Sashe 15
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e bayan ya ga shigewar tasu, kafin ya furzar da iska a hankali ya lumshe idanuwansa.
…..
Washegari da Asubah, misalin 4:00am, Daddy da Abhi suka nufi airport domin d’auko su Hajiya Mama.
5:00am dai-dai jirginsu ya yi landing (ya sauƙa) a garin Kano…
Suna tsaye suna jiransu,
Daddy ya hango Junior ya karyo kwana..
Murmushi Daddyn ya yi
kafin ya ce ’’Wai!!Tubarkallah!
Ai ban ga
chanjin a hotuna da video calls ba kamar yanzu a fili’’.
Da sauri Abhi ya d’ago shima ya kalli direction d’in da ya ga Daddy ya na kallo yana tsananin murmushi…..
Dogon saurayine wanda a k’alla zai kai kimanin shekaru 27 a duniy, kalar
fatarsa bak’i ne, irin mai shek’i da kyau d’in nan. Ba shi da muni kuma ba za a kirashi da kyakkyawa ba. Yana da fad’in k’ashi sannan jikinshi a murd’e yake wanda tun a kallo ɗaya ake iya fahimtar ya saba da ziyartar gym.
Sanye yake da dogon wando pencil bak’i irin na maza, sai bak’in takalmi sauciki, da farar riga mai gajeran Hannu me kama jiki an rubuta ‘lucky trip’ a jikin gaban rigar,
yayinda Kanshi yake sanye cikin hula irin ta sanyi bak’a itama ya d’an tura ta baya kad’an, sai jakarsa bag pack da ya goya da trolly…
Daddy yana cikin k’are mishi kallo ya k’araso daff dashi,
Yana zuwa ya sa Hannu ya rungume Daddyn sannan ya ce
’’I miss u Daddy.”
Murmushi Daddy ya yi ya d’agosa yana mai sake k’are masa kallo kafin yace “Imam ya gida, ya uk, ya aiki??’’
Murmushi yayi ya ce ’’Alhamdulillah,
Ina wuni’’
Cikin katsesu Abhi ya ce ‘‘Ina Hajiya Mama?’’
Dariya Junior ya yi kafin ya ce
‘’Suna chan tana karb’ar number wata Mata…
wai Matar ta ce mata tana Maganin mayu da asiri, shine ta tsaya karb’ar numberta saboda tana so za ta yi inviting nata gidan a yi maka feshi da ruwan addu’a.’’
Ya ƙarasa faɗin hakan yana kallon Daddy yana dariya.
Shiruuu duk su ka yi kafin Daddy ya ce ‘’Allah ya kyauta’’
Dai-dai nan wasu Mata guda biyu suka tunkaro su, d’ayar ba za ta kai shekaru hamsin ba..bak’a doguwa, sanye cikin doguwar rigar abaya ta rufa
mayafinta.
Sai d’ayar Matar kuma wacce a k’alla za ta kai shekaru 70 a duniya…fara ce k’all sannan doguwa ce sosai amman bata da jiki, kyakkyawace sosai dukda ta tsufa amma hakan bai b’oye kyawunta ba, tana
sanye da laffaya blue black
Idanunta kuma sanye cikin farin glashi.
Magana suke yi k’asa-k’asa itada d’ayar Matar wanda kana gani ka san sirri ne akeyi shiyasa har ba su ma lura da su Daddy waenda suka nufesu ba, dan sai da suka k’arasa daff da su tukunna suka lura da su.
Har k’asa su Daddy suka durk’usa suka gaida ita, da kyar ta iya cewa ’’lafiya Alhamdulillah’’
Idanunta suna masu ciccikowa da hawaye tun lokacin da ta kalli Daddy, kafin a hankali ta d’an rissina ta d’agosa tsaye.
A hankali take kallon shi tana me shafa gefen fuskarshi kamar wani Yaro tana jin tsananin tausayin sa yana sake ratsata.
Murmushi yayi yana mai kallon Mahaifiyar tasa kafin ya kama Hannunta wanda ke a gefen fuskarshi ya rik’e a hankali ya ce ‘’ya hanya?’’
