← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 152

Sashe 13

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Yaa Musbah ne suka tartare
Pepper chicken da su cake da doughnuts da lemukan da ya Nafi’u ya kashe uban kuɗaɗe ya yi order, dan a cewarshi bai kamata a ji kunya ta ko wanne b’angare ba, ya san ba za su yi
abunda ya kamata ace sun yi wa mutane masu uban arzik’i kamar su Daddy ba amma koma yaya dai ya kamata su kamanta.

Har mota suka kai musu suka jibge, Daddy ya na ta faman saka musu albarka da shi da Abokin shi, daga nan suka yi musu sallama suka shiga motocin su suka wuce, suka bar su Baba suna mamamakin Yassir!
Ko da ya shigo fa sune
suka gaida shi, tunda ya zauna a cikin masallacin bai ce komai ba hakanan ya had’e fuska yana kallon mutane akan hanci, ko irin murmushin nan bai yi ba lokacin da Daddy ya gabatar da shi a matsayin d’an uwan Yashjub wanda yake bi masa,
daga k’arshe ma tashi ya yi ya fice gaba d’aya, yanzun ma da suke yi masa sallama bai ko kalli inda suke ba ballanta su sa ran zai amsa,
Har Hannu Kaka Mallan ya mik’a masa amman ya wuce da sauri ya shige motarshi…..addu’arsu d’aya itace
‘Allah dai ya sa ragowar y’an uwan Yashjub ba haka suke ba’
dan yanayin Yassir da yadda sam Daddy ya kasa tsawatar mishi ko da da ido ne ya ba su mamaki ya tab’asu matuk’a.
Daddy dai shi ba shi da matsala, amma sun lura hatta k’aninsa (Abhi) bai yi wani farin ciki da wannan hadi’in ba…

Gudun kar ma su kawo wani tunanin su je su janyo wani mugun abun da Bakinsu ne ya sanya gaba d’ayansu su ukun sukayi shiru kawai, ba wanda ya kawo zancen rashin da’ar Yassir, kowa ya rik’e abun a cikin ranshi kawai.

Su biyu suka tartare
masallacin, suka kunna turare,
daganan Ya Nafi’u ya d’auki jakar kud’in dama shi su Baba suka cewa ya k’arba tun lokacin da Abokin Daddy ya mik’o.

Da sauri Kaka Mallan ya ce ‘’yanzu menene abun yi?’’
bai jira an bashi amsa ba ya d’aura da cewa
“ku kawo kud’in, akwai
wani Abokina da d’ansa yake kayan d’aki na gani na fad’a, kunga sai a basa ya had’a mata komai, mu samu mu fita kunya, itama Yarinya ta fi k’arfin gori, kar ku biyewa Mahifinsa wai dan ya ce kar a kawo komai, ya zama dole mu yi mata ko dan mu fita kunya.’’

Da mamaki Ya Nafi’u yake kallonsa, daman tun d’azu ya k’ule da shi sabida yanayin yadda ya dinga abubuwa a gaban su Daddy, gaba d’aya ya basu kunya sai wani zumud’i yake yi…
shiyasa yana shirin ci gaba da magana yanzun Ya Nafi’un ya ce ’’dakata Kaka Mallan,
da kai da wa za ku fita kunya??’’ bai jira jin amsar shi ba ya d’aura da cewa’’Bayaga haka ma me ka ke yi anan ne?’’
Ya faɗa mishi hakan kanshi tsaye, dan wasu mutanen in ba a ajjiye kunya da kara a gefe an yi musu wuta wuta ba! Tabbas sai su kassara mutum cikin sauƙi.

Da sauri Baba Habu ya juya
ya fice gaba d’aya daga cikin masallacin

Cikin takaici Ya Nafi’u ya ɗaura da cewa
‘’Ba Kai ne ka ce ba zaka zo ba jiya?ina har hantarar mu ka yi da muka je gaya maka?’’

Cikin fushi Kaka Mallan ya ce
‘’Ka ci ubanka Nafi’u! Ashe baka da hankali ban sani ba?
Banza d’an
karere kawai’’

Da sauri ya Musbah ya ce
‘’A’a kaka Mallan Nafi’u kam ba d’an karere bane a wannan lamari, a ko wanne lamari ma na rayuwarmu Nafi’u ba d’an karere bane, dan ya yi mana uwa ya yi mana uba’’

Salati Kaka Mallan ya rafka kafin ya ce ‘’Musa kana ji abunda suke yi min ba za ka
ce komai ba?’’
Sai kuma ya fashe da kuka daga nan kawai ya juya ya fita
yana cewa ‘’Dama amana nakeso in rik’e, amman tunda bakwaso shikenan, kai Musa ubanka yana chan kabari
amman na san an haska mishi wanna son datse zumuncin da kake k’ok’arin yi’’.

Numfashi Baba ya fesar ya girgiza kai yana msmakin yadda sam kaka mallan
ba shi da lissafi, baya jin
shakkar ya ji kunya ko ya zubar da kanshi indai ta b’angaren abun duniya ne.

