Sashe 127
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiruuu Mommy ta yi haka itama Yahanasu…tun shekaran jiya da Yahanasun ta je d’akinta ta yiyyi threatening d’inta, a take ta san tsaff za ta iya yin abunda ta fad’a ɗin, shiyasa ta ke so ta lallab’ata..tana son y’arta kuma ta na so su fahimci juna Sannan da gaske ne Baba larai asiri ta yi mata ta kawar da Yahanasun daga ranta gaba d’aya, amma ita Mommy a halin yanzu Babban tashin hankalinta shine kar Yahanasu ta tona mata asiri!
Ta ji haushin Baba Larai kuma ta na so ta san ta yi mata laifi ta yadda ba za ta sake yunk’urin yin wani ba shiysa ta barta ta tafi kuma ta hana a nemota amma fa Yahanasu tana daga cikin dalilin da ya sanya ta yiwa Baba larai abunda ta yi saboda tana so Yahanasu ta gani sannan ta san ta yi abu Babba haka duk dan ita, sai dai kuma ta lura hakan ko a kwalar rigar Yahanasun, gashi a iyaka maganganunta na yanzu ma ta lura Yahanasu fa ta san har case d’in abunda ta aikatawa Khadija(amaryq)….dan haka dole ta d’auki risk ta aikata dukkan abunda za ta iya domin ta samu ta yi manipulating Yahanasu, ta shawo kanta su fahimci juna tun kafin ta b’allo mata ruwa.
Dan haka
A hankali ta ce mata “ki zauna mu yi magana Yaha, zan fad’a miki duk abunda na yi tare da alk’awarin ba zan sake ba..kuma na san idan kika ji bayani na za ki yi mini adalci idan kika fahimci dukkannin abubuwan da na yi na aikata su ne saboda ku y’ay’ana.”
Yahanasu ba ta zauna ba ganin ba ta da niyyar zaman ne ya sanya Mommy ta fara magana.
“Kamar yadda na fad’a, ba zan b’oye miki komai ba, saboda Ina so ki yarda da ni, mu fahimci juna.
……….Idan ana maganar rashin jituwa da rashin zaman lafiya da rashin so da k’auna to shine asalin ma’anar zamana da mahaifinku tun lokacin da muka yi aure…ko
Irin soyayyar nan ta amarci bai nuna mini ba, iyaka k’arshen rashin mutunci da kyara shi Imam ya dinga nuna mini.
Tunda muka yi aure sam ba ya ja na a jikinsa, ba ya nuna mini kulawa.
Ban rufe watanni biyu a gidan Imam ba ya tubure ya dage ya d’agawa kowa hankali akan shi fa sai ya k’ara aure…sai ya auri budurwarsa wadda na san yana masifar so kamar ransa, dan k’iri k’iri ya kan ce mini saboda sunana ya zo d’aya da ita ne dalilin da ya sanya yake d’an kulani.
Babu kalar masifar da ban yi ba, amma sai da aka d’aura auren nan, lokacin ma da aka d’aura ba na nan ya kaini gidanmu yace a yi mini fad’a, Abban mu kuma ya goyi bayansa aka mini horo mai tsanani ta inda aka ce ba zan koma gidan ba, Ina ji Ina gani aka yi auren Khadija ta tare suka gwangwaje amarcinsu ni kuma Ina gidanmu hankalina a tashe.
Yadda na fita daga haiyyacina sai da ya bawa mahaifiyata da Hajiya Mama tsoro dan haka suka fara ƙoƙarin yin wani abun, amma sai mazajensu suka tsawatar musu, aka ce a rabu da ni hakanan.
sai da na gama shan wahala, imam ya gama cin amarcinsa tukunna Abbanmu ya ce in koma!
tare da zazzafan warning d’in ‘idan har ya ji case ya taso daga waje na to na bar Imam kenan har abada! ba zai bari in koma gidansa ba.’
Ina mutuwar son Mijina, ba zan tab’a iya rayuwa babu shi ba. gashi ba zan iya zama da kishiya ba, shiyasa na shiga tsaka mai wuya! na rasa abunyi! na rasa tudun dafawa…
A dai-dai wanchan lokacin ne kuma dama larai ta dawo hannun Mahaifiyata da zama (matsayinta na y’ar uwar mahaifiyarta), saboda an samu matsala da ita a k’auyensu an d’aura mata sharrin maita.
Itama tana da damuwa nima Inada damuwa shiyasa muke zama muke tattaunawa…Larai ta tausaya mini sosai haka kurum da na zo komawa tace ‘Tana so za ta biyo ni.’
A wanchan lokacin da kyar su Abba suka amince saboda Larai a k’alla ta bani shekaru sha biyar, kuma suna so in je in zauna lafiya ni kad’ai in yi hankali shiyasa suka ji tsorom kar mu je da larai in ga mu biyu ne in yi ta rashin mutunci..amma sai mahaifiyata tace ‘ba komai, mu je kawai’
saboda ta ga mun shak’u muna d’ebewa juna kewa, sannan tunda Larai ta zo ba mu sameta da wata muguwar d’abi’a ba in banda addini da sanin ya kamata da muka santa da shi.
Haka nan aka tambayi Imam ya amince shima dan haka muka tafi gidana tare da Baba larai.
