← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 152

Sashe 52

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A ɓangaren Yashjub ɗinnkam hakan take dan sunan Kausar da Mommy ta kirawo ne ya b’ata masa rai matuk’a a take, ya san matsananciyar tsana ba ta da kyau a musulunci shiyasa yake so ya d’an rage tsanar Kausar a ransa amman sam ya gagara, cikin son kawar da ita a kansa yace”Ba komai Mommy. Bara in je in gaida Daddy sai na wuce, na barta ita kad’ai.”

“To”kawai ta samu damar cewa kafin ya fice fitt!.

Binsa kawai ta yi da kallo Baki a sake ganin yadda
yake ta uban rawar k’afa, ko zama fa bai iya yi su gaisa da kyau ba, “wanne irin abu ne haka?” ta yi wa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsa ba.

Baba larai ta ce mata ta kuncewa Manu jini sannan shima yanzu a yanayin maganarsa ta d’an fahimci babu abunda ya shiga tsakaninsu amman kalli yadda yake ta rawar k’afa wannan Allah ya rufa asiri duk ranar da ya san Manubiya a Mace ai ta su ta k’are!
Ya zama dole fa su yi sauri su san na yi da Manubiya tun wuri, a samu ta kama gabanta dan tabbas idan har suka bari Yashjub ya santa a matsayinta na Ƴa Mace to abun zai yi musu dank’o kafin su iya fitar da ita a gidan.

Daga side d’in Mommy direct side d’in Daddy ya wuce ya gaida shi….sai da yayi da ya sanin zuwa kuwa saboda yadda Daddyn ya tusa shi a gaba da tsokana, har da cewa ya ƙara yin fari overnight (a dare ɗaya) sai wani kyalli yakeyi….har hajiya mama wadda ya shiga ya tarar suna
video call itama sai da ta tofa albarkacin bakinta.

Ganin Yashjub yana shirin shigewa cikin k’asa ne ya sa suka d’aga masa k’afa…

Daga nan, Daddy Hajiya Mama da Ummi wadda ta shigo da breakfast suka saka sa a gaba suka sake yi masa nasiha sannan Daddy ya nuna masa muhimmanci y’an uwansa, ya ɗaura da cewa “dan Allah kar ya yi fad’a da su saboda Matarsa, kuma kar ya yi musu wani abunda bai dace ba a gabanta”wanda Daddy ya yi hakan ne saboda idan akwai abunda ba zai so gani ba to shine ‘rabuwar kan y’ay’ansa!’
kuma ya san abunda su Yassira suka yi ba su kyauta ba, shiyasa yake so ya yi saurin yi wa tufkar hanci tun kafin abu ya fara tab’arb’arewa tun yanzu.

Jinjina kai Yashjub ya yi bayan ya kammala sauraron Daddyn kafin yace”inshaaAllah Daddy zan kiyaye”
A ranshi yana lissafin
…maybe Daddy ma ya ji tab’argazar da su Yassira suka yi a gidan su Manu, shiyasa ya yi hakan!
Daddy yau da kansa ya rok’esa abu while he’s in a good mood (yayinda ya ke cikin yanayi na farin ciki) kuma tunda har Daddy yace’saboda Manubiya’ to ya san yanzu yana yin wani abun bak’in jini zai janyo mata a wajen Daddyn,
shiyasa kawai ya saka a ransa zai bar maganar ta wuce inshaaAllah, ba zai yi musu komai ba, amman still zai yi wa Yassira warning!…..

Maganar Ummi ce ta katse masa tunani jin tana cewa “ga breakfast d’inku chan, da har na cewa driver ya yi maza ya shirya ya mik’a muku ashe ma kazo, idan kun gama ka yi min magana sai mu je in nuna maka, idan kuma ya riga ya shirya gwaggo ta basa ya wuce da shi shikenan.”

Murmushi ya yi yace”Thankyou Ummi”

Tsaf Daddy ya lura Yashjub so yake ya tafi shiyasa ya tsaida Ummi wadda ta ke shirin fita ta basu guri ya had’ata da Yash d’in ya sallamesa suka fita shi da Ummin shi kuma suka ci gaba da video call d’insu shi da Hajiya mama.

Ko da ya biya d’akin Yahanasu ya ga kamar bata jin dad’i a take ya shiga tambayarta “me ya faru?” A mugun dame!!
Dan ko fitala ɗaya bai tarar a kunne a ɗakin ba gashi ta duƙunƙune a bargo wai ta na jin sanyi sannan ba ta son haske….

Kai tsaye ta ce masa “babu komai”dan ta san idan ya ji to yanzun case zai tashi a cikin gidan hankalin kowa sai ya tashi,ita kuma ba ta son ta ɓata masa ranakunsa na musamman dan yadda ta gansa cike da annuri da annashuwa hakan ba k’aramin dad’i ya yi mata ba. Shiyasa ta yi iyaka bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta saka shi ya yarda da cewar ‘ba komai’ ɗin.

