk’atar zan watsa ruwa,jikina ya b’aci da amai.”

Cikin fushi Mommy ta ruk’o ta tace”ba fa ki isa ba
Kausar!!!
Wallahi sai kin gaya mini gaskiyar lamari..dukda kuwa na riga na sani amma inaso in ji daga bakinki”.

Kallonta Kausar d’in ta yi na y’an dakik’u kafin ta fesar da numfashi tace”A cikin ƴan kwanakin da su ka shuɗe bakya ko kulani, fushi kike yi da ni!
Dan haka banga dalilinki na titsiyeni akan sai kin ji ta bakina ba!.
Ai Ina ce haushina kike ji?
Kin gama rayawa kanki abunda zuciyarki ta aiyyana miki a kaina,ko ba haka ba?
To me kuma ya faru yanzu
da kike son jin ta bakina? kawai inaga gara ki ci gaba da yarda da duk abunda zuciyarki ta baki.”
Kausar ta dire aya
cikin tsare ta da idanuwa kafin ta ci gaba da cewa”Besides ai gashi kin ma ce kin riga kin sani, so meyasa kike so ki ji a bakina?ko dai Baki sanin ba?”

Cikin fushi Mommy tace
“Kausar na san ki ciki da waje
na san komai!
bari ki ji in gaya miki abunda ya faru abunda
kuma kika shirya kike so ya tabbata!
…Na san
Magani ko kuma wani abun kika shakawa Yashjub
a ranar da aka ganku tare ke da shi.A wannan ranar abunda ban fahimta ba shine dalilinki na yin hakan gashi na san mun riga mun gama magana a kan zamu san yadda za a yi ki aureshi.
Yanzu kuwa na fahimta
Dama burinki ki samu ciiki
saboda ki aureshi kenan ko?
Bima’ana dai idan na fahimceki da kyau
baki gama yarda da ni da Baba larai ba!shiysa kikaje kikayi gaban kanki!!
Shiyasa kike ta faman b’oye mini ki ka k’i gaya min komai….

Hakane ko ba haka ba??”.

Ajiyar zuciya Kausar ta sauk’e
kafin ta matso kusa da Mommy sosai tace”Mommy
Taabbas na san Yashjub a buge yake a wannan ranar,
Wataƙila daga office ko wani wajen ko asibiti ne aka samu
wata ta so cin galaba a kanshi
Allah bai yi ba ya dawo gida da wuri abun ya fad’a kaina…dan ni dai da hannuna ban shak’awa ko na sakawa Yashjub komai ba.!
Na san kin daina yarda da ni kuma kin daina aminta dani
amman tabbas idan kika yarda da abunda nake fad’a miki yanzu to za ki ji dad’i za kuma ki samu salama saboda hakan ne gaskiya…
‘Ban bawa Yashjub komai ba,
ban zuba masa komai ba,
sannan ba shirina bane in samu ciki da shi wannan tsarin Ubangiji ne.’.
Ko a gaban waye hakan zan fad’a tunda hakan ne gaskiya
Ruwan ki ki yarda
Ruwanki karki yarda..ba damuwa ta baceba!!
kawai dai Ina takaicin cewa
kin daina yarda da ni sannan kin daina so na.”
Tana gama fad’in haka ta juya ta shige toilet da sauri a ranta tace
“komin lalacewa na san Yashjub d’anki ne…ba zan bayarda k’ofa a kowa ba banda Yassir, har sai na ganni a d’akin Yashjub zaune a matsayin Amaryarsa.
Yadda Yashjub ya gigice d’innan tsaf za ki tausaya masa, shi kuma na san in dai ya ji wani abun to ba zai ɗauki matakin da nake shirin d’auka a gaba! Da mahimmanci ba…

Mommy ta dad’e tsaye a dakin
tana tunani, amma kwakwalwarta ta kasa yin lissafin abu mai kyau…da kyar dai ta ja k’afafuwanta ta fita bayan ta yanke shawarar yarda da abunda Kausar d’in ta fad’a mata.

Shiruuu!!!haka gidan ya koma kamar na zaman makoki…daga jigum sai tagumi….sai da Daddy da Abhi suka gama ji da Hajiya mama tukunna Daddy ya kira Junior yace a kuma yin wani test d’in.
Yana fitowa daga wajen Daddy ya nufi d’akin Kausar domin ya d’auki jininta ya wuce office d’insu…
Knocking ya yi bai jira an basa izini ba ya tura k’ofar d’akin nata ya shige…a nan ya tarar da Yasssir.

Yana shiga Yassir d’in ya fara murmushi ya taso ya nufi bakin k’ofar inda Junior ya ja ya tsaya,kamar zai yi
hugging d’inshi haka Yassir d’in ya matso shi yana cewa”Amintaccena! Gwarzonmu..Our savior…”

Daddagewa Junior ya yi ya zuba masa naushi yana huci.
D’agowa Yassir ya yi yana dariya ga jini yana zuba daga hancinsa dan ya fasa mishi hanci,yana murmushin yace”My pleasure!”

Tsaki Junior yayi, bai
damu da ya sake bi ta kan Yassir ba ya k’arasa ya kamo hannun Kausar ya d’auko sirinji

Cikin rashin fahimta tace “me kuma za ka yi??”
“Test zan kuma yi”
Kawai yace mata
dan ya tsaneta.

Matsowa Yassir ya yi yace
“Ki barshi ya d’auka,ba komai ai.Kawai dai ka tabbatar ka sake kawo result d’in 12 days!
Besides me yasa ma kake buƙatar jinin natat?Tunda dai ka riga ka san k’arya za ka sake rubutowa, ka kawo??”
Ya fad’i hakan yana mai dafa kafad’arshi.

Juyowa Junior yayi ya zuba mishi ido fuskar nan tamau!!
kafin ya tunkud’e hannun Yassir d’in.
Ya riga ya gama d’aukar jinin, dan haka ya tartara komai ya fara k’ok’arin juyawa.

“Oh no!
Haba Junior
Da ni da kai amintattun juna ne fa!
Ba zan iya jurar wannan attitude ɗin(kyaliyar) daga bestiena ba.
Chapter 114 · 0% Book details