← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 152

Sashe 136

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aikuwa suna isa suka shaida wajen…
Mutumin tsoho tukuff dashi, duk wanda ya gansa ba zai yi tunanin ko gani yanayi ba ma tsabar tsufa..hakanan ya k’araso inda suke dan suna yin parking suka ga ya fito dama….
yana zuwa yace”lale marhaba Khadija, yau kuma ina Larai??”
Sunkuyar da kai Mommy ta yi ta girgiza kanta a hankali wasu siraran hawaye suka zubo mata….

Shiruu ya yi, ya d’an k’ura mata idanu, kafin yace”Allahu Akbar! amma an yi babban rashi..Allah ya ji k’anta!mu je daga ciki”
Daga haka suka nufi cikin.

Shi wannan tsohon! wanchan bokan na k’auyen su Baba larai shi ne ya had’ashi da ita tun asalin farko kafin ya rasu kafin ta baro ma k’auyensu ta dawo nan Kano inda yake…..idan abubuwa suka shige masa duhu ya kan tambayeta, itama haka,har nan suna zuwa ita da Mommy idan aikin da suke son yi ya had’a da wanda mace ba zata iya yi ba sai su kawo shi ya yi musu.
….
Sai da ya sake yi mata gaisuwa ta amsa, tukunna ba tare da b’ata lokaci ba tace masa ”Yashjub ya yi aure ba ta samu abunda take so ba har yau, kuma Yarinyar ta zo da farar k’afa! mutuwar Baba larai na daga cikin masifun da Manubiya ta zo mata da shi! saboda dama Baba larai tace
muddin aka aurota to fa an yi ta ganin bala’i kala kala.
Yanzu haka ma ba ta gidan Daddy jiya ya yi musu korar kare ita da Yassir….”

Salati tsohon ya yi, kafin ya janyo wata tukunya mai ɗauke da ruwa fall a cikinta, ya hau duba cikin nata yana jimami….

Sun fi mintuna ashirin a haka, kafin chan ya d’ago ya kalleta ya ce ”ai kin yi kuskure! irinsu waennan ba a barinsu a doran k’asa!
ai idan aka yi aiki akaga ya k’i ci ya k’i cinyewa to rabasu da duniyar gaba ɗaya ake yi, tunda sun fi k’arfinka dan haka ta ya zaka tsaya fafatawa da su? ai ba zai you ba!
Dan fafatawa da irinsu babu riba!.”

Ajiyar zuciya Mommy ta sau’ke, dan ba k’aramin dad’i ta ji da jin wannan batun ba, saboda dama itanma takanas abunda ya kawota kenan!!a yi ta ta k’are kawai.

Cikin k’aguwa tace”aikin gaggawa nakeso ka yi mana, ba na so Larai ta kwana uku a kabari ba tare da Yarinyar nan ta bi ta ba!”
Cikin tarar numfashinta Yasira tace
“Mommy wai kisan Kai kike nufi??”

Murmushi tsohon ya yi, kafin yace”to ai hakan kawai ce mafita! saboda Wallahi Allah muddin Yarinyar nan tana raye tou fa bala’i da masifu yanzu kuka fara gani!!!”.

K’ura masa ido Yasira ta yi, kafin chan ta d’auke kanta ta mayar ga Mommy tace”Mommy mu je gida ma yi magana, Plss, dan Allah ki bar maganar nan!”.

Girgiza Kai kawai Mommy ta yi kafin ta ce”Yasira har yanzu ke Yarinyace..dan gashi duk abubuwan da suke faruwa a gaban idanunki ba kya gani!
inaga sai na mutu kin binne ni tukunna za ki fahimci abunda muke nufi!!!”

Da d’an zafi Yasira tace”Mommy Manubiya b….”
Cikin katseta da tsawa sosai Mommyn tace”za ki yi mini shiru ko kuma in kora ki waje????”

alamun ta yi shiru su Ya’isha suka yi mata, dan haka kawai ta yi shiru ba dan ta so ba, kuma wallahi wannan tab’argazar ba da ita ba, ba za ma ta bari a yi ba…

Sai da Mommy ta yi kusan minti d’aya tana hararar Yasirar, tukunna ta mayar da kanta ga tsohon wanda shima yake cewa Yasirar “ki tsaya ayi abu a nema muku mafita, hatta rashin aurenku duk itace dan gashi nan na gani a nan! ko ba kwanan nan wanda za ki aura ya yi aure ba???”