Da taimakon Ummi wadda ta shigo d’akin basa basket d’in abinci aka samu Yash ya yarda ‘ba komai, kawai gajiya ce ta saukar mata da zazzab’i’

Daga haka yayi musu sallama bayan ya karb’a basket d’in abinci, ya wuce nndc quaters.
…
A tsaye ya sameta tana d’aura d’ankwali, ta chanza kaya zuwa wani red lace mai d’ankaren kyau shima d’inkin fitted gown,
ya zauna a jikinta d’ass!! Kamar
A saceta a gudu.

K’arasowa ya yi, ya ya tsaya a bayanta ya rungumota yana mai sauk’e ajiyar zuciya.

Tunda ta ji shigowarsa dama ta ji gabanta ya fad’i amman sai ta dake….cikin sunkuyar da kanta ta yi masa sannu da zuwa….
bai iya amsata ba sai juyo da ita da yayi ya zuba mata ido, ya shiga yi mata wannan kallon k’urillar nasa..

“Ya su Mommy??”
Ta yi masa tambayar cikin son kawo k’arshen kallon.

Ahankali ya ce
“Um..l-afiya s una gaida k e”
Sai kuma yace
“K inyi k yau s osai”
Ya yi maganar kamar Yaro mai koyon magana

“Thankyou”ta ce, ta d’an kallesa tanaso ta tambayesa ko ba shi da lafiya ne ta ji
muryarsa a rarrabe kuma yana d’an shivering(karkarwa.)

bai bata damar tambayar tasa ba
sakamokon kissing d’inta da ya fara yi cike da so da ƙauna…
Tun yana yi a hankali a hankali har abun nasa ya soma zarta misali…
sai da tafiya ta yi nisa tukunna Manubiya ta fahimci dalilin yanayin maganar tasa, ai kuwa tace ba zai yiu ba shi kuma ya ce ba ta Isa ba!.
Tou dai wannan karon su Manubiya har da cewa “Allah sai ya yi musu hisabi!”.
…
Tayi kuka kamar ranta zai fita! jiya ta fi jin zafi amman wahala da azaba kuwa sai yanzu ne ta san menene ma’anar su, dan ashe jiya bata ga komai ba somin taɓi ne akayi mata…..

shi kansa Yash sai da yayi mamakin yadda kwata kwata ya kasa
Sarrafa kansa, fahimtar da ya yi komai fa ba a hannunsa yake ba ya sa ya daina ƙoƙarin sarrafa kan nasa kawai ya ci gaba da nemawa kansa nutsuwa yana mai godiya ga Allah, ba tare da ya san lokacin da Allah zai ba sa ikon tsayawa ba……

After 3 days…..

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 22*

After 3 days

Ramar da Kausar ta yi a cikin kwana biyun kacal da su ka shige sai da ya bawa kowa mamaki, har
duhu sai da ta yi, gaba d’aya ta fita a haiyyacinta, wanda hakan ne ya sake tasowa da Yassir tsumin zargin ta da ya yi a kwanakin baya.
A kaff cikin sisters d’insa babu wadda bai tambaya “mai yake damun Kausar?” ba, amman duk suka b’oye masa…
Kuma Mommy ce ma ta sake bada goyon bayan a b’oye masa d’in, dan ta san ba k’aramin aikin sa bane ya d’agawa kowa hankali ya hautsina komai ba tare da sun samu yadda suke so ba.

Shi kam zuwa yanzu ya san tabbas akwai abunda ake b’oye masa….ya na zargin Kausar tana son Yash tunda sai da ya yi aure tukunna ta zama haka, kuma ko a baya chan ma sai wata maganar aurensa ta taso tukunna take burkicewa, shiysa ya kullaci su Mommy yana mamakin ta yadda suka iya goyawa
Kausar baya shi kuma su ka ci amanarsa….tabbas ba zai barsu ba kuwa musamman ma Kausar d’in wadda a kwana biyun nan ko wajenta ya je sai ta ke yi kamar ma irin takurata d’innan yakeyi.

Munirat kuwa idanunta sun rufe ba ta ji ba ta gani har side
d’in Yassir zuwa takeyi su
sha hira su sha soyayaya, hakan kuwa ba k’aramin dad’i yayiwa Yassir d’in ba dan Munirat ta sakar masa ragamar rayuwarta….kamar yadda ta yi zato kuwa tabbas ta taimaka wajen yaye masa tunani da muradin Jidda amman fa ko kad’an ba ta samu gurbi a cikin zuciyarsa ba, dan tsantsar so da kishin Kausar ne cike taff a zuciyarsa…a halin yanzu yanzu bayan san ganin bayan Yashjub babu abunda ya fi sakawa a gaba kamar ya samu ya gano gaskiyar lamari ta fannin Kausar.

Sir Najeeb ma yana cikin damuwa, dan kusan kullum sai ya kira Siyama, amman sam ba ta d’auka, jiya kam ya san saboda shi ne ma ta kashe wayartata gaba d’aya…zai ba ta sarari ta huta daga gajiyar biki ,sannan ta d’an yi tunani, shima kuma ya samu ya rabu da Ya’isha cikin lumana kafin ya fara yi mata nacin da shi kansa ya san sai ya takurawa kansa.
Chapter 52 · 0% Book details