A ranar da na koma ma Imam ba a d’akina ya kwana ba, ko kallona ba ya son yi. sai bayan kwana hud’u ya kiramu ya raba mana kwana Akan za mu dinga yin kwana uku uku ni da Abokiyar zama na.
Sai da girki na ya zagayo sau hud’u tukunna ya fara kwana a cikin d’akina saboda da a parlour yake kwana, ko da ya fara kwana a d’akin nawa shima kuma babu abunda yake shiga tsakanina da shi!
Dan sai dare wajajen 12 ma tukunna zai shigo, Idan aka kira assalatu kuma ya fita, daga nan ba zan sake saka shi a idanuna ba sai wani daren, a cewarsa ‘aiki ya yi masa yawa!’.
Da gaske na san ba ya gidan tun safe har dare, amma kuma sai ranar girkina ne ya ke yin scarce (ƙaranci da wuyar gani) dan duk ranar da aka ce miki yau girkin Khadija ne to tun kafin Magrib yake shigewa d’akinta ba abunda yake fito da su sai sallah da cin abincin dare da ake yi tare, daga sun yi isha kuma ya ke kiranta daga nan ba za mu kuma sake ganinsu ba sai washegari,
haka nan wasu lokutan zan yi ta jin hirarsu yana dariya yana raha.
Abun ya ishe ni, gashi ban Isa yin rigima ba dqn na san in na yi tsaf su Abba za su raba auren! ni kuma ba zan iya rayuwa babu shi ba, shiyasa na yanke shawarar kashe kaina kawai!!!!…
ranar da zan yi abun Allah ya taimakeni na d’aga kwalbar fiya fiyan kenan zan sha Larai ta shigo, ganin yadda na firgita ta fahimci ba ni da gaskiya
aikuwa tun kafin ta gama dubawa ta gane menene a ciki.
Hankalinta ba k’aramin tashi ya yi ba, dan haka ta fito min a Mutum k’iri k’iri tace min ‘Itafa dama ta biyo ni ne saboda tana so za ya taimaka mini..’
Ba ta b’oye mini komai ba tace ‘akwai wani boka a k’auyensu, mutumin tun yana zuwa mata a mafarki sama sama, har ta gano location d’insa (inda ya ke) a cikin mafarkin, a wata bukka chan a cikin daji, ta je..nan yake sanar mata tun ranar da aka haifeta ya san dama itace za ta gaje sa…
Tun bata d’auki abun da gaske sannan da mahimmanci ba har ta d’auka!!!
bata da uwa sai Matar uba, dan haka bata yi shawara da kowa ba ta biye masa!
Ba a yi wata d’aya ba ta koyi kusan komai, ta inda ya zage ya kokkoya mata abubuwa, yace ‘ta rik’e da kyau, hannunta yana da zafi fiye da zaton mai zato’.
Akan wata k’awarsu da suka yi fad’a ta fara gwadawa, ta inda matar har yau tana nan a k’auyen namu ba ta gani, daga nan sai ta gayawa babbar k’awarta…tun daga ranar duk wani abu da k’awar take so ko ta kwallafa rai akai to sai Larai ta yi mata aiki a Kai, ta samu!!
Itqma kuma da kanta ta kan yi wa kanta abubuwa..
A b’oye suke yin abun nasu kuma daga ita sai waenda ta yarda da su shiyasa abun bai baza gari ba.
Amma ta ce mini abu d’aya ne har yau ta kasa yi wa kanta aiki a kai shi ne ‘mijin aure,’
dan har wajen bokan da ya koya mata duba da abubuwa ta je suka taru suka duba ranar aurenta amma sai su ka ga ‘babu!’..
Dukda hakan bai sa ta fidda rai ba, hakanan har gobe Larai take neman mijin aure ido a rufe amma babu shi babu alamarsa.
Ragowar k’awayenta da k’annen k’annen k’awayenta duk sun yi aure, kuma ba laifi sun rik’e mata sirrinta ba su fad’awa kowa ba…
Mutuwar wannan boka itace ta tona mata asiri, dan da ya kusa mutuwa sai ya raba sunanta ma clients ɗinsa (kwastomominsa), to ta hakane da wata mata ta zo wajenta ta sanya Laran ta yi wa d’an kishiyarta asiri ya yi ta rashin lafiya d’aga k’arshe Yaron har ya zo ya rasu..shine fa da bincike ya yi bincike aka ganota aka ce za a k’onata a k’auyen! ai mayya ce!
tunda gashi dama ta rasa miji kuma zan iya ce miki kaff k’auyen mu har yau ba ayi mai kyan larai ba, shiysa su kuwa suka ce ai mayya ce.
Ina gama jin labarinta ko wasu-wasi ban tsaya yi ba na amince da tayinta, muka fara aiki babu dare ba rana a kan Khadija(amarya) da Imam.
Ba a yi sati d’aya ba kusan gaba d’aya hankalin Imam ya dawo kaina, dan kusan yaddda yake mu’amala da Khadija amaryarsa nima haka yake mu’amala da ni, sai dai kuma ni kaina na san soyayyar Amaryarsa ta daban ce kuma ta gaskiya ce duba da yadda ba ya kishi na kamar yadda yake kishinta, dan haka muka sake zage damtse, aiki ba dare ba rana, ga kuma kissa da muka bawa mahimmanci, dan ko
wani abun aka yi sai dai in shige d’aki in yi kuka in goge daga ni sai larai ba ma tab’a bari wani ya ji ko ya gani…