Sashe 22
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Umm um fa Ummi, ba ki san
halin matar chan ba, kuma na san duk zolayar Yadira ba za ta
fad’i abunda zan yi wa uwarta fad’a ba ai.
Anyways tunda kowa b’oyemin yake yi ba komai.”
Tana gama fad’in haka ta cika Yashjub ta Isa gaban Mommy ta tsaya ta ce ”ko za ki mutu! Sai
Yashjub yayi aure da yardar Ubangiji, kuma idan kin haifu ki
je ki yi wani abun da zai jawo tangard’a, ko a makirce ko a asirance ko a Isa da mallaka na matsayinki na uwa!
A nan ne za ki gane shayi ruwa ne!”.
Tana gama fad’in haka ta wuce sama ta bar ta anan ita da su Yasmeen waenda suka kawo iya wuya!
Mom da Ummi ne suka bi bayanta, daga haka aka fara watsewa daga parlourn.
Sai da Yash ya k’arasa wajen su Daddy da Abhi suka d’an gaisa tukunna ya juya ya nufi side d’insa…
Har ga Allah yadda Mommy ta durk’ushe tana kuka duk sai ya ji bai ji dad’in abun ba.
Da ruwa mai zafi sosai ya yi wanka, ya d’an gwada kiran Manu, jin shiru bata d’auka ba ne yasa ya fahimci ta yi barci, dan haka ya ajjiye wayoyinsa ya fito ya nufi wajen Mommy bayan ya rufe side d’in nasa dan tuni Junior ya tartare kayansa ya koma side d’in Yassir tun lokacin da aka gama yi masa gininsa.
Allah ya so shi kuwa basu rufe ba, dan haka ya shige ya haye sama yana mai sake jaddadawa da tirsasawa kansa
“dole ya sasanta tsakaninsa da Mommy, dole ya nemi albarkar ta! dole ya lallab’ata! uwa uwa ce!”
Ya yi mamakin samun su da ya yi a d’akin Mommyn su dukansu har Baaba Larai da
Yadira kamar wasu masu yin meeting.
Sake gaidashi suka yi gaba d’ayansu, daga haka suka fara mik’ewa suna yi wa Mommyn sai da safe suna ficewa one by one, dan yana gama amsa gaisuwar ta su ya koma gefe ya chake ya tsuke fuska…
Sai da Baaba Larai ta zo fita tukunna ya kamo Hannunta ya ce “Banda ke Baaba”
Kallonshi ta yi ta kalli Mommy kafin tace “to d’an albarka”
daga haka ta koma kusa da Mommyn ta zauna anan gefen gado.
Shiruu d’akin yayi kafin ahankali Yashjub ya fara takawa zuwa inda suke zaune, yana zuwa ya durk’usa a gaban Mommy.
Ba k’aramin shock suka shiga ba dan ko da wasa ba su tab’a kawo hakan ba, yaushe ne ma Yash ya durk’usa mata irin haka ba lalle ta iya tunawa ba…
Suna wannan tunanin suka ji a hankali ya fara magana yana cewa “Mommy akwai abubuwa da yawa da kuma misunderstandings (saɓanin fahimta) a tsakanin mu.
Ke mahaifiyata ce, shiyasa duk yadda na so in rik’e ki a raina hakan ba zai yiu ba dan ya zame min dole in yafe miki
sannan kuma in nemi gafarar ki…
Amman pls Baaba ki zama shaida sannan ki nuna mata mahimmancin mu musamman ma ni
a wajenta.
Akwai abubuwan da kikayi min da yawa shiyasa idan na tuno raina yake b’aci, idan
nine wani abun ya faru da ke hankalina a tashe har sai na ga an yi miki adalci amman ke sam bakya dubani a ko da yaushe..
Anyways komai ya wuce yanzu albarkarki da yafiyarki nake nema.
Sannan akan abunda kika yimin magana d’azu shima ki yi hak’uri, zan yi k’ok’ari in gyara kema
kuma dan Allah ki gyara Mommy.”
Ahankali ta sa Hannunta duka biyu ta d’ago shi ta zaunar dashi a gefen ta.
Shiruu ne ya biyo baya kafin ta sauk’e numfashi tukunna ta fara magana “Yashjub ba wai ban damu da kai bane
A ‘a
Ina duba ɗabi’ar al’amura ne…
Sannan na san kana jin haushina akan Yassir. Yashjub! Ba ka riga ka haihu ba, shiyasa ba za ka tab’a sanin yadda na ji a lokacin da naga Yassir kamar gawa ba….inaso ka fahimceni ka fahimci ba wai dan na fi son shi akan ka bane ya sanya na fad’i maka abubuwan da na fad’a ba a wachchar ranar…
na fad’a na sake fad’a gaba d’ayanku ya’yana daidai kuke a cikin zuciyata, na san ko kai ne ka tarar da d’anka a halin da na ga Yassir a wachchar ranar na tabbatar sai ka yi kuma ka fad’i abubuwan da su ka fi waenda ni na yi na kuma fad’a.
Amman duk da haka ka yi hak’uri, ba zan sake ba, inshaaAllah, b’acin rai ne”
A hankali Yash ya rik’o
Hannunta, ya girgiza mata Kai sannan ya ce “ba komai Mommy, ba sai kin bani hak’uri ba”
Murmushi ta yi ta d’an shafa fuskarshi kafin ta ce ”I love all of you amman kuma in ka lura mahaifinku ya fi fifita ka sama da kowa, idan nima na yi hakan
to tabbas mu da kanmu zamu taru mu lalata tsakanin ku ne musamman ma tsakaninka kai da
Yassir wanda yake ganin kamata ya yi ace kunada equal right (haƙƙi dai dai wa dai da) da kai da shi, shiyasa dole wani abun zan ke kauda kai ba wai dan ban damu da kai ba sai dan son ganin an zauna lafiya.
