Sashe 39
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A gaggauce tace mata ”Ammi ce ta kirani, wai in zo mu kai Al’ameen asibiti, yanzunna haka kurum yana shiga gida ya yanke jiki ya fad’i…
Dama fa ni tunda ya dawo wallahi na lura kamar ba shi da lafiya kullum wani iri nake ganin sa.”
Cikin rashin jin dad’i ta k’arasa ta rike Hannun Inna kafin ta ce ”ki yi hak’uri inna, na so in zauna na raka Manubiya d’akinta, amman Alhaji baya nan, dole suna buk’atata!”
Da sauri Inna ta ce ”kar ki damu, ki je ba komai, hakan ma wallahi na gode kwarai Mama, Allah ya basa lafiya”
A hankali ta jinjina Kai tukunnan ta yi musu sallama ta wuce…..
sai da ta fita tukunna Inna ta lura da yadda Jidda ta cusa kanta a tsakankanin cinyoyinta jikinta har wani irin vibration yake yi tana wani irin silent kuka kamar ranta zai fita, ajiyar zuciya ta sauk’e saboda dama sai da ta saka hakan a ranta daga jin bayanin Mama….a hankali ta k’arasa kusa da ita ta zauna tukunna ta sa Hannu ta d’ago fuskarta wadda ta yi dagaje-dagaje da hawaye da gumi har ma da majina, sai da ta share mata fuskartata tukunna ahankali sosai ta ce ”kin had’u da shi ne yanzu?”
Cikin kuka Jidda take kallonta tana so ta yi magana amman sam sai ta gagara, shiyasa kawai sai ta afka jikin Inna ta sake fashewa da wani Irin kuka abun tausayi.
Ajiyar zuciya wannan tsohuwar ta sauk’e kafin ta k’araso kusa da su ta ci gaba da rarrashinsu dan ita ba ta ji abunda innar ta ce da Jiddan yanzu ba……Sun jima sosai matar tana rarrashinsu kafin da kyar aka samu Jidda yi shiru ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a jere a jere.
A haka Siyama ta shigo ta same su itama idanunta sun yi jaa alamun ta taya Manubiya kuka, sai da ta k’arasa kusa da su ta zauna jikinta duk a sanyaye tukunna ta ce ”Ummaa tace wai ace miki iyayen ango sun zo, a je a ce musu su shigo ne?
Dum!!
Haka duk su biyun suka ji k’irjinsu ya buga.
A hankali Inna ta kalli Jidda tace mata
“su je ita da Siyama su shiga da su parlourn su Siyaman. “
Ba su dad’e da fita ba itama suka fita ita da wannan Iya ramma wadda ta tilasta mata dole suka wuce parlourn su Siyaman tare…..
Su Jidda suna fita da Baaba Larai suka fara cin karo tsaye
a bakin motar Yassira tana zazzare ido tana k’arewa gidan kallo fuskar nan a yatsine.
“Ya salam”
Jidda ta ambata a cikin zuciyarta, kafin ta d’auke Kai
ta k’arasa wajen Yahanasu
wadda ta gani suna fitowa daga mota itada wata, kusa da
motar Yahanasu motar Ummi ce itama su biyu dan haka Jidda ta d’an saki fuskarta….Su Ummi dama tun ranar farko ba su raina gidansu Manubiya ba, to haka yau suma k’awayensu da suka zo tare da su haka….. talaka da mai kud’i duk Allah ne yake yinsu,kuma Ubangiji yana iya maida talaka mai kud’i cikin dare d’aya vice versa(haka ma ɗaya ɓangaren),
sannan
kowa da kalar tasa baiwar, kuma babu wanda ya fi wani a wajen ubangiji sai wanda ya fi bauta masa ya fi tsoronsa, shiyasa su kam basuga kuma basuji komai ba, iyakar abunda ya ke da mahimmanci shine Yash yana son Matarshi kuma tana da tarbiyya, hankali da nutsuwa.
Sab’anin su Yassira waenda hankalinsu ya sake tashi,
ransu ya sake b’aci….”tabbas
dama a yadda Yash yake nuna halin ko in kula a garesu da Mommy kanta! Ta san cewa yanada matsala kuma bai san ciwon kansa ba amman bata tab’a sanin cewa shi mahaukaci har haka bane ba sai yau.
Yanzu nan ya zo? Ashe dama
akan wadda ta fito a wannan gidan Ya Yash ya ke abubuwan da yake yi da uban rawar k’afar da yake ta faman yi kamar wanda zai auro y’ar gwal!?.
Sannan su kansu k’annenta ashe daga nan suka fito amman har suke da ƙarfin hali da kwarin guiwar wani ciccin magani a gabansu?
Ba laifin kowa bane laifin Yash ne da ya had’asu da su..tabbas Yash ya janyo musu babban insult da abun kunya a rayuwa….wallahi ko gidan su gwaggwo mai aikin su ya fi wannan kyan gani…….”
Yasira ta zaiyyane hakan a cikin ranta. Iri ɗaya da su Ya’isha suma, dan duk lissafin da suke yi kenan.
Yasmeen kam ji takeyi kamar ta fashe da kuka, dan ba kad’an ba a ganinta wannan abun insult ne, ta ya Yash zai had’asu family da Irin waennan mutanen, “mai ya shiga kansa har hakan?” ta yi kanta da kanta tambayar sannan cikin bawa kanta amsa tace “tabbas wannan aikin asiri ne, babu tantama, amman za ta gane inda ta zo ne!……dan ba ta jin za su iya jurar Yarinyar nan na wata ɗaya ma wallahi.
Gara da Allah yasa ba su yi gaiyyata ba, yau da sun kwashi abun kunya!…..
Yassira bata iya fitowa a mota ba sai da ta kira Mommy a video call ta shiga nuna mata gidan.
