← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 152

Sashe 87

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Jidda ta yi cikin jin tsananin tausayin kansu tace”Adda Manu kin manta su waye dangin mijin naki ne?ai kema kin san zaman mu a cikin gidanki ba abu mai yiwuwa bane ba….”

Shiruu duk suka yi kafin Jidda ta sake cewa”Ya Yusuf dai tunda ya zo ya ke ta bada hak’uri, kuma ya kawo takardu wai ya siye mana gaba d’aya filin daga wajensu har ya kira an fara gyarawa…..
To dai wannan karon gaskiya Baba ya zuciya dan tunda Ya Yusuf ya zo bai sake da shi ba, daga amsa gaisuwa ya ja bakinsa ya yi gum!Inna ce ma ta d’an saurare sa kad’an,har da cewa wai ya sayi sabon fili zai yi maaana gini waye waye Baba ya yi hak’uri kar ya damu dan ya Musbah ya daina kula mu, inshaaAllah indai yana raye da shi da Inna ba za su yi kukan rashin d’a ba.”

“Wai shi Yusuf yana nufin aikin bankin ne duk ya azurtashi haka??”
Cewar Manubiya..

“Hmm”Jidda tace kafin ta d’aura da cewa”Siyama ta ce mini idan fa kika shiga side d’in Baba Habu za ki d’auka a hotel kike tsabar yadda ya gyara sa,ya yi interlock a gaba d’aya compound d’in gidan ya sakawa iyayensa solar shi kuwa gidan da ya gama ya koma akace har abun tsoro hawa biyu fa,motocin sa fa uku,wayarsa wadda ta fito last month ita yake rik’ewa…y’an unguwa sai magana ake yi amma iyayensa da kaka mallan sunce hassada ce! ya ci gaba da business d’insa kawai ya dage da addu’a! ya yi harkar gabansa, kar ya kula kowa….”

“Ha’a Manu yaushe kika zo??”
cewar Inna wadda ta fito da niyyar bin bayan Jidda, dan ta ji shirun ya yi yawa…a hankali Manu ta tafi jikinta ta rungumeta…cikin rashin jin dad’i inna tace “yanzu Yarinyar nan sai da kika fito?duba fa hannunki har da cannula!to Allah ya kyauta..””Bismillah”daga haka ta juya ta nufi ciki suka mara mata baya.

A zaune suka tadda Muhsin yana assignment, Baba kuma yana zaune a kan gadon jinyarsa yana kallon k’ofar da alamun shigowar tasu yake jira dan ya ji Inna ta ambaci sunan ‘Manu!’.

A hankali ta k’arasa ta d’an durk’usa ta gaida shi tukunna ta zauna a kujerar mai jinya, ta shiga tambayarsa ya jikinsa..
Murmushi ya yi duk da bai so ta fito ba duba da yanayin jikinta amma kuma ya yi matuk’ar jin dad’in yadda ta damu ta taho dukda itanma a kwance take…
Cikin fesar da numfashi ya yi ta’auzi ya kawar da shed’an d’in da ya fara comparing masa himmar Manubiya da Ya musbah a kansa,tukunna yace”ya jiikin naki?”
A hankali tace”Alhamdulillah”
“MashaaAllah Allah ya inganta”ya ce, kafin ya d’aura da cewa”ki kira mijinki ku koma Manu, dare fa ya yi,ai na warke ma Alhamdulillah”
Murmushi ta yi tace”ya tafi siyo abu, sai ya dawo za mu tafi..”
Jinjina kai kawai Baba ya yi, daga haka suka d’an tattauna Akan batun su Uncle,Manubiya ba ta so ace Yashjub ne ya bawa iyayenta gidan da za su zauna a ciki ba,amma ba ta da wani zaɓi, tashinsu a kusa da su Uncle shine mafita dan abun nasu ya yi yawa..shiyasa har wani sanyi ta ji da ta ji Baba yana gaya mata “ai Ya Nafi’u ya yi masa batun maganar da suka yi shi da Yashjub shi kuma
ya amince,inshaaAllah yana fita daga asibiti za su tare,dan d’azu ma Yash d’in ya zo ya d’auki ya Nafi’u suka je ya basa gidan tare da makullai da takardun.Da Nafi’un ma har yana cewa zai zo ya kawo yanzu to sai yace ya barshi kawai dare ya yi..sa had’u gobe.A gidan ma har da b’angaren Musbahu Allah ya sa dai Baraka ta yarda ya dawo gidan su zauna….”

Ahankali Manubiya ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “zai dawo inshaaAllah Baba, ku dinga yi masa addu’a, kar ku bar b’acin ransa a cikin zuciyoyinku, fushinku a garesa masifa ne.”

Jinjina kai Baba ya yi kafin yace”ki na da gaskiya kam,Allah ya sa mu dace.”

Knocking suka ji dan haka Muhsin ya mik’e ya je ya bud’e k’ofar….cikin girmamawa ya gaida Yash shi
Kuma ya amsa masa da kulawa, tukunna suka k’araso cikin d’akin a tare bayan Muhsin ya maida k’ofar ya rufe.

Sai da Yashjub ya d’an russuna tukunna ya gaida Inna da Baba suka amsa ya tambaya ya k’arfin jikin yace”Alhamdulillah”

Wallahi dama shiyasa d’azu bai shigo ba yanzu ma kawai ya ga dare sosai ne shiyasa ya shigo tafiya da Manubiya kar ya barta tana yawo ita d’aya da dare…Sam ba ya so su Baba su yi masa godiya amma suna gama gaisawa suka hau yi masa godiya har da su Jidda wadda itama sai yanzun ne ta ji batun daga bakin Baba.

