← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 152

Sashe 10

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi d’aya ya fahimci na mene ne, sai kuma d’ayan takardun mota ne, motar da ya dad’e yana ta yi wa Yash d’in nacin ya siya masa…

Ajiyar zuciya ya sauk’e bayan ya gama duddubawa, kafin
ya ajjiye takardun a gefenshi ya d’ago ya kalleshi ya ce ‘’What’s the catch?(ina gizo ke saƙar?)”

Dukda dama Yashjub bai yi tsammanin Yassir ya huce da wuri ba amman
sam bai ji dad’in yadda ya yi ɗin ba, dan ko d’igon murna bai gani a fuskar Yassir ba.
Kud’in da ya kashe ya siyi motar ba wani abu bane a wajenshi, amma wahalar da yasha wajen registering da had’a mishi company d’in nan
ba kad’an bace.
Ganin ransa yana shirin b’aci ne ya sanya yayi saurin cewa ‘’Auzubillahi’’a cikin ranshi,
sannan ya fesar da iska ya
mayar da hankalinshi ga Yassir wanda ya tsareshi da dara-daran idanuwanshi tun d’azu, cikin sigar rarrashi ya ce
‘’Na yi kuskure Yassir, sorry,
amman fa dukda haka ka nisanci Yarinyar nan (Munirat), saboda ka ga ko ta fannin Daddy in muka ɗauka yanzu haka ya na zargin ita take kai kanta gareka ne, kar ka
shiga tsakaninsu dan in ka yi hakan abun ba zai yi musu kyau ba. Idan kuma ka san son ta kakeyi tsakani da Allah
to ka yi magana a aura maka ita.

Yassir, muna da Yarinya mai shekaru 17 a gida, inda ace ita ta ga abunda ni na gani ranar a kai da Munirat mai kake tunani?..

Anyways, ya riga ya wuce, ka yi
laifi dan Allah ka gyara, nima kuma na yi laifi
I’m sorry.

Company d’in na yi maka ne saboda inaso inga kaima ka tsaya da k’afafunka…dan dukda kana b’oyewa amma na riga na san abunda yake faruwa a
building d’inka..pls Yassir!!
Put all your hard work into this new one
(Ka sanya dukkan ƙoƙari da jajircewarki a wannan sabon).

Ya kamata ka farka, ka fara abunda zai fishsheka.

Sannan motar na siya maka ne
As
Peace offering (a matsayin kyautar neman sulhu)..Ka yi hak’uri akan abunda na yi maka that very day(a wachchar ranar), ya kamata ace naa fahimci ka riga ka girma.’’
Ya k’arashe maganar yana murmushi.

Da kyar Yassir ya samu ya k’ak’alo murmushi ya yafawa fuskarshi tukunna shima ya mike tsaye,

Rungume Yashjub ɗin ya yi kafin ya ce ’’na gode’’

Bubbuga kafaɗan Yassir Yashjub ya yi a hankali, tukunna ya ce ’’We’re good right?(mun shirya ko?)”

‘’Of course we are, (e mna, mun shirya)”
Yassir d’in ya ce daganan ya cika shi ya sake cewa ‘’na gode’’

Murmushi duk sukayi, daga haka suka had’a y’an kayan Yashjub….
Yassir ne ya kira wata cleaner ta tayashi kaiwa mota,
Yashjub kuma ya je ya rufe duk wasu bills daganan suka kama hanyar gida.

A motar ma Yashjub hira yayi ta jan Yassir da shi, yana basa
ideas da yadda zai janyo Mutane da yadda abubuwa suke da yadda zai fi mishi sauk’in samun shigowar kuɗaɗe.

