← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 152

Sashe 63

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai kawai Baba yayi daga haka ya mik’e ya ce “Allah ya yi albarka.”
Yana gama fad’in haka ya sa kai ya fice.

Sai chan dare tukunna Baraka ta tafi ta barsu da abubuwan mamaki…ko magana za ta yi da Inna sai ta sunkuyar da kai k’asa,
Hatta Jidda yadda take janta a jiki abun sai da ya basu matuk’ar mamaki…
Gashi tace za su tare ne tare da Muhsin!
Shi dai Muhsin ya bita da to ne amman har ga Allah in ya tuno halayenta sai ya ji baya son bin su, matar da ada kwata kwata ko dariya ba ta yi masa bata jansa a jiki yanzu kuwa tashi d’aya ta dawo kamar za ta goya sa! dukda Yarone amma ya saka a ransa watakil dan ta ga Innaa ne kuma dan taga Gidansu ta zo shiyasa take ta faman lallab’asa, dan haka ya san yana zuwa gidanta zata fara cin k’aniyar sa.
Dukda yadda yanzun yake jinta har cikin ransa amman still yana iya tuno halayen Baraka a gidanta….

Jidda kuwa Allah Allah takeyi Baraka ta tafi ta samu ta kira Manubiya, dan kanta ya rabu biyu, ta inda take tunanin
Ko dai
Fad’a akayi mata a gida da kuma yanayin duniya da ta gani ta gane gaskiya ta yi dana sani ta shiryu da gaske
Ko
kuma dai
Wani abun ne a cikin zuciyarta, dan Barakar da ta sani ba zata nutsu irin haka a lokaci guda ba tare da kwakkwaran dalili ba……

Sai chan dare su Manubiya suka isa Gida, dan sai da suka biya suka ci abinci suka d’an zagaya suka fara rage siyayyar su tukunna suka nufi gida kowa a gajiye.Suna zuwa Yashjub ya cewa Yadira “ta zab’a d’aki”

Na nan saman opposite d’akin Manubiya ta ce tana so, dan haka ya cewa drivern gidan “ya tayasu hawowa da kayayyaki, ya saka mata kayan ta a ciki”.

Wanka kawai ta yi ko sallah ba ta nutsu ta yi ba ta d’auki abunda su Mommy suka bata ta fito.
A zaune ta sami Manubiya tana waya da Jidda tana bata labarin Baraka……
Kamar Manubiya za ta had’iyi zuciya kuwa haka taji..ashe dama shiyasa ta ga yanata tunani a cikin makonnin da suka gabata, d’azu kuma ita a tunaninta ma ko kukan da ta yi ne ya b’ata masa mood d’insa ya saka shi a damuwa ashe shi tunanin shegiya Baraka yakeyi.
Taya Ya Musbah zai so Baraka ta dawo, wanne irin abu ne haka!…a hankali ta lumshe idanuwanta ta bud’e kafin ta d’ago ta kalli Yadira tace “zauna mana”
Sai kuma ta sake sunkuyar da kanta tace “zan yi kiranku Jidda”
daga haka ta katse wayar, tana mai jin kanta yana wani irin juyawa tsabar takaicin Baraka da Ya Musbah.

Tsaki Yadira ta yi kafin tace
“Ai ko ba ki fad’a ba!”
Sai kuma ta zauna tace”duk fushin da Mutum zai yi nan gani nan bari..zama daram babu inda zanje”

Ahankali Manubiya ta d’ago ta kalle ta, har za ta bata amsa sai kuma kawai ta mayar da kanta k’asa.

Ba tare da b’ata lokaci ba
kawai ta ga Yadira ta mik’e tafad’a toilet d’inta wuff!
A shirye da shirin ta na bacci tsaff ta ganta shiyasa abun ya bata mamaki ta shiga tunanin ‘to mai ta shige za ta yi…’
A b’angaren Yadira kuwa, babu kalar barbad’en da batayi ba a banɗakin, gashi ta ji daɗi dama toile babu camera dan haka ta zage ta dinga zubawa… dukda ta ji ba dad’i kuma tana ganin abun wani iri amman hakanan ta rufe ido ta yi ta bankawa tana yi tana jin wani iri, dan kusan kullum a makaranta ita da k’awayenta basu da aiki sai zagin masu asiri da uwar da take koyawa ƴaƴaanta asiri amma sai gata yau tsulum a cikin harkar dumu-dumu…

Tunda ta shige Manubiya ta saki Baki dan Yarinyar ta bata mamaki sosai…
Ita ba ma wai batun zargi ko wani abun ba ƙarfin halin Yarinyar ne ya fi bata concern.
Tashi d’aya kuma sai ta ji gabanta ya yanke ya fad’i! tsigar jikinta tana tashi, dan haka Yadiran tana fitowa ta mik’e tace
‘’Dakata Yadira’’.
Ko kallon ta Yadira bata yi ba haka ta juya ta kama hanyar fita…tsabar takaici Manubiya bata san lokacin da ta matsa da sauri ta ruk’ota ba, dan a ganinta wannan k’arshen rainin wayo ma kenan!!
Ta shigo ta gaya mata magana, ta mik’e ta shige mata toilet, kuma ta fito ko sallama ba ta yi mata ba zata fice…
Shiyasa ta na ruk’ota ta juyo da ita cikin fushi tace
‘’akwai band’aki a k’asa na bak’i, akwai a dakinki akwai a corridor d’in saman nan sannan akwai a d’akin bak’in dake a k’asa, duk wani uzurin ki ki je ki yi a chan ko da wasa kar in sake ganin kin shige mini band’aki, bamuyi wannan sabon ni da ku ba dan a iyaka sani na da kuma yadda kuke nunawa ‘kun tsaneni!’.’’