Ita dai Yasira banza ta yi da shi, Yayinda Mommy da Ya’isha suka aminta da maganar ta shi d’ari bisa d’ari…

Murmushi kawai ya yi, ya mayar da dubansa ga Mommy yace”kar ki damu, komai ya zo k’arshe inshaaAllah!”

Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin tace”yanzu nake so a yi aikin..saboda na gaji na tsani…”

Cikin tarar nunfashinta yace”sai dai a yi aikin a yau da daddare gobe a tashi babu ita!!”

Jinjina kai ta yi tace”hakan ma ya yi”

“To Alhamdulillah” yace, kafin ya d’aura da cewa”yanzu akwai yadda za a yi in samu hularta???”

Kallon juna suka yi ita da Ya’isha suka yi shiruu, kafin chan Ya’ishan tace”eh!!
Da me kuma??”

“Iyaka hula, kawai!.
Ki tabbatar tana cirewa daga kanta kin kawo mini kai tsaye ba tare da kowa ya saka ba!
Shikenan abunda na ke da buk’ata.”
Sai kuma Cikin yin serious da fuska sosai, ya ture tukunyar gabansa ya mayar gefe ya kallesu da kyau tukunna ya ce
”da farko dai inaso ku fahimci cewa shi RAI!!
Bayar da shi da karb’arsa wannan Ubangiji ne kad’ai ya isa! bi’ma’ana Ubangiji ne kad’ai yake bayar da Haihuwa yake kuma kashewa, bayan shi babu wanda ya isa ya yi hakan, duk bala’in mutum bai Isa ya kashe ko ya raya ba…”

Jimm Mommy ta yi, tana jin wani sabon tashin hankali yana rifeta, kar dai mutumin nan yace ba zai iya yi mata komai ba kuma!!!
Tana wannan tunanin ta ji ya ci gaba da cewa”Abunda mukeyi idan matsala irin taki ta taso shine wannan aikin da zan yi muku a yanzu, ammafa yanada matuk’ar haɗari kuma yana buk’atar taka tsantsan!”
Sai da ya sauk’e numfashi tukunna ya d’aura da cewa”ita wannan hula da za’a kawo! itace nake so a kiyaye kar a samu matsala
wani ya saka bayan ita Yarinyar kafin a kawo min, ko kuma a samu matsala ta hanyar kawo min wadda ba tata ba, ko kuma dai wani abu makamancin hakan…
saboda idan aka samu matsala, to fa shi wanda ya saka bayan itan, ko kuma shi wanda aka kawo tasa a maimakon ta Yarinyar, ko kuma dai duk wani wanda ya gilma a tsakani har ya ja matsalar ta samu, uwa uba wanda ya ɗauko hular ya kawo!
Duk ɗinsu aikin zai haɗa ya faɗawa.
Bima’ana dai duk wanda ya ja aka samu matsala a aikin ko wacce iri ce to maimakon aiki ya faɗa akan Yarinyar (Manubiya) aiki zai faɗa ne a kansa ko a kansu!…
saɓanin idan ba a samu matsala ba, aikin zai faɗa ne akan ita Yarinyar (Manubiya) ita ɗaya kawai…
kuma idan aka yi aikin aka kammala komai ya kankama to ba’a janyewa, bima’ana idan aka yi ya kammalu komai ya hau saiti to an riga an yi kenan ba a taɓa iya karyawa.”

Jinjina kai Mommy ta yi tace
“na ji na fahimta, inshaaAllah za a ayi taka tsantsan..ya aikin yake?”
Ta yi masa tambayar tana kallonsa.