A fuska kam ba laifi,
Yassir yayi iyakar bakin k’ok’arin shi dan sam bai bari Yashjub ya yi tunanin komai daga gareshi ba, amman fa a zuciyarsa ji yake kamar ya mutu…..saboda bashi da shi!! Saboda shi talaka ne wato ta kai har Yashjub ya ci mishi mutunci
kuma yake k’ok’arin ci mishi hanci da mota mai tsada.
Sannan shine ma zai nuna mishi yadda zai yi business da ragowar abubuwa wato kenan shi an maida shi ma bai san komai ba!!!!.
Shi ne ya kamata ya zama shi yake rabon kud’i da abubuwan alfarma amman kullum akasin haka ake samu, kullum sai dai Yashjub ya basa ya bawa wasu….
Shakka babu lokaci ya yi da zai kawo ƙarshen hakan!!
Dukda Daddy shine sila,
amman ya fi jin haushin Yash
tunda shike da kud’in yanzu…
Ya tabbatar inda ace Daddy
bai ci mishi fuska ya fifita Yash tun farko sama da shi ba to da tuni haka ba ta faru ba! Da tuni shima yanzu yanada company wanda ya yi nasara har ma da estates kamar Yash………
….
Yasmeen tana isa gida, direct wajen Mommy ta nufa, tsabar
rashin tunani da tsananin son Kai su fa ala dole sai dai a tarwatsa maganar auren gaba d’ayanta kuma a yi musu farrak’u(Yash da Manu).

Tana zuwa ta zayyanewa Mommy yadda Yash ya
shanyata a bakin k’ofa tanata uban bugu! Bayan ya bud’e kuma ya disga ta, ya hanata shiga inda yake, bayan ya san Manubiya tana ciki kuma tana ji sannan tana ganin komai, sannan da k’annen Manubiyan suka zo ya mutunta su ya amsa gaisuwar su da kulawa, ita kuma aka barta a tsaye a bakin k’ofa, su suka shige ciki.

Kamar za ta fashe da kuka ta d’aura da cewa ‘’Mommy kinga yadda Yarinyar take kallon mutane kuwa, ‘akan hanci’ mun had’a ido da ita amma ko gaishe ni bata yi ba……

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 06*

Kamar za ta fashe da kuka ta d’aura da cewa ‘’Mommy kinga yadda Yarinyar take kallon mutane kuwa, ‘akan hanci’, mun had’a ido da ita amma ko gaishe ni bata yi ba, k’annenta ne kawai suka gaishe ni, amman ita d’auke Kai ta yi ta sake tamke fuska’’

Yusra da suke tunanin Yarinya ce itanma yau kam ta bi bayansu….dan a lokacin da Yasmeen ɗin ta shigo itama Yusran tana d’akin Mommyn, a tare ta gansu tana taya ta gyaran wardrobe…sosai itama Yusra ta taya Yasmeen zuga Mommy..
Dama chan ba son auren suke yi ba, yanzu kuwa ganin Manubiya da kuma abunda Yasmeen d’in take ik’irarin an yi mata shi ya sake tunzura su Yasmeen d’in, a cewarsu ’sam ba zai yiu su bari Yash ya auro wata chan daban ba, gashi tun yanzu k’annenta sun fi su daraja da mutunci a idanun Yash, ba ma ita ba. Dama irin abunda suke gujewa kenan, ga shi kuwa an fara tun yanzu,…’
Dan in ba hakan ba fisabilillahi ta ya zai shanya
Yasmeen a waje ya hanata shiga, sannan ya dinga wani ririta k’annen wata chan daban wai ita budurwarsa!.
Sam bai ma nuna musu wacece Yasmeen d’in ba
ballantana su girmamata.

Dan haka a gaskiya ba zai yiu su bari Manubiya ta rayu da Yash ba,
tunda ya fara haka to akwai babbar matsala a gaba, gara kawai a tarwatsa wannan auren a had’a shi da Kausar tunda itace tasu, ta hakan ne kuma za su zama d’aya kansu ya had’u da d’an uwansu.’