Mommy ta san Yash ya wulak’antasu, kuma ya k’ask’antar da su da shi kansa, amman kuma ta d’an ji dad’i, dan a yadda Manubiya take bata da gatan nan tabbas ta tabbata k’aramin alhaki a hannunta…..
shiyasa har Kausar wadda take ta faman rarrashi tun d’azu ta nunawa video call d’in da Yassira takeyi sannan
ta sake tabbatar mata da cewa
‘Ba su da wata matsala, dan Yarinyar da ta fito daga wannan gidan ba za ta zame
musu jidali ba InshaaAllah’.
Har waje Yassira ta fito, tana video call d’in tana nunawa Mommy gidan da layin ba tare da damuwa ba, wanda hakan ba k’aramin d’aurewa Mutanen da suke kai kawo Kai ya yi ba, saboda a ganinsu saboda me ya sa za ta yi hakan!? Akan wanne dalili za ta fito tana yin video d’in da kowa ya fahimci layin da gidan kawai take d’auka, dan in da ace videos d’in d’aukar Amarya za ta yi ai kowa ya san
sai an shiga ciki tukunna ake farawa
Bayaga hakan ma yanayin yadda take yin video d’in nata kana gani za ka san gidan kawai take d’auka cike da raini ba komai ba. Waenda
suke kusa da ita sosai ne suka fahimci video call ne, ragowar
kuwa sam ba su fahimta ba…..
Girgiza Kai kawai Ummi ta yi ta fito da ga cikin motarta, kafin ta k’arasa inda su Yahanasu suke tsaye ita da su Jidda…
Da farko Siyama da taga abunda Yassira takeyi har za ta kula ta su yi, amman kawai sai ta basar da ita gudun kar su yi abun kallo ta ja wa Manubiya abun fad’e, kuma tana juyawa suka had’a ido da Ya’isha, ta san idan ta biye su to tsaf za a yi ta ba dad’i dan ta lura kamar Yarinyar fad’a take nema da ita dan yanzun ma tana juyawa ta zabga mata harara shiyasa kawai ta rabu da su amman wallahi ba dan
yau ranar Manubiya bace da sai ta koya musu hankali gaba d’ayansu.
Kallon duk su biyun Ummi ta yi kamar ta san me ke a cikin zuciyarsu, ta ce ”ku yi hak’uri, ku yi komai saboda yar uwarku, kar ku bari ayi abun fad’e a ranar aurenta, ku danne
zuciyoyinku kunji y’an albarka”
Murmushin k’arfin hali Jidda ta yi, dan ba k’adan ba itama zuwa yanzu ta hau saboda har wata dariya take jiyo su Yusran sunayi
Irin dariyar rainin hankali da k’ask’anci d’innan, a hankali tace”inshaaAllah Ummi”
Daga haka suka sake gaisawa suka gaida k’awayensu kafin su ce musu “bismillah”
Su Jidda a gaba su Ummin kuma a baya, haka suka nufi gidan.
Dai-dai su Siyama sun zo wucewa kenan Yusra ta ce ”Am Yasmeen ni kam anya ba kejin kaji da tumaki aka mana kwatance ba kuwa?inaga
gara fa mu kira mu sake tabbatarwa….”
Wani irin tafarfasa zuciyar Siyama ta shiga yi, inda ace iyakar i su iskancin nasu ya tsaya to da da sauk’i amman kejin kaji da tumaki da Yusra ta ambata it means tana nufin har da iyayen su kennan, shiyasa duk yadda Siyama ta yi alk’awari ta kuma so ta kyale su sam sai ta kasa, ta san tana juyawa za ta iya kifawa Yusra mari shiyasa still sai da ta kuma tausar zuciyarta tukunna ta juyo ta ce
“Group leader d’in ‘rashin sanin yakamata‘
kuna iya shigowa kuma idan kun so, ku d’auki Amarya
kamar yadda aka umarceku ku yi daga gida”
Tayi maganar tana kallon Baaba Larai dan Babba bai fi Babba ba.
Tana gama fad’in haka ta wuce ciki.
Shiruu duk suka yi, saboda ba su yi
tunanin za ta kulasu ba!
Dan sun lura kamar Yaran sunada d’an tsoro, amman fa sun ji dad’in kulasun da ta yi hakan ya nuna ta ji zafin maganar tasu kuma wallahi sai sun nuna mata ba su san ya kamatan ba kuwa!.
Yasmeen ce ta ce “mu je ciki mu d’auki Amaryar”
daga haka duk suka yi ciki suma……
Sam Ummi ba ta so Siyama ta tanka musu ba, dan ta san za su yi mata shirme ne a gaban dangi da y’an uwa, kamar
ta san hakan kuwa suka shirya d’in!….
Siyama ta yi zaton za su tanka mata amma sai ta ga ba su ce komai ba, kusan tare ma suka shiga parlourn nasu kafad’a da kafad’a ita da su Ya’isha ba wadda ta kalle ta a cikinsu.
Parlourn cike yake taff da Mutane…Dukda k’amshin turraren wutan da yake tashi tundaga k’ofar gidan hakan bai hana su yatsine fuska ba
sannan suna tafiya kamar kar su taka k’asa sai kace masu tsallake kwata….Lace ne a jikin Yassira wanda a k’alla ya kai naira miliyan ɗaya, haka itama Ya’isha dan nata da na Yassira kala ce kawai ta bambanta na Yassira blue na Ya’isha kuma brown, mayafi 3D suka rufa a kansu y’an k’ananu suka zagaye wuyan su da shi,
Yassira bubu ne a jikinta
Ya’isha kuwa fitted gown.
Iyaka zobuna da awarwarayen gold d’in dake a Hannayensu kad’ai sun isa su gigita Mutum.