Murmushi ya yi kafin kanshi tsaye yace”rik’e mata numfashi zan yi!…idan kaff likitocin duniya ne za ace su zo su taru a kanta to fa babu wanda ya isa yace tana da rai! saboda komai tsayawa zai yi.
Daganan Idan aka yi mata wanka, akai mata sutura aka kai ta kabari aka binneta! muka tabbatar an kai ta ɗin, ni kuma sai in saki numfashin nata ya dawo..kinga dai ai bata isa ta fito ba ko? sai dai ta k’arasa a chan!!”
Ya k’arashe maganar tasa yana sakin dariya…
Da sauri Yasira ta mik’e ta fita, hankali a tashe ranta a masifar b’ace..Tabbas bayin Allah marasa Imani suna da yawa a duniya..ta ya mutum zai iya aikata haka a d’an Adam musulmi d’an uwansa?.

Wani sanyi da nutsuwa Mommy ta ji daga jin bayaninsa, dan bata tab’a jin hukunci mafi dacewa da ya dace ace ta yankewa su Manubiya ba kamar wannan!!!

Har za ta yi magana, sai kuma ta tuna da su Yusra a wajen, dan haka ta kallesu tace”ku d’an bamu guri!”

Sai da ta tabbatar sun fice daga cikin gidan gaba d’aya, tukunna ta kallesa tace”Ana iya yiwa Namiji ma ko?”

Dariya sosai ya yi kafin yace”Yashjub ko?
Tsaff za ki yi masa shima, amma shi gashin kansa za ki kawo.”

“……….Samun gashin kan Yashjub zai d’an yi wuya, amma hular Manubiya yanzunnan ka jira a daren nan za ka samu, za ‘a iya kawo ribbom ma?”
Cewar mommy..

Jinjina kai yayi yace”indai ya tab’a kuma ya yi muamala da gashin kanta to ku kawo!!”

Wani irin farin ciki ne ya lullub’e Mommy, gudun ma kar su ci gaba da b’ata lokaci ya sanya ta mik’e da sauri tace masa ‘ya bata awa d’aya da rabi’
daga haka sukayi sallama ta fita jikinta har yana b’ari, ranta fess.

A mota duk ta samesu a zaune, Yasira ta had’e rai kamar ba ta tab’a dariya ba!!
Mommy Ta san idan ta biyewa Yasira b’ata mata lokaci kawai za ta yi, dan haka ta sa Hannu ta d’auki Jakarta ta kalli Ya’isha tace mata “zo”
Su kuma su Yasira tace”ku wuce gida.”
Yasira za ta yi magana tace”na rantse da girman Allah Yasira zan yi miki Baki!!
idan kuma kema Yasmeen da Yadira za ki zama to bismillah, ki tattara ki koma gidan ubanki kar ki damu da damuwata! Allah zai yi mini gata!”
Sai kuma tafashe da kuka tace”Larai ce fa ta rasu, amma kalli Yadira da Yasmeen ko yunk’urin zama inda nake basuyi ba ballanata su taushe ni, tunda Manubiya ta zo cikin rayuwarmu komai ya hargitse, ku kanku ƴaƴana an juya muku lissafi kalli fa abunda kuke yi mini sannan a haka ki ce wani in hak’ura?”

Cikin zubar hawaye Yasira tace”gaskiya fa nake gaya miki Mommy, kuma son da nake yi miki ne ya sanya nake k’ok’arin kub’utar da ke daga hanyar halaka in saita ki a hanyar tsira!
Saboda Allah ta Ina kashe Manubiya ya zamto hanyar warwarewar waennan abubuwan da kika lissafa, Ina riba a kashe rai??….kece fa baki tsaya kin nutsu kin fuskancemu ba shiyasa kike ganin kamar mun juya miki baya, Yadira fa ciki ne da ita amma baki ma lura ba kina ta abubuwan gabanki! tunda ta yi aure ba ki damu ki duba ya take ba! ko d’azun ma amai ta yi shiyasa junior d’in yace su wuce asibiti, kuma na san za ta dawo ba wai k’in zama ta yi a wajenki ba.
kawai bamuga kin nustu bane balle har ki bamu listening ear shiyasa kika ga bama…”
Chapter 136 · 0% Book details