Kuma ya tabbata inda gari banza ne Nafi’u ya yi masa haka ya san da sai ya tara musu jama’a ya yi musu tijira, amma da yake ya ga da akwai abu a wajen su shine ya kwantar da Kai har da kuka…
a hankali a fili ya ce ’’Allah ya kyauta’’ yana aiyyanawa a ranshi ‘inshaaAllah zuwa anjima zai je ya yi musu godiya da shi da Baba Habu, Allah ya sa su k’are lafiya.
…
Suna zuwa suka mik’awa Manubiya kud’inta…kasa karb’a ta yi dan tashi d’aya fargaba da kunya suka rufe ta ,daga k’arshe ma sai ta saka musu kuka

Murmushi kawai duk aka yi ana kallonsu ita da Jidda da Siyama da Muhsin da suka shiga taya ta yin kukan.
….
Ƴar tattaunawa aka yi, ta inda ya Nafi’u ya soma da ‘Daddy yace kar azo da komai…
amma dukda haka tunda ga kud’i nan ta samu sai a siya mata gado mai kyau da tsada da shi.
Shi kuma da Ya Musbah da Baba za su siya mata y’an kayan kitchen, dangin su flask sannan za su yi y’ar walima.’

Kowa yayi amannah da hakan banda Manubiya, dan tashi ɗaya sam ta k’i yarda a yi hidima ko wani kayan daki, saboda ko da su Ya Nafi’u ma suka fita cewa
ta yi ’’kud’in a barshi kar a siya mata komai, za ta bawa Baba ya Nafi’u da Ya Musbah jari bayan auren da shi.
‘Dama ta shirya za ta gayawa Yashjub ba za ta zo da komai ba, to kuma yanzu tunda iyayenshi sun buk’aci hakan ai Alhamdulillah’”.

Murmushi Mama ta yi kafin ta matso ta dafa kanta tana jin
tsananin k’aunar Manubiyan a ranta, za ta iya cewa bata tab’a had’uwa da Yarinyar da ta shiga ranta lokaci d’aya ba
kamar Manubiya tanada hankali da hangen nesa…..
A hankali Mama ta sauk’e ajiyar zuciya bayan ta dafa kanta nata tukunna ta ce ’’Ba za ayi
haka ba Manu, ba zai yiu Mutanen nan su kawo har naira miliyan biyu sannan ga sadaki a gaba da zasu kawo
amma ki ce ba za’a kai ki da komai ba, ni sai naga rashin dacewar hakan’’
ta fad’i hakan tana mai juyawa ta kalli Inna kafin tace ‘’ko ya ki ka ce??’’
Lumshe ido innar ta yi ta bud’e alamun eh sannan a hankali ta d’an yi murmushi, murmushi suma duk suka yi kafin Aisha tace ‘’Nima na bi bayan su Inna!
Dan Gaskiya Manubiya kamar yadda baban khairat ya ce ya kamata ko gado ne wanda za ki saka a d’akinki d’an waje mai kyau a samu a siya miki, ki je da shi, ba dan komai ba ko dan kema ki dinga gani kina jin dad’i sannan ko ba komai muma za mu ji dad’i bamu kai ki haka ba komai ba, kuma ke kanki kin wuce gori, dukda dai na san a yadda suke da kud’in nan ba lalle su yi k’arancin tunani irin na k’ananun Mutane ba
amman fa y’an uwanshi Mata har su shida ya ce miki ko?
kinga kuwa ai Mata ba‘a rabamu da k’ananun maganganu ba.
Dan haka gara kawai ki bari ayi miki wani abun, su Baba Allah zai duba su suma’’.

Da sauri Siyama ta ce ‘’Na san ma zai bawa Ya Musbah aiki shi Mijin naki inshaaAllah’’

Murmushi Aisha ta yi kafin ta ce
‘’Ban d’au wannan akai ba,
amman dai in ya bayar Alhamdulillah’’

Ba yadda Manubiya ta iya, haka nan ta yarda ba dan ta so ba amma dukda haka sai da aka ware duba d’ari d’ari
akan zata bawa Ya Musbah d’ari Ya Nafi’u d’ari Baba d’ari,
sannan ta ware kud’in saka Muhsin a makaranta.
Ba dan
Mama da Aisha sunso ba, haka nan suka yarda suka mutunta tata shawarar itama.

Still, Manubiya ba ta so ba amma sai da su Siyama suka fitar da anko, ba yadda ta iya haka ta yarda ta biye musu ta barsu akan za su yi ankon atamfa wadda za su saka ranar da za a kaita, dan walimar ma
tace
“dan girman Allah su hak’ura, tunda za ayi wuni in an d’aura aure, kar su d’aurawa kansu hidima da yawa.”
..
Siyama dama tanada ƴan kuɗaɗenta, dan haka ita da Aisha da Manubiya da Mama suka cikawa Jidda..
A take a lokacin Aisha ta fitar musu da atamfar da za su yi aka turawa Siyama a wayarta
akan za ta nunawa anty umma sai kuma sukace zuwa
anjima za su lek’a ita da Jidda har side d’in su Uncle duk su nunawa kowa dukda dai an ja layi an musu tsakani amman za su gwada sun san ko ba komai za su samu lada.

Bayan kamar awa biyu
su Aisha suka tafi kasuwa itada Siyama da Jidda, suna fita Mama ma ta yi musu sallama ta tafi dan tanaso ta
karb’i number wata mata
a wajen Ammi mai sayar da magungunan gyara na mata,
InshaaAllah ita za ta yi wa Manubiya uwa, tana tsananin k’aunar Yarinyar sannan ba ta samu sa’a da damar aurar da tata y’ar ba wadda a yanzu tana kyautata zaton ta riga ta yi aure ta ma hayayyafa, dan
haka inshaaAllah za ta zamewa Manubiya uwa, ta yi mata duk wani gata,ta
aurar da ita.

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 08*
Chapter 13 · 0% Book details