Cikin fushi Yadira ta fincike hannunta sannan tace
‘’Eh lalle Manubiya kin auri mai kud’i, Allah sarki d’an Adam mai manta gobe, yanzu ke har kin manta yadda ke da uwarki da ubanki kuke sharing band’aki shine yanzu har ke kike da Bakin ce mini wannan personal toilet d’inki ne…..”

Mahaukacin marin da Manubiya ta d’auke ta da shi ne yasa ta gagara ci gaba da magana, dai-dai nan ne kuma
Yashjub ya shigo cikin d’akin.

Da sauri ya k’arasa inda suke a tsaye yana cewa “lafiya??!Baby mai ya faru har kika mareta haka?..”
Ihun kukan da Yadira ta fasa ne yasa ya kasa cigaba da magana, da sauri ya juya ya kalleta ya shiga duddubata yana kallon yadda shatin y’an yatsun Manubiya suka fito rad’au a fuskarta..cikin kid’ima da tashin hankalin ya shiga addu’a a cikin ransa’Allah ya sa kar Yadira ta gayawa su Mommy an daketa’, dan idan akwai abunda Daddy ya tsana to shine ka tab’a masa Yaro”

Cikin d’an fushi ya juya ga Manubiya yace “nan gaba idan ta yi miki laifi, u report to me! (Ki kawo min ƙararta), kar ki sake marin ta.”
Daga haka ya ja Hannun Yadira suka fice tanata uban kuka tana kiran sunan Mommy.

Suna fita Manubiya ta share zafafan hawayen da suka zubo mata, ta durk’ushe a wajen….anya auren Yashjub ba mistake bane ba kuwa!
anya zata tab’a samu farin ciki a cikin gidan nan kuwa!
Gashi tun ba a je ko ina ba ta fahimci kamar so yake ya hanata karatu!… dan da farko yace mata ‘ba ya son chud’anyar ta da maza’, yanzu kuma ya zo yace ‘ya riga ya yi wa Najeeb magana shi kuma Najeeb ɗin zai sanar da ex colleagues d’insa su yi mata chuku-chukun deferring zuwa nan da har zuwa lokacin da za su dawo.
Shi kuma Zai yi tunani kafin nan…’

Ta jima a tsugunne a wajen, kafin ta mik’e ta fad’a toilet domin ta wanke fuskarta…

Tana shiga cikin band’akin lokaci guda ta ji duk duniya babu wanda ta tsana sannan ba ta son kallon ko da fuskarsa ne kamar Yashjub!
Ita tunani ma ta fara yi wanne dalilin ne ya sa ta aure shi in the first place, dan ta nemi soyayyar da take yi masa tashi d’aya ta rasata….
…
Suna shiga d’aki Yadira ta juyo tana kuka tace
“Wallahi Ya Yash ban yi mata komai ba!”
Cikin katseta Yashjub yace”ban tambayeki ba!.
Yadira kin bani mamaki…ashe haka kika zama, haka kika koyi k’arya?Manubiya mahaukaciya ce da za ta dake ki ba tare da kin yi mata komai ba?
Dama zuwa kika yi ki kashe mini aure? Ashe bakya sona a matsayina na d’an uwanki ni ban sani ba..”

Tashi d’aya ya fahimci yadda jikinta yayi sanyi k’alau, dan haka ya sake tabbatarwa tabbas akwai abunda ta yi wa Manubiya….a tunaninsa su Mommy sun turota cid ne, amman yanzu ya fahimci an turota ne ta kashe masa aure!
mai ya yi wa su Mommy ne da har suke son rabasa da Manubiya su had’a sa da Kausar, dan ko shi Yarone tou ya kamata ace zuwa yanzu ya fahimci manufarsu kenan!!
Mai yayi musu da zafi har haka, mai yasa duk yadda yake k’ok’ari wajen ganin ya shafe laifukan Mommy dole ita kuma sai ta san yadda ta yi ta nuna masa bafa ta son shi…..
Kasa ci gaba da tsayuwa a d’akin ya yi, dan haka kawai ya juya ya fita zuciyarsa tanata faman tafarfasa….

Kitchen ya fara zuwa ya zauna a kan dining table d’in ya yi shiruu, kafin chan ya nufi fridge
ya d’auki ruwan sanyi ya b’alle murfin ya kafa a Baki ya hau shaa..
sai da ya shanye tukunna ya ajjiye robar yana mayar da numfashi….ya jima kafin ya fito, ya nufi sama d’akin Manubiya.

Yana shiga dai-dai ita kuma tana fitowa daga band’aki…d’auke Kai ta yi ta turo Baki gaba ta yi kamar bata gan sa ba.

Murmushi yayi ya k’arasa inda take anan gaban madubin ya rungomata ta baya.
Yadda Manubiya ta ji ita kanta saida abun ya bata mamaki dan ji ta yi kamar wani k’aton arne ne ya rungumeta..
saida ta yi da gaske tukunna ta rarrashi zuciyarta da take azalzalarta akan ta hankad’e sa.
Ahankali ya d’an sunkuyar da kansa ya yi kissing wuyanta kafin yace “ki yi hak’uri, Yadira Yarinya ce,um…”
ya fad’i hakan ya na sake rungumarta sosai izuwa jikinsa .
…Inaa!! Ba za ta iya jurar hakan daga garesa ba!!!
dan haka ta juya da sauri ta hankad’esa!
Kalar hankaɗewar da
ba dan Yashjub yana da k’arfinsa ba to da sai ya zube a wajen.
Chapter 63 · 0% Book details