Sannan maganar Kausar dan itama na san kana ganin kmar Ina fifitatata sama da ku ko?”
Bata jira jin amsar sa ba ta d’aura da cewa “Kamar yadda ka kauda duk wani abun da kake tunanin na yi maka ka zo
ka bani hak’uri sannan kake neman yafiya da albarka ta a matsayina na mahaifiyarka
To
nima albarkar tawa mahaifiyar nake nema dukda kuwa ba ta
raye, saboda inaso inga na cika mata burinta dan kafin mahifiyarmu ta rasu sai da ta damk’a min amanar maman Kausar tana kuka tana rok’ona in zame mata uwa da uba mu had’e kawunanmu, to haka itama maman Kausar a lokacin da ta zo rasuwa tana kuka haka ta bani amanar Kausar,
ta yaya
kake tunanin zan zubar da wannan amanar??
Kuma bayaga haka ma
Allah ya d’aura min tausayi da k’aunar Kausar sannan ka duba kaga Yarinyar nan ko uban da ya haifeta bata saniba wasu lokutan a gaban idonta Mama da Daddynku
suke kiranta da ‘shegiya!’
Na san ba mu Isa chanza wannan fact d’in ba amma kara ai tana da dad’i,
kuma abun yana damunta sosai sannan gashi ba uwa ba uba, ka gaya min idan ban ja ta a jiki na sa ta ji itama tana da family sannan na bata mahimmanci ba wa zai yi?
ina za ta saka kanta?
Ba wai na fi son Kausar a kanka ba ne, kai kanka ka san hakan ba zai tab’a yiwuwa ba tunda
kai a cikina ka fito
kawai dai
Ina k’ok’arin inga ban biyewa son zuciyata na cutar da kowanne a cikin ku ba, kuma
kamar yanda kake fushi da ni akan na fi son wasu akanka
ko kuma kake ganin kamar ban damu da kai ba to haka nima nake fushi da kai, shiyasa ka ga kawai Ina rabuwa da kai wasu lokutan dan sai inga kamar baka damu da ni sosai ba, d’azun ma k’ureni ka yi kuma ai kai kanka ka san gaskiya na fad’a Yash baka shawara da ni, ban gama jin d’uminka ba aka d’auke min kai kuma ban Isa in ce wani abun ba sannan kai d’in da nake saka ran za ka share min hawaye gaba d’aya ka k’i ka sake da ni da y’an uwanka gashi har za ka yi aure ka sake yin nesa da mu shikenan na san burina na ganin mun had’e kai
Ni da Kai da y’an uwanka ba zai tab’a yiwuwa ba kenan??”
Kasa ci gaba da magana ta yi
sakamokon kukan da ya taho mata…
Ahankali ya janyota ya saka ta a jikinshi ya shiga rarrashinta,
kafin cikin kwantar da murya ya ce “Mommy sam ba haka bane ata b’angare na, su Yassira Mata ne
Yassir kuma kinga yanayinshi,
Idan ban tsaya na yi haka akansu ba akwai matsala sannan Mommy ba wai ban saki jiki dake bane kasa fahimtata kikayi…amman inshaaAllah zan gyara.
Ina da fatan za ki daina fushi da ni sannan ki saka min albarkarki.”
Ahankali Baba Larai ta ce ”Ku dai gyara tsakanin ku, jini ya fi ƙarfin komai, kuma sabuwar member za ka kawo Yashjub,
duk abunda ta ga kana yi wa family d’inka to itanma haka za ta yi musu”…Cikin son fahimtar da shi su biyun suka shiga nuna mishi mahimmancin family kama daga y’an uwanshi har iyayensa.
Tabbas kuwa maganganun nasu sun ratsa Jikinshi matuk’a…
Daganan suka fara maganar auren nashi…ya saki jiki da su sosai bai b’oye musu komai ba,
ya ji dad’in yadda Mommy ta ce”komai komai ya wuce” sannan ta nuna farin cikin ta a auren ta kuma gaggaya mishi abubuwan da shi ba su ma shirya ba daga shi har Yahanasun.
Tabbas duk lalacewar uwa
Uwa ce kuma tanada matuk’ar amfani ata ko wanne b’agare
na rayuwar y’ay’anta, dan shi sai yanzun ne ma da suke maganar tukunna yake jin wasu aladun da kuma abubuwan da ya kamata a yi waenda da duk ba za ayi su ba.
Bai bar wajen ba har number Manubiya sai da ya bawa mommy, hakanan suka rabu ran Yashjub fess…Mommy ta sake sosai
sannan ta amince kuma ta sanya albarka a auren d’ari bisa d’ari.
Yana murmushi haka ya fito daga d’akin, da fari ko sanda ya shigo cikin gidan ko kallonta baya son yi amman gashi da ya danne zuciyarshi ya zo suka fuskanci juna ya ji sanyi a ranshi. Addu’ar sa itace”Allah ubangiji ya bashi ikon had’a kan Manubiya da su gaba d’aya, Allah ya sa komai ya zo mishi da sauk’i dan no matter yadda mutum yake jinshi jajirtacce indai lamari ya had’a da Mata dayawa kuma ya zamana shine a tsakiya to fa
abun babu sauk’i.
Yashjub yana fita Mommy ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ta kalli Baba Larai ta ce “yanzu menene abun yi na gaba???”
Shiruu Baba Larai ta yi, kafin ta furzar da ajjiyar zuciya tukunna ta ce ”ki yi hak’uri, mu ajjiye komai, mu hak’ura a yi auren”.
A mugun furgice sannan da k’arfi Mommy ta ce “watt!!”