‘’Lafiya’’
kawai tace still idanunta suna a kansa kafin
daga bisani da kyar ta kauda idanunta ta maida kan Abhi ta ce ‘’Hankalina bai kwanta ba sam, shiyasa nake ta jera addu’o’i tunda muka taho.
Yanzu haka ma a jirgi yi nake ta yi,
da ikon Allah kuwa sai na ji Matar bayana suna magana da ta gefenta, daga yanayin conversation d’insu (hirar tasu) na fahimci maganar tasu, shiyasa da aka fito na tsaida ita, shine
take ce min
‘Dad d’inta babban malamine, kuma da ya zo rasuwa ita ya barwa malintar’
shine fa na tsaya na karb’i numberta, to cut it short dai (a taƙaice dai) na bata adress za ta zo ta yi feshi
gaba d’aya gidan da ruwan addu’o’i’’
Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e
Abhi kuma ya sunkuya da kanshi k’asa saboda a da yana ganin rashin kyautawa da rashin gaskiyar Hajiya Mama amman shima yanzu gaskiya ya d’an fara bin bayanta…
A hankali Daddy ya ce ’’Mama pls mana, Matar da ba ki gama saniba itac……’’
Wani kallo Hajiya Mama ta yi mishi wanda yasanya shi had’iye ragowar maganganun nashi, ba ta sake bi ta kansa ba ta juya ta kalli Abhi ta ce ’’take me to the car”.
‘’Right away’’Abhi ya ce da sauri, daganan suka nufi inda Junior yake tsaye gaba d’ayansu har wad’anda suka
turo akwatunan su Hajiya Mama.
Suna zuwa Junior shima ya bisu duk suka d’unguma zuwa wajen motocin da aka taho da su.
Ana kiran sallah suka isa gidan, dai-dai Yashjub ya fito kenan zai tafi masallaci, sai da aka yiyyi murna da oyoyo tukunna su Hajiya Mama suka shige ciki bayan Daddy ya kira gwaggwo ya ce mata “ta nuna musu inda aka gyara musu’’
Junior ma da wucewa zai yi, sai da Daddy yayi mishi da gaske tukunna ya yarda ya bi su masallacin
a cewarshi wai ’’ya gaji bacci yake ji.’’
Ana idarwa kuwa ya ce a nuna mishi inda Yassir ba ya nan,
dan ya san indai suka had’u to
ba zai yi baccin ba.
Side d’in Yashjub suka nuna mishi, daganan Daddy suka nufi sama side d’insa dan akwai maganar da suke so su yi both akan business da kuma family issue.
Sai around 7:00am,
Tukunna y’an gidan suka shirya kowa ya fara shirin sauk’a k’asa domin yin breakfast.
Sai da numfashin Mommy ya yi sama! A lokacin da ta fito, dan ta na fitowa suka yi ido biyu da mom, ta san kuma indai ta ga mom tou kamar ta ga Hajiya Mama ne.
Murmushi ta k’ak’alo da kyar, tukunna ta k’arasa inda mom din take tsaye jikin k’ofa.
A hankali tace’’Sameeha,
sauk’ar yaushe?’’
Murmushi mom ta yi bayan ta juyo tukunna ta ce ’’Khadija ykk, ya gida? Ba mu dad’e da zuwa ba’’
Dai-dai nan Hajiya Mama ta fito daga d’akin inda mom ta rik’e mata k’ofa, tana fitowa suka yi ido biyu da Mommy dan haka ahankali a fili ta ce “A’uxubillahi
Bismillah’’
Sunkuyar da Kai Mommy ta yi
kafin ta ce ‘’ina kwana Mama,
sannu da zuwa’’
Banza Hajiya Mama ta yi da ita
dan haka Mommy ta sauk’e numfashi kafin ta durk’usa sosai har k’asa tukunna ta ce
‘’Ina kwana mama’’
‘’Ashe dai kinada tarbiyya kad’an’’
cewar Hajiya Mama ba tare da ta kalle ta ko ta amsa gaisuwar tata ba.
