← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 152

Sashe 2

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddy yana dasa aya cikin
tsananin murna
Munirat ta ce ’’Allah ya sanya alkhairi’’
Ta fad’i hakan fuskarta d’auke da faffad’an murmushi
Sai kuma ta yi shiruu da sauri ganin babu wanda ya ce komai sai ita sannan tsabar yadda da fad’a cikin murna da kuma yadda duk aka yi tsit sai muryar tata ta fita da ƙarfi sosai ta cika d’akin.

A b’angaren su Yassira kuwa, tun daga kan Mommy har izuwa kan Yadira babu wadda a take a lokacin bata shiga cikin maɗaukakin tashin hankali ba…sun san da maganar ba wai basu sani ba amman kuma fad’a musu d’in da Daddy ya yi a yanzun ya sanya suka sake tabbatar da dahir d’in maganar wanda hakan ya sanya damuwar da suke a ciki tun farkon lokacin da suka ji zancen auren ta sake hauhawa.

Murmushi Ummi ta yi tukunna ta ce
“MashaaAllah Yashjub, na yi matuk’ar farin ciki….dukda bamu da isashshen lokaci
amman in sha Allah
za mu zage dantse a yi hidima sosai.
Na ji dad’i kwarai
Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya ya sa Matarka ce har abada har a gidan aljannah’’

Murmushi ya yi, a hankali kuma sai ya ce
‘’Ameen Ummi, na gode.’’
Kafin ya d’ago lumsassun idanuwansa ya zubasu a kan Mommy
dai-dai itama shi ɗin take kallo tana nazartar fara’ar da yake ta zubawa.

Diriricewa ta yi, dan haka sai ta hau kame-kame
kafin ta ce ’’ni na ma rasa Bakin
magana’’

Shiru Daddy, Ummi, Munirat da Yashjub sukayi suna tsammanin su ji ta d’aura da wani abun amman sai suka ji ta yi shiru,
dan haka duk sai aka zuba mata idanu.

So take ta yi magana amman da ikon Allah sai ta kasa, gashi dama kuma tama rasa me za ta ce ne shiyasa kawai sai ta hau wasa da bakin mayafinta kamar wata Yarinya.

Girgiza Kai kawai Daddy ya yi tukunna a hankali ya ce
‘’Hmm’’

Cikin son kawar da yanayin, Ummi ta ce ‘’na san yanzun ba lokacin da ya dace bane duba da kasancewarka a gadon jinya
amman kuma duba da yanayi na lokaci na ga yakamata ko zuwa anjima ne idan ka d’an huta sai mu
fara maganar had’a lefe…
dan na san Maza ba ku iya zab’ar test d’in da mu Mata muke so ba.

Ka yi mana magana, sai in taya Mominka tunda bamu da isheshshen lokaci.’’

Murmushi Yashjub ya yi kafin finally ya d’auke idanuwanshi daga kan Mommy ya mayar kan Ummi tukunna ya ce ’’am..actually Ummi
Yahanasu ce za ta had’a,
na ma tambayeta tun-tuni…’’

Cikin katse shi Yasmeen ta ce’’ au,wato Yahanasu ta riga ta san maganar auren naka ahead of us(tun kafin mu mu sani) kenan, ko Yaha??’’
Ta k’arashe maganar tata tana mai kallon Yahanasu da alamun tambaya.

Wani kallo Yash ya d’ago ya watsawa Yasmeen ɗin wanda hakan yasanyata ta kawar da kanta gefe.

Yahanasu tana shirin yin magana Ya’isha ta sake cewa
‘’Yaha ba ki amsa tambayar Yasmeen ba’’

Sai kuma ta kalli Yash ta ce ‘’I mean no disrespect(ba wai da nufin raina ba) amma
a ganina Allah fa ya baka ƙanne Mata very classy! Kuma wayayyu har kusan mu shidda, dan haka mai yasa za ka zaɓi Yahanasu wadda ba ta san komai ba a matsayin wadda za ta haɗa maka lefe??
No offense (kada ku ji haushi)
Amma duk nan ai mun san bata da wayewar mu, gashi bata son shiga mutane tunda ita haka nan yanayi da ɗabiarta suke.