Ita Yasmeen wani sabon abunda ya sake d’aga mata
hankalin ma shine ‘Yarinyar y’ar gidan talakawa ce’
Saboda yanayin abayoyin Jidda da Siyama da hijabin jikin Manubiyan kad’ai sun isa su sanya mutum ya fahimci talakawa ne…
Shiyasa in dai suka barsu tare to fa Shikenan ta san akanta zai k’are ita da dangin ta! Dan yadda yake ta uban rawar k’afar nan ta san bud’e musu bakin aljihu zai yi! ya yi ta b’arin kud’i, su tatike komai, komai ya koma wajenta!!
ita kuma ita da su Mommy a ajjiyesu a gefe, dan ta lura Yarinyar bata da kunya sam kuma bata da mutunci, dan haka tashi d’aya za ta raba shi da su.

Haka nan dai kamar za su haɗiyi harshe Yusra da Yasmeen suka yi ta mita su biyu,
dan sam Mommy ta ma kasa magana saboda ita duk ba wannan ne abunda ya fi d’aga mata hankalin ba! Dan ta san ta riga ta gama tsarawa ‘indai ta haifu cikin uwarta da ubanta!
to Manubiya ba ta isa ta auri Yash ta shigo mata cikin family d’inta ba wallahi,’
dan ko hauka take yi ba zata tab’a bari Yash ya auri Yarinyar da take tafe da downfall d’in ta ba, saboda Baaba Larai ta ce ‘’indai har Manubiya ta kasance a tare da Yash to ba za ta (mommyn) taɓa cimma burinta ba sannan duk wasu sirrinkanta na sama da shekaru talatin ma da y’an kai sai sun bankad’a a fili kowa ya ji ya gani, kuma sai ta shiga masifar da bata tab’a tunani ba’’.

sannan bayaga haka indai tana raye to Yashjub bai Isa ya auri wata mace idan ba Kausar ba, saboda ta san duk fad’in duniyar nan Kausar d’in ce kawai za ta iya yi mata yadda take so.

Shiyasa ta tsaya tsayin daka take ta fafutukar ganin ta yi ko ma menene ya kamata muddin za ta samu ta hana auren Yash da Yarinyar nan, dan ba ta da guri a cikin family d’inta. Sai dai kuma idanunta da suka rufe akan hana auren shi kaɗai sai ya kaita ga kasa yin tunani mai zurfi, dan kamata ya yi ace ta raba shi da ita har abada, tun a karon farko, ba wai iyaka auren ba tunda ko babu aure indai har suna tare to akwai matsala…
gashi kuwa yanzu Yasmeen ta zo mata da wani zance na sabon tashin hankali wanda zancen ne ya sanya ta fahimci tabbas ta yi tuya ta manta da albasa…
dan ba k’aramin tashi Hankalinta ya yi ba da ta ji
Yasmeen ta ce ’Yash ya shanyata a waje sama da mintuna talatin, tana ta knocking, sun ƙi su bud’e mata da shi da Yarinyar’….
A yadda Yash yake da kud’in nan, ta san ba ko wacce irin Mace ba ce zai nuna yana buk’ata ta k’i amincewa da shi, ballantana Yarinyar da ta riga ta san ita zai aura nan da kwanakin da ba su fi goma ba.
Karfa ta je tanata k’ok’arin hana d’aurin Aure aje Yarinya
ta samu ciki kafin ma ta shigo cikin gidan, dan indai ta riga ta samu ciki to komai ya zo musu k’arshe kenan, dan ta zamewa Yash k’arfen k’afa kenan.

‘’Mommy!’’
Ɗin da Yasmeen ta ce mata ne ya katse mata tunani, fir-gi-git! Ta yi, sai kuma ta kallesu, ta ga gaba d’aya su biyun ransu a b’ace, hankalinsu a tashe!!

Yasmeen ta bud’e Baki za ta yi magana kenan Mommy ta katseta ta hanyar ce mata ‘’Tashi ki je ki kira min Baaba Larai, Yusra kema bita ku
turo min ita’’

Wani sanyi Yasmeen ta ji a ranta, dan haka ta mik’e ta fice da sauri, Yusra ma ta bi bayanta.
Chapter 10 · 0% Book details