Dai-dai nan Yassira ta fito, sanye cikin skirt da suite,
sai d’an mini hijab iya kafad’arta, yanayin tsayuwar tasu kawai ta gani ta fahimci har an fara, da farko ba ta yi niyyar zuwa inda suke ba sai
kuma suka had’a ido da Hajiya Mama dan haka kawai sai ta dake ta k’arasa inda suke, tana zuwa rungume Hajiya Maman kafin a hankali ta ce ’’welcome, we are glad u make it(sannu da zuwa? Mun yi farin cikin isowarki lafiya)”
D’an guntun murmushi tsohuwar ta yi kafin ta ce ’’ya aiki?’’
‘’Alhamdulillah’’
Yassira tace,
Sannan ta cika Hajiya Mama ta kalli mom tace ‘’Sannan ku da zuwa, i’m late muna da baƙi kuma, bari in yi sauri in wuce, we’ll
catch up later(za mu haɗu anjima)”
Tana gama fad’in haka ta wuce .
Ganin suna shirin wucewa suma kamar ma sun manta da ita ne ya sanya Mommyn ta ce ’’bara in yi sauri in d’an had’a muku special, ba ku ce za ku zo yau ba ai da an had’a muku special ɗin tun wuri’’
‘’Eh ni na cewa d’an albarkar kar ya gaya miki ai, gudun kar ki hana, ki bar abincinki zan ci na masu aiki’’.
Cewar Hajiya Mama.
Baki Mommy ta bud’e, za ta yi magana
su Abhi waenda suka fito yanzu suka k’araso, Abhi ya ce ‘’Mommy mu je gaba d’aya mana’’
Sai da ta juya za ta yi
mishi magana tukunna ta lura da su Yasmeen….shi kanshi Abhi d’in ta san ya zo amman bata ganshi ba sai yau dan haka ta ce ’’duk sannun ku da zuwa”
daganan ta miƙe ta juya ta nufi d’akinta dan ba ta jin za ta iya had’iyar ko da ruwa ne a yau kam.
Sai da Daddy ya yi wa su Yasmeen wani irin kallo, tukunna suka matsa kusa da Hajiya Mama suka gaida ita
Itada Ya’isha, dan Yusra da Yadira ba su tashi ba tunda ba fita za su yi ba!
Yusra ta gama finals d’in ta,
Yadira kuma sun fara hutu.
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 09*
Ba yabo ba fallasa ta amsa musu, daga nan aka sauk’a aka nufi dining table.
Ko zama
Daddy bai yi ba ya shiga kitchen dan ya san Ummi tana ciki, ai kuwa yana shiga da ita ya fara yin tozali ita da Munirat da masu aiki…a gaban mutane ne shiyasa Ummi ta d’an gaida Daddy da kulawa ba yabo ba fallasa amma fa dukda hakan a baɗini ji takeyi kamar ta je ta shak’e sa! Dan ita kanta tana mamakin yadda haka kurum tsanarsa ta nunku ta ke sake yin ninƙaya a cikin zuciyarta kwana biyun nan, wani irin mugun haushinshi takeji.
Amsawa ya yi yana mai binta da kallo, dan ba kad’an ba ta yi masa kyau yau d’in sosai, dad’in dad’awa yana son Matarshi kuma ya yi missing d’inta ‘’Daddy Ina kwana’’ d’in da Munirat ta ce masa ne ya dawo da shi cikin kitchen d’in.
A hankali ya juya ya kalleta tukunna ya amsa da kulawa, kafin ya maida dubanshi ga Ummi ya ce ’’Hajiya Mama sun zo, tare da d’an uwana da Matarsa, ki fito ku gaisa’’
Tukunna ya shiga amsa gaisuwar masu aikin.
Murmushi ta yi tana mai jin wani tsananin farin ciki yana lullub’eta dan suna waya da hajiya mama, kuma suna shiri sosai, shiyasa ko gama abunda take yi ba tai ba haka ta cika ta kira gwaggwo ta bata ta ce ta ƙarasa daga nan ita ta fita, ita da Munirat, da murna kwance akan fuskarta.