Wannan fa shine biki na farko da za a yi a family d’in nan so inaga bai kamata mu bawa kanmu kunya ta ko wacce hanya ba.
Sam bai kamata a bar Yaha ta je ta ta had’o abunda bai kamata ba gudun kar ta ja mana jin kunya, tunda na san itama Yarinyar da za ka auran dole ƴar manya ce.

Anyways, raina ya riga ya ɓaci tun farko da na fahimci ’sai da ka fara gaya mata har kuka fara had’a lefe tukunna mu muka sani’
Dan haka a gaskiya ba zan iya ci gaba da zama a ɗakin nan ba!
bara kawai in wuce saboda kar raina ya ci gaba da ɓaci in je in fad’i wata maganar da za ace na yi rashin kunya!!’’

Shiruu kawai Yashjub ya yi ya zubawa Ya’isha ido…ranar da Najeeb ya fito mishi a Mutum ya ce masa ’’Ya’isha bata da kunya, kullum rashin kunyarta k’aruwa take yi’’
dukda ya san tsiwa nature d’inta ne dama amma sai da ya ɗin ji zafin Najeeb ɗin!
Yau kam tabbas ya tabbatar, dan gashi shi a karon kanshi Kansa ya kasa ɗaukar yadda take magana da kuma attitude d’inta, sam babu shayi ko alamun girmamawa a tare da ita.

Muryar Ummi ce ta katse mishi tunani jin cikin kwantar da murya tana cewa “Ya’isha wa ya ce miki ta san maganar kafin ki sani?
Ai cewa ya yi ita yakeso ta had’a kawai, bai riga ya ce ya bata ba, bayaga hakan ma ko ta sani ɗin
ai itace Babba kuma naga kamar ya fi shak’uwa da ita’’.

Cikin katseta Ya’ishan ta d’aga mata Hannu ta ce “Ummi Plss’’
Sannan ta juya ta kalli Yashjub ta ce ’’Allah ya sanya alkhairi
Allah ya baku zaman lafiya
Allah ya baka lafiya’’
Daga haka ta juya ta fita fuuu
kamar zata tashi sama.

Tsayawa kawai Yashjub ya yi yana kallon inda ta bi ta fita a ransa ya raya’wato dai yanzu ita bata tsoro ko shakkar kowa’

Yassir dama neman hanyar fecewa yake yi, dan haka da sauri ya samu ya juya shima ya fice hankalinsa a mugun tashe.

Ajiyar zuciya Yasmeen ta sauk’e kafin itama ta mik’e ta ce ’’nima bara in bi bayan Ya’isha mu tafi tare.’’

Har ta yi gaba sai kuma ta juyo ta ce “Ummi dan Allah nan gaba kar ki sake cewa wani wai Yash ya fi shak’uwa da Yahanasu ko kuma wani abun makamancin hakan! Saboda
ba haka family d’in nan yake ba…babu banbanci a tsakanin sibling d’in gidan Daddy, duk ɗinmu ɗaya ne kuma iri ɗaya ne, duk kanmu munnshaƙu da juna equally…..

Iyakar faɗin hakan ma da kikayi ya soosa min rai’’
A hankali ta kalli Yashjub sannan ta ce ’’ina fatan za ki yi hasashen kalar zafin da zan ji idan aka yi treating d’ina hakan sannan aka nuna bani da wani muhimmanci.”
Daga haka ta ce masa
“Allah ya ƙara sauƙi
Allah ya baka lafiya”
Tana gama fad’in haka ta juya ta fita.