Kamar zai nutse k’asa haka ya ji,hakanan ya sunnar da kai yana ta faman cewa”Ameen Ameen.”

Ba su wane dad’e ba,suka yi azamar tafiya,Saida duk ta yi musu sallama tukunna ta yi hugging Jidda ta ba ta atm card d’inta da ta d’auko
daga jaka tace “gashi”
karb’a Jidda ta yi tukunna ta fara shirin rakasu,murmushi Yashjub ya yi ya ce “ta barshi ai su biyu ne.”
Daga haka suka tafi Yashjub yana tunanin
“Ba dan suma a asibiti suke ba da sun tafi da su Jidda”.

A mota Manubiya ma ta so yi masa tata godiyar amma ya yi kicin kicin”wai idan ta yi sai sun yi fad’a”
Har da wani turo baki wanda hakan ya sa ta fara dariya….

“Shine amma baka gaya mini ba?”

“Na san zugawa za ki yi ai ki hana,shiyasa na zagaye ki!”
Ya bata amsar yana mai d’an juyowa ya kalleta.

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace”da Ya Nafi’u kuka yi magana kenan?”

Sai da ya d’an yi shiru tukunna yace”ni ne na tambayesa na nace shi ne ya gaya mini komai”

Cikin mutuwar jiki tace”ba lalle ai ya Musbahn ya yarda ya tashi daga gidan da yake d’in ba.”

Kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace”na sa a nemo mini number landlord d’in nasu,kar ki damu zai tashi.”

Shiruuu ta yi haka shima Yash d’in daga nan har suka k’arasa asibiti.Kowa da tunanin da ya ke yi,Yashjub gaba d’aya hankalinsa yana a kan wayar Manubiya ne! ya lura wayar a silent take kuma sai faman kiranta ake yi tana rejecting shiyasa ya tafi tunanin ko dai wannan wanda ya kira ta ta k’i cewa komai jiya ne?
To kenan ta san waye tunda har take k’in d’auka…bai yi tsammanin za ta b’oye masa wani abun ba shiyasa shima ya yanke a kan ba zai tambayeta ba,zai danne kansa ya ga iyakar gudun ruwanta.Amma fa yadda zuciyarsa take yi sakamokon kishin da ya ke tunzurosa hatta jijiyoyin gaban goshinsa sai da suka fito rad’au!.

A b’angaren Manubiya kuwa Abbakar ne yake ta nacin kiranta da messages na ban hak’uri wai yana son magana da ita, yana neman taimakon ta,ta ji zafin yadda ya banzatar da ita amma kuma babban dalilin ta na ƙin kulasa Yashjub ne! Ba ta so su samu matsala ita da shi saboda wani Abbakar kuma Yash ɗin ya fito mata a mutum ya tabbatar mata cewa ba ya son alaƙarta da Abbakar d’in kwata kwata ko gaisawa ba ya so su yi!…ta san ba ya son shi saboda yana tunanin kamar son ta yake yi kuma ta tuna b’acin ran da ta ji a muryarsa ta kuma gani a fuskarsa duk a ta dalilin Abbakar d’in,shiyasa yanzun ta ke jin tsoron gaya masa ‘Abbakar d’in ya na ta kiranta, ya turo mata message yana buk’atar taimakonta.’
Ta zab’i kawai ta rabu da shi, da zarar ta nutsu za ta nemo yadda ake block ta yi blocking d’insa gaba d’aya, ta san Abbakar ya taimaka mata, in ta yi masa hakan ba adadi dan ya kamata ace ta taimakesa yanzun itama, amma Yashjub comes first(Yashjub ne farko) a komai na rayuwarta, kuma tunda ya nuna ba ya son ko gaisawa ne su yi da shi inashaAllah za ta yi masa biyayya…..

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 31*

Sai dare tukunna Baba larai ta tambayi Mommy ‘ya suka yi da Daddy?’…
Duk yadda suka yi ta zaiyyane mata,tashi d’aya Baba larai tace mata
‘bugar cikinta ya yi, amma tunda ta ga bai yi mata komai ba to yana so ya tabbatar ne, dan haka ta nutsu!! ta sa ido sosai sannan ta yi taka tsantsan.’

Tashin hankalin da Mommy ta shiga ba zai misaltu ba, dan sai da Baba larai ta yi mata bayani dalla dalla tukunna itama ta fahimci tabbas bugar cikin nata yayi..yo Ina zata fahimta? gaba d’aya d’azun duk a rud’e take hankalinta a tashe.

Sai wajajen k’arfe sha biyu na dare tukunna Yassir ya yi sneaking daga d’akin Kausar ya tafi ɓangarensa, a lokacin ya san kowa ya yi bacci babu mai ganinsa….
Ba k’aramin mamakin ganin Munirat a zaune a cikin d’akinsa ya yi ba…shaf ya manta da lokacin da ya bata makullan ɓangaren nasa shiyasa kai tsaye ya ce mata ”ta ya kika shigo?”
Murmushi ta yi ta mik’e tace”har ka manta lokacin da ka mallakamin makullan d’akinka har ma da na zuciyarka kenan??”
Sai kuma ta girgiza kai tace
“hmm..of course you do,
(Tabbas ka manta)”

Numfashi ya fesar a ransa ya aiyyana”lokaci ya yi da zan daina hulɗa da Yarinyar nan fa”
Tunda ya riga ya samu abunda yake so, kuma Ummin bata tafi ba dan munirat ɗin bata bada ƙofar da aka gane suna tare ba, amma dukda hakan dai ya yi nasara dan ko a haka ya barta ya cuceta kuma ya cuci Ummin sannann in wani case ɗin ya taso wanda ya dangancesu ya san Ummin za ta iya tafiya.
Chapter 87 · 0% Book details