Dafe Kai Ummi ta yi tana dana sanin kula su Yasmeen da ta yi a yau ɗin bayan ta yi wa kanta alk’awarin fita a harkar su har abada,
Wataƙilan kawai dan tana cikin farin ciki ne shiyasa ta manta ta biye su..dan har ga Allah ta ji dad’in maganar auren Yashjub, ta san ko wacece Yarinyar to tabbbas tana da hankali da tarbiyya dan a yadda Yashjub yake tana sa yaƙinin ba zai d’auko musu ballagaza ba da izinin Allah, tun a bakin Daddy take jin labarin Yashjub lokacin shi yana uku,
da kuma ya dawo ya fara aiki da su nan ta tabbatar tabbas Yash Mutum ne asalin jajirtacce me hankali wayo nutsuwa neman na kanshi me mutunci kamala da sanin ya kamata………….

…..ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e kafin ya ce ’’Yash! Da gaske su ke Yahanasu ta san maganar auren nan kafin su??’’

Lumshe idanu yayi ya bud’e kafin ya ce ’’Daddy plss mana….’’

Cikin d’an fushi Daddy ya ce ‘’tambayar ka nake yi, ka bani amsata kawai!’’

A hankali Yashjub ya jinjina Kai kafin ya ce ’’eh’’

Shiruuu Daddy yayi kafin chan ya kawar da kanshi gefe kawai.

A hankali Mommy ta matsa inda Yash d’in yake ta dafa kanshi tukunna ta ce ’’Allah ya ci gaba da kare ka a duk inda kake, Allah ya baka sauk’i’’
Tana gama fad’in haka ta juya ta fice…

Hatta Yadira bata ci gaba da zama a d’akin ba dan Mommy tana fita suma duk suka bi bayanta suka fice.
Yassira ce kawai ta tsaya sai Ummi da Munirat da Daddy da Yahanasu.

Cikin sanyin jiki,
Yassira ta matso kusa da su ta ce ’’Ya Yash,aure zaka yi,
new member zaka kawo mana! Shin tayaya kake tunanin za ta yi respecting d’in mu a matsayinmu na ƙannenka idan kai da kanka ka nuna mata akwai banbanci a tsakaninmu?.
Aƙalla idan mu Mata baka gaya mana ba ai ya kamata ka gayawa Yassir tunda shima Namiji ne kamar kai, ya kamata ka fara jan shi a jikinka.
Mata, surukan gida fa…idan aka auro su, su ne suke tarwatsa kan family musamman idan suka ga akwai hanya mafi sauk’i da za su bi su yi hakan…..
Na san za ka ce wannan k’aramin abu ne amma mu a wajen mu da kuma yadda yanayin rayuwa yake sam wannan ba k’aramin abu baneba.
Kamata yayi idan aka fara auratayya to mu had’e kawununamu mu yi sticking together kar mu bawa kowa damar shiga tsakaninmu…..
Amman a yadda ka fara nunawa ɗinnan tun yanzu ta fahimci Yahanasu ce favorite d’inka ita ka fi so kaf cikimu
To fa idan(matar taka) ta zo Yahanasun kad’ai za ta ja a jikinta, mu kuma ba za ta bamu muhimmanci ba
wanda hakan ba k’aramin matsala zai janyo ba.

Dan Allah ka yi la’akari sannan ka duba maganata, idan kuma na b’ata maka rai to ka yi hak’uri amma
dan Allah ko ba komai ka yi k’ok’ari ka gyara tsakaninka da Mommy da kuma Yassir
kafin Matar nan ta zo ta fahimci wani abun.
Ka duba fa ka ga duk kowa ya ji haushi ya fice,
Mommy fa ko Allah ya sanya alkhairi bata ce ba, ka san maanar hakan kuwa?
wallahi duk lalacewa dole sai da albarkar ta.
Dan Allah kar ka bari Matarka ta fahimci kana da issue da su, na ji na yarda mu ci albarkacinta
ka jawo Yassir Jikinka sannan ka dinga nunawa duniya Mommy itace ta haifeka
Plss Ya Yash dan Allah.’’

A hankali ta juya ta kalli Daddy ta ce ’’Daddy ka sa Baki’’.
Daga haka ta juya ta fita itama.
Chapter 2 · 0% Book details